Showing 222001 words to 225000 words out of 411050 words
Chapter 75 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ta nufi Baban ta
Papa bienvenue , ta ƙarasa shigewa jikin sa da ya buɗe mata hannunwan sa , ta kwantar da kan ta a ƙirjin sa , ya shafi kan ta yana sauƙe idanun sa akan Falmata da take ƙarasowa wajen jikin ta sanye da dogon hijabin ta har ƙwauri ta zauna daga ƙasa a gefe ,
Sashin da take hasashen yana wajen ta fuskan ta cikin nutsuwa ta gaishe shi fuskar ta kadaran-kadahan .
Ya amsa yana bin fuskar ta da kallo da kitson da aka mata ya sake fiddo ƙyallin fatar ta tare da bayyana hasken goshin ta ,
Hajja wacce bata zama a tsakanin su ta yunƙura ta miƙe riƙe da jakankunan a hannu ta nufi ɗaki , tana ƙiran mama wacce tayi biris da ita taƙi amsawa sai ma sake lafewa da tayi a jikin baban ta .
Fatima ya shiri ? Kin kammala kou ?
Eh mun kammala tace
To madallah gobe insha Allah zamou tafi ku zama cikin shiri kin ji kou ?
Toh ta amsa tana gyaɗa kai !
Shiru ne ya ɗan gitta tsakani , kafin mama ta ɗago kan ta daga jikin Baban ta ,
Papa , an mana kitso ni da Mamaa na ka gani yayi chau ?
Ta janye hular kan ta , manyan kitson chuku da aka mata suka bayyana , duk da kitson manya-manya ne amma sun yi kyaun zane kasantuwar ta me yalwar gashi sai ya ƙarawa kyaun kitson armashi .
Shafa kan nata yayi yana murmushi yace ,
wow c'est très beau ,
Da dariya ta bar jikin sa ta nufi Falmata tana zuwa ta fara kici-kicin buɗe mata kai ,
Mamaa ke ma ki nunawa papa kitson ki , yafi nawa ma chau ko papa ?
A hankali ya gyaɗa mata kai yana jingina bayan sa da jikin kujerar ba tare da ya janye ganin sa daga kan su ba ,
Ture hannun ta Falmata tayi ta ɗan ɗaga sauti ,
Ki bari mama ba na hana ki buɗe min kai ba ?
Ba tare da ta sauke hannuwan ta daga kan falmata ba tace
Ai papa ne zai gani .
Tsawa tayi mata lokacin da take son ta sauƙe mata hijabin a tilas ,
Firgita tayi ta ja baya ta rakuɓe tana ƙwalan-ƙwalan da ido tare da raba kallon ta tsakanin mamar ta da baban ta ,
A hankali wasu siraran ƙwalla suka silalo daga gurbin idanun ta ganin an mata abunda ba'a saba yi mata ba ba kuma tare da an rarrashe ta ba ,
Cikin ran ta taji shirun da tayi tare da sanin manufar sa , dagulewar zuciyar ta ya zo dai-dai da zubar hawayen Mama ,
Hannu ta ɗaga ta fara lalubar inda take jin tashin shisshiƙar kukan ta , ta jawo ta jikin ta tare da ɗaura ta akan cinyoyin ta ,
Kwantar da kan ta tayi da ƙarfi a jikin mamar ta gami da fashewa da kukan da tayi tanadin sa ,
Kamar ruwan maɗaci haka take jin ɗacin sautin kukan ta daga cikin zuciyar ta, dan haka ta fara aikin lallashin ta ,
Hannu ta kai ta zame hajibin nata , ƙananan kitson da aka mata yir-yir suka bayyana
Ta karya murya cikin kuikoyon muryar mama tace :
Papa ka ga kitso na yayi chau ??
A hankali ta ɗago kan ta daga jikin ta idanun ta jage-jage da hawayen rikici , ta washe ƴan haƙoran ta lokacin da take kama dogon jelar kitson shade ,'( me hawa biyu ) da aka tufke shi ya sauƙa kan dokin wuyan ta , ta waiga tana duban Baban ta wanda duk abunda suke yana bin su da ido ,
ransa cike taf da ƙauna tare da shauƙin soyayyar dake tsakanin uwa da ɗiyar ta .
Muryar ta kamar ba ita ke kuka yanzu ba tace ,
Papa ka ga kitson mamaa na yayi chau ko ?
Yunƙurawa yayi ya matso sosai gaban kujerar da yake kai ,
Yana ƴar dariyar yadda fuskar falmata take a ɗaure tana wani takurewa yace ,
Ai tayi nissa daga can bani ganin kitson nata , ta matso nan kussa na gani kou ? Ya ƙarasa zancen yana karya wuya .
Eh Mamaa ki zo ya gani ,
Ta jawo hannun Falmata , gudun rikici ya sa Falmata ta biye mata ta taso ta biyo ta , gaf da ƙafafun sa Mama ta zaunar da ita ,
Idanun sa ya sauƙe akan kitson da suke yir-yir kamar inji ne ya jera , ƙwarai kyaun kitson ya birge shi .
Basu yi aune ba ta jaa hannun Baban ta ta ɗora akan Falmata ,
Papa ka ga ni ?
Ta ce tana washe masa haƙoranta .
Kasa janye hannun nasa yayi daga kan ta , saboda wani irin yanayi da yake ji yana zagaya illahirin jikin sa ,
Tundaga kan yatsar kafar ta taji tashin tsikar jikin ta , da wani yanayi da ya tsinka gudun jinin jikin ta , irin yadda bata taɓa ji ba a rayuwar ta , bakiɗayan jikin ta babu kuzari ,
Ganin shirun su ya tsawaita ya sa Mama ta raba ganin ta a tsakanin su , kafin ta ɗan turo baki ,
Papaa , baka ce kitson mama yayi kyau ba ??
Cikin dai-daita nutsuwar sa ya janye hannun sa daga kan ta ya janyo Mama Zuwa jikin sa ,
Kitson Maman Mama yayi kyau sossai
très belle .
Batare da ta ƙara daƙiƙa guda ba ta miƙe , tana nufar hanyar ɗakin hajja , zuciyar ta na cigaba da tsananta bugu , cikin kowanne takun ƙafafunta take jin idanun sa na yi mata rakiya .
9:30pm
Falmata ta sake muskuɗawa tana rufe bakin ta daga gajerar hamma da take yi akai-akai saboda bacci da ya fara cin ƙarfin ta ,
Ita bata kaiwa dare sosai take yin bacci a yawancin lokuta ƙarfe takwas da rabi na dare sun yi bacci ita da Mama , shiyasa yau da hajja ta buƙaci son suyi magana ta zo kuma ta tadda ta tana shafa'i da wutiri , bayan ta idar kuma ta ɗora da addu'o'i , duk sai zaman jiran ya gundure ta bacci yake kawo mata samame ,
Falmata , Falmata . Ko kin yi baccin ne ?
Na'am hajja idona biyu .
To taso ki zo nan kusa da ni magana nake so muyi ,
a hankali ta taso ta taho inda take jin tashin muryar hajja ta zauna daga gefen ta bisa dardumar sallah .
Fatima ki nutsu da kyau ki saurareni , da kunnen basira , kin ga wannan tafiyar da za kuyi ke da Mijinki tamkar wata babbar dama ce Allah ya baki da za kiyi ƙoƙari ki dai-daita zaman ku ke da shi , ki ƙarbo martabar ki ta ɗiya mace , cikakkiyar matar aure , ke yanzu ba yarinya ƙanƙanuwa bace ba , da za'a zauna ana yi miki bayani dalla-dallah baƙi da fari akan aure , shekaru biyar ana cikin na shida da yin auren ku , lokaci yayi da yakamata ku kawo ƙarshen wannan zaman kai da ƙafar da kuke yi a tsakanin ku , ku haɗa kai ku rungumi junan ku cikin inuwa da alfarma irin ta aure ,
Ke kece mace bance ba ki bada kan ki ba , amma ki yunƙura kiyi hoɓɓasa cikin dabarun ki na ɗiya mace da Allah yayi miki baiwa da su , ki karkato da hankalin mijinki kan ki , tunda jajayen sawun ki , da sauran damar ki , kina kuma tare da makaman yaƙin da zasu taya ki karɓo kambun ki tun kafin damar ki ta kufce miki , futsanci , jin kai , halin ko inkula da miji ba naki bane , yanzu anwuce wannan zamanin , zamani ne muke ciki na tarairayar miji a gatata shi ta yadda za'a masa riƙon tsauri da kufcewa zata masa wahala , kin dai ji na faɗa miki .
turai zaku je , kiyi ƙoƙari ki sau jiki , ki shige masa , ƴan kananun kayan nan da yace ana saka su a can ki sa ya kawo miki su dayawa kullum ki dunga yi masa ado da su , daman ga ki da kyakkyawan jiki.....
Ƙananun kaya fa kika ce hajja ?
Falmata ta katse ta tana yamutsa fuska .
Eh su nace to meye ba mijinki bane ? Wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗi ? Cewa nake kowa a garin su yake sawa ? To ke meye laifin ki idan kin yiwa mijinki ado da su ? Ji min rashin wayo .
Ta mula kafin ta cigaba da cewa :
Ƴar rangwaɗa da kisisina irin ta mata dunga yi masa , ki raba kan ki da ƙwalafacin Mama ki fara tunanin hanyoyin da za ki bi ki faranta ran mijinki saboda kin ga dai dai-dai gawargado shi yana nuna miki kulawa ke kece kike ƙin bada haɗin kai , to ki sake zane tun dundumin ki da danshi , shi mijin mace huɗu ne .
Ga ƴan magunguna nan na karɓo miki su musamman a wajen uwar zainaba , ta tabbatar min da ingancin su su ma zasu taimaka miki ƙwarai da aniya .
Anya hajja idanun nawa kuwa magungunan nan zasu min aiki ? Amma dai ba na sawa a ido bane kin san fa a asibiti sun hana ni zuba magani a ido ,
Mts' ana raba ki da kiwon awaki kina kyalla ta haihu , wanne maganin ido kuma ?? Wannan maganin gyara tsakanin ku ne ke da mijinki , idan kika daure da shan su suma zasu taka rawar gani wajen karkato miki da hankalin sa .
Ni zan dunga sha ko shi ? Nifa bangane bafa hajja .
Yo ina kuwa zaki gane ana nuna miki gabas kina bauɗewa yamma , kina girma kina sake shiga daji ., maganin mata ne .
Maganin mata ?
Ta maimaita da sigar tambayar
Eh
hajja ta amsa tana dangwara mata kullin maganin a hannu ,
Karɓi ki sa a cikin akwatin tafiyar taku , da madarar ruwa ko ta gari ake shan su ,
Taɓe baki falmata tayi ,
Tana ciro Envelop daga hijabin ta ,
Hajja ga hotunan Mama din an karɓo ɗazu Baban ta ya bata ta kawo min,
Karɓar envelop ɗin tayi ta zaro ƴan madai-daitan hotunan Mama da aka ɗauketa kwanaki uku da suka wuce da zummar hajja zata tafi da su Maiduguri ta kaiwa mutanen gida su ganta domin rabon su da ganin hoton ta tun tana ƴar shekaru biyu ,
Kai ɗanɗashi hotuna kuwa sun yi kyau kamar a ƙirata ta amsa tar-tar da su , ƴar wayayyar fuskar nan ta fito , ai kin ga hakan yafi a tafi musu da hoton ta su ganta ko dan yadda Rahima da Alhaji suke begen ganin ta .
Murmushi tayi , jin daɗin Hajja ta yabi 'yarta
Hajja kar ki manta dan Allah da saƙon gaisuwata , ga Baba , Yaya dakta , Rahima , kai kowa da kowa dai hajja , ki miƙa musu gaisuwata tare da fatan alkhairi .
Insha Allah kuwa duk zasu ji Falmata , kin dai ji duk abubuwan da na faɗa miki ko ?
Eh duk naji Hajja ,
To ki dai yi amfani da cewa ta , idan Allah ya yarda za ki ga amfanin sa .
To Hajja .
Ƴar dariya Hajja tayi, to Allah shi sa idan kun dawo nayi farin ganin gamdakatar da sabon ango ko kuwa sabuwar ƙawa .
Falmata ta yunƙura ta miƙe tsaye , tana cewa
Aina kenan Hajja ? Ko daga can za'a kawo miki ɗan turawa ? kai kai kai Hajja baki da dama .
Saƙare Hajja tayi bakinta buɗe , sai kuma ta gallawa Falmata harara .
Kinci gidan ku da sauyawa zancena launi , ƴar nema ai nasan sarai kina fahimta ta da gangan kike bauɗewa , oho ni dai na faɗa miki kowa rai yayiwa daɗi ai bayan me shi ne .
tana ƴar dariya ta ƙarasa barin ɗakin , kalaman Hajja na kutsawa cikin tunaninta tana ɗora su a mizanin nazari .
Washegari
Da farar safiya direban da zai kai Hajja Nigeria ya iso , daman da shirin ta tsaf , dan haka babu wani jinkiri aka fito da kayanta aka sanya su cikin mota ,
Tare da rakiyar Biyamuradi , Falmata da Mama suka ƙaraso jikin motar sallamar bankwana suka yi , Hajja ta shige mota direba ya tada motar suka miƙa hanya Mama tana ɗaga mata hannu .
Allah ya kiyaye hanya Hajja ta
Falmata ta furta a sarari tana jin yadda kewar ta ke fara kamata , "sabo tirken wawa ',
Muje cikki Fatima kafin zouwar le chauffeur mu tahi I'aéroport .
Hannun ta cikin na Mama wacce take ta zuba surutu suka juya zuwa cikin gida ,
kai tsaye ɗaki ta shige ta zauna a bakin gado , tunaninnika suka yi mata dirar mikiya , kewar ahalinta na kassara duk wani karsashi nata , shekaru biyar ɗin basu zo mata da sauƙi ba , ba kuma sun rageta da kome ba wajen jin ƙauna tare da muradin sake ganin wani jinin ta a duniya bayan Mama ,
duk kuwa da cewa ita ɗin ta kasance daga cikin jajirtattun mutane masu yaƙi da damuwar su, tare da danneta su binne ƙarƙashin ran su , su yunƙura wajen gina rayuwar su a yadda ta zo musu ,
ba domin ƙarfin zuciyarta ba da tuni damuwar halin da ta tsinci kanta ciki sun kaita ƙasa .
A hankali irin nata akwai hangen wani ƙalubale da take yi wanda take hasashen zai iya ɓullowa cikin rayuwar su ita da Mama ,
daga dangin Biyamuradi , wanda har kawo yau da Mama tayi shekaru a duniya da yake dai-dai da shekarun auren su babu wani dangi nasa ɗaya da ya taɓa zuwa wajen su , ya gan su .
Shi kaɗai suka sani , duk kuwa da yana ikirarin cewa yana da iyaye da danginsa makusanta , to ina suke ? Meyasa basu taɓa zuwa inda suke ba ko su su ziyarce su ? Shin menene aboye wanda su basu kai ga sani ba ? Tsakanin ƙarya da gaskiya wa ake yiwa wasan ƴar ɓoye a tsakanin su da dangin sa ? Tabbas akwai lauje cikin naɗi .
Sai dai koma menene a shirye take tsaf da taryar sa , zata yi kome domin ta bada kariya ga Mama , ƙuɗirinta bazai taɓa sauyawa ba muddin tana numfashi ita zata cigaba da kasancewa garkuwa ga Mama .
Ya jima yana tsaye daga dokin ƙofar yana duban ta , a tsawon zaman su da shi da ita koyaushe yanayi ɗaya yake hangowa a fuskar ta idan bata san da wanzuwar sa ba a guri , "damuwa" tana da damuwa wanda yake danganta damuwar ta ta da kansa .
Yana sane da cewa shi da ƴar sa sunyi kutse tare da yin karan-tsaye cikin rayuwar ta , ba kuma tare da suna amfanar mata da kome ba .
Anya yana yi mata Adalci ??
Gyaran murya yayi da ya sa tayi firgit!
Tana gyara zaman hijabin kanta ,
Fatima tasso le chauffeur ya zou .
Jakar kayan su uku babbar ƴan kayan cimaka ne a cikin su da sauran ƙananan tarkacen matafiya , ƙananan biyun suturun su ne a ciki .
A shirye suke tsaf , Falmata tana sanye da doguwar riga ruwan sararin samaniya me ɗan nawi ta ɗaura mayafin rigar akan ta ( tayi ɗankwali da shi ) da ɗan madaidaicin hijabin ta , takalman kafafun ta marasa tudu sun shiga da hijabin ta kalar ruwan hoda me haske ( baby pink )
Mama anshirya ta cikin ƴar riga iya guiwar ta da dogon wondo kanta rufe da hular saƙa me nawi mahaɗin safar ƙafar ta dake sanye da rufaffun takalman yara .
Biyamuradi ya riƙo hannunta da shima yake shirye cikin shigar kwat da wando ( suit ) ruwan ƙasa , ita kuma ta riƙe ƴan ƴatsun Falmata , sun sanyata a tsakiyar su suka fito farfajiyar gidan , Biyamuradi ya kulle ƙofofin gidan bayan ya kashe duk wasu na'urori masu amfani da lantarki .
tazarar ba wata me yawa bace tsakanin su da farfajiyar tashin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa ( Diori Hamani International Airport )
Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci suka isa , bayan Bayan bin duk wasu tsare-taren da ya kamata matafiya masu tsallakawa ƙasashen ƙetere suyi tare da zaman jiran dai-daituwar jirgi da ya ɗauke su tsawon awanni uku da rabi ,
Biyamuradi Youssouf tare da Falmata da Mama suka bi sawun takwarorin su masu tafiya zuwa United States of America , a sawu na farko suka taka matakala , kafaɗar sa ta dama ɗauke da Mama wacce ta sarƙafo hannayen ta a jikin wuyan sa , ɗaya hannun nasa ya zare daga cikin na Falmata da tunda suka shigo airport ɗin yake kaffa-kaffa da ita yana riƙe da hannun ta , duk kuwa da yadda take yawan mutsu-mutsu da hannun tana son zamewa amma ya ƙi kulawa bare ya bata dama , ya maida hannun sa bisa ƙugunta tare da matso da ita jikin sa , a hankali yace da ita ,
Fatima ki kulla da kyau ki saurari takun ƙafa ta bissa matakala muke ,
ba tare da ta amsa ba ta gyaɗa kanta , tana jin yadda tsikar jikin ta ke miƙewa .
Cikin jerun kujerun first class suka yi mazauni akan kujerun su masu ɗauke da numbobin su da suke fuskantar juna , sai ɗan teburi a tsakanin su , bayan zaman su ya yunƙura tare da ɗaurawa Falmata seatbelt ɗin ta ya koma ya zauna tare da ɗaurawa Mama nata , bai tsimaya ba ya ɗaura nasa .
A hankali ya kai hannun sa ya kamo hannun Falmata da yake kan teburin gaban su , ya damƙe hannunta guda cikin nasa dai-dai lokacin da zazzaƙar muryar shugabar masu dauke da alhakin kula da walwalar mutanen cikin jirgin "Chief flight Attendant ," ta karaɗe cikin jirgin ɗauke da sanarwa da take cewa :
“Ladies and gentlemen, this is Rose jackson and I’m your chief flight attendant. On behalf of Captain Mike Abraham and the entire crew, welcome Turkish Airlines flight non-stop service from Niamey Niger Republic to Washington DC United States of America.
Our flight time will