Showing 54001 words to 57000 words out of 411050 words

Chapter 19 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14375

ya zo yi cikin nasara , tabbas burkutu ta zama mahaɗin rayuwar sa domin ji yake kamar zai iya rasa ran sa idan ya ƙara wasu awanni bai zubawa cikin sa ruwan zafin burkutun ba ,"

Da sauri ya fita daga tantin yana jin yadda kan sa yake jujjuyawa ," a take sojojin dake da alhakin kula da shi , kama daga tuƙa shi idan zai fita da masu rakiyar sa ,zuwa masu yi masa wanki da girki da sauran aikace aikace duk suka taso ,"

dakatar da su yayi ya kira direban sa kawai tare da yi masa umarnin ya tuƙa sa zuwa cikin birnin maiduguri ," .

Lol 😂😂
Anya ma na kai 3k words ???
Aradu ban kai ba 😂

Well amma ai nayi koƙari koh ??

Alright naga ra'ayoyin ku kuma naji daɗin su sai dai kun sani fah akwai tarin aiyuka akan mu koh ??

Ok zaku cigaba da ji na akai-akai kamar yadda na Alƙwaranta muku insha Allah ,"

Kar ku manta da danna ɗan tauraron nuna yabawa , tare kuma da faɗin ra'ayoyin ku domin bani karfin guiwar cigaba da rubuto muku .

#fikrh
#umm'muazMAFARI ......
       ( Hargitsin Rayuwa )

14

umm'muaz



Babban Barikin soja dake tsakiyar birnin maiduguri nan direban youssouf ya dakata ,

Karo na uku biyamuradi youssouf yana yunkurin faɗawa takwaran aikin sa kuma sabon aboki agare shi wanda ya kasance babban sojan nigeria mai matsayi irin na biyamuradi ( colonel ) amma sai ya ji ya kasa , saboda shi da kan sa yana jin kunyar mummunar ɗabi'ar sa duk da cewa kusan hakan ba bakon abu bane wurin su soji , amma yadda yake da kamala da nutsuwa a zahiri ,uwa uba kasantuwar sa ɗan nasaba da akan san su da kyaun tarbiyyah , tashin farko zai yi wuya ayi hasashen yana kurɓar burkutu ,"

Sake ƙutawa yayi a karo na barkatai yana me jin duk ya gundura da hirarrakin da abokin nasa mai suna "colonel nuhu " yake yi masa , ya kai ɗan yatsan sa ɗaya gami da sosa ƙeyar sa .

Taɓo sa nuhu yayi lokacin da ya lura baki ɗaya youssouf ɗin bai bashi amsar hirar da yake yi masa tamkar ma hankalin sa bai tare da shi yayi zurfi cikin tunani .

   Abokina yaya dai ?
   Meye yake damun ka haka da har ka zurfafa cikin tunani ?

Ɗan ƙaramin tsaki youssouf ɗin yayi kafin ya ce

Bari kawai abokina akwai abun da nake bukata ne ,

Wani shu'umin murmushi nuhu yayi domin shi tun tuni ya harbo jirgin youssouf ɗin duba da yadda duk yake a birkice ga fuskar sa da take bayyana matsanancin halin da yake ciki ," amma dan ya sake tabbatarwa tare da son ya tsokani youssouf ɗin ganin kamar yana son boye masa cikin sa , ba tare da ya san shi da shi dukkanin su ƙwaryar sama da ta ƙasa ne ( duk kanwar jaa ce )

Me kake bukata haka abokina ??

Ɗago kan sa yayi da yake a sunkuye ya wara idanun sa da suka sauya launi zuwa jaa yana jin yadda nawin da ya tokare shi a kirji akan rashin samun kurbar burkutun yana sake ƙaruwa ta yadda yake jin tamkar matse masa jikin sa ake da dukkanin hanyoƴin jinin sa ," cikin wata irin sarƙaƙƙiyar murya yace ,"

   Burkutu ," Burkutu zan sha nuhu ,' dan Allah ka taimaka ka kaini inda zan samu burkut da farko , zan yi maka bayani daga baya ," 

Wata shu'umar dariya nuhu ya kwashe da ita ,'

haba abokina ai ba ma sai ka min wani bayani daga baya ba duk su biyun za'a tanadar maka a lokaci guda , kaga daga ka gama kora ruwa sai kuma a faɗa harka ,"

Shi dai biyamuradi youssouf bai ce kome ba hasalima bai kai gano ba cikin kalaman nuhu illah kawai ya ji ya fara samun nutsuwa tun da nuhu ya ce zai samar masa da abun da yake muradi ,"

Direban sa yayi niyyar kira amma sai youssouf ɗin ya dakatar da shi tare da faɗa masa shi yana bukatar sirri ne dan haka so yake su tafi su biyu kawai ', a cikin ran sa yana ƙudurtawa zai sanya ido sosai ya gane hanyar domin duk lokacin da ya bukata kawai ya tafi shi ɗaya ya shaa abar sa ba tare da rakiyar kowa ba , ba kuma tare da kowa ya sani ba. ( mai kowa me kome ya sani kuma yana ganin ka youssouf amm )

Haka suka kama hanya tare nuhu shi ke jaan motar suka keto titi tare da bullowa ta bayan kasuwa suka gangara zuwa cikin unguwar BULABURIN wacce kaf cikin garin anan kaɗai ake iya samun giyar gargajiya gangariya ƴar asali ,"

Suna yin fakin a harabar wurin da ya cika ya tumbatsa da mutane zuwa ababen hawan su sakamakon yamma da tayi ," kiɗa yana tashi ta cikin manyan sifikokin da suke a kusurwa huɗu na zagayen filin ,ga matan banza da shigar fitsara burjik suna kai kawo cikin sigar tafiyar tallata baiwar jikin su , kowacce taci bilicin tare da izgar doki a tume a kan ta yayi tozo kamar na tsohon rakumi ,"

Juyowa nuhu yayi tare da kallon youssouf da ya lura yana ƙarewa matan wurin kallo , cikin yanayin da shi nuhu bai kai ga fahimta ba ,"amma sai ya fassara kallon da na tsantsar zalama da nuna muradi ,"

Abokina duba waɗannan ba irin naka bane waɗannan duk ajawos ne na kananan yara ," daina ma kallon su irin naka suna daga ciki a adane ba kowa ke hayar su ba sai ire-iren mu manyan yara ,"

Yana kammala faɗin hakan bai jira cewar youssouf ɗin ba ya balle murfin motar gami da fita ,

Kutsa nan bulla ta chan suka bullo ainahin wurin da ake sayar da  burkutun da mashayan ta suka tabbatar da tafi ta ko'ina inganci a cikin da'irar wajen watau ( burkutun madam saly )

Suna doso wurin youssouf ya shaƙi ƙaƙƙarfan warin burkutun ya lumshe idanu yana sake jin nutsuwa tare da matsuwar ya ji ya kwankwaɗa , dan haka ya sake sauri ,inda suka tadda mutane akan kujeru gaban tebura ,

Ɗaya daga cikin ƴan matan wajen da suke da alhakin rabawar ga masu saya wacce take raƙube a gefe ita ce ta zaburo ta nufo wurin su ,'

Tun da ta nufo su nuhu yake mata kallon sheƙeƙe , saboda sam ba ita yayi zato ba , ba kuma ita ya so gani ba ," budurwar sa ko kuwa ace farkar sa samy baby , yarinyar da take tashe a da'irar ta su ita yake son ganin kamar yadda ta saba taryar sa kaf ƴan matan wurin sun san shi kwastoman samy baby ne ,

saɓanin ta sai yaga wata yagwalgwalalliyar ƴar yarinya tana tahowa gare su hasalima shi tun da yake zuwa rumfar madam saly bai taɓa ganin wannan ƴar ƙwailar ba ,"

Da zuwan yakaka wurin ta ɗan rage tsawo tare da tambayar su kofi nawa zata kawo musu ," ɗauke kai nuhu yayi yana wani hura hanci domin shi gaba ɗaya ma ransa ya gama baci ,"

Biyamuradi youssouf da yayi baya da jikin sa akan kujera tare da yin ƙasa-ƙasa da idon sa tamkar dai yana gudun wani ya gan shi a wurin ",alhalin nan kuwa shauƙin burkutun ne ke kwasar sa da kamshin ta suka haɗu suka samar mishi da mutuwar jiki ," shine ya amsa mata cikin hausar shi ta bamarɗe ,"
  " Ki ɓido min mai auki kawai "

Kasaƙe yayaka tayi a tsaye cikin rashin fahimtar abun da ya faɗi ," hasalima hausar da ake yi cikin maiduguri ma da bata da nisa ba gane ta take yi sosai ba bare fa wannan gangariyar hausar sam bata tsinci koh kalma guda ba ,"

Sake rusunawa tayi tana me sake maimaita tambayar da tayi masu cikin gurbatatciyar hausar ta ,"

  Wannan karon nuhu ne ya amsa mata a fusace ,'ke dallah cewa aka yi ki kawo dayawa ,"

Sum-sum yakaka ta juya da nufin zuwa ta kawo musu,
'conole youssouf ya bi takun kafafun ta da kallo yana saƙe ƙagauta,"
" dai-dai tahowar samy baby wacce shigowar ta kenan wurin aka yi dace idanun ta suka sauka kan yakaka tana abun da ta ayyana shi a taɗi da gwarzon ta na wannnan wattanni "conole nuhu" wanda a yanzu kaf samarin ta babu kamar shi a kuɗi da shi take tinƙaho ,"

A take wutar kishi ta ruru a ƙarƙashin ran ta ," wata irin bangaza tayi wa kafaɗun yakaka tare da sanya tsinin dogon takalmin kafar ta ,  ta take mata kan yatsun ta biyu tare da tsayuwa akan yatsun kafar sannan cikin raɗa bayan ta kawo bakin ta kusa da kunnuwan yakakan wacce ta ɗimauce cikin jin azabar takun da samy baby tayi mata tace

," yarinya ki kiyaye wannan ɗan itacen marmari  nane zan iya kashe wacce ta shiga gona ta har tayi gigin taɓa ɗan itaciya ta ,'

Duk tsayuwar samy baby akan ƙafar yakaka biyamuradi youssouf yana ankare da hakan saboda idanun sa da suke wurin daman ," ji yayi tausayin wacce aka takewa kafar ya ɗan kama shi wanda tun daga kan kafafun nasu ya fahimci banbancin da ke tsakanin su ,ganin kafar yakakan duk dadbare-dadbaren datti ,ga manyan tsagun faso da datti ya samu mazauni na dindin-din wanda idan aka kwatanta da kafar samy baby da take a wanke a goge sumul-sumul tashin farko za'a fahimci baiwa ce da uwargijiyar ta , dan haka yayi tunanin yakakan wani laifi tayi wa samy take hukuntata ," sai dai duk da haka yaji haushin samy saboda shi mutum ne wanda sam baya son zalinci ," take yaji ya tsane ta ,

Ɗago idanun sa yayi ya sauke su akan fuskar samy baby wacce idanun ta da hankalin ta baki ɗaya yake kan "ɗan itaciyar ta nuhu "😁

da sauri yakakan ta wuce lokacin da ta ji samy ta janye kafar ta tare da yin gaba ," 

Kichibis tayi da madam saly wacce ta sawo kai kallon ta sama da ƙasa madam.saly ta jefa mata,"
yanzu yaks dan ubanki ban baki kayayyaki nace ki daina yawo cikin waɗannan shegun tsunmokaran ba , ace tsawon sati kenan yau da kuka fara zuwa min nan amma shegu ƙazaman banza kullum da daƙalkalallun kaya ɗaya? Kalen ku dunga sa min kostomomi amai ? Kuna yawo yarkace yarkace uwa sabbin  mahaukata ? A haka waye zai karbi abun hannun ki ya shaa ? Aaa ah ku ji min shegiyar yarinya zata min kashin kasuwa ta janyo min hasara ? Toh dan uwarki wuce maza ki je ki sauya kayan nan kamar yadda ƴar uwar ki ta sauya nata ,'idan ba haka ba a bakin aikin ki kin ji ko baki ji ba ?

Da sauri yakaka take gyaɗa kai daga inda take rakaɓe ,"

Sake ɗaga kayan yakaka take tana jujjuya su tare da ɗora su a jikin ta tana gwada tsawon rigar wacce take ƴar ɗigil da kaɗan zata rufe mata cibiyar ta da ƴan guntayen hannu maƙale hammata , tare da ɗan siririn siket ɗin da ya shaa tsagu a gefe da gefen sa har fiye da rabin tsawon siket ɗin ,

Niyyar ta ta kaiwa falmata a ɗinke mata wuraren da suka yayyage a tunanin ta ," sakamakon ganin kayan ƙanana ne tunanin ta sun ɗangale mata ,  dan haka ta yanke shawarar kaiwa ƙanwar ta ," duk da tayi tunanin kayan zasu matse falmata kasantuwar ta ɗan fi ta kaurin jiki ," gefe guda na zuciyar ta tana jin zata fi samun farin ciki idan falmata ta samu sauyin sutura fiye da karan kan ta ,"

Zabura tayi tare da fara kokarin zare kayan jikin ta sauya , jin motsi da tayi yana nufo ɗakin da yake zaman mallakin ƴan aikin madam saly a nan masu kwana a gidan suke kwana su kuma da suke yini su tafi anan suke cin abincin su , ita da yagana da suke duddungura sallalolin su suyi sallah a ɗakin ," domin bayan su babu wacce ta damu da sallah cikin sauran ma'aikatan manyan su da yaran su da tsoffin su ,"

Juyowa tayi bayan ta sanya rigar a zaton ta madam saly ce ta leƙo ta ga koh ta shirya ,"

Karaf suka haɗa ido da ɗanliti wanda ya ɗaga labulen bayan ya tokare hannayen sa da jikin kofar yana ƙare mata kallo da jajayen idanun sa da suke cikin maye ,"

A firgice yakaka ta rarumi chukuikuyayyen hijabin ta ta suturta jikin ta ", tsaki ɗanliti ya jaa tare da ƙarasa shigowa ɗakin .,'
   Aikin banza da wofi toh yarinya meye zaki boye min iyee ? Baya koh gaba ?? Baya dai kin san nima ina da shi , gaban ma idan naƴi niyya zan taso su ehe ,"
    Jin tayi shiru ya sa ɗanliti buga tsaki dai-dai lokacin da yake zama a gefen wata yamutsatsiyar tsohuwar katifar da take yashe cikin babban ɗakin ,"

    Ƙwaila ma irin ki me zan gani a wannan busasshen jikin naki da bana zaton koh nonon kirki kina da shi ," duk abun da zan gani na riga na gani a jikin jigajigan manyan mata ƴan uwana ," ya ƙarashe zance yana wani jijjiga da girgiza gwangonin kirjin sa da yake a bushe ƙaranbau,"

Raɓar jikin bangon yakaka tayi bayan ta sunkuya ta ɗauki tsohuwar rigar ta da sabon siket ɗin , ta suɗaɗa ta fice a ɗakin tare da nufar bayan gida domin ta sa siket ɗin ,"

Bayan ta ya bi da kallo ,"
   Wai sunan wata kalma", Luwai ," yau naga ƴar kauye da lafiyayyar farar fata luwai-luwai,"ji yadda fatar ta take sheƙi da wani ɗan uban su fari na ainahi babu algus irin na su madam saly ," yarinyar nan idan ta samu hutu tabbas zata jaa gayu ahaayyee ,"gwara da babu ni a harkar ƴan maza ai da ganin da nayi wa bayan yarinyar nan da ace ina harkar maza da yau babu zaman lafiya,."

Da raɓe-raɓe ta fito daga banɗakin tana tafe tana sake sauke siket ɗin ƙasa-kasa sakamakon tsagun sa da yake har ya zarta gwuiwar ta ,

Wurin karɓar burkutun suka haɗu ita da yagana da tun safe madam saly ta sata gyara mata cikin ɗakin ta ,"amma tsabar shirgin da yake cikin ɗakin bata samu damar kammala gyaran ba sai yanzu ,"

Kallon kallo suka yi da ita da yagana wacce ita ma take tsuke cikin sabuwar shigar da madam saly ta bata na wani chasasshen wondon jins da yake a ɓarƙe ta wurin cinyoyin sa da wata ƴar ɗangalalliyar riga mai siririn hannu ," fuskar yagana ta kalla kawai ta fahimci ita ma tirsasa ta madam saly tayi ,ta sa ta sanya kayan a dole kamar yadda tayi mata ,"

Ba wacce tace ga ƴar uwar ta ƙala suka ƙarbi manyan farantan silver da larki da hema suka ciccika musu ruwan burkutu a kofuna tare da jerawa akan farantan ,"

Tana shigowa ƴar rumfar ta doshi gurin da ɗazu wasu mutane biyu suka bukaci ta kawo musu burkutun dayawa ,"

Turus ta yi lokacin da ta tadda kujerun da ta bar su akai wayam babu kowa ,"

Ɗan waiwayawa tayi tana dube-duben wurin da zata hango su ,ga zaton ta kou sun sauya waje ne ,"

Sai dai jajayen idanun mazan da taci karo da su suna kallon ta ya sa nan take ta diririce saura kiris ta saki farantin hannun ta ,"fiye da rabin maxan wurin kallon farar doguwar yarinyar da take sanye cikin jaan yadin da ya sake fidda kyau tare da hasken fatar ta suke," giyar da suka shaa suka yi tatil tana sake ƙawata musu tare da girmama musu sassan halittar jikin ta daga yar ƙanƙanuwar yarinya zuwa cikakkiyar babbar budurwa ," nan take suka fara kawo mata wawura da chafka cikin tamɓelen su na mashaya," 

Zilliya da zamiya ta haɗa Allah ya bata ikon tsalleke farmaƙin da suke kawo mata , " dan haka gudu-gudu ta maida tiren burkutun tare da shaida wa larki, masu neman burkutun sun tafi .

Ganin lokacin tashin su ya riga yayi "karfe biyar tayi " ya sa ita da yagana suka nufi ainahin cikin gidan inda anan ɗaki da falo gami da banɗakin madam saly yake ,"

Suna isa kamar kullum iwar haka suka tadda cikin falon nata a cike da manyan ƴan matan da suke ji da kan su ire-iren su samy baby ," sai karta suke da cha-cha suna yi suna haɗiyar ƙwayoyi tare da kora ruwan maganin mura da yake mahaɗin ƙwayar da suke sha ,"

Madam saly tana daga gefe zaune tsakanin wasu manyan Alhazawa biyu da alama wata magana mai muhimmanci suke yi ,"

Ɗan rakuɓewa suka yi daga bakin kofar a durkushe sannan suka sanar da madam saly lokacin tafiyar su gida yayi ,"

  Kallon hadarin kaji madam saly ta watsa musu kafin ta balbale su da masifar basa ganin tana tare da baƙi ne ? Su waɗanne irin wawaye ne ?

Hakuri suka bata tare da cigaba da tsugunno nan bakin kofar suna jiran ta ta kammala da bakin nata ,"

Sai da aka kwashe fiye da mintuna arba'in har duhu ya ɗan fara shigowa karfe shidda ta gabato , zuwa lokacin kuwa har kafafuwan su sun sage duk sun muzanta tsabar gajiya .,"

Sai da suka kammala maganganun da su basa iya jin me suke faɗi daga inda suke a sakamakon hayaniyar da take sake cika illahirin da'irar wajen ," basu ankara ba suka ji ta watso musu kuɗin aikin nasu ,"

  Ga shi nan ,' ku tabbatar gobe kun zo akan lokaci sannan ku tabbatar baku dawo min nan wajen da waɗannan shegun tsunmokaran kayan naku ba ,"  idan kuwa kuka yadda kuka doso min nan wajen da wannan shigar taku uwa masu kwana akan bola toh kuwa a bakin aikin ku ," ni bana son ƙazanta ,"ta karashe zancen tana jawo wata jakar bagco ta tura musu a gaban su ," ga kaya nan kowaccen ku shiga bibbiyu da su nake so na dunga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login