Showing 102001 words to 105000 words out of 411050 words

Chapter 35 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14370

madam saly tayi ta zo har cikin ɗakin nasu tana bawa yakaka wani abu tare da shaida mata idan har ta sha shi da madarar ruwa ko nono , ba ƙaramar kyauta saurayin ta zai yi mata ba ƙila ma ya bata "mota ,"

Saurayi kuma yakaka ?
  Wanne saurayi ? Tambayar da falmata ta jefawa yakaka kenan , bayan ta cika bakin ta da donut,  wacce ita ma yakakar ta toshe mata baki da kayan maƙulashen da biyamuradi ya ciko mata manyan ledoji da su ,lokacin da ta so tada bori akan kwanan da yakaka ta sake yi a waje ,!
    Ba saurayi na bane wanda nake taimakawa ne ,"
    Wai yakaka wane irin taimako kike yi masa da har yake baki kayan daɗi haka ? ga turare mai ƙamshi da kika ce ya baki har da su mai ," to kawai mu koma gidan su mana mu dunga yi musu aikin tare koh ba taimakon sa kike da aiki ba ?

Cikin diriricewa yakaka ta ce,"
    Ba-ba ba agidan su muke aikin ba a wani waje ne ,falmata kiyi zaman ki anan tun da ni ina zuwa nemo mana , kuma ina samo mana kuɗi , kin ga tunda kuɗaɗen dayawa idan suka taru har ɗaki zamu iya kamawa mu bar gidan nan , mu kama sana'a a hankali a hankali muna neman su maman mu ko ? 

Take falmata ta hau murna jin za'a nemo maman su ," nan dai ta hakura zata dunga zama yakaka ita zata dunga zuwa sabon aikin da ta samu !

Haka kwanaki suka jaa har yau da suke kwanaki goma sha huɗu da fara tarayyar su , zuwa yanzu yakaka tayi nisa cikin makauniyar soyayyar biyamuradi bata ji bata gani wata irin mahaukaciyar soyayyah take masa da bata ƙi ba su tabbata har abada a tare ,

Ta bangaren biyamuradi kuwa shi tun farko babu batun so atsakanin sa da yarinyar , hasalima ya ɗauke ta ne kawai a matsayin mai bashi maganin cutar da yake ganin ta kama sa a kwanakin nan na jarabar mace , wanda a yanzu kuma yake jin ya fara samun sauƙi domin a ƴan kwanakin nan yanayin da yake ji mai tsanani a duk ranar da bai kusance ta ba ya ragu , dan haka zuwa yanzu ya fara jin zai iya daina harkar gaba ɗaya tunda daman dole ce ta sanya shi farawa ,( a cewar sa )

A yau yayi niyyar sallamar yarinyar da ƴan kuɗaɗe masu tsoka domin yau idan ya koma daji ba zai sake fitowa kwana kusa ba zai maida hankalin sa kachokam kan aiki , giyar da kan ta zai gwada barin ta na kwana biyu ,

Daga wanka ya fito jikin sa ɗaure da towel , kai tsaye ya nufi ƴar wadrobe ɗin da take ɗakin ya fiddo da mai tare da mataji ,( comb ) ya shafa mai tare da taje ƴar sumar sa da bata cika yawa ba ,  , ya jawo ƴar ƙaramar jakar matafiya da yake sako kayan sa a ciki shiga ɗaya idan zai shigo gari ya fiddo kakin sa na soji ya sanya ya fesa turare tare da ɗaura agogon sa , kayan jikin sa da ya cire wanda yake riga long-sleeved da dogon wando , ya ɗauka ya mayar cikin jakar tare da haɗo ƴan sauran tarkacen sa duk ya zuba a ciki ,

Ya samu wuri ya zauna a gefen gadon ya jawo takalman sa mahaɗin kayan sa yana ɗaurawa a kafar sa ,

Duk abun da yake yakaka wacce take shirye tsaf a kishingiɗe a gefen gadon tana bin sa da kallon so da ƙauna haɗi da burge ta da duk wani motsi na sa yake , "

Tunani take ina ma ina ma ace wannan kyakkyawan mutumin da har yau bata kai ga sanin sunan sa ba duk kuwa da kusanci mafi girma da suka samu a tsakanin su , ina ma da zai AURE TA , ?
   Da ita kuwa ta gama jin daɗin rayuwa tare da nasarar rayuwa ,

Ɗago kan sa yayi ya kalle ta , ɗan gajeren murmushi yayi mata
    Yaya irin wannan kallo haka ƴan mata ?
Kayi kyau bature kam silum ," amma ina ta tambayar ka meyasa kai kayan ka ba irin na sauran sojoji ba , baka bani amsa ," 

A  takaice ya amsa mata saboda ni ba sojin ƙasar ku bane ,"

    To inane ƙasar ku ?

     Wani wuri ne mai nisan gaske ! ,"ya amsa mata

  Wallet ɗin sa ya ɗauka ya fiddo da dukkanin kuɗaɗen ciki , da suke sabbin ƴan dubu ɗai ɗaya , " ya tako ya zagayo ta bangaren da yakaka take ,
  Kamo hannun ta yayi tare da ɗora mata kuɗin ,"
  Ƴan mata ,( kamar yadda yake kiran ta tun haɗuwar su a zahiri ya manta sunan ta bai kuma taɓa damuwa ya sake tambayar ta sunan ta ba toh ina ruwan sa da sunan ta ? Amfanin me sunan zai masa ? )
    Ni zan tafi yau kuma bazan dawo nan kusa ba saboda yanayin aiki na , ƙila na dawo cikin sati biyu masu zuwa ƙila sai cikin wani watan watakila kuma .... Sai ya ɗan yi shiru  tare da duban fuskar ta ,"

Wacce tunda ya fara bayani idanuwan ta suka cika da ƙwalla , wani irin bugu zuciyar ta take yi ,

Zame hannun ta tayi kuɗin suka sauka akan katifar ,"  
        "ka bar kuɗin ka bature kam silum ba sai ka biya ni ba , ni dai dan Allah kar kace baza ka dawo yau ba , ka dawo dan Allah ni ko baka bani kuɗi ba zan taimaka maka kamar kullum , akwai wasu sauran kuɗin da kake bani ma ina tara su duk zan dawo maka da su ni dai dan Allah bana so na daina ganin ka , idan bana tare da kai zuciya ta bata min daɗi , na saba da kai .

tun da ta fara magana yake bin fuskar ta da kallo wacce kafin ta kammala ta jiƙe da ruwan hawaye , wani irin tausayin ta ne ya kama shi , tausayi mai tsanani , ya fahimci yarinyar ta faɗa a tarkon son sa , wanda shi kuma sam bai so hakan ba domin kuwa a zahiri bata da gurbi cikin rayuwar sa ko kaɗan , " shi kuwa ina zai kai ƴar talakawa marar galihu irin wannan yarinyar toh ya kai ta ina ? Masarautar su ? Ai auren ɗan sarki sai ƴar sarki idan kuwa ba ita ba toh sai fa ƴar manyan attajirai ," kai shi bai taɓa ɗaukar ta da wani matsayi ba ma da ya wuce macen da yake biya ta gusar masa da sha'awar sa , bata da wani banbanci da sauran karuwai !

  Duba ƴan mata ," ni akan aiki na zo ƙasar ku , batta kasancewa kullum mu zauna tare , ki ɗauki kuɗin ki riƙe a hannun ki zasu miki amfani watarana , ni akan hanya nake ," ki manta da ni kiyi rayuwar gaba har yanzu ke yarinya ce kin ji kou ? Tashi mu tai na sauke ki gida .

A motar ma share hawaye yakaka take sosai take jin ciwon barin ta da zai yi , yace wai ta manta da shi , anya ? Ita ta san baza ta iya mancewa da shi ba ," ya samu wani irin gurbi mai girma ya kafa kan sa cikin zuciyar ta ," 

kiran wayar sa shi ya katse shirun su , samun waje yayi ya tsayar da motar a gefen hanya , " nan ya amsa wayar
    Kira ne na gaggawa ake yi masa daga sansanin su na soji !

Da sauri ya buɗe murfin motar da hannu yake yiwa yakaka alama na ta sauƙa masa a mota ,"

Jikin ta a sanyaye ta sauƙa tana gama ficewa a motar ya ja murfin da ƙarfi ya harba motar bisa titi a guje .'

tsumu ta tsaya a gefen hanyar tana sake kallon kuɗin hannun ta ," kome bai mata daɗi wani irin ɗaci take ji daga ƙasan ran ta yana taso mata ,
  Matsawa tayi jikin wata mota da take tsaye a gefe ta jingina jin da tayi tsayuwa na neman gagarar ta ," kuka take son yi so take ta samu wuri tayi ta kuka ko zata ji saukin abun da take ji a ran ta , da gaske ya tafi bazai dawo ba ? ko wasa yake yi mata ?

Tun kafin ya tsallako titin daga ɗan shagon da ya tsaya ya saya kayan marmari a gefen titin ,  hasken ta ya dalle masa idanu , amma kasancewar sa mai tsananin kamun kai da nutsuwa babu ruwan sa da harkar mata (irin yadda samarin yanzu suke )  ya sa yayi saurin ɗauke kan sa ,

Har ya ƙaraso jikin motar da take jingine da take mallakin sa ce bai sake kallon inda take ba ,"

Murfin motar ya kama zai buɗe sannan ya juyo ya dube ta ,"
    Baiwar Allah zan ɗauke motar daga wurin ,!
    Ko gizau bata motsa ba
  Ɗan tsaki ya ja marar sauti , wasu matan dai basu da kamun kai dubi wannan yadda ta zo ta dogare a bakin titi duk masu wucewa idon su akan ta .
Ya sake maimaitawa da ɗan karfi ,
   Zan ɗauki motar nace baiwar Allah

a hankali ta juyo da fuskar ta inda take jin tashin muryar sa , kamar ta san muryar ,!
   Kallon juna suka yi ido cikin ido ,
Tsai yayi yana kallon ƙwarar idon ta , shin ita ce ne ko ba ita bace ? Ƙwarar idanun ta suna tabbatar masa ita ce wacce ya shafe fiye da watanni biyu yana neman ta tsakanin sansanin su da zagayen kasuwa ,wacce a karshe ƙawar ta tace sun gudu sun bar garin ," sai dai kuma yanayin shigar ta da gogewar da ya hango tare da wannan suna ƙarya ta masa ita ce , wacce ya sani ai ƴar ƙauye ce ƙazama , wannan kuwa ƴar birni ce wayayyiya kuma ƴar gayu ," kai sai dai kamanni ,

," da sauri ya saita kan sa daga ruɗanin da ganin kamar wacce yake bulayin nema ce ya sanya shi ,"

  Ya ɗaure fuska gami da maimaita maganar sa ta farko cikin ƙosawa ,"

A hankali ta janye jikin ta daga motar , "
    Ta gane shi sarai shine likitan da ya sha taimakon ta tun farkon zuwan ta garin ,"! Sai dai halin da zuciyar ta ke ciki a yanzu babu damar da zata tsaya yin magana da kowa ko da kuwa kalmar gaisuwa ce , domin tana buɗe baki kukan da take yi a zuci ne zai fito fili , dan haka ta ɗauke kan ta ,' ta matsa bakin titin sosai domin tarar adaidaita ya kai ta gida tayi jinyar gangar jiki da ruhin ta da tun yanzu suka fara kewar bature kam silum ,"

Tana matsawa a jikin motar ya shiga gami da jan motar sa , a cikin ran sa yana mamakin al'amarin hatta tafiyar su iri ɗaya ya furta hakan a fili yana sake leƙen ta ta jikin madubin motar ,"  gefe guda na ran sa ƙaunar yarinyar da har yau bai ko kai ga sanin sunan ta ba yana tasowa , ya so ƙwarai ya nemo ta , domin a ranar da suka bar asibiti ita da ƙanwar ta ba ƙaramin damuwa ya shiga ba , so yayi ya ɗauke su ya kai su gidan sa inda yake zama tare da mahaifin sa da ƙannen sa ya ɗau nawin su ya inganta rayuwar su ita da ƙanwar ta , ya sha wahalar neman su da kwatance su a sansanin su dakyar aka samu wacce ta san su aka ce tare suka zo , tashin farko da ya tambaye ta game da su tace da shi YAKAKA DA FALMATA SUN BAR GARIN .

Assalamu Alaykum  my dear sisters ! How are you guys doing today  ? I hope everything is well ? Please don't delete comments because I didn't reply straightaway . I hardly get time to come frequently , but I do dedicate some time every now and then to reply to y'all Insha Allah  !

I hope you guys enjoyed this chapter  ??  buckle up cause chapter twenty is going to be a sadness one! 

LET ME KNOW WHAT YOU GUYS THOUGHT ,PLEASE  COMMENT , VOTE, AND SHARE WITH YOUR FRIENDS AND FAMILY.
    THANK YOU .

   

     
   
[10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Mafari .......
( Hargitsin Rayuwa )


umm'muaz

21





A tsorace suka juyo , yakaka tayi arba da wani mutum jikin sa sanye da shuɗin kaya hannun sa ɗaya rike da wata ƙatuwar kulki , gefen sa kuwa wannan mutumin da take zaton sun yi masauƙi a bakin shagon sa ne

Nan take ran ta ya aina mata , ", ya ƙira musu jami'in tsaro ne ," dan haka ta matso falmata gami da sake riƙe hannun ta ƙam-ƙam ,

Daga chan inda yake tsaye yace !
Su waye ku ?
Kuma daga ina kuke ?
Meye kuma kuke tafe da shi a baccon hannu ku ?kuyi gaggawar sanar da mu kafin naje na kira sojoji .

Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoro .

Mu mune su falmata kuma mu ƴan gudun hijira ne daga ƙauyen mairambiri , kayan mu ne a cikin bacco .
    Falmata ta amsa musu cikin dakiya .

Wanne irin kayan ?

Kayan sawar mu .
    Suka haɗa baki wurin amsa masa !

Ku buɗe mu gani ?

filla-filla suka yi da suturun nasu , ba tare da gardama ba .

Meyasa kuke yawo da kaya ? Ina ne sansanin ku ? Bai kamata kuna yawo da jakar bacco ba saboda kun san halin da gari yake ciki ba'a yadda da duk wani mutum da aka gan shi da kaya niƙi-niƙi kuma yana nuƙu-nuƙu a cikin taron jama'a bare ma ku yara mata ga kuma irin yanayin ku , kowa ya gan ku dole zai zarge ku har ma ya tsora ta , saboda yadda mafi yawancin lokaci ake amfani da ku ta hanyar rataya muku nakiyar bam ku shiga taro ku tayar ,

Ku godewa Allah ma lokacin da na gan ku a bakin shago na ba jami'an soja ko na ɗan sanda na kira ba mai gadin kasuwa ne , da ace ɗaya daga cikin jimi'an tsaro ne da sai sun hukunta ku dan haka nake baku shawara da ku koma sansanin ku , ku ajiye wannan jakar kayan naku sannan idan ma zaku shigo gari harkokin ku sai ku shigo , yawon ku a haka hatsari ne ga rayuwar ku ,!

Duk wannan dogon bayanin da mutumin nan yake musu yakaka ta zurfafa cikin tunani , jin ya ambaci komawar su sansanin ƴan gudun hijira ,"
      Cikin ran ta ta ƙudurce baza su koma sansanin su ba , saboda tun bata tare da ciki ma ƙuƙaƙƙiyar wahala ce zaman sansani ƴan gudun hijira , sanan ga tozarci uwa uba fyaɗe da ake yi wa mata , to bare fa yanzu da take ɗauke da cikin da bashi da uba , ta koma sansanin su a gan ta da ciki ,? Tace aina ta samo shi ? Alhalin duk wanda ya san ta ya san ta ne a matsayin budurwa wacce bata taɓa aure ba ,

ai ta tabbatar fanne baza ta bar ta ta kurɓi ruwa ba zagi da aibatawar da zasu dunga mata sai ya samar mata da cuta , dan haka gara sun hakura da zaman sansanin sun nemi wani wurin fakewar ,"

Da wannan tunanin ta ɗago kan ta ta dubi mutumin , da taji falmata na bashi amsa da cewa

    Sun ɓata ne sun kuma manta sunan sansanin su .

Malam dan girman Allah ka taimaka mana ka samar mana da wurin da zamu dunga kwana , " bamu da kowa a garin nan mamar mu da ƙannen mu sun ɓata tun a ƙyauyen mu baban mu ya mutu , mijina ma ba'a san inda yake ba ,"
   Ta ƙarasa zancen tana mai sunkui da kai domin gujewa kallon rashin yadda da wannan mutumin yake jifan ta da shi ," cikin ranta kuwa kunyar sabuwar ƙaryar da ta gilla take yi ,

    Saitin inda take jin tashin sautin muryar yakaka ,  falmata ta maida fuskar ta , cikin ran ta tana mamakin yaushe su duka suka koyi ƙarya ? ?

Shiru yayi yana nazari , kwarai zai so ya taimakawa yaran ko dan kasancewar su mata , duk da cewa cikin ran sa ba wai ya gama aminta da zantukan su bane gaba ɗaya ,

toh amma shi ya san ba ƙaramar fitina zai tadawa kan sa ba muddin ya ɗauki yaran nan ya kai su gidan sa ya jefa su tsakanin matan sa uku ," yana da tabbacin sai an dafa su da ran su , shi kan sa ruwan gidan sai ya gagare shi shaa da kwanciyar hankali ,  dan haka da muguwar rawa gamma ƙin tashi .

Yarinya ni bani da wajen da zan kai ku , ku samu wurin kwana saboda yanzu duniya ta lalace ba'a saurin yadda da mutum . Alfarma ɗaya zan muku shine na yadda duk lokacin da dare yayi muku kuna tsakanin nan bakin kasuwa ku gangaro cikin rumfa ta ku kwana bazan hana ku ba ,' har ma tabarma zan ajiye muku , bayan na sanar da masu gadin kasuwa wanzuwar ku awurin kun ji ko ?

Ya furta hakan yana danne yanayin da yake ji na rashin kyautawa yana taso masa , ya san ba haka ya kamata yayi musu ba yasan taimakon da suke nema ya wuce wannan yasan bai ji tausayin su bai kuma basu kariya ba , toh sai dai yana jin iyakacin taimakon da zai iya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login