Showing 96001 words to 99000 words out of 411050 words
Chapter 33 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ya saukewa larurar sa ,'? Shin wai ma meya sa ita yarinyar nan bata yi masa turjiya ba yana tune da shine mutum na farko da ya fara tarayyah da ita , shin ko ita ma abun da ya faru da shi ne a jiyan ita ma ya faru da ita ? Toh amma kuma ai ita ta so taƙi yadda da shi sai dai a ƙurarren lokaci ne , har yanzu yana tuno amsa kuwwar kalmomin ta waɗanda suka gaza tasiri wurin daƙile shi ga aikata abun da yayi niyya a jiya da yanzu kuma kalmomin suka zama tamkar ɗigar ruwan dalma a kunnuwan sa , bai ko son tuno da su ," ko ma menene ita ma tana da nata laifin a wurin shi na yadda ta gaza yin hoɓɓasa wurin dakile fadawar su ga halaka ,"
Tsaki ya ja tare da auna mata harara , ki tashi na maida ki inda na ɗauko ki ,!
Tafiyar kuramen suka sake yi babu um ba a ah ," kowannen su yana sauraren taɗin zuciyar sa ,
Ga yakaka ita har yanzu bata daina mamakin mutumin da bata kai ga sanin ko da sunan sa ba har zuwa yanzu , bata wani jin nadama koh damuwa akan halin da suka kasance ciki tare idan aka ɗauke ɗan raɗaɗin da take ji a jikin ta,
dalili shine bata kai ga sanin girma tare da darajar budurcin ta ba , rayuwar kaɗaici suka taso a ciki , ko a garin su a ware suke cikin jama'ar gari sannan mahaifiyar su bata yi wani yunƙuri wajen nuna musu girman budurcin su ba , basa makaranta illa mahaifin su da yake koyar da su karatun sallah a gida ,"
Chan wani saƙo na zuciyar ta kuwa yaba gayu tare da gogewar biyamuradi yousouf take har ma take jin yana matuƙar burge ta , hakan ya sa take yawan satar kallon sa zuciyar ta na tuno mata da mahaukaciyar soyayyar sa da ya gwada mata a daren jiyan tamkar zai cinye ta ,'
Ga biyamuradi youssouf kuwa tunane-tunane barkatai cikin kan sa har ya rasa takamaimai na kamawa , shin yaya iyayen sa zasu ji lokacin da labari ya isar musu na irin lalacewar da yake ace wai bayan shan barasa shi youssouf har neman mata ya fara yi yayi nadama da bai amince an ɗaura musu aure shi da maimouna ya taho da ita ba da duk wannan masifar bata auka masa ba da bai lalata ƴar mutane ba shin yaya shi zai ji lokacin da wani abu makamancin wanda ya aikata ga ƴar yarinyar nan ya faru akan meramar sa ?? Runtse ido yayi yana mai jin nadama na sake lulluɓar sa , yayi nadama kuma yana alƙawartawa kan sa ba zai sake yi ba , burkutun da kan ta a yau yana jin wani irin karfin imani da ya jima bai ji irin sa ba akan barin shan ta, ya bar shan burkutun ma , zai yi nesa da duk wasu manyan zunubai tare da yaddar Allah ,
Yana tsayuwa ya juyo ya dubi yakaka wacce daman shi take kallo , suna haɗa ido ya murtuke fuska ,
Duk wasu kuɗaɗe da suke aljihun sa na niger da nigeria sai da ya tattaro su ya zube su akan cinyar yakaka , " maida hannun sa yayi kan Steering ya ɗauke kan sa da nuna alamun yana jira ta fitar masa a mota ne ,
A hankali yakaka ta ɗago kai tana kallon sa bayan ta kalli kuɗin da ya zube mata su a jiki , kuɗin na menene ? Wani abu zata sayo masa ? toh amma ai waɗannan kuɗin sun yi yawa a sayan abu a dai unguwar nan tasu , anya anya kuwa mutumin nan kan sa ɗaya , ???
Ta wutsiyar ido yaga irin kallon shakkun da take yi masa wanda ya fassara shi a kallon rainuwar yawan kuɗin da ya bata , dan haka ba tare da yace ƙala ba ya sunce agogon hannun sa na ɗanyen farin azurfa da aka ƙawata shi da ƙananun duwatsu masu daraja , ya ɗora mata akan kuɗin ,
Idan kin ka saida shi kudi ne me tarin yawa ," ki gaugawar fita ina da tafiya mai nisa a gaba na ,"
Cikin in-ina yakaka tace
Me zan sayo maka da kuɗin toh ?
Wani kallon baki da hankali biyamuradi youssouf ya wurga mata ,"
Kuɗin biyan ki taimakon da kika min ne , ki fita ni zan tafi ,"
Toh ai wannan kuɗin sun min yawa babu abunda zan yi da su ta furta hakan tana mai sauke masa kudaɗen tare da agogon nasa agefen kujerar ta saka kafafu da nufin ficewa a motar kamar yadda yake buƙata ,"
Wata razananniyar tsawa ya daka mata
Ke bani son sokonci kwashi abun da na baki kiyi tafiyar ki , bana so na sake ganin fuskar ki ,"
cikin ran sa yana jin takaicin yarinta tare da rashin wayewar ta da take nuna masa a fili wanda yake sa shi ƙara ganin laifin sa tare da zubewar ƙimar sa wai ace kamar shi ya haiƙewa ƴar yarinyar da bata ma kai ga sanin kan ta ba a matsayin mace," wannan abun kunya agare shi dayawa yake ,'
Yadda yayi maganar cikin hargagi yasa ba shiri yakaka ta kwashi duk abunda ya bata ta naɗe cikin zanin rufuwar ta da ta tafi da shi a jikin ta jiya ," cikin sauri ta sauka daga motar
Bata yi taku biyu ba ya jaa motar a zabari ya bar harabar wajen yana mai jin yadda bugun zuciyar sa ya fara sauyawa tare da iya adadin nisan tazarar da yake yi da yarinyar ,"
Jiki a sanyaye yakaka ta juyo cikin gida tana mai jin yadda wani abu mai kama da rashin jin daɗin rabuwar su a wannan lokacin yana mamaye ta bata ƙi ba ya zauna tayi ta kallon sa ita dai yana burge ta ɗan gayu ne bugun farko .
Biyawa ta fara yi ta ɗakin samy baby domin ta ajiye kuɗin da ya bata amma sai ta tadda ɗakin a datse da kwaɗo ga alama samy baby bata kwan a gidan ba ,
Zubawa Kuɗaɗen ido tayi tana kallon su kuɗaɗen suna da yawan da ita bata san adadin su ba , ta san suna buƙatar kuɗi ko domin su jaa jari kamar yadda suke da ƙudirin yi , to amma ina zata boye kuɗin ba tare da wani ya gani ba , samy baby tayi niyyar baiwa ajiya ita kuma ga shi bata nan , tana da tabbacin idan har ta shiga da kudin cikin gidam madam saly ta ƙyalla ido ta gan su , raba ta da su zata yi ,
Hannu ta sa gami da ɗaukar agogon da yake ta ɗaukar ido a hasken ranar hantsi , tsaruwar agogon ya burge ta ko ba'a faɗa mata ba kuma ko da ta kasance bagidajiya ta san wannan agogon mai daraja ne , bare mamallakin agogo da bakin sa ya ce agogon mai kuɗi dayawa ne ," shin har taimakon da tayi masa ya kai ya bata wannan agogon da dukkanin kuɗaɗen sa ? Watakila shi ɗin mai kirki ne ,
Ɗaga rigar ta tayi ta soka agogon a bakin zanin ta tare da gyara ɗaurin zanin gam-gam ,
Burum aka shigo ƴar kewayayyiyar rumfar katakon da samy baby tayi a gaban ɗakin nata ,"
A firgice yakaka ta ɗago kan ta tana mai kokarin boye kuɗaɗen hannun ta ,"
Karaf suka haɗa ido da yagana wacce wannan ne zuwan ta na uku ɗakin samy baby neman yakaka wacce aka tabbatar mata da bata kwana a gida ba kuma babu wanda ya san inda take wanda hakan ya tashi hankalin yagana tare da falmata wacce tun da ta farka ta laluba gidan taji babu yakaka take ta surfa kuka babu ƙaƙƙautawa ,"
Kai kawo suke ta yi daga waje zuwa harabar gidan da kewayen sa ɗaki-ɗaki neman yakaka , wayam babu ita babu wanda ya ce ya gan ta ma sai mutum ɗaya ne babasho yace tabbas ya ga fitar yakaka tare da wani mutum a daren jiya ,
Da sauri yagana ta ƙaraso
Yakaka ina kika je ? Daga ina kike ? Aina kika kwana ?? Sune tambayoyin da ta jero mata ,"
Na raka samy baby gidan su ne ! Ina falmata ? Mu ƙarasa ciki ,"
Tare da shakku yagana ta tsare yakaka da ido , domin sarai ta ga kuɗin da yakaka ta boye mata , uwa uba wani fitinannen ƙamshi da take ji yana tasowa daga jikin yakakar
Amma ganin yakakar taƙi nuna mata da kan ta sai ita ma ta bar batun .
Ki taho muje falmata taji muryar ki ko ta daina kukan da take ta faman yi tun farar safiya ,"
Bata ƙarasa rufe baki ba yakaka ta taka da gudu ta nufi cikin gidan ,
Zaune ta tadda falmatan ta haɗa kai da guiwa a inda ta saba aiki bakin fanfo ga tulin wanke-wanken kofuna da faranten sana'ar su a gaban ta ,"gefe guda kuma kwanan da ta saba sayo musu waina ƴar tsala da suke karin safe da ita ne , a rufe ga alama ko sayo wainar bata yi ba , "ta gaza yin aikin sai kuka ,"
Da sauri ta ɗago ta tare da rungume ta cikin jikin ta ,'falmata ki bar kuka gani nan na dawo ,"
Yakaka ina kika je kika kwana ? Meyasa baki faɗa min ba ? Kin sa hankali na ya tashi , yakaka ya zan yi a wurin da bakya nan ? Dan Allah duk inda zaki tafi kike tafiya da ni kin ji ?
Naji falmata kuma bazan sake tafiya na bar ki ba ," ta furta hakan tana mai bubbuga bayan ta sigar lallashi ,"
Yakaka ƙamshin meye ne haka a jikin ki ? Aina kika samu ƙamshi ko a gidan turare kika kwana ?
Eh__Ah ah
Unm falmata muyi wanke-wanken kafin rana tayi sosai kin ga mun yi jinkirin fara aiki ,
Toh ai duk ke kika jawo mana !
Madam saly ma ta zo tayi ta masifa tace wai kin fara yawo ,'
Tsam yakaka tayi da jin cewar madam saly tayi masifa ," a duniya tana tsoron madam saly , tana matuƙar gujewa bacin ran ta gani take ita ce gatan su ,"
Kafin rana ta take sun kammala aikin su da suka saba yi har sun fara hidimar abokan cinikayyar su kamar yadda suke a kullum ,"da hakan ya kwaci yakaka daga shan masifar madam saly , dan ita faɗan ta akan harkar ta ne ba wai dan rashin kwanan yakakar a gida ba ! Yo me ya shalle ta ?
Babu wanda ya bi ta kan yakaka akan rashin kwanan ta a gida yo bariki ce fa ! ?
Yagana ce ma ta so matsawa ta ji toh amma ganin yakakar taƙi bada haɗin kai ta gaya mata inda ta kwanan sai ita ma ta haƙura , har lokacin rabuwar su yayi suka kammala aikin su na yinin ranar ,
Yakakar ta rako yagana bakin titi kamar yadda suka saba kullum idan yaganar zata koma sansanin su ,"
Kuɗin da suke dunƙule a hannun ta ta kamo hannun yaganar ta danƙa mata su ,"
Ga shi yagana ki sayi wani abu nima bani aka yi ,"
Da sauri yaganar ta ce wa ya baki ? lokacin da take warware ƴan naira dubu guda biyu da yakakar ta miƙa mata su a dunƙule,
Wanda na taimakawa ne ya bani !
Taimako ? Wane irin taimako waye shi ?
Yagana yanzu ba lokacin hira bane kin ga an kusa rufe hanya kiyi sauri ki tafi sai da safe !
A sanyaye yagana tace
Toh nagode !
Sai gobe ," ta kaɗa kai tayi tafiyar ta zuciyar ta na shakkun ina yakaka ta samu kuɗi haka masu yawa ? Koma menene ita dai tayi farin ciki da kudin da yakaka ta bata koh banza ta toshe wasu daga cikin tarin matsalolin da suke kewaye da ita na talauci !
Akan hanyar komawar ta gida yakaka take tuhumar kan ta meye yasa ta boyewa kowa abun da ya gudana tsakanin ta da mutumin da ta taimaka ? Oho ita da kan ta bata san dalili ba , abun da ta gane kawai shine tana jin kunyar bada labarin yadda suka kasance tare ,"
Dai-dai ta shawo kwanar layin su ƙamshin balangu Barde mai nama ya daki hancin ta , tun ba yau ba tasha haɗiyar mugun yawu akan ƙamshin balangun da kullum take wuce wajen da tunanin ina ma ina ma Allah zai kawo wani tsautsayin da zai gifta ya sa tukubar balangu barde ta tuntsira ita kuwa ta daka wawaso ,! Saboda ba ƙaramin ran ta biyawa yayi da balangun nan ba ,! Rabon ta da nama shekarun da ƴan yawa ,' to su da suke ta abinda zasu ci su kori yunwa ina su ina nama ,"kayan wadata "
Yau da take jin ƙugun ta danƙam da kuɗi , tana shaƙar ƙamshin ta saki hannu ta bishi , har cikin ƴar rumfar barde ,
Cikin nutsuwa ta gaida barde
Ya amsa mata haba-haba irin na ƴan kasuwa ,"
Ta miƙa masa gudar ɗari biyar ɗin da ta ciro daga ƙugunta ,
Na nawa za'a yanka miki Ƴan mata ,?"
Na dukka ! yakaka ta furta hakan tana mai gyara tsayuwa jin kan take a sama ," naman ɗari biyar ai ba kusa ba ,"
Take barde ya washe baki ya fara yanko naman daga gefe-gefe yana kachal-chala shi akan ƴar takarda neɗe nama ,'
Da sauri yakaka tace a ah ba nan zaka yanka min ba nan nake so wuri mai nama-nama da mai ɗin ," ta nuno wurin da yafi ko'ina sheƙi a jikin naman yana ta nason mai da yaji ,"
Au to toh bari a yanko miki nan ɗin,"( kuturu da kuɗin sa ai alkaki sai na ƙasan langa )
Ƙarbar balangun tayi bayan ya naɗe mata yaji a wata ƴar takadda daban ya haɗa ya sa mata cikin leda ,"
A ci daɗi lafiya ƴan mata !
Tun a harabar gidan ta fara ƙwallawa falmata kira wacce take zaune daga gefe a babban filin , inda ɗan asharalle ya baje gangunan sa da shi da yaran sa suna ta bugun ganguna ," kalmomi ne na batsa ake rera waƙar da su , mata Sun shiga layi kowacce tana nuna ƙwarewar ta a fannin girgiza kwankwaso tare da juya sassan jiki ,' mazan da suke zagaye da su suna kallon su tare da yin eho har wasu suna faɗawa filin su yi wa budurwar su ko wacce ta birge su liƙi ,"
Ta ko'ina jama'a ne birjik a harabar masu cha-cha da karta nayi masu hira musun ball suna fama ,!
Kamo hannun falmata tayi suka shiga daga ciki sashin madam saly inda babu yawaitar mutane sosai saboda mafi yawa suna filin chasu ,"
A gefe ta zaunar da falmata kan wani ɗan dutse , ita ma ta zauna gami da warware ƙunshin naman ta ɗauko ƙatuwar tsoka bayan ta ɗan ɗangwalo yaji ta nufi bakin falmata da shi , wacce tun da aka buɗe naman ƙamshin sa ya buge ta yawun ta ya tsinke ,"
Ungo falmata buɗe bakin ki kici nama ,"
Unm unm yakaka waye ya baki wannan naman mai daɗin tsiya ?, cewar falmata a lokacin da take ƙoƙarin haɗiye na bakin ta ,!
Ni na sayo mana falmata ,
Yakaka ta furta hakan tana mai sake nufar bakin falmatan da wani yankan
Chak falmata ta tsaya da taunar wanda yake bakin ta .
Aina kika samu kuɗi yakaka ?
Wanda na taimakawa jiya ne ya bani !
Waye shi , ?
Wani ne baki san shi ba falmata nima kuma ban san shi ba , taimakon sa kawai nayi ya tafi kuma yace ba zai sake dawowa ba , ta furta hakan tana jin wani yanayi marar daɗi yana taso mata kalaman sa na ƙarshe suna mata amsa kuwwa cikin kunnen ta ," Bana son na sake ganin fuskar ki ,"
Kenan ba zai dawo ba ,
zuciyar ta ta aiyana haka!
Kai amma yana da kirki ! Cewar falmata lokacin da zaƙin naman yake ratsa ta ,"
yakaka bata samu zarafin amsa mata ba saboda zuciyar ta da tayi ƙunci ," a take ta ji ta daina jin garɗin naman dan haka ta miƙe gami da cewa falmata tana zuwa ," ta ci naman iya cin ta .
Shagon sayar da kayan masarufi da amfanin yau da kullum ta tafi wanda bashi da nisa sosai da gidan su ,
Ta miƙa dubu ɗaya tace a bata manyan jakar bacco guda biyu , da sabulun wanki guda uku da na wanka sinki ɗaya da kuma omo babbar jaka ,"
ɗan jim tayi tana tunanin bayan su kuma me yakamata ta saya ?
Har zata ƙarbi sauran chanjin ta idanun ta suka sauka akan jerin ƴan mukullaye da suke jikin wani ɗan karfe ," wani tunani ne ya faɗo mata
A bani ƴan mukulli ƙanana guda biyu ,"
Ta haɗo sayayyar ta ta komo gida kai tsaye ta wuce ɗakin da su falmata ke kwana , ta jawo yagaggen jakar bacco wanda suke tara kayan su a ciki ita da falmata ,
Ta fiddo dukkanin suturun su ,"babu laifi yanzu suna da ƴan kaya ,"
Ta warware sabbin bacco , ta ware kayan falmata ta jera mata su tsaf a ciki bayan ta gyara ninkin ta ɗauki ɗaya daga cikin ƴan mukullin ta kama bakin zif ɗin ta sarƙafa shi ta bame ,"
Ta warware ɗayar bacco ta buɗe ciki ,
Ta fiddo kuɗaɗen ta tare da agogon da ya bata ta saka kuɗin a cikin bacco , ta riƙe agogon a hannun ta , ta tsura masa ido , " kyakyawar fuskar sa tana mata yawo a zuci , ƙamshin da yake manne da jikin agogon ya mamaye mata hanci , ta ji wani irin nishaɗi tare da shauƙi suna huda ta, ina ma ina ma da ace har yanzu suna tare tana kallon sa tare da shaƙar ƙamshin sa