Showing 69001 words to 72000 words out of 411050 words
Chapter 24 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
fuskar ta da tsadadden murmushin ta , dan haka yanzu ma da babasho yake kwala mata kira koh kallo bai isheta ba haka ta cigaba da tafiyar ta ,' shi kuwa ya bi bayan ta da kallo yana lashe leɓe tare da lanƙwasa ƴan yatsun sa cikin ransa yana fatan Allah ya kai damo ga harawa koh bai ci ba yayi birgima,",
Karo taji tayi da mutum wanda zurfin da tayi a tunanin ta ya sa bata ga tahowar sa ba ," da sauri tayi baya ,tare da durƙusawa ta ɗauko masa makullin motar sa da ya faɗi a hannun sa ta sanya bakin gyalen ta ta goge ƙasan jikin ɗan makullin bakin ta ɗauke da kalmar ban hakuri ta miƙa masa mukullin ba tare da ta ɗago kan ta ba ,
Miƙa wankakken hannunsa mai ɗauke da wankakkun fararen farata ƙal yayi ya karbi makullin agogon hannun sa na ta ɗaukar ido ,"hannun ta bi da kallo wanda kyaun sa da gogewar sa a tsafta irin wanda bata taɓa gani ba ya ɗauke hankalin ta , muryar sa ce ta dawo da ita daga shagalal da tayi cikin hausar sa ta bamarɗe yace ,"
", Ai ni ke da laifin ina gaugawa ban lura da ke ba yi mini afouwa ,"
Da hanzari ta ɗago kan ta jin muryar sa da ta yi kamar ta san ta , tana ɗagowa yana gifta ta sai tashin mabuwayin ƙamshin sa da ta shaƙa wanda ya sa ta jin tsaftar sa ta burge ta har ta waiwaya tana bin takun sa da kallo ,"
Har ta je ta amso aiken da aka mata tana jin ƙamshin turaren sa cike taf da hancin ta ," bayan samy baby ta ci indomie da soyayyen ƙwai ta cika cikin ta har ta barwa yakaka sauran ta cinye tas tare da wanke kwanon , ta tashi da niyyar fara gyaran ɗakin , samy baby ta dakatar da ita tare da cewa ta bata hankalin ta ," nan tayi mata bayanin jinin haila da ta fara da yadda ake wankan sa , ta kuma jaa kunnen ta akan ta kula kar ta yadda wani ɗa namiji ya ɗirka mata ciki kar ma ta kula kowa a yanzu idan lokacin fara harkar ta yayi ita da kan ta zata kaita a bata maganin hana ɗaukar ciki ta yadda zata ji daɗin cin kasuwar ta ba tare da wata fargabar yin ciki ba , nan dai suka ɗauki lokaci samy baby tana mata huɗuba wanda mafi yawan su ba na kirki bane , idan aka cire wankan hailar da ta koya mata a taƙaice babu wani abun kirki cikin sauran shawarwarin da ta bata ,'
Ki lura da kyau da lissafin kwanakin menses ɗin ki domin ta haka ne idan kin fara harka zaki gane lokacin da kike danger ɗin ki dan ki kiyaye harka a waɗannan kwanakin duk da dak zamu je a miki ƴan dabaru amma kau da bara sai ana haɗawa da zamiya ,"kin ga yau ɗaya ga wata kika fara duk inda wata ya kai shidda takwas zuwa goma zaki iya gamawa toh kwanaki bakwai da zasu biyo bayan kwana uku na kammala jinin al'adar ki sune ranaku mafi hatsari gare ki idan kin fara harka domin tabbas kina iya samun ciki idan kika sake kika yi koh da wasa da lawurjen namiji ne ehee ,sai ki kiyaye kin ji koh ?
Ba tare da yakaka ta fahimci mafi akasarin bayanan samy baby ba ta amsa da "toh" hankalin ta ya fi karkata ga son sanin wacce harka ce zata ɗora ta akai wacce har akwaj hatsarin samun ciki ?? Ita fa tana tsoron zancen ciki kowacce irin harka ce zata iya hakura da ita idan har zata iya yin ciki , toh amma tayaya ma ake samun cikin ?????? ( ta miƙa tambayar ga masu karatu 😂)
Cikin sanyin jiki ta koma bakin aikin ta inda duk take a takure domin gani take kamar kowa ya san tana fitsarin jini bini-bini ta leƙa ta kalli bayan siket ɗin ta ,kou kuwa ta shiga bayi tayi tsarki , duk a matse take jin kan ta , sai dai tata damuwar ta kau koh kuwa ace ganin damuwa kwance ɓaro-ɓaro akan fuskar falmata ya sa ta daina jin ta ta sai wani sabon tashin hankali tare da damuwar da ta fi ta farko da taji ya mamaye ta , sam bata ƙaunar ganin falmata cikin damuwa
Falmata nah ! faɗa min menene ?? wani ne ya zage ki ? Koh baki da lafiya ne , yunwa kike ji ?? Koh kina son wani abu ne ?? Koh jiya ɗan liti ya miki wani abun da ya ɓata miki rai ne ? Gaya min dan Allah menene
Ɗan guntun murmushin da daga ganin sa na ƙaƙale ne shi falmata ta ɗora a fuskar ta ,"
Yakaka ni babu wanda ya min kome kuma lafiyata ƙalau , bana jin yunwa ,"
Toh meye ne koh kin tuno da su mama ne ??
Da sauri falmata ta gƴaɗa kai tana me rushewa da kukan da tuntuni yake cin ta , sakamakon abun da ya faru da ita a wurin wani mutum wanda ɗan liti ya ɗauke ta jiya ya kai ta a matsayin shine ubanɗakin sa wanda yake bashi kayan daɗin da yake kawo mata tana cika cikin ta da shi ,"
Ita dai bata san ina ɗan litin ya kai ta ba domin a mota suka tafi ,
Duk da cewa ba gani take ba amma ta fahimci gidan da ɗan liti ya kai ta gidan me hali ne , domin maɗaukakin sanyin da ta ji a parlour da suka tadda mutumin har zuwa kan lallausar abun da aka zaunar da ita akai kujera zata kira abun koh gado ?? Ita dai bata taɓa zama a makamancin abu mai taushin sa ba ga wani fitinannen ƙamshi da ya cika wurin , bata ji ta fara tsorata ba sai da ɗan liti ya ɗibo wani abu mai matsanancin sanyi ya cusa mata a baki da ya umarce ta da ta buɗe bakin ta zai bata wani abu wai shi "ice cream" anan ta ji ta tsorata domin kuwa dawo da abun tayi ta tofar da shi saboda bata taɓa shan abu mai tsananin sanyin irin sa ba ,"
Mutumin da suka tara a falon ya buɗe ƙatuwar muryar sa marar daɗin sauti kamar fasasshiyar gangar ya dunga tuntsira dariya ɗan liti yana taya sa harda shewa ,"
Watau kachallah bai taɓa shan ice cream ba ?? Ai kuwa daɗi ya bar ka , toh liti bashi gasasshiyar kaza ya ci nasan dai koh daga kan dutse ya sauko ya san nama ,
Wata ƙatuwar cinya ɗan liti ya fisgo ya damƙawa falmata a hannun ta bayan ya miƙa mata kwalin lemun ,"five alive" a ɗaya hannun ,
Maza ɗan kachallari ci kaza ka sha lemu yaro ai ka zo gidan arziki duk wasu kayan daɗi da nake kai maka kana ci kana lashe baki "ya tsohon kare nan ne tushen sa kaɗan ne daga cikin ire-iren kayan maƙulashen da suke jibge a gidan nan yaro saki jiki ka ci arziki ka bar shi a inda ka gan shi ,"
Cikin sanyin jiki falmata ta kai cinyar kazar bakin ta ta gutsuri kaɗan tana taunawa ," zaƙin kayayyakin ɗanɗano irin na alfarma tare da zaƙin naman kazar suka haɗu suka sa kunnen falmata motsi har bata san lokacin da ta cinye wacce ɗan liti ya bata ba ,
tana tanɗe baki , ɗan liti wanda suke kus-kus da wannan ɗan tsurut ɗin mutumin shi ya lura da ita ya sake fisgo ɗaya cinyar ya ɗangwala mata a hannu ,"
ungo maza cinye har ƙashin ka tauna ka haɗiye , yau ta shiga ranakun tarihi a wurin ka ɗan kachallari ,"
Miƙewa ɗan liti yayi bayan sun gama kitsa abun da suka kitsa ,"
Ɗan kachallari ni zan ɗan je na dawo nan kusa ka jira...
Koh kafin ya ƙarasa abun da yake nufin cewa falmata ta miƙe zuruf ta dangwarar da sauran naman hannun ta '',
Ah ah mu tafi tare nima zan bika ,"
Haɗa ido ɗan liti da wannan mutumin suka yi , mutumin ya yiwa ɗan liti alama da ido akan ya tafi kawai zasu yi waya ,"
Saɗaf-saɗaf ɗan liti ya fita ya jaa musu kofar wanda ƙarar rufe kofar ya sa falmata wacce take tsaye tana jiran amsar ɗan liti ta farga da barin ɗan liti wajen ,"
Kuka ta sa tare da fara taku tana nufar hanyar da ta ji motsin rufowar kofar da ɗan liti yayi lokaci ɗaya tana jera kiran sunan ɗan litin ,"
Dariya ta ji mutumin ya kwashe da ita kafin ta ji ya fara tahowa inda take yana cewa haba ɗan kyakkyawan yaro kachalla menene abun kuka yi shiru yanzu ɗan liti zai dawo aiken sa nayi , kafin ya dawo zo muyi wasa ,"kafin ta ankara ta ji ya sure ta sama yana cewa ," A ɗaga sama anyi wa wada kwace 😂 ,"
Na so na baku ya fi haka , sai dai yawan cewa kuna jira da kuke yi , yasa na dakata anan kuyi manage da wannan sai mun hadu a shafi na gaba cikin yardar Ubangiji,"
A kan karo mutunci
#umm'muaz
#vote
#comments
#share with your Family and friends.Cikin sati biyu da tarewar su yakaka a gidan madam saly ,sun zama ƴan gari a da'irar ta yadda yakaka ta san ɗakunan manyan kilakai da ƙananun karuwan da suke unguwar saboda aiken ta da madam saly take wurin su , a gefe ɗaya kuma ta zama ƴar ɗakin samy baby , wacce bayan dawowar yakaka gidan madam saly ta gama nazarin yarinyar tsaf , ta gane bata san ma mai kalmar bariki take nufi ba kamar yadda da tayi zaton yakakar ƙaramar karuwa ce , sai ta fahimci ashe yakakan neman abun sawa a bakin salati take tare da wajen da zata sanya haƙarƙarin ta , dan haka sai ta jaa ta a jiki ta maida ta mai gyara mata ɗaki tare da yi mata ƴan kananun aike da aiki , ita kuma tana bata ƴan kuɗaɗe bayan jibgin suturun ta da ta fitar ta bata kwance , tun yakakan tana ɗari-ɗari ganin abun da samy baby tayi mata a farkon haɗuwar su , har dai ta zo ta saki jiki da ita , sosai take kyautatawa samy baby da ta riƙa a matsayin uwarɗakin ta , wacce take samun alheri tare da sakewa a wurin ta, domin a lokuta da dama har ƴar hira samy baby take zama su yi da yaks ,
Aikin gidan madam saly kuwa tuƙuru yakaka take yin sa domin gwanintar da take nunawa ya faranta ran madam saly da take ganin ta a matsayin ginshiƙin su cikin duniya a yanzu , bata da wani lokaci nata na kan ta sai na aikin burkutu wanda ba'a sanya ba ma yi take kamar su wanke dawa , juya ruwan dahuwar burkutun da kuma tace shi wanke kayan madam saly da gyara mata ɗaki , tun safe idan ta kama aiki sai dare karfe sha ɗaya take samun hutu ," wanda hakan ke matuƙar farantawa madam saly rai har take ganin wautar kan ta da farko, da ta so korar su ashe dai maganar ɗan liti dutse ,
Ga falmata ma sai sam barka domin kuwa har ɗan kumatu tayi ta sake mul-mul , sakamakon cika mata ƙundu da ɗan liti yake da cimar daɗi kullum dare kafin su kwanta bacci , ga kuma labaru masu sanya nishaɗi da yake bata har bacci ya ɗauke ta ,bata zuwa ko'ina daga ɗakin ɗan liti da yake daga wajen filin rawa sai cikin gidan madam saly da take aikin wanke-wanke kofuna tare da farantan aikin burkutu tsawon yini a cikin gidan , bata da wata matsala saboda duk lokacin da yakaka ta ɗan zagaya zata taho bakin fanfon da take zaune din-din a gefen sa ta shafi kan ta koh kuwa fuskar ta , ta kuma tambaye ta bata da wata matsala koh ? Nan zata amsa mata cikin farin ciki da ita bata da wata matsala ,
Haka zata sake komawa bakin aikin ta tana mai farin cikin sauyin rayuwar da suka samu , musamman farin cikin da take hangowa a fuskar ƙanwar ta wacce ɗan liti ya wadata ta da ƴan kayayyakin gonjo na ƴan matasan yara maza sa'annin ta fes-fes da ita hasken ƴar luwai ɗin fatar ta ruwan zuma yana bayyanuwa,
Ranar da suka kwana huɗu a gidan ɗan liti yayi mata kyautar kayan wanda daga ita har falmata kyautar bata wani faranta musu ba , saboda ƴan rigunan basu da wani girma kayan turawa ne , su kuma sun san kayan nan burguza burguza da falmata ke sanye da su sune rufin asirin su a kasantuwar falmata namiji saboda kayan ya boye ɗan tudun kirjin falmatan wanda suka fara tasowa tare da bunƙasa ,
Da kƴar yakaka ta shawo kan falmata wacce da farko ta tubure akan shawarar da yakaka ta kawo na falmatan ta dunga sanya riguna biyu bayan ta tamke kirjin ta da ɗankwali ,saboda boye tudun tare da yi mata gargaɗi kada ta yadda ta sauya kaya a gaban ɗanliti duk juyin duniya , ta kan ce
Kiyi hakuri falmata har mu ɗan tara abun da muka tara anan ɗin zuwa lokacin kuma mun san gari sosai idan ya so sai mu koma wani wurin da babu ƴan iska mu raɓa ki koma saka kayan mu na mata , kamar kowacce mace ina nan ina ware miki kayan ki cikin kayan da nake samu ,"
Ranar da ta fara ɗaure kirjin ta yini tayi tana fama da ciwon kirjin , amma da ta kwana biyu sai ta saba ta daina jin ciwon ,
Bata taɓa yin wanka sai sun tabbatar da ɗan liti ya bar da'irar wajen sannan zata yi wankan a gurguje yakaka ta raka ta ta sauya kaya tare da sake gyara mata ɗaurin kirjin ta wanda ya taimaka ƙwarai wurin boye halittun kirjin ta , sai dai salon takun tafiyar ta tare da tudun bayan ta ke sa samy baby tana yawan tsokanar ta da
"Kachallah me jikin mata ,"
tafiyar ka sai kace ta hamshaƙan mata , koh kuwa tace shege kachallah da kai mace ne da anyi manyan kaya a wurin ka ,"
Idan yagana tana wurin tayi ta sheƙa dariya ,wacce ita ma a yanzu sha'awar rayuwar su yakakan take , domin kuwa har kuɗi da suturu yakaka ta bata daga cikin wanda samy baby ta bata ,"
Haka kwanaki suka yi ta tafiya har suka samu wata guda da ƴan kwanaki a dafdalar wannan gidan , wanda zuwa lokacin yakaka tayi jazur wannan maɗaukakin hasken fatar ta ta ya sake bayyana dal tamkar fitila haka take a waje , ƴar kyakkyawar ƙaramar budurwa mai sanyi tare da yawan fara'a koyaushe cikin murmushi take , ko magana yakaka take haka zaka ga fuskar ta da yalwatattacen murmushi dasashin ta a waje , wanda hakan yake tasiri matuƙa wurin bayyana ƴan ƙananun kyaun ta wanda hasken da take da shi ya fi jaan hankalin mazan da suka fara ƙaraƙaina akan ta fiye da kyan nata ,"
Zuwa lokacin samy baby ta fara jaan ɗamarar wanke yakaka daga dauɗar datti gami da ƙazantar ƙauye a cewar ta yakaka haja ce me matuƙar tsada , wacce sayan ta sai alhajin da ya rufu ya tada kai , " sai ya so zama tamkar gasa a tsakanin ta da madam saly wacce ita ma take bada sumfurin tata kulawar ga yakaka domin ta farga gaba kaɗan yakakan zata zame mata hanyar samun arziki ,dan haka ta fara kokarin janye ta daga wurin samy baby da ta lura tana son kawo mata tsaiko domin kuwa ga alama so take ta fanɗarar da yakaka ta sanar da ita daɗin ƴancin kai kamar yadda ita take da nata ƴancin a hannu domin samy baby ba'a ƙarƙashin kowa take ba cikin magajiyoyin gidan , da karfin ta ta shigo bariki da kuma nawin aljihunta tare da gatan ta domin ba kukan yunwa koh na rashin wurin kwana koh kuwa na neman kuɗin zuwa asibiti zubda ciki ne suka kawo ta bariki ba , ƴar cikin ƙwaryar gari ce da gatan ta da kome iyayen ta ma manyan mutane ne sanannu , uwa uba bata da duhun jahilci domin kwalin digiri ke gare ta ," sha'awar rayuwar barikin take tare da taimakon matar uban ta wacce take sake ingiza ta , uwa uba shaiɗan da yake tsakiyar kan ta yana buga ganga ,
Gidan kakaf ba wata tsohuwar kilaki da take shakka , sai ma su da idan jarabar su ta busa sigari koh afa ƙwayoyi suka motsa , kuma suka laluba lalitar su suka ji wayam , su je wurin ta neman ƴan kuɗaɗe sanin da suka yi kaf cikin karuwan gidan ba wacce ta kai ta kama kuɗi , da kuma kyauta domin hannun ta a sake yake bata da rowa ,"
Ranar wata litinin da safe yakaka ta wayi gari da wani irin matsanancin ciwon mara wanda tun kwanaki biyu da suka wuce take jin sa kaɗan kaɗan amma ta daure ,
Har zuwa yanzu da take kan hanyar ta ta zuwa ɗakin samy baby domin ta gyara mata ɗakin ,bayan ta gama kintsa na madam saly kamar yadda ta saba kafin su duƙufa aikin sana'ar su ,"
A dudduƙe da jaan ƙafa ta ƙarasa cikin ɗakin samy wacce take kwance tana sharar bacci daga ita sai ƴar ficiciyar rigar bacci kan gadon duk a hargitse kayayyakin ta tun daga kan rigar mama da ɗan kafai duk a wurge a kan gadon , tayi ɗai-ɗai da kafafu gashin dokin da yake kan ta ya baje akan filon da tayi matashin kai da shi ," idan da sabo yakaka ta saba tadda ta a haka