Showing 249001 words to 252000 words out of 411050 words
Chapter 84 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
wannan gantalalliyar yarinyar ?
Ya tambayi kansa a zuci .
" okay ,
Yace a taƙaice yana mayar da hankalin sa ga fuskar wayar sa ,
"irin karuwan nan ce masu tsayawa a bakin hanya suna ne...
Fitowar Hajja cikin Murna ya katse mata zance da ta ɗauko yi ,
" a a' ah Babban likita kaine tafe iwar haka ? Sannu da zuwa sannu da zuwa ka sha hanya tun daga birnin tarayya,
Da 'yar fara'a Doctor Hamza yake amsawa Hajja gaisuwar da take masa ,
Hajja ta ɗora ganin ta kan Sofi wacce ta jirkita sosai kan kafaɗun Doctor Hamza kirjin ta daf da fuskar sa , fiye da rabin cinyar ta na kan jikinsa , kan ta a ɗage sai shan ƙamshi take , ko ƙala bata cewa Hajja ba , "ah to wacece ita 'yar aikin zata gaisar ?
Ƙanƙan da ido Hajja tayi ,
" Yau ina ganin taɓara maigida da kukan tsarki , mene haka wata shaɓatartar da ke kin wani ɗaɗɗane ɗan mutane ƙin kalmashe shi ? O ni hauwa'u inda ranka ka sha kallo , ikon Allah 'ya'yan zamani , mu lokacin mu ina muke iya ɗaga ido mu dubi miji a gaban mutane ?
Cike da 'yar kunya doctor Hamza ya miƙe bayan ya ture Sofi daga jikin sa , yace ,
" Rahima bata nan ko Hajja ? A ɗan sama mana abinda zamu ci please ina tare da yunwa ,
" Rahima bata nan likita , bata ƙaraso ba daga Makaranta , to babu laifi yanzu kuwa za'a samar da abinci ,sannun ku da hanya ,
Wani banzan Kallo Sofi ta jefawa Hajja tana bin bayan mijinta , cikin ranta cike da haushin kalaman Hajja , cikin ran ta tana cewa ,
"ji min tsohuwar nan da kinibibi ? Ko ina ruwanta da ni ," ? Idan har ta ce zata shiga harka ta kafin na bar gidan nan sai na ratsa mata tarbiyya ,'
" Mts
Hajja ta saki tsaki bayan barin su falon
, "abun haushi Nama na jan kare , me ake da mace marar kunya da kamun kai ? Kunya ai ado ce .
Murnar labarin da Falmata ta bata na samun warakar ta ya taso yayi awon gaba da takaicin da sofi ta bata ,
*****
Washegari bayan Doctor Hamza ya shirya kai tsaye ya nufi yin abunda ya kawo shi garin .
Bayan ya je sun gaisa da Prof shi da Sofi , daga bakin mashigar sashin Prof ya dakatar da ita daga binsa ,
" Sofi ki koma ciki , ni fita zan yi sai na dawo ,
Zunɓur-ɓur ta turo baki ,
Cikin salon da koyaushe take amfani dashi idan tana gaban shi na ƙoƙarin ta nuna masa ƙuruciyar ta da a zahiri ta riga ta yi mata adabo ,
A shagwaɓe tace
"Haba mana Doctor please zan bika mu tafi tare naga gari , ka ga fa irin yanayin gidan shiru ba...
"please Sofi kar ki ɓata min lokaci a banza ai kin san yanayin gidan babu abokin hira kika dage sai kin biyo ni , kuma ni wajen aiki zan tafi ba yawo a gari ba ,
Juyawa yayi ya ƙarasa ga motar sa ya shige ciki bai ko sake waigowa ta kan ta ba ya tada motar yayi tafiyar sa ,
" jagale ! Tayi a tsaye ranta cike da ƙuna ,
"so take ta san meye Doctor yake ƙullawa a garin da yake ta zirga-zirga a tsakanin Maiduguri da Abuja ,
Cikin wata guda wannan ne zuwan sa na uku , ita fa duk wani abu da zai sha gaban ta , ya mata katanga kome ƙanƙantar sa da Doctor Hamza yaƙi take yi da koma menene ,
Ko aikin sa dan bata da ikon hana shi ne amma da tuni ta shata layi tsakanin su , so take koyaushe ya zama bashi da uzuri sai nata ,
A fusace ta juya ciki ,
****
Kai tsaye gidan Amne ya nufa , ya taddata tana karin kumallo da Fankaso da miyar gandar ƙafar sa ,
Ya gaishe ta cike da ladabi , ta amsa tana mai farin-cikin ganin sa ,
Tambayar sa tayi ya safiyya ?
Ya shaida mata ai tare suka zo garin .
"Shine kuma baka kawo min ita mun gaisa ba ?
Ta furta haka lokacin da take zuba masa miya akan fankason da ta zuba masa ,
"Amnee fita zamu yi tare zuwa wani waje ,
Ya furta haka lokacin da yake kai lomar farko bakin sa.
" ina kuma zamu ? Allah yasa dai Lafiya .
"lafiya lau Amne sai Alheri ,
cikin nutsuwa ya gama cin abincin sa ,
Bayan ya wanke hannu , yace
"Amne zamu iya tafiya yanzu ko kina da wani uzurin da zaki yi ?
"ba abunda zan yi , amma tukun wai ina zaka kai ni ? Kaƙi sanar da ni .
"kiyi haƙuri Amnee mu je ki gani ,
"to bari na yafa mayafi na ,
Tare suka fito shi da ita ya buɗe mata gidan baya na mota ta shiga ya rufe , gami da zagayawa ya shiga ya tada motar yana barin unguwar ,
Ya riga ya gama tsara hanyoyin da zai bi domin ganin ya dai-daita lamarin iyayensa , wanda daman burin sa ne tun ma kafin bayyanuwar Khaalty Rahima a gare shi ,
Bayyanar ta ya sauƙaƙa masa lamarin , ya kuma ji daɗi domin yasan dawowar ta a dai-dai lokacin matakin nasarar gyaruwar kome ne wanda hargitsewar kome yake da nasaba da ita ,
Bayan duk lallamin da yayi mata akan ya mayar da ita gida , amma taƙi amincewa ,
Cikin dogon nazarin da yayi ya yanke shawarar haɗa su kitsumun , ba tare da sanin kowaccen su ba .
Dan haka a yanzu da ya ɗau Amnee kai tsaye ya nufi gidan da Khalty Rahima take ba tare da ya sanar da kowaccen su game da 'yar uwarta ba .
Suna 'yar hira shi da Amnee har suka iso ƙofar gidan , ya fita a motar ya nemi iznin shiga gidan daga maigadi inda ya amince nan take har ma yake sake jaddada masa , ai kuwa Mamar Bulama tana ,
Tare da Amnee suka shiga wacce take cike da mamakin ina Hamza ya kawo ta ? Gurin wa suka zo ? Allah dai ya sa lafiya ,
Shi ya fara shiga sashin da Khaalty Rahima take , daga bakin ƙofa ya dogare , yana fuskantar Cikin gidan
daga inda yake yana hango Khaalty Rahima wacce ta duƙufa yin wanki daga gefe ,
Babu Alamun ta san da tsayuwar sa a wajen ,
"Bissmillah Amnee shigo ,
" Assalamu Alaikum ,
Amne ta ce lokacin da ta shigo filin gidan ,
Dai-dai da ɗagowar Khaalty Rahima wacce sautin Hamza ya ankarar da ita tsayuwar shi a wajen ,
Zuciyoyin su suka buga da wani irin yanayi mai girma , daga ƙasa har sama Amnee take kallon ta ,
Kowanne irin jirkituwar halitta ce ta samu Rahima ƙanwar ta , ba zai sa ta gaza gane ta ba ,
"Rahma, Rahmatullah ,
Ta ƙira ta da wani ɗan guntun sauti ,
"Rahmatullah hal hdha haqiqiun lak 'Yaa ukhtee ? ( shin dagaske ke ce 'Yar uwata ? )
A hankali ta saki rigar hannun ta da take wankewa ,
Da hannu biyu Amnee ta rufe fuskar ta lokacin da hawayen farin-ciki ya fara zarya akan fuskar ta ,
Bata jira ƙarasowar Rahima ba wacce take tahowa da sassarfa , ta taka da sauri ta tadda ta ,
Rungume juna suka yi hawayen murnar ganin junan su na sauƙa ,
Khaalty Rahima bata san haka take cikin maricin tare da kewar 'yar uwar ta , yayar ta , madadin uwa agare ta ba sai yanzu da ta gan ta tsaye a gaban ta bayan tsawon shekaru fiye da ashirin da suka kwashe basa tare .
Hannu biyu Amnee ta sa ta riƙe fuskar Rahima ,
"ke ce wannan Rahimatullah ? Meyasa kika tafi kika barni ? Kina garin nan Rahimatullah duk tsawon shekarun nan bakya nema na ? Meye na miki mai girma haka Rahimatullah ?
"Rahimatullah wacce irin Rayuwa kike yi tunda kika barni ? Nan ne gidan ki ? Kin yi aure ne ? Ina maigidanki ? ki min magana mana ƙanwata
Muryar Doctor Hamza ta ratsa tsakani , shi da kansa ƙwalla ta taru masa a ido , irin ƙaunar da yake hangowa a fuskar kowaccen su ga 'yar uwar ta , ta masa yanayi da na yaran nan biyu 'yan gudun hijira .
"Amnee ki kwantar da hankalin ki , Khaalty Rahima ta gamu da larura tana jin magana amma bata iya mayarwa ,
Sabon Kuka Amnee ta fashe da shi ,
"Rahimatullah ce ta kurunce ? Meye haka ya faru da ke Rahimatullah ?
Cikin ruɗani ta waiga ga Hamza
" mu tafi asibiti a duba min ita yanzu Rahimatullah Amana ce a wajena ,
Da sigar rarrashi khaalty Rahima ta jijjiga hannun Amnee da yake cikin nata ,
Waigowa tayi tana kallon ta ,
Murmushi tayi mata , ta kai hannu ta goge mata hawaye tana girgiza mata kai ,
ƙoƙarin taro ta Amnee take lokacin da ta ga tana ƙoƙarin tsugunnawa ,
tare suka durƙusa ,
Khaalty Rahima ta rubuta mata a ƙasa cikin yaren su ,
"ki daina kuka , murna yakamata muyi da sake ganin junan mu Yaa Amina .
Bayan Awanni biyu
Doctor Hamza , tare da Amnee da Khaalty Rahima da Bulama suka kama hanyar komawa gidan Amnee.
Ga mamakin Hamza Khaalty Rahima bata yiwa 'yar uwarta irin tirjiyar da tayi masa kan komawa gida ba ,
Ko daman dan bata ga 'yar uwar tata bane a gaban ta ?
abunda ya ɗan riƙe su a gidan shine batun tafiya da Rahima da ɗan ta da suka yi wanda da farko matar da khaalty Rahimar take yiwa aiki bata Amince ba .
sai da suka bata gamsassun bayanai tare da ƙwararan hujjoji ta kuma ga shaida tare da Amincewar ita kanta Khaalty Rahimar tukun ta yarda ta sallami Rahima tare da yi mata fatan Alheri .
Da shigar su gida Amnee ta shiga hidimar Khaalty Rahima , kama daga shirya mata wajen zama na musamman har zuwa gyara mata shimfiɗar da zasu kwana ita da ɗan ta.
Abunda ya sake bawa Hamza tausayi shine duk inda Amnee ta gusa , Khaalty Rahima zata matsa kusa da ita tana yunƙurin karɓe aikin da take yi , Amnee taƙi sakar mata ,
banda murmushi mai cike da tarin ƙauna da tausayi babu abunda suke yiwa junan su .
Sai da Amnee ta gama gyara musu waje tsaf sannan ta dawo ta zauna kusa da Rahima , ta riƙo hannun ta tace ,
"Rahimatullah ina son jin labarin yadda kika yi rayuwa bayan barin ki gida , amma babu dama a yanzu , inshaAllah daga gobe zaki fara ganin likita ,
Gyaran murya Doctor Hamza yayi ,
"Amne
Ya ƙira sunan ta , a hankali ta waigo gare shi ,
"Amnee ina son dan Allah yau ki bani labarin abunda ya faru da rayuwar ku ke da Baba da Khaalty Rahima ? Dan Allah kar ki ƙi , ki ban labarin a matsayin tukuicin dawo miki da Khaalty Rahima da nayi .
Shiru tayi na wani ɗan lokaci , kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ,
***
"Labarin ba wani mai daɗi bane da kake naciyar sanin sa ,
"Kamar yadda ka sani ne mu 'Yan asalin ƙasar Chad ne daga Babban birnin N'Djamena , inda aka haife mu , iyaye da dangin mu baki ɗaya.
"Mahaifin mu sajjan ne ( mai gadin gidan yari ) a babban alsijn na ƙasar mu , albashin sa bai cika yawa ba dan haka mai ƙaramin ƙarfi ne sosai , dangin sa duk talakawa ne , haka ma mahaifiyar mu ta fito daga gidan talakawa sosai , sana'ar iyayenta sarrafa gishiri daga bakin teku su kawo cikin gari su sayar ,
ni ce Babbar 'yar su sai ƙanne na maza huɗu "Salihu , Mohammed , Usman da Jamil sai ƙaramar mu Rahimatullah .
"Rahimatullah tana shekaru biyar ni ina da goma sha shida Mahaifiyar mu ta rasu , inda ba'a ɗau lokaci ba bayan mutuwar ta Maifinmu ya sake yin aure , ya auri wata mata mai 'ya'ya huɗu daga ƙabilar N'gambaye mabiyar Adinnin Christian ƴar ainahin ɗarikar Roman Catholic .
"zuwan "Aichawa rayuwar mu shi yayi sanadiyyar faɗawar mu ƙunci domin Aicha irin mugayen matan nan ce marar imani , babu irin aikin wahalarwa da bata sanya mu , Su salihu sun zame mata masu nemo mata kuɗi , inda ni kuma na zama baiwar ta mai yin duk wasu aikin cikin gida,
hatta Rahimtullah da take ƙanƙanuwa bata tsallakewa izaya daga hannun Aicha ba .
"shi da kansa Mahaifin mu bai tsira ba daga bala'in ta dan a wasu lokutan har duka take yi masa , idan ta nemi kuɗi bai bata ba, hakan ya sa yake masifar tsoron ta ba shi da kataɓus , ya auro jaraba .
"mugun neman kuɗi irin na Aicha ya sa nima ta sama min aikin goge-goge a babban ofishin jakadancin ƙasar mu tun a wancen lokacin da ba'a cika barin 'ya'ya mata fita neman kuɗi ba ,
"karatu ma alokacin iyakata primary ban ci gaba ba .
"da murna na fara zuwa aikin saboda ganin zan huta daga masifar Aicha da wahalar aikin gida , sai dai kuma tunanin Rahimatullah da zan dunga bari a gida ya rage min karsashi ,
" ganin cewa aikin nawa shara ne da goge-goge sai na nemi iznin na dunga zuwa da Rahimatullah tana zama a gefe ni nayi aikina , saboda nasan idsn na bar ta a gida azaba za'a dunga gana mata , cikin sa'a aka amince min .
"Tafiya ce miƙaƙƙiya a ƙafa daga unguwar mu zuwa wajen aikina , amma haka nake goyon Rahimatullah daga alfijir ya keto mu ɗau hanya , kafin lokacin da muke isa gari ya waye sosai ,
"Haka zan yi aikina Rahimatullah tana ƙiriniyar ta ,
"Rahimatullah irin yaran nan ce masu son wasa , hakan ya sa sai ina aiki ina kaffa-kaffa da ita kar ta yi musu ɓarna dan wani lokacin ma sai na neme ta na rasa ta shige ƙarƙashin tebura ko tayi wani wajen ,
"Amne ta tsagaita tana duban fuskar Khaalty Rahima wacce take murmushi ,
"Ashe Bulama ba a ƙasa ya tsinta ba gado yayi ,
Doctor Hamza ya kitsima hakan a ransa ,
Amnee ta cigaba da cewa ,
"Na ɗau tsawon watanni shida ina aikin goge-goge a ofisoshin guda biyar kafin a rage min yawan su zuwa kula da ofishi biyu rak , na wata mata Basudaniya ( Sudanese )"Mademe Laura , da kuma na wani jakadan ƙasar Nigeria "Al-Mustafa Dilmari .
"tsakanina da su Gaisuwa msi cike da girmamawa ne idan sun iso ofis sun tarad dani a bakin aikina ,
"wata alaƙa bata taɓa gifta tsakanin mu ba sai Ranar da Rahima tayi wata mummunar ɓarna a ofishin Ambassador Mustapha , inda ta yayyaga wasu takardu masu muhimmanci da ya mance ya tafi ya bar su a ofishin sa ba tare da ya adana su ba ,
"Ranar na shiga tashin hankali domin kuwa faɗa sosai ya dunga yi min , bai tsagaita ba sai da Rahimatulla wacce take goye a bayana , saboda zamu tafi ƙiran sa ya cimmin , ta leƙo da kanta cikin harshen larabci ta ce da shi yayi haƙuri ya daina yi mana faɗa irin yadda Aichatuwa take yi mana kullum ai ita ta yaga takardun tana so ta yiwa ƴar tsanar ta kaya ,
"Ban san dalili ba sai naga ya sassauta fishin sa , a ƙarshe yace mu tafi kawai ,
"tun daga ranar sai naji tsoron sake zuwa da Rahima domin kar tayi wata ɓarna sa zata sa a kore ni daga aikin wanda albashin sa a lokacin da shi nake yi mana hidimar yau da kullum ni da ita duk kuwa da cewa kaso uku Aichatuwa take raba albashin ta ɗau kashi biyu da rabi ta bani guntun ,
"daɓ dole nake barin ta a gida tana kuka , wani lokacin nima har ta saka ni ƙwalla , nake tafiya na bar ta ,
"ba'a yi sati guda ba wata safiya har na kammala aiki zan tafi , Ambassador Al-mustapha ya ƙira ni , zuciyata cike da tsoro na je na ɗauks batun laifin Rahima ne bai wuce ba ko kuma ni ce na sake yin wani laifin .
" ga mamakina sai naji yana tambayata ina ƙanwa ta take meyasa na daina zuwa da ita ?
" na ce masa tana nan , inajin tsoron kar ta sake ɓarna shiyasa na daina zuwa da ita ,
" sai ya umarceni da mu cigaba da zuwa tare amma na dunga lura da ita kar ta dunga yin ɓarna ,
"shikenan Tun daga ranar na cigaba da zuwa da Rahima ,
"a hankali sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin Ambassador Al-mustapha da Rahimatullah saboda 'yan kayan maƙulashe na yara da yake mata hasafin su ,
"kafin wasu watanni shaƙuwar su da Rahima ta shafeni wanda a ƙarshe cikin shekara guda tsakanin mu ya rikiɗe ya zama soyayya ce mai ƙarfi ,
"duk kuwa da tazarar matsayi da yake tsakanin mu hakanan Allah ya kulla auratayya a tsakanin mu , bayan rigin-gimu da suka taso daga dukkan ɓangarorin biyu , daga Aichatuwa , da bangaren iyaye da 'yan uwa Al-mustapha na jini , wanda suks tirje akan ba zai auri 'yar wata ƙasa ba wacce ba ƙabilar su ta kanurai ba , alhalin ga 'yar uwarsu wacce take dakon jiran sa suyi aure ,
"hakanan ɓangaren Aichatuwa wacce ta bi duk wata hanyar da zata iya bi domin ganin auren mu bai yiwu ba da Mahaifin ka , amma dayake shi aure Kaddara ce daga kaddarorin da Allah yake yi ga bayin sa .
"A ƙarshe aka ɗaura Auren mu ni da Mahaifinka tare da Amincewar kakan ku wanda ya taka har ƙasar mu ya nemawa ɗan sa aurena cikin mutuntawa , bai duba ƙasƙancin mu da shi yake babban Attajiri