Showing 15001 words to 18000 words out of 411050 words

Chapter 6 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14372

jim mai martaba yayi bayan kammala jin dukkanin kalaman uwargidan sa ," sosai yaji daɗin kyakkyawar niyyar ta sai dai yadda ta ture Al'amarin bayan bayyanuwar maimouna ya sanya shi jin wani iri tamkar dai akwai sautin son kai cikin lamarin nata ," sai dai yayi saurin kauda zargin daga ransa akan sanin da yayi a duniya idan ana kirga masoyan siyama hajiya umma tana daga sahun farko ƙwarai yana alfahari da ita akan irin kyakyawan riƙon da tayi wa ƴar kanwar sa , " dan haka yace idan har ita siyama ta amince da shi youssof ɗin ya zama dole ga youssof ya auri siyama a matsayin matar sa ta biyu shekara guda bayan auren sa da maimouna idan Allah ya yadda ",

Nan take maɗaukakin farin ciki ya bayyana akan fuskar hajiya umma ,' tana mai sake jaddada masa da ƙaunar da ita siyama ta lura tana yi wa youssof ɗin tun shekarun baya ," nan dai mai martaba ya tsaida batun auren siyama da youssof sai dai ya nemi hajiya umma da ta bar batun nan a tsakanin su ,"saboda gujewa ƴan kai-kawo ', .

*Mairambiri Borno Nigeria*

Hasken ranan da ta ɗago ta fara ɗan zafi ita ta sanya ta fara motsi , kafin ta buɗe dogayen manyan idanun ta da suke farare tas tas , da sauri ta miƙe daga kwanciyar da take a cikin taɓon da ya cakuɗe da ruwan da ya kwanta a cikin ƙonanne ɗakin nasu wanda wuta ta riga ta ƙona azaran saman ɗakin ," da sauri ta fara lalube gefe-da-gefen ta , jin bata ji almun mutum a ɗakin ba ya sa ta miƙe tsaye ta fara laluben hanyar fita tare da kiran sunan ƴar uwar ta "yakaka "yakaka " santsi ne ya kwashe ta suuu ta tafi ta faɗi dabas a bakin kofar ," bayan ta ya bada ƙara ƙaƙas , " wani kuka ne ya taho mata a lokacin da wani mugun tsoro ya ɗarsu a ranta koh dai ƴan tawayen boko haram sun dawo ne jiya ? Sun tafi da yakaka ," tunanin hakan ya sa taji wani karfi ya zo mata ta yunƙura da karfin ta ," ta miƙe ta fara tafiya a cikin ruwan da ya cika tsakar gidan nasu da ƙasa bata kai ga shanye sa ba ',

Cigaba tayi da ƙwalla kiran sunan yakaka ' yakaka ' yakaka , ruwan hawaye yana me cigaba da ambaliya akan fuskar ta da karfi take jefa kafar ta ba tare da tana laluben gaban ta ba burin ta kawai ta tafi neman ƴar uwar ta ɗaya da ta rage mata," ji tayi ta kaiwa bango karo tayi taga-taga ta tafi da baya ta sake faɗuwa," da gudu take jin takun tahowar mutum kafin taji sautin muryar ta itama cikin firgici tana ƙwalla kiran sunan ta 'falmata 'falmata falmata'

Da gudu ta shigo gidan ,"wurgi tayi da ledar da take hannun ta tare da ƙarasawa gurinta zuwa lokacin ita ma kokarin tashi take tana mai sake kiran sunan "yakaka ', ɗago ta tayi tare da rumgume ta cikin jikin ta ,' itama kamkame ta tayi ," kafin su dukkanin su biyu su saki juna suna masu haɗa baki gurin tambayar junan su,'
"Falmata baki ji ciwo ba koh ?
Yakaka ina kika je babu abun da ya same ki koh ?
Banji ciwo ba yakaka ina kika tafi kika barni kin sa hankalina ya tashi kar ki sake tafiya ki barni yakaka ,"falmata ta furta hakan tana me laluben fuskar yakaka ,"

Hannun ta kai gami da share mata hawayen da suke gudu har yanzu akan ƙuncin ta ,"kafin cikin ƙarfin zuciya tace kiyi hakuri kanwata lokacin da gari ya waye naji wucewar mutane ɗai ɗaya hakan ya sa na lallaɓa na leƙa anan naga wani mutum shi ɗaya da gudu zai wuce shine na bishi nima ina tambayar sa koh ya ake ciki a gari ," shine yake gaya min shi hanya ce ta biyo da shi ta nan ƙauyen mu ,'daga ƙaramar hukumar Bama yake ," a yau suka wayi gari da afkawar ƴan tawayen boko haram a yanzu haka sun farma ƙaramar hukumar Bama suna ta kisa ,"irin dai yadda suka yi anan jiya ", mutumin ya tabbatar min da gwara na gudu domin ƴan tawayen boko haram zasu iya dawowa su mamaye dukkanin ƙauyukan da suke tsakanin Bama da Konduga tun da sun riga sun mamaye garin bama ", na tambaye shi to ina zamu ? Shine ya ce min ance wai a cikin Birnin Maiduguri gwamnati ta tanadi wurin da mutane irin mu ƴan gudun hijira zamu zauna a kula da mu kafin a yaki ƴan tawayen boko haram ,"

Tashi mu tafi falmata kar mutumin nan ya yi mana nisa kin ga mu ba mu san hanyar Maiduguri ba bamu taɓa zuwa birni ba ," zame hannun ta da yakaka ta kama tayi kafin cikin muryar kuka ta fara cewa "yakaka ni babu in da zan tafi , yakaka ba mu san inda su mama suke ba , idan muka tafi kuma su mama suka dawo neman mu fa ? Mu zauna yakaka mama zata dawo neman mu zata dawo ta tafi da mu inda ta ɓuya ,"

Share ƙwallar idon ta tayi kafin ta ce falmata su mama fa su ma sun tafi Maiduguri suna jiran mu a can ," da zasu dawo ai da tun jiya zasu dawo idan muka zauna anan koh ƴan tawayen boko haram basu kashe mu ba wuya da yunwa da kishirwa zasu kashe mu ," miƙa hannu tayi ta kamo baƙar ledar da ta shigo da ita wacce take yawo akan ruwan da yake tsakar gidan ," kin ga wannan ma tsintowa nayi a hanya wata kaza tana ta so ta fasa ledar ta kasa shine na bita na ƙwace" biredi ne a ciki ki ƙarba ki ci mu tafi falmata," ta karasa zancen da sigar rarrashi ,"

********************

Hannun su sarƙafe da na juna suke tafiya ," bayan sun fito daga gidan nasu kowaccen su tayi shiru da abun da take saƙawa a cikin ran ta .

A hankali yakaka ta waiwaya tana me kallon kofar gidan su ," sosai ta tsirawa gidan ido tamkar me son kirga adadin yawan bulon da akayi amfani da shi wurin ginin gidan ," gizo idanun ta ya fara yi inda ta hango mahaifin ta ya fito kamar yadda ya saba hannun sa riƙe da hular sa , gefe guda ita ce a tsaye hannun ta riƙe da buhun su na zuwa gona daga bakin kofar kuwa mahaifiyar su ce tana ɗaga musu hannu kamar dai yadda ta saba ," hawayen idanun ta ne suka gangaro gami da ɗiga akan kafar falmata ɗan jijjiga hannun ta da yake cikin na yakaka falmata tayi kafin ta ce mu tafi mana yakaka,"

Mu tafi falmata cewar yakaka wacce ta ke bin dukkanin ginin unguwar su da kallo hotunan al'amuran da suka gudana tun daga tasowar ta a cikin unguwar suna ta wucewa ta cikin tunanin ta ," wata irin kewar mahaifarta tana mamaƴar ta tana jin tamkar ta tafi kenan ," tana jin tamkar karshen ganin ta da gidan su da garin su kenan ," gefen zuciyar ta tana jin wani sabon karfi tare da karban sabon sauyin da rayuwa ta zo mata da shi ,"yayin da take jin nawin girman da ya hau kan ta na rike kan ta da kanwar ta falmata yana kama ta,' sai dai tana jin kome runtsi da Wahala zata kula da falmata ko da ita zata rasa rayuwar ta," miskin falmata ,"

Taku Falmata ta fara yi tana me jin yadda duhu yake mamaye zuciyar ta kamar dai yadda duhun yake a zahiri a idon ta ," tana jin duk wani farin cikin da ta san ta samu daga lokacin da tayi wayo zuwa yau yana barin jikin ta ,' wani irin ƙunci yana mamaye cikin ran ta ," tana jin kuncin yana ƙaruwa da dukkanin wani takun ta guda ɗaya da take yi da niyyar barin garin su mahaifar ta , zuciyar ta tana cike da tsoron sabuwar rayuwar da zata fuskan ta alhalin tana makauniya a garin da bata da kowa bata san kowa ba sai ƴar uwar ta ," tsoro sosai ya ɗarsu a ranta " , sai dai wani sashi na ranta yana faɗa mata zata dawo watarana , wataran zata dawo garin su mahaifar ta , zata sadu da mama da sauran kannen ta ," bata san lokacin da wani matsanacin kukan da yake cike da tsoro da kuncin zuciya ya kufce mata ba ,' kuka take bilhaƙ ,"

Matsa hannun ta yakaka take yi alamun rarrashi domin a zuwa yanzu ita ma bata da karfin zuciyar rarrashin falmata domin tana da tabbacin tana buɗe baki kukan zuciyar da take yi zai bayyana a zahiri ," ita ma bukatar rarrashi take tana bukatar matallafin da ko da ba zai taimaka mata da kome ba ," zai furta mata kalmar ZAKI IYA YAKAKA,

Hanyar da mutumin nan ya gwada mata ita su yakaka suka kama," suna tafe basa jin motsin kowa sai kukan tsuntsaye ," ɗan turus yakaka tayi ganin hanyar bakin jeji sosai ta kawo su ," jin sun tsaya ne ya sanya falmata wacce ta fara gajiya tace yakaka har mun kawo Maiduguri ne ? Cikin sanyin murya yakaka tace falmata gani nayi hanyar da muke tafiya a kan ta ta kawo mu bakin jeji ," jin batun jeji ya sanya falmata sake cukumo rigar yakaka tare da cewa mu koma kawai yakaka ," na faɗa miki daman kar mu taho ,"

Jin takun tafiya tare da hayaniya kamar har da kukan yara da suka ji shi ya sa su saurin juyawa " wasu gungun mata (sun fi su goma ) tare da yara da namiji guda ɗaya suka hango ," bisa ga dukkan alamu su ma a jigkace suke daga su sai kayan jikin su ," wucewa suka yi ta gaban su ba tare da sun ko kula da su ba ," cikin sauri yakaka ta saki hannun Falmata tare da cewa ", bari na tambayo su koh su ma maiduguri suka nufa ," da ɗan gudu ta cimma su saboda saurin da suke zabgawa cikin harshen su take tambayar su ," ko maiduguri za su ?" Ba tare da sun waiwaye ta ba ɗaya daga cikin su ta bata amsa da ",Eh ",

Da gudu ta koma baya gami da kamo hannun ƴar uwar ta tana jaan ta tare da cewa zo mu tafi falmata mun samu abokan tafiya waɗan nan mutanen su ma maiduguri suka nufa ,' ita dai falmata bata ce ƙala ba ta bi yakaka suka faɗa jeji tare da bin bayan mutanen nan da har sun fara yi musu nisa cikin duhun ciyawa ,"

Doguwar tafiya suka yi sosai cikin ƙungurmin dajin nan da yake cike da itatuwa da ciyayi gami da ƙayoyin da suke ta faman huda musu takalman su suna sukar kafafun su, ba sa cewa ƙala a tsakanin su ," har zuwa lokacin da rana ta ɗan gota tsakiya alamun azahar ta yi ", namijin ciki shine ya basu umarnin tsayawa a dai-dai wani wurin da ruwan sama ya ƙwanta yayi kamar ƙaramin kududdufi " , cewa yayi a huta a sha ruwa sannan ayi sallah a cigaba da tafiya ,"

Yaraf ,'duk suka zazzauna wasu ma kwanciya suka yi warwas a ƙasa ,kallo ɗaya za'a yi musu a fahimci tsabar gajiya da yunwa a tare da su ," yaran ciki kuwa daman tuntuni suke kukan yunwa da kishirwa dan haka ko da su ka ga ruwan nan , nan take suka nufi wurin wasu suka sa tafukan hannayen su biyu suna ɗebo ruwan suna sha wasu kuwa bakin su suka sa a kan ruwan suna sha ",

Yakaka da falmata suna cikin waɗanda su ke shan ruwan da hannayen su ,ɗauro Alwala su ka yi bayan sun sha ruwan ," su ka kuma jira sauran matan su ma su ka zo sha ruwan tare da ɗaura alwala ," namijin ya jaa su jam'i haka a cikin dajin ,"

Ƙarar wucewar wani abu me tsananin karfi da matsanancin ƙara da yake barazanar kashe musu dodon kunnuwa shi ya sanya a firgice ! Su dukkanin su, su ka ɗaga kai sama ba tare da sun sallame sallar da su ke ba ," yaran ciki kuwa nan take su ka fasa kuka tare da ƙanƙame iyayen su

Shawagi wannan abun da wasu daga cikin su , su ka ce "jirgi ne " ya cigaba da yi ," yayin da su kuma su ke tsaye carko carko , kawukan su a ɗage suna hango jirgin da yayi ƙasa ƙasa da har su ke iya ganin launin sa da yake koren kala , ruwan madara da kuma ruwan hanta "(coffee),"

Falmata lalubo hannun yakaka tayi tare da riƙe ta gamgam cikin karkarwar murya tace yakaka menene shi jirgin ?

Basu yi aune ba kawai su ka ji an saki wani abu kamar bom ," wanda ya faɗo kurkusa da mutumin nan da yake jagorar tafiyar su tare da wasu mata biyu da suke tsaye ,' nan take su ka tarwatse jinin su ya watsu a jikin sauran su ,"

wani irin kururuwa su ka yi a tare da yake nuna tsantsar firgicin su ," karo suka fara yi da juna cikin gigicewa suna masu neman hanyar gudu jin yadda jirgin nan ya sake sakin wanna abun da basu kai ga fahimtar harsashi ne ko kuwa bom ?,"

Fisgar hannun Falmata, yakaka tayi wacce take ta faman waige-waige tare da ihun tambayar yakaka me yake faruwa ? Ba tare da yakaka ta bata amsa ba ta fisge ta cikin ihun kukan da ƙarar jirgin nan ya dusashe ƙarfin sautin take cewa mu gudu Falmata idan ba haka ba zamu mutu ,"

Takawa su ke da matsanancin gudu suna jefa ƙafafun su wanda ko takalma babu "domin basu samu damar sanya takalman su ba " wurin da duk suka tsinci kan su nan suke jefa kafa basa duba gaban su bare su waiwaya baya ,"wasun su kuka da ihu suke yayin da tsiraru daga cikin su suke addu'a ," gudun ceton rai suke cike da tsananin tsoro tare da tashin hankalin jin kamar ƙarar jirgin nan na bin su  ,"

Cikin tsananin gudun da su ke ne yakaka taji hannun falmata da take riƙe da shi gam-gam suna gudun tare ," hannun ta ya fisge daga cikin nata lokaci guda kuma taga falmata tayi ƙundubala ta tafi gaba ɗaya ta faɗi ta gaba fuskar ta ta bugu da ya sa ba shiri ta saki wani irin ihun azaba tare da ƙwalla kiran sunan Allah ,"

Cikin kaɗuwa yakaka wacce har ta yi gaba saboda matsanancin gudun da suke ," ta dawo da baya da gudu gami da durƙusawa ta tallafo falmata wacce hancin ta da bakin ta ke fidda jini ," sai dai wata ƙarar da falmata ta sake saki a lokacin da yakaka take koƙarin ɗago ta ya sanya babu shiri ita ma yakaka ta fashe da matsanancin kuka ,"
Falmata sannu Dan Allah ki tashi
" ta furta hakan tana me gogewa falmata jinin da ya bata mata fuska da ɗankwalin kan ta da ta zame lokaci guda kuma tana me ɗaga kanta sama tare da yawata idanun ta a sararin samaniya cikin tsammanin ganin jirgin sojojin nan ,"
Ƙafata yakaka ƙafata ta maƙale a rami wayyo Allah na yakaka zan mutu ,"
Falmata ta furta hakan a lokacin da ta ruƙo ɗayar ƙafar ta, take ƙokarin zaro ƙafar daga wani ɗan ramin da yafi kama da na "ƙurege" ko kuwa dai kananun dabbobi dangogin sa ",

Cikin tashin hankali yakaka ta sake fuskar falmata gami da miƙewa ta koma ta wurin ƙafafun ta ,"kokarin zaro ƙafar ta fara yi ,"idanun ta suna zubar hawayen tausayin kanwar ta da ya sa ta kusan mance halin tsaka mai wuyar da suke ciki ,"

A gigice ta ɗago kan ta ganin wani hannun da tayi ya kama kafar falmata "cikin taya ta kokarin zaro kafar ,"

Ɗaya daga cikin abokan tafiyar su ce ," ita ma yarinya ce wacce zata iya girmewa yakaka da kadan ",

Da karfi su ka samu nasarar fusgo kafar falmata wanda hakan ya sa yakaka tayi faɗuwar ƴan bori akan ciyawar farar ƙayar da ta soki bayan ta ya sa ba shiri ta sake zabura ta miƙe gami da rugowa ta ɗaga kafar falmata wacce tayi futu-futu da ƙasa," ta ɗora akan cinyar ta ,"lokaci guda tana tambayar falmata kafar bata ji ciwo ba koh ," ?

Yakaka kamani na tashi mu gudu," Falmata ke furta hakan a lokacin da take laluben hannun yakaka fuskar ta tana bayyana tashin hankalin da take ciki ," da sauri yakaka ta miƙe bayan ta sauke kafar falmata daga jikin ta ,"yunkurawa tayi tare da ɗago ta ," ganin haka ya sa yarinyar da take tsaye a gefe tana kallon duk abun da suke ta matso gami da kai hannu ta kamo ɗayan hannun falmata da nufin taya yakaka ɗaga ta ,"

Wani irin zamiya falmata tayi tare da warce hannun ta daga jikin yarinyar wanda hakan yayi sanadiyar komawar su ƙasa da ita da yakaka ,a lokaci ɗaya ta kanƙame jikin ta wuri guda tare da cewa ,"
Yakaka waye a wurin nan tare da mu ? Aljanu ne koh ?

Falmata wacce ta taya ni muka zaro kafar ki daga rami ce ɗaya daga cikin abokan tafiyar mu ........,"

******************

Kika ce kin san hanyar Birnin Maiduguri Yagana ? Tambayar da yakaka ta jefawa Yagana (abokiyar tafiyar su ) kenan lokacin da suke cigaba da tafiya ," sai dai saɓanin ɗazu yanzu a nutsen su suke tafiya ,"samun nutsuwar su ya samo asali ne daga fahimtar da suka yi jirgin nan ya tafi ya daina bin su ,"

Sai dai fa a yanzu zuciyoyin su cike take taf da tsoron ganin su uku ne rak a ayarin tafiyar su sauran duk sun watse kuma basu sake cin karo da ko guda daga cikin mata takwas da kananun yara biyar ɗin da suka rage

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login