Showing 132001 words to 135000 words out of 411050 words
Chapter 45 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
wuce nan domin kuwa faɗa ta dunga yi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba , wanda tun da yake da ita bai taɓa ganin tayi makamancin sa ba , duk kuwa da abubuwa dayawa da suka yi ta farauwa tsawon shekaru , a ƙarshe kuma ta rantse da Allah akan sai ta zo ita da mutanen ta na arziki wanda ta riga ta aika musu da goron gayya ta , idan ya so a kira hukuma su fidda su daga gidan ,! Ai ita ma tana da hakkin ta na uwa akan zainab ɗin .
Ganin taƙi sauraran ban hakurin da yake yi mata hakan ya sa shi miƙewa cikin sanyin jiki ,
Amne ! ni zan koma , Allah ya huci zuciyar ki ,
Amin
tace da shi tana kawar da kan ta gefe guda ,' tare da karkaɗa kyakkyawar kafar ta da ta ji ƙunshi zajir da shi har wani sheƙi yake yana ɗaukar ido akan farar fatar ƙafar ta ,
Langaɓe kai yayi ya tsaya yana kallon ta ,"
Banza tayi da shi domin tana jin ɓacin ran yadda a koyaushe yaran suke goyon bayan uban su akan ta tamkar ba ita ta haife su ba ,
Gajiya yayi da tsayuwa ya sake cewa
Na tafi amne.'
Ka gaida mutanen gida
tace tana miƙewa ta shige ɗaki
Bayan ta ya bi da kallo kafin ya jaa ƙafafun sa a sanyaye ya fice , ko da ya zo jikin motar sa ma kasa shiga yayi ya tsaya yayi shiru ran sa baki ɗaya a jagule yake duk wani nishaɗi nasa ya kau ,
Fuuuuuw ya ji wucewar mota da matuƙar karfi , ya bi motar da kallo motar ɗazun ce dai , kaɗa kan sa yayi yana jimami lokacin da ya ga kiris ya rage motar ta buge wasu yara ,"
Allah ya kyauta
ya furta a sarari yana shigewa cikin motar sa ,' ya jaa sannu a hankali ya bar unguwar !
*****
Tun safe Ƴan aiki da masu gyaran wurin da za'a yi taron wushe-wushe , suke kai kawo , yayin da masu dafa abinci ma basu zaune basu tsaye domin yin girkin taron baƙi , "tawagar gidan maza da shi kan sa ango da abokan sa da zasu iso a yau ɗin ,'girke-girke ake na alfarma ,
A gefe guda ƙawayen amarya ne zuwa ƴan uwan ta suke ta kai kawo tsakanin tata saloons da gidan domin yin kwalliya da gyaran jiki saboda kowacce so take ta burge so take ta jaa hankali , so kuma take ace ta fi kowa ," !
Amarya kuwa musamman aka ɗauko mai gyaran jiki da kwalliya daga tata saloons domin tayi mata nata shirin a gida ,'
Duk kai kawon da ake yi fiye da rabin hankalin samy baby bai tare da ƙawayen na su , ya tafi ne ga tunanin son sanin haƙiƙanin ina su yakaka suke da zama , domin kuwa a yanayin su na jiya ta hango rashin gaskiya tare da tsoro ɓaro-ɓaro akan fuskokin su ,
Tayi niyyar ta titsiye su su faɗa mata gaskiyar ina suke da zama yanzu ? A hannun wa suke ? waye ya jiɓanci lamuran su tare da cikin jikin yakaka ? A ƙarshe ta ji dalilin da ya sa suka gudu sannan da manufar yakaka na barin cikin jikin ta wanda yayi girma sosai yanzu ya fito ,"!
Sai dai ko alamar su bata gani ba tun da ta zo gidan ɗazu da safe , yau tazo ne da nufin kwana zuwa gobe da za'a ɗaura aure su juya tare da amaryar garin abuja inda a yanzu ta fi zama a chan saboda yadda harkoki suke gara mata sosai ta haɗu da manyan masu kuɗi suna sakar mata bakin aljihun su tana abunda ta ga dama , "
Sofi ita ce ƙawar samy baby ta ƙud-da-ƙud , sosai ta su ta zo ɗaya , wasu halayya ta su suka dace da na juna , kuma ita ce ma ta gayyato ta bikin zainab ɗin a matsayin ta na babbar ƙawar zainab kuma sannan ƴar uwa ta kusa ga zainab ɗin ,"
Tunowa tayi da rahima wacce ta zo tayi musu magana lokacin suna tare , ta ji ta kama sunayen su , ta kuma musu maganar da yake nuna ta san su sosai ,
dan haka a bakin ta zata iya jin wani ɗan bayani akan su yakaka , ko da kuwa inda suke da zama ne ,
domin ita sosai take son jan yakaka cikin irin rayuwar da take a ganin ta gata take so tayi mata duba da cewar su yakakan basu da wani galihu , dan haka gara su tsaya da kafafun su .
Ta maida duban ta ga sofi wacce tuntuni take zaune a gefen ta tana ta faman kiran doctor hamza yaƙi ɗaukar wayar ,
hankalin ta gaba ɗaya bai jikin ta domin tun da ta zo bai yadda sun tsaya sun yi maganar mintoci biyu ba , '
ko ta nace sun haɗu a hanya gaisuwar ta kawai yake ansawa ya wuce , a sarari yake gwada mata rashin kulawa tare da rashin ƙauna ,
amma ta gaza yin zuciya ta janye jikin ta saboda yadda zuciyar ta ta riga ta ginu da ƙaunar sa , duk wata harka da take da maza tana yi ne kawai dan jaraba ba wai dan kuɗi ko so ba ,
so ɗaya tak doctor hamza take yi wa , sai dai ta sani sarai shi kuma baya yi da ita , kuma ta sha alwashin dole shima ya so ta , ya kuma aure ta
sannan duk wata macen da tsautsayi ya sa ta shigo rayuwar sa da sunan so zata iya kome domin ganin ta cisge ta daga rayuwar sa ko da kuwa idan ta kama ta ɓatar da mace ne !
friend ,
Ni ina rahima ne ? Ƙanwar ku ? Ki kira min ita idan kina da number ta zan tambaye ta akan wasu ,"
Samy baby ta ce ga sofi haka ,"
Sai dai ga alama sofi bata ji ta ba domin cigaba tayi da latsa wayar da ba kome take yi akai ba ,illa tana kallon tsawon lokutan da ta share tana ƙiran hamza yaƙi ɗauka , a ƙarshe ma da ta ƙira yanzu jin wayar tayi a kashe ," ji tayi wani irin ƙunci ya mamaye ran ta tana ji kamar an hura wuta daga ƙarƙashin zuciyar ta ,"
Taɓe baki samy baby tayi gefe guda tana jin haushin yadda ƙawar ta ta liƙewa wannan ɗan uwan nata likita , yana ta faman walakanta ta alhalin ga manyan masu kuɗi suna rubibin ta ,ta na jaa musu aji ,"
Mtss ta jaa tsaki gami da sanya hannu ta zare wayar da take riƙe a hannun sofi ,"
Haba mana friend , ya kike bada kan ki irin haka ga ɗa namiji ? Kina bin sa yana walakanta ki , wallahi tun wuri kiyi wa kan ki faɗa , ni idan banda shan koko ɗaukar rai ban ga ma abun nacewa har haka agun wannan ustazun ba shi ba.....
Wani irin kallo da ta ga sofi tana yi mata da idanun ta da suka kaɗa suka yi jaa ya sa ta kasa ƙarasa maganar da take nufin cewa ,"
Samira ki san irin maganar da zaki dunga faɗa min akan doctor , kin san wallahi zan iya ɓatawa da kowa akan sa dan haka ki kiyaye ,"
mtss
samy baby tace tana ɗauke kai ,"
Dai dai lokacin da rahima ta hawo saman domin ɗaukar jakar kayan ta ,"
Yauwa rahima zo mana ,"
Na'am anty samira ,"
Ni ina yaran na jiyan nan waɗanda na ga kun gaisa da su , su biyu yakaka da falmata aina suke ne ? Ƙira min su mana !
Anty samira nima ban san inda suke ba fa ,
Oh na ɗauka anan kusa suke , ?
Ah ah .
Rahima ta amsa lokacin da take sunkutar jakar ta tana barin wajen ,
A sarari ta fara ƙunƙuni
Naƙi na ƙira muku su ɗin , ku sasu a gaba kuyi ta sasu aiki da aike kamar bayin ku ,ba kyau dai walakanta ɗan adam wallahi !
Ta cigaba da tafiya tana mita ,"
Sashin doctor hamza ta nufa wurin su yakaka , a kwance ta tadda yakakar ta miƙe , falmata na zaune daga gefen ta tana matsa mata kafafun ta da tace suna mata tsuku ,"saboda wahalar aiki da kai kawon da tayi kwanaki biyu da suka wuce ,"
Yau har sun ɗan yi kyaun gani daga jigatar aikin da suka sha ," tun safe basu fita a sashin ba rahima ita ta kawo musu abinci suka ci anan suka yi wanka , amma kayan jikin su suka maida domin rahimar tace musu su bari sai anjima idan an kusa fara wushe-wushe sai su yi kwalliya su je wurin .'
Da dariyar ta ta ƙaraso ,
Yakaka , fatima , wai anty samira tana tambaya ta ku nace ban san inda kuke ba ," kun san ta ne ? Nagan ku tare jiya .
Anty samira ? Yakaka ta tambaya tana miƙewa zaune ,"
Ko dai anty samy ?
Falmata ta sake tambayar ta ,
Ita , kun san ta ne ? Ai friends ɗin ta ke kiran ta samy baby ,
Tace wai kuna ina ,? watakila aiki take son sanya ku ,"
Shiru suka yi aka rasa mai ƙwaƙƙwaran motsi ," samy baby tana son kawo musu matsala cikin zaman su a gidan nan ,!
Yakaka ta katse shirun ,
Mun san ta mun yi aiki a gidan da take kafin zuwan mu nan !
Oho toh ina ga shiyasa take neman ku ashe ta san ku ne !
*****
Karfe ɗaya cif jirgin da ya ɗebo tawagar angwaye ya sauka a maiduguri international airport , tun a Abuja tafeedah yake gwada kiran layin youssouf domin ya sanar da su tasowar su , da lokacin da zasu iso domin ƙwarai suka ƙagauta da su ga juna bayan tsawon watanni takwas da suka yi rabo da juna , sai dai wayar tana ƙara ba'a ɗauka ne ,
ji yayi hankalin sa na neman tashi domin ƙarshen wayar da suka yi a daren jiya misalin ƙarfe tara na dare youssouf ya sanar da shi ya kusa shiga birnin maiduguri , yana kan hanya .
A maiduguri international hotel aka yiwa angwayen masauƙi yayin da iyayen kuma aka tafi da su wani babban gidan da ya kasance mallakin mahaifin su hamza ,"
Tun da youssouf ya baro gidan madam saly yake cikin halin gigita da ruɗani , dakyar ya dawo da kan sa hotel ɗin da ya kama ɗaki, ganin abun yake kamar mafarki , duk shirin da yayi kafin zuwan sa ya rushe saboda wacce yayi domin ta bata nan ta ɓata ba'a ma san inda take ba tukun ,"
gefe guda sabon gingimemen al'amarin da yake neman kutso kan sa dole cikin rayuwar sa na barazanar zautar da shi ,"cikin jikin ta da babu wanda ya danganta shi da nasa ,illa zuciyar sa da tunanin sa da suke masa rubdugu wurin tabbatar masa da babu shakka cikin sa ne , saboda me ?? Yarinyar shi ya fara sanin ta ɗiya mace kuma har zuwa lokacin da ya bar ta bata tare da kowa sai shi ,"
Jayayya yake da zuciya da tunanin sa akan lalle cikin ba nasa bane , ai ba jiya suka rabu ba , rabuwar su yanzu tsawon watanni shidda zuwa bakwai , zata iya yiwuwa bayan rabuwar su ta cigaba da bibiyar maza ne har ta ɗauki ciki ,
Sai dai sam zuciya da tunanin sa sun ƙi karɓar bangaren wannan hasashen nasa mai rauni ,"a kowacce daƙiƙa sake bijiro masa suke da dangantakar dake tsakanin sa da cikin jikin ta ,"
tsawon rayuwar sa bai taɓa shiga halin ruɗani irin haka ba , ya zama dole ya nemo yarinyar ko domin ya samu nutsuwar zuciya akan cikin jikin ta , nashi ne ko ba nashi bane ?,"
Bai yadda ya danganta cikin da nasa ba , sai dai ya san ko da ba nasa bane samuwar cikin a tare da ita wani babban ƙalubale ne akan manufar sa game da ita da irin shirin da yayi na gyara rayuwar ta , shi bai san kome akan ta ba , amma yayi mata shiri mai kyau akan hasashen da yake kan dalilin da ya jefo ta rayuwa a wannan gidan da taje a matsayin ƴar aiki ," ko dai ta gudu a gidan su saboda rayuwar matsi da wahalarwa, ko kuwa auren dole , ko kuma tsantsar talauci da rashin galihu ya jawo mata neman kuɗi ra kowacce hanya ,"
Kowanne daga cikin dalilan nan yayi niyyar tunkarar matsalar ta ya magance mata ita , ya tsame ta daga rayuwar gidan saida burkutu zuwa kyakkyawar rayuwa ,
ya maida ta gidan su gaban iyayen ta ya gargaɗi iyayen ta akan sakaci da tarbiyyar ta idan ta kama ma yayi musu barazanar haɗa su da hukuma idan ya kama su da laifin wahalar da ita ,
kuma ya tsaya mata tayi karatu, idan ta kama ya buɗe mata account ne ma zai buɗe mata wanda ko da ya bar nigeria saƙon sa zai dunga isowa gare ta , a ƙarshe ya bar mata numbobin wayar sa wanda a duk lokacin da wata matsala mai girma ta taso mata kowacce iri ce ta neme shi ,
Insha Allah zai magance mata idan ta kama ya tado da mutane ne ma daga chan ƙasar su zai turo , shi dai babban burin sa kar ya zamto a dalilin sa yarinyar ta faɗa mummunan rayuwar karuwanci wanda za'a dunga raba zunubin ta da shi , da ya fara lalata da ita ,"
Sai dai ashe ya makaro aikin gama kuma ya gama , ƙarshen lalacewa dai har ciki tayi ba tare da aure ba , "
Sam yaƙi ya bawa kansa dama ya hasaso kan sa a matsayin uban cikin jikin ta , " ya san tabbatuwar hakan wani al'amari ne da zai iya yin ɗai-ɗaya da farinciki na duk wani mahaluki da yake da girma cikin rayuwar sa , a karan kansa kuwa tunanin sa yayi kaɗan wajen tsinkayo irin halin da zai iya kasancewa a ciki .
Har tsuma yake lokacin da yake tunanin yadda zai sata a gaba ta kai shi har gurin ɗan iskan da ya ɗirka mata cikin , bai tunano irin azabar da zai gana masa ko da kuwa biyan ta yayi da amincewar ta yayi mata cikin ," a fili ya furta
Mtss doluwar watakila shima taimakon sa tayi ,"
tsabar kan sa ya ɗau chaji bai ma lura da wanda yake kiran sa ba ya ɗau wayar ya danna ta silent lokacin da ya ji tana neman damun sa da tsuwwa ,"
Ya ɗauki tsawon lokaci a ɗakin yana saƙa da warwara har bai san lokaci ya tafi dayawa ba sai da ya tsinkayi kiraye-kirayen sallah daga nesa ,
Wayar sa ya ɗauka dan ya ga lokaci anan ya tarar da miss calls ɗin tafeedah dayawa , ɗan dafe kan sa da ya fara sara masa yayi , shaf ya mance da lamarin bikin ma baki ɗaya ," bin bayan ƙiran nasa yayi
mon amie kana lafiya kou ? Ina ka bar téléphone ɗin ka ? je vous ai appelé mais vous n'avez pas répondu ,
Lafiya nake ɗan ouwa , kun kai ga isowa gari ?
Muna a gari yanzou haka ,
Aina kun ka yi masauki ?
Maiduguri international hotel, , " kai kana ina ?
Barwee hotel ,
nan tafeeda ya tambayi angon da yakasance haifaffen garin yanayin tsaro ya sa suka yi ƙaura daga garin zuwa birnin tarayya ," ko ya san barwee hotel ? ɗan ouwan sa da yake bashi labari chan yake da masauƙi ,
Nan take ya ce zai tura a ɗauko shi yanzu idan har ya shirya ,"
Da haka suka yi sallama bayan an sanar da youssouf tasowar driver ,
****
Karfe huɗu da rabi angwaye suka iso harabar gidan su amaryar inda anan aka riga aka fara wushe-wushe , dukkanin su sun yi anko na shuɗiyar shadda mai duhu ," kan su da jajayen hulunan dara ,"shigar su ta kanurai !
Ta ko'ina filin ya ƙawatu da adon gargajiya na kanurai , yayin da makiɗan ,"ganga kura" ( kiɗan kanurai na gargajiya ) suke tsaye daga gefe suna ta buga manyan gangunan su ga masu hura algaitun su na gargajiya suna hura ta tana bin kiɗan da mabanbanta sauti ,
Ƙamshin turaren wuta da aka sa a kowacce kusurwa na wajen yana tashi a hankali ta cikin electric burner ,"
Isowar angwayen bai ɗauki lokaci ba amaryar ma ta iso ƙarƙashin rakiyar ƙawayen ta waɗanda su ma suka yi ankon shuɗiyar shadda haɗe da baƙi ," ( danga-shaw ) sun rufe kan su da jaan gyalen ,"( mandil ),"
Amaryar kuwa wata farar haɗaɗɗiyar lafayyah ce ta naɗe jikin ta da shi , wuyan ta ya ƙawatu da babbar sarƙar mirjani haɗi da siririyar sarƙar gold ,"
Nan amarya da ango suka zauna a mazaunan da aka tanadar musu , yayin da ƙawayen amarya suka fara shiga filin rawa suna bin kiɗan malikii da yake tashi sannu a hankali suka fara rawa ta burgewa mai cike da ƙasaita , ɗaya bayan ɗaya abokan angon ma suka fara takawa zuwa cikin filin rawar kowannen su yana fuskantar ɗaya daga cikin ƙawayen amaryar suna bin kiɗan tare da rawa kamar yadda tsarin rawar kiɗan malikii yake ,"
Nan take guɗa ta fara tashi daga bakunan manyan matan wajen ,
Jayayyar rahima taƙi ta ƙare da su yakaka waɗanda suka tirje kan su fa baza su fita wurin wushe-wushen ba , a ɗaki zasu yi zaman su ,"
Ai wallahi da na san haka zaku min ku ƙunshe cikin ɗaki da ban ɓata lokaci na nayi muku kwalliya ba , sannan shi da kan sa bro ai ya saya muku kayan