Showing 207001 words to 210000 words out of 411050 words
Chapter 70 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
mata kuɗi ??
Two Million Naira
Ta furta cikin gatsali
Bani account number da zan zira miki su ,
A ɗan jirkice ta dube shi cikin ran ta tana son ƙure shi , domin kuwa duk da sanin da tayi wa kamal na shahararran ɗan masu hali da iyayen sa suka gama gurɓata tarbiyyar sa , ya zama tamkar ɗan taure wajen bibiyar mata , manya da ƙanana kyakkyawa da mummuna shi baya zaɓe kawai dai idan ran shi ya biya ya samu ya maida mugun yawu shikenan kuma bai ƙara bi ta kan mace , bata zaton wasan sa da kuɗi ya kai ya haka .
A ɗage ta karanto masa account number da suna , cikin abunda bai gaza mintuna biyu ba sai ga wayar ta dake cikin jaka ta ɗau ƙara ,
Jikin ta na mazari ta fiddo wayar ta duba ,
Alert ne na adadin kuɗin da ta buƙata cif .
Ɗan wara ido tayi da sigar mamaki , sai kuma ta kaɗa idon cikin yanayi na shanye mamakin ta irin na gogaggun matan bariki .
Babu shakka ka ɗau haja me girma , kuma na san baza ka yi wadarai da ita ba , yaushe kake buƙatar ta ?
Haɗe fuska yayi kafin ya watsa hannu
Ka duba wannan da wata maganar iska ? Irin waɗannan kuɗaɗen da na cire har sai kin min iyaka da ita ? Ai yadda ta sani haɗiyar mugun yawu dole daren yau na fanshe kuɗi na , daman ga gari ya ɗau sanyi yanayi ne na shiga daga ciki da sauri .
Ta saki Wata dariyar da take bayyana farin cikin ta akan kuɗaɗen da ta samu da dama tana tsakiya da buƙatar su ,
Alhaji kamalu , to baka da damuwa , yanzu ka tafi , sai ka aika mun address ɗin da kake son na kai maka ita ni da hannun na zan miƙa maka ita anjima da dare ,
Kasan na faɗa maka sabuwa ce bata harkar nan to sai na maka yaƙin shawo maka kan ta ,
Ɗaga kafaɗa yayi cikin nuna halin ko oho ,
Ni dai ki tabbatar kin mata Wankan irin yadda ya kamata
Ya ƙarasa zancen yana kashe mata ido ,
Alhaji kamalu , kar ka ji kome .daren yau na kai ne a sama .
Yakaka wacce take zaune dirshan a cikin ruwan sama ta jikin bangon ɗakin ta ta baya ,
Ta kai hannuwan ta duk biyu ta toshe bakin ta a ƙoƙarin ta na hana kukan da take fitowa sarari kar su samy baby su ji , kamar yadda duk zantukan su ya ratsa kunnuwan ta .
Ashe daman anty samy yaudarar take akan kome , ashe burin ta ta tsundumata cikin irin rayuwar da tunda ta fahimci girman saɓon da ake aikatawa ta hanyar zina take yi mata addu'ar Allah ya sa ita ma ta tuba ta daina ,
Manufar ta ashe ta mayar da ita ga aikata zunubin da tayiwa ubangijinta Alƙawarin ta daina baza ta sake ba !
Ƙuka take da hawaye wani na korar wani , tana jin yadda tsoro ke mamaye ran ta , tsoron kowa da kome , tsoron sake yin zina ta hanyar tirsasawa ,
Takurewa tayi ta sanya fuskar ta tsakanin ƙafafun ta , sanyin ruwan da ya ɗan sake dawowa da ƙarfin yana ratsa ta ta hanyar jiƙa kayan jikin ta .
Assalamu Alaykum .
Gaisuwa tare da fatan Alkhairi a gare ku baki daya!
Nagode.
[10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
35
Doctor hamza ba tare da ya dubi sashin da Yakaka take tsaye ba yayi wucewar sa yana waya da ɗaya daga cikin abokan aikin sa na nan Asibitin Maiduguri wanda ya masa ƙiran gaugawa sakamakon neman sa da ake a asibitin jahar saboda wani aiki na gaugawa da za'a yiwa wata mata da take halin buƙatar taimako ,
Kan ta a ƙasa tana satar kallon gefen fuskar sa , zuciyar ta cike taf da addu'o'i iri-iri , ta wuce ta ƙarasa wajen maigadi wanda ya tattara dukkanin hankalin sa akan ta ,
Sama-sama ya amsa gaisuwar ta ya ɗora da tambayar ta wajen wa ta zo ?
Wajen Rahima na zo .
tace da shi tana fatan kar ya hana ta shiga gidan saboda wannan maigadin baƙon fuska ne ba wanda ta sani a da ba ne
Kallon tsanaki yayi mata bai hango wani alamun rashin gaskiya a tattare da ita ba ,
Ki shiga tana ciki .
Yace yana komawa kan ɗan bencin sa na zama .
Hamdala tayi bayan ta yi masa godiya ta taka tana nufar cikin gidan da bai zamto baƙo ba a gareta , tsarin sa bai sauya ba illa zuciyar ta da take cike da taraddadin hasashen da irin fuskar da Mutanen gidan zasu ƙarbe ta da hakan ya hana ta kuzarin isa cikin gidan cikin ƙanƙanin lokaci
Da duk takun ta guda kunnuwan ta suke sake kusanto mata tashin muryar ta suke,
da bata riga ta manta amonta ba ko dan ita ɗin tana daga cikin mutanen da suka gwada mata ƙauna a duniyar ta ne ?
Hajja dan dai kince kin manta fuskar maman ta ne amma idanunta sak na mamar ta ne , sosai tana ɗibar yanayi da mamarta sai dai ko kamannin Baban ta yafi ƙarfi ,
ai babyn nan ƙarshe ce a kyau wallahi kamar naje Niger na kwato ta nake ji , Allah sarki baby na Allah dai ya baki lafiya , yasa a dace wajen neman maganin nan , Allah kuma ya jiƙan Mamar ki me kirkin nan .
Da murmushi hajja ta amsa da Amin Amin Rahimatu
A hankali ta sauƙe idanun ta a bayan Rahima lokacin da ta ƙaraso ƙofar falon , wacce ta juya baya tana ƙoƙarin saƙala tangamemen hoton Mama cikin jerin hotunan da suke killace a jikin bangon inda aka tanadi sashi na musamman domin ajiyar hotuna ,
Ɗaya daga cikin hotunan da hajja ta zo da su ne da ta kai aka wanke mata shi zuwa Babban takardan hoto aka yi mata gidan sanya hoto na musamman tare da sanya shi a cikin gilashi .
Ganin ta ta mika kan hoton , fuskar da ta gani jikin hoton ya sauya bugun zuciyar ta nan take , a hankali take wara idanun ta tamkar wacce ta warke daga makanta , kamar yadda take jin zuciyar ta tana buɗewa da wani irin yanayi ƙaƙƙarfa , ƙofofin gashin jikinta baki ɗaya suka buɗe suna tsattsafo da gumi ,
Taku ta fara yi tana ƙara kusantar hoton da zuciya da tunaninta baki ɗaya suka tafi ga fuskar dake jikin sa.
Haƙiƙa bata taɓa ganin ta ba amma kusancin dake tsakanin uwa , mahaifiya da abunda ta haifa daga cikin jikinta ya wuce wasa ya kuma wuce hankalin duk wani me tunani ƙauna ce me rassa da take yaɗo a dunƙule da babu me iya ganin zurfn ta bare a iya hasaso iyakar ta ,
Bayan Rahima ta zo daf ta tsaya tana sake nutsar da idanun ta akan fuskar mama wacce tayi ƴar kyakkyawar dariya a hoton.
Hajja wacce ta miƙe tsaye daga gefe tayi sororo tana bin Yakaka da ido kafin tace
Ke , Ke , Ke baiwar Allah lafiya kike kuwa ? Zaki shigo mana gida haka sangam-sangam babu sallama bare neman izni ? Kin kuma zo kin yi tsaye ƙere-re uwa wacce ta haɗiyi taɓarya ince ko baki da lafiya ne ?
Rahima wacce bata ji tsayuwar Yakaka kusa da ita ba , saboda raggon taku marar sauti da Yakaka tayi a yayin isowa wajen , ta ɗan waiga sashin hajja lokacin da take gama sarƙafe hoton a inda ya dace tare da janye hannun ta daga jikin hoton ta waigo tana cewa
Hajja da wa kike magana ne ?
Fuskar ta ce ta kusan haɗuwa da ta Yakaka da ya sa ta ɗan jaa baya
Bismillahi waye ha...
Kalmomin ta ta haɗiye muƙut , maƙwallon maƙogoron ta ya motsa kamar yadda idanun ta suka firfito da mabayyanin firgici baro-baro a cikin su ,
Shekarun da suka raba haɗuwar fuskokin su basu yi yawan da zasu sa su mance da kamannin juna ba .
Ya-Ya-Yakaka ke-ke kece ??
Rahima ta furta muryar ta tana makyarkyata kamar yadda kwakwalwarta take hautsinewa da kokonto ,
Yakaka wacce zuciyar ta ta zaƙu da son samun tabbaci akan gudan jinin ta , ba tare da ta janye idanun ta daga kan hoton ba ta lalubo hannuwan Rahima ta damƙo su da ƙarfi ,
Rahima, Rahima ni ce ,
Ta zarce da tambayar ta
wannan ,? wannan Mama ce ? Ƴa ta Mama ?
Rahima wacce tunanin ta ya gama dunƙuluwa waje guda , ta fisge hannuwan ta da matuƙar ƙarfi bata tsaya ba ta taka da gudun gaske tana nufar ƙofa , kafin ta ƙarasa ficewa ta ɗaga murya tana sanar da Hajja .
Hajja ki gudu wallahi Fatalwar Maman Mama ce wannan .
Turus hajja tayi tana bin bayan Rahima da kallo , kafin ta sake waigo Yakaka wacce bata bi ta kan kalaman Rahima ba tamkar ma dai bata kai ga fahimtar me kalaman Rahima ke nufi ba .
Ta saka hannu ta ɗago Hoton ta ciro shi daga mazaunin sa , tare da riƙe shi da hannuwan ta duk biyu , tamkar ta riƙe yar jaririyar ta .
Kai tsaye ta nufo Hajja da hoton , fuskar ta da wani irin yanayi na chakuɗuwar tsantsar farinciki da kuma fargaba tace
Wannan ƴata ce ko ? Mama ce ko ?
Kafin ta ƙaraso hajja ta juya da ƴar sassarfa tana ɗingisa kafafun ta da basu cika lafiya ba ,
Un-un-un ƴar nan , ni kuwa ina zan sani ?
Mutum dai baya ƙin ta Mutane wai ance da ɓarawo ya gudu , Bi Rahima can dai kin tambaye ta Dan Allah .
Garam !
Hajja ta rufo ƙofar ɗakin ta .
Saƙare tayi a tsaye tana son harhaɗa tunanin ta domin ta kai ga fahimtar meyasa ta ga kamar ana gudun ta ? Ashe girman laifin ta har ya kai ya sa ta zama abun gudu a wajen mutane ?
Falmata ina Falmata ? Ta san idan kowa zai guje ta a duniya a zare Falmata a cikin su , Falmata baza ta taɓa gudun ta ba , ina take ?
Ta juyo da nufin fitowa ta nufi sashin Baba , sai ga Rahima tare da wani mutum wanda bata kai ga sanin sa ba .
Mallam Kabir ga ta nan , ta nuno Yakaka wacce take tsaye ƙiƙam rungume da hoto .
Dan Allah kana ganin ta ?
Ina ganin ta mana Hajiya Rahima , ai wannan Mutum ce , ba Fatalwa ba , hala an samu akasi ne wajen jin wani labari akan ta ?
Ke baiwar Allah wacece ke ? Daga ina kike ? Me kuma kika zo yi nan?
Zuwa lokacin Yakaka ta fara hasaso abunda yake faruwa , dan haka fuskar ta na bayyana sabon alhini ta matso tana cewa .
Rahima ni ce Yakaka , ba Fatalwa ba ce ni , ban mutu ba , waye yace na Mutu ???? Ina Falmata ?
Ba tare da Rahima ta ce ƙala ba , bata kuma yadda ta ƙarasa kusa da Yakaka ba ta sake juyawa da ɗan gudu ta nufi sashin Baba , da daman daga can ɗin take shine ma ya haɗo ta da Mallam kabir ɗin da ta zo ta same su tare suna ganawa ,
Tana cikin yiwa Baba bayanin dawowar Yakaka ƴar gudun hijira wanda suke da tabbacin mutuwar ta a wajen haihuwa shekaru kusan shidda da suka wuce ,
Sai ga Mallam kabir tare da Yakaka wacce take biye da shi .
Da ido Baba ya bisu bayan ya amsa sallamar su , har suka ƙaraso cikin falon inda Yakaka ta nemi waje daga can gefe guda ta durƙusa bisa guiwowin ta ,
Mallam kabir bai zauna ba yayi bankwana da prof tare da juyawa kan takun sa ya bar wajen .
Prof bai yiwa kamannin Yakaka sani na sosai ba amma tabbas ya shaida fuskar ta , saboda ya taɓa ganin ta a farkon zuwan ta gidan sa , sannan a ɗan taƙaitatcen zaman da tayi a gidan tana zuwa gaishe shi lokaci-lokaci .
Babu alamun firgici a tare da shi yake amsa gaisuwar Yakaka , wacce kan ta ke a sunkuye .
Cikin nutsuwa irin ta manyan mutane da suke da tarin ilmi ya soma da tambayar Yakaka daga ina take ? Me kuma ya faru da ita tsawon shekarun da tayi bata nan ? Bai shigo mata da batun labarin mutuwar ta da yake tabbatacen Al'amari ba a wajen su a tsawon shekarun da tayi bata nan .
Tambayoyin sa suka fargar da Yakaka tare da tuno mata da Malama Maryam da ta baro can a layi fiye da mintoci ishirin ,
Wacce ta san zata taya ta fuskantar mutanen ta da tarin laifukan da suke kan ta ,
Tare muke da baƙuwa Baba , a min iznin na shigo da ita .
Je ki shigo da ita babu kome .
Bata jima ba suka dawo da tare da Malama Maryam wacce har ta fara shiga halin damuwa ganin lokaci ya ɗan jaa batare da ta ga dawowar Yakaka ba .
Cikin nutsuwa da kamalar da Allah ya hore mata Malama Maryam ta gaishe da prof , sannan ta gabatar da kan ta a matsayin Malamar Yakaka wacce ta ɗau darasi a wajen ta tsawon shekaru biyar da ɗoriyar watanni , a garin Abuja , daga haka ta tsagaita .
A hankali muryar Yakaka ta fara tashi tiryan-tiryan take bada labari tun daga irin Gadar zaren da Samy baby ta haɗa mata har kawo ranar barin ta Maiduguri da ta sanyata ta tsallake ta bar Jaririyar ta a ranar da ta haife ta , da zummar zata kai ta Abuja wajen mahaifn ƴar ta suyi aure ta dawo ta ɗau yar da ƙanwar ta .
Wacece ita Matar da kika bi ? Menene dangantar ku da ita ?
Tambayar Prof ta katse Yakaka .
Shiru Yakaka tayi na ɗan wani lokaci , tunowa da tayi da irin rufin asirin da Doctor Hamza ya yi mata a farkon kawo ta gidan ya bayyana ta a matsayin ƴar gudun hijirar da mijinta ya mutu ya bar ta da ciki ,
Ƙaramin tunani irin nata tare da mummunar ƙaddara suka sa ta sanya ƙafafu ta hamɓarar da irin tarin rufin asirin da Allah ya yi mata a tun wancen lokacin da hakan ya jawo a yau ita da kanta zata tona binnannen sirrin nata .
Domin a yanzu ta ɗau alƙawarin baza ta sake yin ƙarya ba , dan haka idanun ta na tara ƙwallar nadama da irin laifin da ta aikata ta koma baya , kan haƙiƙanin gaskiya ta ɗorar da labarin ta tun daga farkon shigowar su birnin Maiduguri zaman su a sansanin su, da zaman da suka yi a gidan Madam saly , shigowar Biyamuradi rayuwar ta wanda ta ambace shi da "sojan wata ƙasa ," har zuwa zaman ta a Abuja tare da dawowar ta a yau bata boye duk wasu gaskiyar da yakamata ta bayyana su ba ga mutumin da shine na farko da suka samu mafaka mai cike da karamci da tarin ƙauna a ƙarƙashin sa ,
Shiru ne ya gifta na tsawon wasu mintoci , da hakan ya bada dama ga malama Maryam ta ɗora da sake bada kyakkyawar shaida ga Yakaka , yadda ta jajirce wajen neman ilmi haɗi da yadda ta cije tare da taimakon Allah ta hayewa faɗawa ga rayuwar karuwanci kamar yadda ita samy baby ta so da ta aikata .
Mamakin mazajen guda biyu shi yafi kome yin tasiri a tunanin Prof, da har ta kai shi ga gaza cewa wani abu .
A zahiri yau ta bayyana a gareshi cewa daga Ɗan sa Hamza har shi wancen mutumin da ya zo har nan gurin sa ya ƙarbi auren ƴa a wajen sa duk ƙarya suka wanzu tsawon lokaci suna gindaya masa akan rayuwar marayun yaran su biyu .
Wanda a zahiri ƙaryar ta su ta cutar matuƙa gaya , ba su kuma kyauta ba .
Ƙaryar da Hamza yayi ita ta tokare ta hana shi yayi yunƙurin nemo yarinyar ya dawo da ita ta zauna ƙarƙashin kulawar sa kamar yadda a tun ranar da ya karɓe su ya alƙawartawa kan sa , wanda hakan ba wani abu ne me wahala ba kasantuwar sa babban Mutum , amma sai hamza yayi masa ƙarya cewa ta mutu har ma yayi jana'izar ta a asibiti , wanda a zahiri tun lokacin shi Hamza yana da masaniyar guduwa tayi , ko me yasa yayi hakan oho !
Sai kuma shi wancen mutumin Niger da ya riga ya san irin mummunan ta'asar da ya aikata na lalata tarbiyar yarinyar nan , amma kuma shine ya sake dawowa ya rufe shi a baibai tare da karɓe ɗiyar sa domin sake samun garaɓasa har aka ƙara masa da ƙanwar ta a matsayin mata duk a tafarkin ƙarya ??
Wannan wane irin son zuciya ne ? Meyasa ne gaskiya tayi ƙaranci ? Shin ƴan gudun hijara ba 'ya'ya bane ba ? Ba mutane ne masu ƴanci da galihu irin na sauran Al'umma ba ? Da rayuwar su zata zam ba a bakin kome ba ? Za kuma a dunga yin walagigi da su cikin rashin kulawa da tozartawa , a maishe su ba a bakin kome ba , shin zaɓin su ne rabuwa da iyayen su , dangin su , garuruwan su ? Ko kuwa ƙaddara makamanciyar wannan bata iya faɗawa kan kowa ne ?
Idan har ya tabbatar da duk labaran da suka bayyana a gare shi gaskiya ne , babu shakka zai yi tsayuwar daka cikin rayuwar ƴan gudun hijirar nan guda biyu , zai zama katanga tsakanin su da duk masu shirin tozarta su a sannu kuma zai ɗau hukuncin da ya dace akan Hamza da ɗan mutan Niger .
Muryar Malama Maryam ita ta sanya shi nisawa , ya maida ganin sa kan ta .
Baba ayiwa Yakaka hakuri a yafe mata babu shakka tayi laifi tare da zallar wauta