Showing 216001 words to 219000 words out of 411050 words
Chapter 73 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ɗaya .
Washegari
Tara na safe ta yi musu a ofishin Dr Williams inda bayan gaisuwa Suka makala pilot-in-ear a kunnuwan su
Da bayani game da irin matakin cutar Mama ya fara , yana cigaba da bayani kan magungunan da zasu ɗora ta akai wanda zai iya taimakawa wajen rage tasirin cutar da tsananin ta duk cikin harshen turanci
Falmata da ta ƙosa ta ji maganin da zai warkar mata da Mama ta katse Dr Williams da tambayar sa cikin harshen farasanci
Dr la drépanocytose peut-elle être guérie? ( shin cutar amosani jini tana warkewa ? )
Kai tsaye ya amsa mata da cewa cutar amosanin jini a halin yanzu ba'a kai ga gano maganin ta da za'a sha a warke ba a duniya sai dai hanya guda da ake yin amfani da ita wajen samun warakar cutar , hanyar ita ce dashen Ɓargo ,
Ana yin dashen Ɓargo/dashen ƙwayoyin jini ga masu ɗauke da cutar amosanin jini daga kan masu shekaru bakwai zuwa sama ,
ana amfani ne da ɓargon dake jikin ɗan uwa/ƴar uwa na jini ga marar lafiyan wanda jinin su ya zo ɗaya .
Duk da ba'a da tabbaci na samun waraka baki ɗaya ga mai ɗauke da wannan cutar bayan an masa dashen ɓargo amma fiye da kashi hamsin na waɗanda aka yiwa aikin an samu nasara sun samu waraka daga cutar baki ɗaya,
Sai dai akwai yiwuwar hatsari a yayin aikin da bayan yin sa , zai iya kawo hauhawar wasu cututtukan da yake tsakanin Rayuwa da Mutuwa da kashi hamsin cikin ɗari .
Bayan ɗan uwa ko ƴar uwa shin mahaifiya zata iya bada kwayoyin jinin/Ɓargon ta ga ƴar ta ??
Baza ta iya ba , sai dai idan an rasa ɗan uwa ko ƴar uwar da suka haurawa shekarun balaga , ana amfani da ƙwayoyin jinin cibiya na ɗan da ke cikin mahaifiyar sa da ya kasance ɗan uwa ne ga shi marar lafiya da jinin su ya zo ɗaya .
A hankali Falmata ta zare Ambassador dake kunnuwan ta , hawayen idanun ta na sauƙa bisa kan hular Mama da take cinyar ta ,
Ashe cutar Mama Babba ce daga cikin manyan cutuka , ? Tausayi me tsanani ya taso mata yana kassara gaɓɓan jikin ta . Rungumeta tayi tsam a jikin ta , tana shafar bayan ta .
Mama bata da ɗan uwan da zai iya sadauƙar da jini da ɓargon sa a gare ta , a halin yanzu
Bani da damar sadauƙar miki da jini ko ɓargo na Mama .
Amma ina da damar zama uwar jaririn da zai sadauƙar miki da jinin sa Mama tun kafin ya zo duniya ..
Jama'a duk mu diba , shekara biyar yau a cikin wata na goma , shugaban mu babban mu ya nuna hanya na gyaran ƙasar mu , Sannu , sannu ,kwana nesa , sannu bata hana zuwa , Allah kare ƙasar ta mu Rabbana dai ya riƙa
Hehehe ,ina ƴan 80s ? Ku zo mu chafke , wayyo jiya ba yau ba! 😢
duk wacce /wanda bai san lokacin da aka yi yayin saka waƙar nan ta ƴan matan Niger a gidan Tv Nigerian television Authority Ba,? Ko kuwa mutum yana ɗan ɓingilin yaron sa ko mitsilar yarinya , ko kuma jaririya/jariri ? 😂 to ya gusa daga nan manyan yayun sa ne ke baje koli . Ehe ,( ah kai ƙannen mu ƴan 2000 Ayi shiru kawai a wuce wajen nace ayi hiru babies )
A
ssalamu Alaikum waramatullah
ƴan uwa maza da mata , ina miƙa saƙon gaisuwa tare da fatan alheri agare ku baki ɗaya .
Kamar koyaushe ina mai sake miƙa godiya ta bisa ga yadda kuke bayyana ƙaunar ku tare da jimirin bibiyar littafin nan duk kuwa da irin tarin tsaiko da tsaye-tsaye , tafiyar tsutsa kai har ma da ta kunkuru wani zubin ma ana taɓa salon takun hawainiya a yayin rubutun nan lol # duk babu kome Tafiya sannu bata hana zuwa insha Allah wataran zamu kai ƙarshen sa .
Masu ƙiran waya tare da barmin saƙonni dubiyar yara , Nagode ƙwarai ƙwarai Alherin Allah ya cimm muku a duk inda kuke . Jikin yara Alhamdulillah sun warware .
Idan nace ina da tarin aiyukan da suke katange ni daga taɓa wayar kan ta , za ku iya cewa ba gaske ne ba , sai dai hakan ba zai taɓa zama baƙon lamari ba ga Mamar Yara , Ƴar kwaɗago , kuma Ɗaliba , huh !
Nagode .
[10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Fikra writers association
MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)
umm'muaz
34
Fiye da awa ɗaya Samy baby ta kwashe tana shirya Yakaka , wacce ta sha fama da kanta kafin ta iya tsayar da hawayenta batare da bari Samy baby ta fahimci cewa ta san manufar ta ba ,
Wacce ta shagaltu wajen shirya ta tana jaan ta da hirararrakin da suka shafi jin daɗin duniya , wankan da kansa so tayi ta wanke ta sai dan ganin ba fuska ya sanya ta tsayawa daga bakin ƙofar banɗakin tana sake jaddada mata ta fa yi wankan nan siral ta fita , domin inda zasu tafi waje ne na manyan ƴan gayu kar ta sake tayi abinda zata jawa kan ta raini ,
Daga cikin banɗakin nan ta ci kukan ta a ƙarshe ta tattara duk wani tunani nata da Allah ya mata baiwar sa ,ta matse ƙwaƙwalwar ta, ta haɗa kai da bango akan tunanin hanyar da zata bi ta samarwa da kan ta mafita .
Ƙarfe baƙwai na dare suka fita a motar Samy baby dukkanin su sun ɗau kwalliyya ta gani a faɗa ,
Duk da fuskar Yakaka a tamke take da bayyanannen ɓacin rai hakan bai hana kyaun da tayi ratsowa ba , dai-dai tana karya kan motar ta fito kan titi sosai Samy baby ta dubi sashin Yakaka a kaikaice ,
Yanzu ke Yaks meye haka ? Dan asara akan na hana ki saka wannan uban barigizan hijabin naki shine kike wannan ƙuncin ? Mts!
Ji wannan ƙatuwar jakar da kika ɗauko kamar wata wanzamiya na faɗa miki bata dace da ƙwalliyar nan ba , ƙwalliyar nan taki ba ta babbar jaka bace ta ƴar ƙaramar jakar hannu ce amma kin ƙi ji , ai daman ɗan ƙauye sai ya shekara hamsin a birni yake barin ƙauyenci da gidadanci , ke kika sani sautun mahaukaciya !
Ta danna motar da gudun gaske suka cilla kan titi cikin manyan unguwannin abuja da ko sau ɗaya Yakaka bata taɓa kai ƙafar ta bigiren ba tun zuwan ta garin .
Bata cewa samy ƙala ba illa sake rungume jakar ta da tayi wanda a ciki ta saka hijabinta da niƙab ɗin ta , ƙwaƙwalwar ta a hargitse take da sabon tsoron da yake mamayar ta ,
Ƙofar wani tafakeken gida samy baby ta tsaya tare da zaro wayar ta ta latsa lamba , bugu ɗaya ya ɗauka
Gamu mun iso tace tare da sauƙe wayar daga kunnen ta ,
ba'a yi mintuna uku ba sai maigadi ya buɗe musu ƙofar gidan , samy baby ta danna kan motar a hankali
shigar su gidan yazo dai-dai da ƙaruwar firgici a fuskar yakaka , saboda girman gidan da ya wuce hankalin ta ga fitulu da suke a watse birjik a harabar gidan haske ya wadata tamkar tsakar rana ,
Gefen wasu tsirarun motoci da basu wuce guda shida ba samy baby ta ajiye motar ta ,
Muje Yaks ,
A tsorace ta fito tana bin gidan da kallo , ba tare da samy baby ta kula ta ba tayi gaba , cikin jaan ƙafafu ta bita a baya maƙale da jakar ta , suka dumfari katafaren ginin da yake tsaye a gaban su ,
Babu yalwar mutane a babban ɗakin hutawar da suka shiga , mata da mazan da suke harkokin su a wajen babu wanda ya kula su ,
Samy baby ta jagorance su suka zauna , basu jima da zama ba aka murɗo ɗaya daga cikin ƙofofin da suke ta cikin falon aka shigo ,
Kamal ne ya shigo yana ɗan gama hanya ya ƙaraso tare da sakin jiki ya faɗa kan kujerar kusa da yakaka , rigijib !
a tsorace ta miƙe tana raba ido .
Idanun sa da suka yi nawi saboda kayan mayen da ya ɗibga ya ɗaga ya watsa mata wani kallon ƙasƙanci ,
Ke wai ji mana , ya kike wani safurewa haka kina wani ƙoƙarin waskewa , ? Kamar baki da sanin cewa na biya kuɗin ki , zo nan na fara morar kuɗi na dallah
Ya miƙa hannu ya fisgota ta koma da ƙarfi ta zauna ,
Ganin sa ya mayar kan Samy baby
Yane to yawa kike fa, Zaman me kike ? Ko kina neman me tayi ne ? Nan duk suna da chicks ɗin su dan haka ki ƙara gaba ,..
Ke kuma zo muje ki fara tausa min gaɓɓai da waɗannan tausasan hannuwan naki tuɓus-tuɓus , wayyo laushi!
Ya fisgi hannun Yakaka suka miƙe tsaye ,
Fuskar samy baby ta kalla , idanunsu suka gauraya cikin na juna ,
Ga mamakin samy baby ba kamar yadda ta zaci zata ga hawaye a idanun yakaka ba , saɓanin ta idanun ta a bushe suke ƙyamas ,ɗauke da wani irin yanayi wanda yayi tasiri ƙwarai wajen rage mata kuzarin tashi ta bar gurin kamar yadda aka mata umarni ,
Kallon da yakaka take mata kallo ne me kaifi da yake ɗauke da fasasarori da dama ,wanda ta gaza ɗaukar masa fassara guda ,
tana ganin lokacin da ta fisge hannun ta daga cikin na kamal ɗin ta nufi ƙofar da ta ga ya nufa da ita , ba tare da ta sake waiwayowa gare ta ba ,
A sanyaye ta miƙe cikin ran ta tana harhaɗa kalmomin da zata yi amfani da su wajen kalmaso kan yakaka ta rarrashe ta kamar yadda ta saba yi mata a duk lokacin da tayi mata wani gagarumin laifi ,
gefe guda tana tunanin ware wani kaso me ɗan tsoka daga cikin kuɗin da kamal ɗin ya bata ta danƙa mata su duk domin su taimaka wajen shawo kan ta cikin sauki.
Da wannan tunanin ta faɗa motar ta bar gidan tana duban agogon hannun ta da yake nuna ƙarfe tara saura ƴan mintoci , sama ta haskaka da hadarin da yake haɗuwa da ke nuni da koyaushe cikin dare ruwa zai iya sauƙa .
Kar ka kuskura ka sake taɓani ,
Ta ce da shi lokacin da take samun wajen zama bisa kan kujerar gaban tafkeken gadon ɗakin na alfarma .
Wata dariya ya kwashe da ita yayi sufa ya faɗa gadon rubda ciki .
Kai yarinyar nan salon ki na burge ni , wat....
Zan sha BURKUTU ,
Ya tsinkayi muryar ta ta katse masa kalaman sa , waigowa yayi yana daga kwance ya dube ta , fuskar sa na bayyana mamaki yace :
Burkutu ?
Eh
tace da shi tana tsattsare shi da idanun ta ,
Ni bana shan giyar gargajiya ,"blue moon ," ita ce giyar da nafi ƙauna , yanzu ma ita na sha ƴar kaɗan , kin san tana da ƙarfi shegiyar giya ce , ko za ki iya sha na zubo miki kaɗan ki taɓa irin ta ?
Kawo min
ta ce da shi a taikaice .
Miƙewa yayi ya fita
Yana fita ta miƙe tsaye ta shiga kai kawo a ɗakin tana yarfe hannu , da tayi zaton zata iya , a zaton ta tana da ƙarfin zuciya , ya kome yake shirin kufce mata ? Me zai faru da ita idan har shirin ta bai tafi dai-dai ba , ??
Jin motsin taɓa ƙofar ya sa tayi saurin komawa ta zauna ,
Ya shigo hannun sa ɗaya riƙe da kwalbar giyar blue moon ɗaya kuma kofin gilashi da ya zubo ƴar ƙanƙara a ciki ,
Zuba giyar yayi ƴar madaidaiciya ya miƙa mata ,
Idanun ta na duba ƙasa ta ce da shi ka fara sha ,
Jim yayi riƙe da kofin sai kuma ya kai bakin sa ya ɗan kurɓa ,
Ya Sake miƙa mata ,
Ka cika min taf
Tace da shi ba tare da ta bari sun haɗa ido ba ,
Keeeee hahaha , wannan fa blue moon ce ba'a mata haɗama yanzu nan za ki ji ki warwas kin gaza motsi, ba ta wasa bace wannan , ke kin san kuɗin ta kuwa ? Yafi jarin baban ki .
Bana shan wannan , warin ta bai min daɗi ba ka kawo min wata idan akwai , nafi son wacce zata ƙara min kuzari ,
Ɓata rai yayi ! ya tsaya kallon ta sai kuma ya kwashe da wata dariyar sakarci ,
Tunda ta ƙara kuzari kike nema bari na kawo miki Amstel kina shanta yau ji za kiyi kamar an miki allurar da ake yiwa dawakai ,
Ya ƙarasa zancen yana kafa kai ya sha fiye da rabin wacce ya zuba a kofin ya ajiye sauran ya fita yana gama hanya tare da jaan wani siririn fito irin na wanda duniya ta yiwa daɗi .
Yana fita ta miƙe tare da murɗa ƙofar ta fito , ɗan yawatawa tayi da idanun ta cikin daƙiƙoƙi ta fahimci ɗaukewar ƙafar da ya ƙaru a wajen domin mutum ɗaya ta hango a zaune ya tasa kwalaban giya a gaban sa ,
Da sassarfar da take harɗe kafafun ta ta taka tana nufar ƙofar ficewa daga wajen bakin ta ɗauke da addu'o'i iri-iri ,
Siit ji mana , ?
Numfashin ta ya nemi siƙewa da jin muryar wani yana dakatar da ita , bata juya ba sai ma ƙaimi da ta ƙara ba tare da ta bari ta ƙarasa jikin ƙofar ba ta miƙe hannuwan ta duk biyu ta tura ƙofar , ta jefa ƙafar ta waje .
Tana jin sa yana sake sanar da ita ba fa nan kamal ɗin yake ba ,
Ba ta saurare shi ba , ta kara da saurin da yafi kusa da gudu tana keta farfajiyar gidan ta nufi ƙofar da suka shigo gidan ,
Ƴar ƙaramar kofar da take maƙale da babbar ƙofar gidan ta nufa kai tsaye ta tura ta , cikin sa'a ƙofar ta buɗu da gudun gaske ta ƙarasa ficewa daga gidan ,
Tsawa tare da rugugin hadari da ya karaɗe sararin sama bai toshe mata kunne daga barin jin tashin muryar kamal ba , hakan ya sa a diririce ta tura ƙaramar ƙofar gidan da yake daura da ita ta faɗa ,
Ga babbar sa'ar ta babu kowa a harabar ɗan madaidaicin gidan me tsari , dan haka cikin sauri ta cire hijabin ta daga cikin jakar ta ta zira akan kayan ta , ta sake zaro niƙabin ta ta fara ƙoƙarin ɗaurawa ,
Gurnanin da ta ji daga gefen ta kaɗan shi yasa zuciyar ta dokawa da ƙarfi , tare da taimakon hasken ƙwan lantarkin ta waiga da sauri idanun ta suka shiga cikin na wani ƙosasshen kare da yake kwance daga gefe kusa da ita ,
Ɓurɓushin tsoron daga ƙasan ran ta ya fara toroƙo kafin baki ɗayan jikin ta ya ɗauki rawa ,
Cikin abunda yake gaza da minti guda ta juya da gudun gaske ta fita a gidan tana banko ƙofar , karen kuwa bai jinkirta ba ya rufa mata baya da ƙaƙƙarfan haushin sa , suka zuba ƴar tsare akan titin da yake shal babu kowa saboda dare da ya fara yi ƙarfe goma saura , haɗi da garin da yake gangame da hadari .
Gudu take tamkar wacce aka ɗaurawa tayoyi a ƙafa , bata san gabas ba bare yamma , karen wanda haushin sa ya jawo ƴan uwan sa karnai na bakin titi suka zama su uku , su ma bin ta suke da iyakar gudun su .
Ruwan saman da ya tsinke kamar da bakin ƙwarya shi ya sake gigita yakaka , har numfashin ta na barazanar ɗaukewa duhu na fara mamaye ganin ta .
Hakan shi ya hana ta fahimci karnukan sun koma baya sun daina bin ta tunda ruwan saman ya fara sauƙa .
Duk da cewa dare ne kuma titin babu kowa , amma shi ka'idar tukin sa ne haka baya cika gudu , sannu-sannu yake tuƙin sa cikin nutsuwa ƙira'ar Sheik Sudais cikin Suratul Al-Araf tana tashi ta cikin sifiƙun motar , fitowar sa kenan daga asibiti inda ya yini yana wasu muhimman aiyuka ( shigar da bayanai akan marasa lafiyan da yake ɗauke da alhakin duba su ) saboda hutu da yake son rubutawa na sati shidda ya je gida ya gaida iyayen sa , sannan yayi amfani da damar wajen sasantan tsakanin iyayen sa ,
lokaci yayi da yakamata ace an kawo ƙarshen koma menene ya jawo rabuwar ta su tsawon waɗannan shekarun , ga su suna zaune babu abokan rayuwa wanda hakan ko kusa ba martabar su bane , duba da cewa shekarun su sun fara jaa ,
À son ransa a maida auren iyayen nasu kafin bikin Rahima wanda za'a yi a farkon sabuwar shekara me kamawa nan da watanni bakwai masu zuwa ,
Bai yi aune ba ta ɓullo daga kwanar gaban sa da gudun gaske , da ba domin a hankali yake tafiyar ba da babu abunda zai hana ya yi ciki da ita da mota.
Da ƙarfin gaske ya jaa burki ganin yadda ta bugu da jikin motar ta sa , ruwan saman bai hana shi ɓalle murfin motar ya fito ba , ya zagayo da sauri ta sashin da take dai-dai lokacin da ta miƙe tsaye daga faɗuwar da tayi ,
Da gudun ta tayi bayan sa ta ɓuya bayan ta riƙe jikin rigar sa ƙam da dukkanin hannuwan ta biyu , jikin ta ko'ina rawa yake .
Tsai yayi yana jin yadda wani nisasshen yanayi a wani shuɗaɗɗen lokaci makamancin wannan yana bijiro masa ,
KARE , KARNUKA su na bina dan Allah ka taimaka min , zasu kashe ni .
Muryar ta tayi amsa kuwwa a kunnuwan sa ta tafi ta tado ƴar uwar ta da take binne cikin ran sa me ɗauke da salo da kalmomi iri ɗaya da suka fito a jere cikin yanayi me kama sak