Showing 192001 words to 195000 words out of 411050 words
Chapter 65 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
shuɗaɗɗen laifin sa suke barazana ga nutsuwar sa saboda zuwan dodo-dodo da suke masa suna sake maimaita kan su tare da bada fassara akan halin da ya riski matar sa a ciki ,
Hannun sa ya kai da ƙarfi ya jawo ta ya jefa kan ta kan ƙirjin sa yana jin yadda iskancin kukan da take yana sake dagula masa lissafi ,
Ɗan Allah ki min shiru
Yace da ita , a tsawace
Da yake daman kukan gulma ne sai tayi luf kafin gajiyar biki tare da gajiyar farkon daren su danne ta bacci me matuƙar ƙarfi da daɗi ya silalo ya chafke ta ,
A hankali ya zame ta daga jikin sa ya miƙe daga kan gadon , rigar baccin sa ya ɗauka ya saka , ya fara taku yana barin ɗakin ,
Yayi zurfi a cikin tunanin abun da ka iya je ya dawo cikin rayuwar sa , mama ita take ta kai kawo cikin ran sa , rayuwar ɗiyar sa yake hangowa , yana jin wani irin al'amari me girma wanda yake tafe da tsoro akan ta , yana son tsare ta , so yake ya boye ta kar laifin da ya aikata ya shafe ta , tsoro yake kar tarihi ya maimaita kan sa ,
Bakin cikin da yake shaƙa kaɗai a wannan daren yayi masa yawa ma , me yafi ka san cewa matar ka tayi tarayya da wani ta hanyar zina sanya bakin ciki da ruɗani a cikin rai ??
Wani irin kishi me tsanani yake ji , wani irin yanayi yake ji akan ta , ji yake ƙimar ta na zubewa tana zagwanyewa daga ran sa tamkar narkakkiyar roba a cikin wuta , ji yake tamkar yana ƙyamar ta ,
," yaya maimounatu zata min haka,"??
Yake tambayar kan sa , yana sake maimaitawa ,
Meyasa ? Meyasa ? Wai meyasa ?
Bai san cewa ya fito har harabar gidan ba sai da ya ji ƙaƙƙarfar iskar dake wajen tana ɗaga rigar sa da bai ɗaure maɗaurin ba , a hankali ya kai hannu ya ja igiyar yana ɗaurewa ,
Tun da ya fito idanun ta suka sauƙa a kan sa saboda daman ta gagara bacci ban da juyi babu abunda take , ita mace ce me zafin kishin abunda take so , dan haka sanin cewa da tayi yau ɗin biyamurdi zai kasance da gimbiya maimouna ya ta'azzara soyuwar ran ta , ya sa bacci gagara ɗaukar ta duk kuwa da iya satar sa ,
Dan haka ta fito ta barandar ɗakin ta dake sama tana iya hango gaba ɗayan harabar gidan ta kurkusa daga inda take , duk kuwa da sanin da tayi dare ya raba ƙarfe 1:30am , to amma zafin kishi haɗi da bagen so ai rufe idanun me su suke yi .
Me ya fito da shi a wannan daren ??
Ta tambayi kan ta
Ta san shi farin sani kamar yadda duk wani motsi nasa yake kusa da zuciyar ta , take kuma iya fassara kowanne motsi nasa
Kada dai inda ya saba fita ya tafi a dai-dai wannan lokacin ya nufa ?? Wani irin tashin hankali ta ji ya taso mata ,
Zato take ya daina ? Tunda tun bayan dawowar sa daga nigeria bata ji alamun fitar sa ba , bata kuma gan shi ya fita ba ,
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ga ya ɗaga kan sa sama tare da waiwayowa sashin da take ,
Da sauri ta tsugunna tana ɓuya a bayan ginin gaban barandar ,
Cigaba yayi da kallon sashin nata lokacin da zuciyar sa ke kitsa masa wataƙila ita ma wannan ɗin da aka liƙa masa , ta riga ta gama sayar da nata mutuncin a waje ,
ya dangana kome da ya faru a matsayin hakkin baiwar Allah yakaka da ya ɗauka , ya jagorance ta suka aikata mummunan laifi , shi daman Alhaki ai kuikuyo ne .!
*****
Asubar fari ya hau shiri , garin baki ɗaya yayi masa wari , so yake ya tafi , yana son zuwa ya ga mama yasan ganin fuskar ta ne kaɗai zai iya sassauta masa zafin da ran sa ke yi ,
Daga sashin sa kai tsaye cikin gida ya tasamma sashin hajiya umma ba tare da ya dubi sashin kowaccen su ba tsakanin sashin gimbiya maimouna da tun barin sa da yayi cikin dare da sashin siyama wacce bai ko kai da sanin launin kayan da suke cibge a ciki ba ,
Yana ratsa sararik gidan yana amsa gaisuwar bayu da hadiman da suke kai kawo suna gyaran gidan da sanyin safiyar .
A falo na ciki ya tadda hajiya umma tana Azkar , gefen ta ɗan ƙaramin tire ne da aka jera gorar ruwa da ƴan kofunan gilashi ,
Tana ganin sa farin ciki ya bayyana kan sa bisa fuskar ta , cikar haiba da mutuntukar da ta hango tare da shi ya sa ya yi mata ƙwarjini a yau , tabbas aure cikamakin addini ne , cikin sa akwai martaba tare da girma me yawa ,
Gaishe ta yayi sai dai saɓanin da da yake shigewa kusa da jikin ta , yau ɗin tanƙwashe kafafun sa yayi a gaba kaɗan da ita ya sunkuyar da kan sa ,
Kallon tsanaki tayi masa ba sai ya faɗa mata ba ta san yana tare da damuwa me girma wanda a jiya kafin rabuwar su da yamma babu wannan damuwar a tare da shi , dan haka take hasashen ko menene damuwar sa tana da alaƙa da iyalan sa , ita kuma bata da burin zama ɗaya daga cikin iyayen da suke bincikar rayuwar gidan auren ƴaƴan su dan haka sai ta yi kamar bata ga damuwar ta sa ba , ta matsa zuciyar ta da ke son sanin meye ya same shi ?
Yaya kwanan ɗiya na su dukkanin su da fatan kun tashi lafiya ? Basu da buƙatar wani abu ?
Duk kowa lafiya umma na basu buƙatar kome ,
Umma zan tafi bakin aiki doumin an ƙira ni daga niamey bisa ga wani aiki na gouggawa da ya taso ,
Aiki ? Ba an baka houtu ba na tsawon sati gouda ?
Umma aikin mu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma ne koyaushe ana iya ƙiran mu kuma a kowanne yanayi da lokaci , !
Shiru tayi tana nazarin sa , kafin ta jefo masa tambayar da ta sanya shi ɗago kai
Tare da siyama zaku tafi kou ?
Shiru yayi kafin ya tattaro ƙarfin halin da ya yi masa saura
Niamey zan tafi ba dosso ba Umma , idan na dawo daga niamey zamu tafi dosso tare.
bata jaa ba tayi masa addu'o'i kamar yadda ta saba tare da ƴan nasihohi , ƙarshe ta sake tunasar da shi girman nawin da ke kan sa a yanzu , !
****
Tunda ya hau kujerar zaman sa a jirgin da zai ɗaga da shi zuwa niamey ya zurfafa cikin tunani daki-daki ,
Da hantsi ya samu isa ƙofar gidan , kan layin shiru , da yake unguwar babu yawan mutane , ya cire ƙuɗin me taxi ya biya shi , ƙarasawa yayi jikin ƙofar gidan ya ƙwanƙwasa
Hajja wacce take tsakiyar sharar ƴar harabar gidan ta saurara da kyau ta tabbatar cewa gidan nasu ake bugu , ta ajiye tsintsiyar ta ƙaraso jikin ƙofar ta tambaya wanene ??
Hajja ni ne ,
Ta shaida muryar sa dan haka ta zare sakatar ƙofar ya samu shigowa gidan , sai fara'a take masa tana lale marhabin da shi ,
Shiga ciki Babban soja bari na ƙarasa ture ɗan wajen nan zan zo mu gaisa , sannu ka sha doguwar tafiye ince kwana kayi a hanya ?
Murmushi yayi ba tare da ya amsa mata ba ya sanya kai cikin gidan ,
Ƙiiii
Ƙarar turo ƙofar sa ta sanya ta ɗago kan ta ta dubi sashin da ta ji motsi ,
Hajja sannu da aiki !
Tace cikin ƴar muryar ta ,
Bai amsa ba saboda baki ɗaya hankalin sa da idanun sa na ga fuskar mama wacce take jingine da jikin falmata akan cinyar ta , su duk biyun suna fuskantar ,
Taku ya fara yi yana jin yadda shauƙin son ta ke ɗibar shi , da sassarfa ya ƙarasa gaban su ya tsugunna gami da kai hannun sa ya kama ƴan kafafun ta da suke sanye da ƴar safa ya sunkuyo da fuskar sa ya sumbata yana me rufe idanun sa da jin yadda ƙaunar ta ke sake ratsa shi tare da wata nutsuwa ta musamman , me yake ƙauna irin ta tsakanin ɗa da iyaye ƙarfi tare da tsafta ??.
Lokacin da ya ɗago kan sa falmata ta kawo hannunwan ta duk biyu ta ɗora akan fuskar sa , a hankali tayi yawo da hannuwan ta tana shafar fuskar sa da idanun sa ke rufe ,
Tamkar wuta ta jaa ta ta janye hannuwan ta da sauri , tana ɗauke mama ta ɗora kan kafaɗar ta ,
Da farko tayi zaton hajja ce ta shigo, sanin cewa daga ita sai hajja a gidan .
Wa-waye ne ? Tace tana ƙoƙarin miƙewa ,
Koma ki zauna Fatima ni ne ,
Ya kai hannu yana ƙoƙarin karɓar mama ,
Ta gane muryar sa dan haka ta sakar masa mama a hankali , tana dai-daita numfashin ta da firgici ya sa shi hargitsewa ,
Yana karɓar ta yayi mazauni akan ɗaya daga cikin kujerun wajen ba tare da ya janye idanun sa daga kan ta ba ya shiga sumbatar kumatu zuwa goshin ta ,
Bai ko ji gaisuwar da falmata wacce ta zauna daga ƙasa a gefe take yi masa ba ,
ita ma shiru tayi ganin bai amsa ba
Shigowar hajja ya sanya shi rungume mama a jikin sa suna gaisawa shi da hajja ,
Soja garin nan na ku kuwa ya karɓe ka , ka ga yadda kayi fes da kai kana ƙyallin fuska sai ka ce sabon ango ? Ah lalle miyar umma da zaƙi ta sa kayi shar da kai duk wannan hautsinewar sojin sun kau , ke Fatima kin kuwa gaishe da maigidan naki ??
Na gaishe shi hajja ,
To ban ga kin kawo masa ruwa ba , ?
Zata miƙe ya dakatar da ita ƙyale ta hajja ita da take da larura baza ta iya aike ba !
Ƴar dariya hajja tayi
Zata iya Babban soja ai matar ta ka ba dama akwai lura da kaifin ƙwaƙwalwa saurin gane waje ne da ita , ka ga dai ba mu rufa wata guda ba a gidan nan amma ta haddace kusan muhallin kome da kome da yake cikin gidan nan ,
ita da kan ta take zuwa ta ɗau ruwa a firiza ko ta je kitchen ta haɗa madarar mama , kullum addu'a nake mata Allah shi kawo mata waraka .
Ɗan murmushi yayi yana duban falmata wacce ta koma ta zauna ta juyar da kan ta gefe ,
Kalaman hajja sun tuno masa da abunda ya so mantawa , watau kai falmata asibiti tare da samar mata gurbin karatu ,
Ya zama dole yayi duk wani abunda zai iya yi gurin kyautata rayuwar falmata ko domin ya samu girman laifin sa ya ragu a wajen Allah .
Hajja ku shirya zamou tafi babban hospitalisé a duba lafiyar idanun fatima yanzu. !
To to yanzu kuwa , falmata tashi ki shirya bari nima na ɗan kintsa , !
Niamey national hospitalisé nan suka je , inda basu wani ɗau dogon lokaci ba suka ga ƙwararren ophthalmologist , bayan haske-hasken da tarin tambayoyin da yayi mata akan idanun nata , a ɗakin gwaje-gwaje .
Suka dawo ofishin sa inda youssouf ke jiran su , bayani ya soma yi masa daki-daki
A sakamakon binciken da nayi a zahiri ban hango wata cuta ba a idanun nata sai dai raunin ƙwayar idanun nata watau ainahin jijiyoyin idanun suna da rauni , a tambayoyin da nayi mata nayi ƙoƙarin sanin tayaya ta fara samun rashin gani ko da shi aka haife ta ? amma sai ta shaida min bata da masaniya akan mafarin samuwar rashin gsnin ta ,
A takaice cikin binciken da muka gudanar da kuma sakamakon amsoshin da ta bayar yayin yi mata gwaji da akwai yiyuwar dawowar wani kaso daga cikin ganin ta idan har za'a samu ƙwararrun kayayyakin aikin da zasu taimaka wajen dawo da ganin nata ,
Sai dai a halin yanzu bamu da waɗannan kayayyakin a nan gida niger da sauran ƙasashe masu tasowa , sai a manyan ƙasashen duniya da suka yi fice wajen samun ingantattun asibitoci masu isasssun kayayyakin aiki tare da ƙwararrun likitoci ,
Dan haka a yanzu abunda zamu iya yi mata kaɗai shine zamu bata magungunan da zasu iya taimakawa wajen bada kariya ga idanun nata daga kamuwa da wasu cututtukan da zasu iya kassara sauran ƙarfin jijiyar idanun da kuma hana idanun yin ciwo ƙaiƙayi da zubar ruwa ,
Da fatan kun fahimce ni ?
Mun fahimta Doctor mun goude zamu dawou gare ka idan buƙatar neman taimakou game da asibitin da ya kamata a kai ta a wata ƙasar ya tasou mun goude ƙwarai Madallah .
Washegarin ranar Biyamuradi bai zauna ba , ya shiga binciken makarantar makafi me kyau da yake son ya kai falmata ta fara karatu kafin lokacin da zai sake yunƙuri me ƙarfi akan lafiyar idanun nata a karo na biyu .
Association Nationale Pour la promotion des aveuglés , nan ne inda ya ji gamsuwar sa akan ya kai falmata nan ta fara ɗaukar darasi , wacce jibiya ce ta koyar da makafi tare da basu tallafi me tushe daga ƙasar amurka , da ta tanadi ƙwararrun malaman makafi ,
Cikin sati guda yayi mata rajista da duk wasu abubuwan da ya kamata , ya samar mata da direba bayan ya sa an kawo masa ɗaya daga cikin motocin sa da suke maradi ya danƙa makullin ga hajja wacce take cike da farin cikin wannan cigaba da falmata zata samu a rayuwa .
Ranar da zai bar garin zuwa bakin aikin sa jahar dosso , ya yi musu sayayyar kayan abinci da abubuwan da zasu iya buƙata tare da ƴar ƙaramar waya me sauƙin amfani ya ba wa hajja bayan ya zuba mata lambobin sa a wayar ya adana ta su a ta shi wayar ,
Suna zaune a falo yana musu sallama akan yau zai koma bakin aikin sa , sai kuma zuwan ƙarshen wani watan zai komo
Godiya me tarin yawa hajja ta yi masa ,
Ya amsa tare da waiwayawa sashin falmata da take ta faman lila mama akan ɗan lilon ta wanda baban ta ya sayo mata su tarkacen kayan wasan yara iri-iri har da wanda ya fi ƙarfin shekarun ta , tun daga kan lilon yara , kekunan koyon zama har zuwa ƴar mota ta yara da ƙananun kayan wasanni irin na ƴaƴan gata na sosai , bayan suturun da ya daɗa jibgo mata.
Fatima baki da wata matsala kou ?
Shiru tayi tana ɗan lila mama a hankali ,
Falmata hala kin samu kurunta ? Kina jin Babban soja na magana kin yi shiru ? Uhum yau ni naga abunda ya shallake tunani na ,
Babu kome kawai ina son unmh
Uhum ina jin ki me kike so ??
A kaini makaranta
Ai na sanya ki makaranta fatima sati me kamawa zaki fara zouwa ,!
Na islamiya ? Ina so a cigaba da koya min karatun addini ma ,!
Toh babu damouwa idan Allah ya yarda zan bincika a samu me koyar da ke na Islama ma ,
Akwai wata damouwa bayan wannan ?
Daman ka gaya musu zan dunga zuwa da mama makarantar ko ?
Babu inda zaki dunga goyon ta kina tafiya da ita anan waje na zaki dunga barin ta idan ya so kafin ki dawo na sauya ta , ko kuwa na gudu da ita, kina nufin baza ki maida hankali kan karatun naki bane ? Zaki dunga ɗaukar ta kina zuwa da ita makaranta ki ɓige da raino memakon karatu ni ke meyasa ana nuna miki hanya kina daɗa bauɗewa ne ??
Ɓata rai tayi ta ɗauke kai
Murmushi youssouf yayi , shi dai rigimar hajja da falmata na ba shi dariya
Duba fatima ki bar mama a wajen hajja har ki tai école ki dawo Kin ji kou ? Ba'a tafiya da yara école.
Shiru tayi idanun ta na kawo ƙwalla ita dai bata ƙaunar abunda zai raba ta da mama ko na ƴan mintoci ne bare fa makaranta da awanni zata yi a can , kai anya zata iya , ?
To hajja mu dunga zuwa tare da ke mana makarantar ? Sai ki dunga riƙe min mama nayi karatun na fito ?
Ke raba ni da wannan gudun birin , gotai gotai da ni zani makarantar ? Yaushe rabon duniya da ayyaraye ? Babu inda za ni ke kaɗai zaki tafi makarantar ki ki dawo ki same ni ina nan , ilmin ai shine Babban gatan ki falmata kin ji ko ?
Naji hajja
Yauwa mutuniyar ai shiyasa nake son ki akwai ki da saurin fahimta ,
Sallama suka yi da youssouf yana sake yiwa hajja godiya me tarin yawa tare da ɗanka mata ƴan kuɗaɗe wanda da kyar hajjan ta yadda ta karɓa sai da yayi ta roƙon ta da Allah .
Daga nan Dosso yayiwa tsinke bai jin marmarin zuwa maraɗi duk da cewa fiye da kaso talatin na ɓacin ran sa game da sha'anin sa da gimbiya maimouna ya kau , domin har sun yi waya ma cikin kwanaki biyun .
Assalamu Alaikum kowa da kowa !
Da fatan kuna lafiya ?
Ina neman afuwar ku bisa jinkirin zuwan wannan shafin , hakan ya faru ne sakamakon tafiya da ni zuwa gida , ban samu zama ba ziyarar dangi da sauran Al'amuran yau da kullum .
Da fatan zaku cigaba da haƙuri da tsaikon da ake samu cikin ajizanci irin na ɗan Adam ?
Nagode [10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Fikrah writers association
MAFARI