Showing 126001 words to 129000 words out of 411050 words
Chapter 43 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
Rayuwa )
umm'muaz
25
BARKA DA SALLAH !ALLAH YA SA MUNA DAGA CIKIN WADANDA SUKA SAMU RABAUTA A WATAN RAMADAN ," ALLAH YA SA AYI BIKIN SALLAH LAFIYA , KUMA YA MAIMAITA MANA !
WANNAN SHAFIN GORON SALLAH NE GARE KU MASOYA !
Idan har kunnuwan su sun jiye musu daidai tabbas muryar samy baby suka ji ," wayyo sun shiga uku , meye ya kawo samy baby gidan ? Kada dai ta san doctor hamza ? Watakila ma ƴar uwar su ce , tunanin hakan ya sa yakaka jin jiri na kwasar ta ,"
Ya-yakaka ,"kamar muryar anti samy ta gidan madam ?" ," falmata ta furta hakan muryar ta na ƴar rawa tare da jin fargaba na rufto mata ,"
Muryar samy baby a kurkusa da su da suka ji wacce basu san lokacin da har ta ƙaraso ba ta katse amsar da yakaka ke shirin bayarwa ,"
Ni ce ba kamar murya ta ba , ta zarce da tambayar su ,"
Ashe kuna garin ?
Yaks baki kyauta min ba , sai kawai ku haɗa kaya ku bar gidan babu bankwana ? Kika sa nayi ta bulayin neman ku har da farko na ɗaurawa madam saly laifi nace ita ta kore ku ashe ku kuka kori kan ku , sai daga baya na samu labari a bakin ƙawar ki wai daman kin ce mata zaku gudu kun gaji da aikin wahala ko ? Ina ku ka koma da zama yanzu ? Ina fatan inda kuka koma yanzun yafi inda kuka baro saukin rayuwa ? Ko da yake ma ai ga ku na gan ku shar da ku , meya kawo ku gidan nan ko biki kuka zo ?
Muƙut !
Yakaka ta haɗiye wani busasshen yawun da yayi guntu a bakin ta , kafin ta tattaro ɗan guntun nutsuwar da ta rage mata ,"
Duk cikin dogon bayanin da samy baby tayi mata tambayar ƙarshe ta fi tada mata hankali ," aina suke kuma me suka zo yi gidan ??? ,"
Anan-anan kurkusa muke anty samy kuma ,unn unn
Aiko mu aka yi nan gidan mu karbi saƙo ,
ta tsinkayi muryar falmata ta amsa tambayar ƙarshen ," da ya sa yakaka ta saki wata boyayyar ajiyar zuci .
Sai dai me ? Muryar rahima ce ta ratsa wurin lokacin da take nufo su tana shirye tsaf cikin shirin zuwa party ,
Wow yakaka , fatima , kun gan ku kuwa ? Ɗanɗashi , haka kuka sha ƙunshi ? Ai da nasan har ƙunshi big bro zai kai ku ayi muku da na bi ku ," kai amma ƙunshin nan ya haɗu , wannan ai ko na amarya bai fi naku kyaun zane ba , ta ƙarashe zancen tana kashe wa yakaka idon ta ɗaya ,"da hakan yake tamkar al'adar ta ce ,"
Murmushin yaƙe yakaka tayi ,tana mai satar kallon samy baby wacce take bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya da guntun murmushi akan fuskar ta ,"
Da murmushi rahima ta dubi samy baby ,"
Sannu anty samira kuma baku tafi ba har yanzu ?
Bamu tafi ba rahima
Samy baby ta amsa mata a takaice ,
Yakaka baza ku je party bane ? Na ɗauka big bro zai wuce da ku ta chan ,?
A ah baza mu je ba rahima zamu shiga ciki mu taya su aiki sai kun dawo ,"
Yakaka ta bata amsa tana fatan ta wuce tayi tafiyar ta ," yau ɗaya ta ji surutun rahima ya fara gundurar ta ,' !
Ok sai mun dawo ,
Cikin sauri yakaka da falmata suka ɗaga kafafun su suna barin wurin tun kafin samy baby ta farga ," domun wata ƙawar su ta ƙaraso wurin ta janye hannun ta zuwa gefe suna ƙus-ƙus ɗin su ,"
Ta chan bayan ɗakunan gidan suka samu wuri suka zauna bisa takalman su a ƴar sassanyar inuwar yammaci ,"
Tab yakaka yau Allah ya rufa mana asiri kiris ya rage anti samy ta tona mana asiri , ai wallahi sam ban ji daɗin jin ta da nayi a gidan nan ba , ko me ya kawo ta kuma oho ?
Ni har yanzu hankali na bai wani kwanta ba falmata , inaga kamar zata faɗa musu gaskiya akai na , watakila ma ƴan uwa ne ita da su rahima , "
Allah dai ya rufa mana asiri yakaka ,
Ameen !
ta amsa tare da rashin kuzari
Ba su suka fito daga maɓoyar su ba , sai da suka ga gari ya fara duhu , daga inda suke suna iya jiyo kiraye-kirayen sallar magariba , ga kuma hayaniyar da suke ji da ke nuni da cewa ƴan bikin ne suka dawo ,' daga wurin party ,"
Da rakaɓe-rakaɓe suka bullo ta cikin gidan , iya ganin su mutane ne ko ta ina da alama an samu ƙaruwar wasu baƙin ,"
Suna tsaye daga gefen kofar falon suna shawarar su shiga ko su koma maɓoyar ta su kawai su kwana a chan , tun da sun san dai ko sun shiga falon basu da takamaimai wurin kwana ," !
Yauwa , fatima , yakaka tun ɗazu nake neman ku , gaskiya kun wahalar da ni kusan ba ɗakin da ban duba ba a sashin mu , ina kuka shiga haka ?ko kun fita ne ? Cewar rahima wacce take ƙarasowa wurin su .
Muna daga nan bayan ɗakuna rahima , kiyi hakuri bamu san kina neman mu ba ,! Har kun dawo ?
Mun dawo , daman big bro ne ya ce duk inda kuke na neme ku , kun ci abinci ne ?
Yakaka ta girgiza mata kai ," bamu ci ba ,"
Yauwaa toh ku zo muje ciki ga abincin ku chan na sa an ɗibar muku,!
Ta cikin falon suka shiga suna biye da ita , suka nufi ƴar hanyar nan da ta hau sama ," suka bi ta ƙafar benen suka haura cikin wani babban falo wanda ya ƙawatu da kayan alatu , da manyan kujeru da tsadaddun labulaye , ga ƙofofi birjik a cikin sa ,"
Nan ɗin ma dai duk tawagar ƴan matan ne wanda ga alama sun yi ƙaura daga ƙasan ne sun dawo saman ,"
Dararrakin su da shewa sun cika wurin banda ɗan wani sassanya sauti da yake tashi a cikin falon ta cikin wasu mulmulallun sifika da suke a kowacce kusurwa na falon ,"
Daga bakin kofa su yakaka suka jaa tunga, rahima ta kutsa kan ta ciki ba tare da ta lura da sun dakata daga bin ta ba ,"
Kai tsaye ta nufi wata ƴar hanya sai ga ta ta bullo cikin ɗan Kitchenette ɗin duk da cewa babu wasu tarkace a ciki , amma Kitchen Cabinet ɗin kan sa abun kallo ne , kwarai Kitchenette ɗin yana da ɗaukar hankali , kamar yadda kome na sashin yake da mataukar tsari da kyau , fiye da na ko'ina a gidan , kai tsaye ta ɗauko ƴan madaidaitan coolers ɗin biyu ta fito da su ,'
", turis ta jaa ta tsaya lokacin da ta lura babu su yakaka a wurin ,"
Ina suke ??",
ta furta a sarari .
Su waye ?
Hafsa ta tambaye ta daidai lokacin da ta kai hannu tana ƙoƙarin karɓar cooler ɗin hannun ta ,"
Ta janye tana bata amsa da ,"
su yakaka da fatima tare da su fa muka hawo saman , wannan ma abincin su ne da big bro yace na ɗebo musu tun ɗazu ,"
Yamutsa fuska hafsa tayi ,"
Su waye kuma fatima ? Ita har ga Allah ta ma manta da sunayen su takamaimai ,"
C'mon bani abinci naci daman yunwa nake ji tun breakfast wani abun kirki bai sake shiga ciki na ba, "
nima wallahi yunwar nake ji cewar wata daga cikin ƙawayen su da take kishingiɗe a gefe ,"
Ƙanƙance idanu rahima tayi ,
Ki rufa min asiri malama kar ki jawo min fushin big bro , domin sai da ya daɗa jaddadamin na basu abinci...
Kewaye su tayi ta wuce
Bata saurari hafsa ɗin ba da take bin ta da tambayar
Wai su waye ne waɗan da kike ta ambato ,"
Leƙawa tayi ta gan su a rakuɓe daga gefe ,"
Haa'ah ya kuka tsaya anan yakaka ?
Ku shigo mana ga abincin naku ,!
Toh !
Suka amsa suna masu sanyo kafafun su cikin falon ,"
A ɗage hafsa take jifan su da kallon tuhuma ,"kallon ku kuma me kuka zo yi nan ??
Ku zauna ,' rahima ta umarce su tana musu nuni da kan haɗaɗɗiyar shimfiɗar dardumar da take shimfiɗe tsakanin kujerun gurin ,'
A ɗarare suka zauna falmata ta matsu da jikin yakaka a saboda ji da take idanu sun yi yawa a wurin ,"
Yakaka ma kan ta a sunkuye yake saboda kallon banzan da sofi take jifan ta da shi a tun ƙarasowar su falon ,"
Ba tare da karsashi ba suke chakalar abincin duk kuwa da uwar yunwar da taje sasuƙar ƴan hanjin su da kuma yadda abincin yake da matuƙar daɗi ya wadatu da kayan girki na alfarma ," amma idanun jama'ah ya musu shamaƙi da jin dadin abincin ,
Ƙarar wayar rahima ita ta dawo da sofi duniyar tunanin da ta lula na son hasaso meye ne a tsakanin doctor hamza da waɗannan yakubayin talakawan ƴan gudun hijirar da har yayi musu matsauki a cikin gidan su ya kuma jiɓanci lamuran su da matukar muhimmanci haka ?? ,"
Hello big bro ,"
Gasu nan muna tare ma ," cin abinci suke ,"
Rahimar ta kai kallon ta ga yakaka wacce kan ta yake sunkuye ,"
Eh tana ci sosai ma ," to idan sun gama zamu zo yanzu ,"toh !
Yakaka wai inji yayan mu idan kun gama cin abincin muje yana ƙiran ku ,"
Toh suka haɗa baki wurin amsa mata ,"
Ba'a kai mintuna uku ba falmata ta zare hannun ta tare da faɗin ta ƙoshi , ita kuwa yakaka daman ba wani na kirki take ci ba ," dan haka ita ma ta miƙe bayan ta tattare ɗan abincin da falmata ta zubar ,"
Ƙarƙashin rakiyar kallon rainin da mafi akasarin ƴan matan wurin ke bin su da shi suka ƙarasa barin falon suna jin su wasai tamkar an cire musu wani mugun dafi da idanun jama'ar suka zuba musu ," daga yakaka har falmatan ba masu son mutane bane ,"
rahima ta jagorance su zuwa wurin da doctor hamza ya ce su same shi ," daga kusa da kofar sashin sa ,"
Tun kafin su ƙaraso ya nacewa kallon fuskar ta , da ita kuma ta shagaltu da kallon haɗaɗɗun motocin da suka cika harabar gidan wannan tana wace waccen a haɗuwa ,",
Suna ƙarasowa suka gaishe da shi , ya amsa tare da haɗa musu da tambayar babu dai wata matsala ko ? Kuma sun ci abinci sosai ko ? Suka tabbatar masa da basu da matsalar kome sannan a ƙoshe suke ,"
Manyan ledojin da aka zubo musu kayayayyakin su da ya saya musu na fitar bikin ya miƙa wa rahima , gami da wata madaidaiciyar leda mai ɗauke da tambarin ', down town, "
Ungo rahima wannan kayan nasu ne na fitar biki , ki dunga taya su shiryawa ,
Ta sanya hannuwan ta biyu ta karɓa tana ƴar dariya ,"
Eyeeh gobe su fatima za'a chanchare gaskiya fatima kin kwace min fada wurin big bro ," ta ƙarasa zancen da sigar zolaya , tana kashe idon ta ɗaya ,"
Ɗan murmushi su duk biyun suka yi cikin ran su suna jin daɗin kulawar da yake basu tare da kyautatawa , hakan ke ƙara sa yana sake girma da ƙima a idon su ,"
Ba tare da ya kula da zantukan ta ba yace ,"
Ga shi
tare da miƙa mata ƴan mukullayen sashin sa , daga yau zuwa lokacin da za'a kammala bikin ku dunga kwana ke da su a sashi ne , daga ke sai su , bance ki haɗo min gayyar ƙawayen ki su ɓata min waje ba , ki kiyaye ,"
Ya ƙarasa zancen da sigar gargaɗi fuskar sa babu alamun wasa ,"
Toh
Kai kuma aina zaka dunga kwana ?
Tare da baƙi a sashin baba ya amsa mata yana barin wajen ," bayan ya basu umarnin su tafi su kwanta dare ya soma shiga ,"
Da zumuɗi rahima tayi gaba suka bi ta a baya ,
Tab lalle yakaka ku ƴan gatan big bro ne , baya fa son kowa ya shigar masa sashi , kana shiga zai fara korar ka kar ka kai masa datti , daga ka fita kuma sai yayi shara ya goge kujerun sa , bala'in tsafta ce da shi kamar mai aljanun tsafta ," ta furta hakan daidai lokacin da ta sanya mukulli ta buɗe ƴar babbar kofar mashigar sashin nasa ,"
Suna sanya kafafun su ciki ," kowaccen su tana gaskata kalaman rahima da ta ce yayan ta mai bala'in tsafta ne , saboda tuno haɗuwar su ta farko yadda ta kaya a tsakanin su , ta yadda ya fututtuke ya ci mutuncin su akan ƙazantar da falmata tayi masa a ofishin sa , wanda a lokacin da za'a faɗa musu doctor hamza mutumin kirki ne mai tausayi da kyautatawa irin yadda yake musu a yanzu zasu ce ,"ƙarya ne ," to ashe aljannu tsafta ne da shi , kamar yadda suka ji daga bakin ƙanwar sa ,"
Ƙamshin furanni tare da sanyin ban ruwa da aka yi a wurin zuwa wani ƙamshi na musamman da yake tashi a ƴar harabar sashin nasa suka haɗu suka bayar da wani irin yanayi mai daɗi tare da samar da nutsuwa ga zukata , "
Lumshe idanun ta yakaka tayi ta buɗe tana mai yawo da idanun ta a kowanne kusurwa ta wurin , ƙwarai yanayin wajen da tsarin sa suka burge ta ,"
Ƴar barandar da take ɗauke da ƙofar falon nasa rahima ta taka ta buɗe kofar tare da tura ta ta sanya kai tana cewa su yakaka ," su shigo ,"
Sanyi da kalolin ƙamshin da ɗakin yake suka sa falmata sakin wani gauron numfashi da tun shigowar su sashin take ta jaan iska ta hancin ta tana jin wata nutsuwa ta musamman na ratsa ta ," tsafta tayi a rayuwa ,"
Cikin shauƙin yakaka ta dunga bin falon da kallo ɗan madaidaicin falon da baya ɗauke da duk wani nau'in tarkace , kome ka gani a falon amfanin sa mai muhimmanci ne kuma yana bigiren da ya dace ,
Tun daga kan ƴan madaidaitan kujerun da suka kewaye falon tare da lallausan kafet har zuwa kan labulayen duk suna ɗauke da launi guda ne ,"ruwan madara ," sai gefe guda kuma girkakken gogaggen teburin katako ne shima ruwan madarar da ƴar kujerar sa wanda aka ajiye wata ƴar computer tare da tulin littatafai akan sa ," daga ɗaya sashin kuma ƙaramin firiji ne ,' daga haka babu kome a cikin falon sai sanyin AC da yake daga jikin bangon ɗakin sai kuma ƙamshin mai ɗakin da ya riga ya kama ko'ina na wajen ,"
A ƙasa suka zauna daga su har rahimar da take ta basu labarin party da suka halarta yau , " lokacin da take zazzage kayan da suke cikin leda ta ɗora da basu labarin , bikin da za'a yi na gobe har sai ya fi na yau haɗuwa da yin kyau domin a na goben har da tawagar ango da abokai/dangin sa waɗanda zasu iso a gobe da safe ,'
Woww wayyo Allah yakaka wanɗannan ɗanɗasa ɗanɗasan rigunan dan Allah aina big bro ya sayo muku ,? Wayyo Allah ,"
Haƙoran ta a buɗe falmata ta fara bata labarin shagon da suka je ,' a ƙarshe ta zame ɗankwalin ta , baki siɗik ɗin gashin ta mai cika da tsawo tare da ƙauri ya bayyana ,"
Kin ga ma har kai sai da aka wanke mana ," ta ɗora da tambayar kin ga takalman da ya saya mana koh ? Su ma masu kyau amma ni dai kamar bazan iya sawa ba dana gwada Su naji sun min tudu ,"
haba ! zaki iya sawa mana fatima , kuma wallahi ba ƙaramin kyau zaki yi ba ,
Wanne ne naki yakaka , wanne ne na fatima ,?
Ware mata su tayi
Rahimar ta cigaba da santin kyaun kayan , a ƙarshe tayi alƙawarin taya su ƙwalliya tare da shiryawa ," inda har ta zaɓar musu waɗannan dogayen rigunan a matsayin kayan da zasu sa a gobe da yamma dai-dai lokacin da za'a fara gudanar da wushe-wushe a ɗora da sanya lalle ,"
ɗaya ledar ta jawo ta cire musu shawarman da take ciki naɗi uku kowacce ta ɗau ɗaya suƙa fara ci suna ƴar hirar su , har zuwa Lokacin da bacci ya ɗauke su ,"!
********
Misalin sha ɗaya na daren Alhamis biyamuradi youssouf ya samu shigowa cikin gari ƙarƙashin umarni da ya samu daga babbar headquarter su dake chan niemey inda aka bashi awanni arba'in da takwas akan ya je yayi uzurin da ya taso masa na gaugawa kamar yadda ya shida musu ya dawo ,"
Shi ya tuƙo kan sa ya keto dazuzzukan da suke da matuƙar hatsari saboda ƴan tawayen boko haram da suka yi bigire a cikin sa ,"
À daren ya so yaje ya gan ta har ma su tattuna cikin awanni arba'in ɗin da yake da damar su yake sa ran zai iya fara gyara ɓarnar da ya tafka ,wanda idan ya samu haɗin kan yarinyar ya na san ran zai wanke hakkin ta da ya ɗauka ya cigaba da istigfari , sai dai yadda garin ya ɗau shiru ya sanya shi barin tafiyar zuwa gobe da safe , ta yadda ko da bai same ta ba kai tsaye zai iya samun abokan hulɗar ta wanda su kuma kai tsaye zasu sada shi da ita ba tare da wata wahala ba ,
Da wannan tunanin ya