Showing 255001 words to 258000 words out of 411050 words

Chapter 86 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14366

Rigar sanyi ribbed sweater ta ɗaura hular sanyi akanta ,

Ta fito ta cimma masa yana zaune a ƙasa ya jingina bayan sa da kujera , hannun sa biyu tallafe da ƙeyarsa ,

Babu wadatar haske a falon saboda duhun dare da ya shigo fitilar falon kuma ɗaya ce a kunne , kasantuwar idanun nata ba gani suke sosai ba , ya sa bata ma kai ga ganin sa a wajen ba sai duhu-duhu take gani ,

"Fatima ,

Ya ƙira sunan ta lokacin da ya ga ta kashe ƙafa daga ƙofar ɗakin , alamun tana buƙatar ɗan jagora ,

"zo nan ,

Yace da ita

Inda take iya hango duhun sa ta nufa a hankali ,

kallo yake bin ta da shi ganin yadda kayan suka karɓi jikinta musamman ɗan wondon da bai kai ga sauka ƙasa ba , daga ƙungunta ya zauna ɗas saboda ɗaura shi da tayi akan rigar .

Hannun ta ya kama ya ƙarasa zaunar da ita akan jikinsa yana jin yadda ƙamshin daddaɗan turaren da ta fesa yana ratsa hancin sa ,

Lamo tayi a jikin sa tana jin damuwar rashin walwalar sa na damun ta ,

" Alhamdulillah Mama ta samu sauƙi ko ?

Tace da shi da dabarar son jin maƙasudin damuwar sa ,

"Mama ta samu sauƙi Alhamdulillah ,

Ya ce yana ƙanƙameta a jikin sa ,

"Har hankalin mu ya kwanta , bana son ciwon Mama ina tausayinta ,

"Fatima zamou kassance cikin shiri zouwa wassu kwanaki nan gaba zamou koma gida ,

" ɗago kanta tayi da son ganin fuskar ko Allah zai sa ta fahimci damuwar sa ,

"Baban Mama na ɗauka sai an samu lafiyar Mama ?

Zai yi Magana wayar sa tayi ƙara ,

Ganin sunan Hajiya Umma a fuskar wayar ya sa zuciyar sa tsinkewa ,

Da sallama ya ɗau wayar , sai dai yadda ya ji ta amsa masa ya sa jin hankalinsa ya sake tashi ,

Sama-sama ta amsa gaisuwar sa , bayan nan abunda ta sanar da shi shine kawai duk me yake ya nemi izni ya taho gida cikin kwanakin nan kusa .

Shiru yayi bayan ya ajiye wayar , tabbas akwai abunda ke wakana game da shi a gida .

"Baban Mama...

Ya katse hanzarin ta

"Fatima zamou kouma gida , a gaba zamou dawo neman lafiyar Mama ,

Sai ta mayar da kan ta jikin sa tayi shiru , baki ɗaya walwalar da ta ɗan samu na murnar samun sauƙin Mama ta kau ,

Daren ranar babu wani armashi agare su musamman ma Falmata da damuwar da take ciki ta haifar mata da zazzaɓi da ɗan ciwon kai , dan haka washegari ta tashi haka sukuku ,

Karin kumallo ma sama-sama suka yi ,

Bayan sun gama karin kumallo su dukkanin su biyun sun yi shiru sai mama ce take ɗan wasan ta ,

" J'ai réservé notre vol, nous rentrerons à la maison le 18 le mois prochain , ( nayi mana tanadin jirgin komawa , zamu tafi ranar sha takwas ga watan gobe , )

Muryar sa ratso shirun wajen ,

"Allah ya kaimu Baban Mama , ko zaka sanarwar da Hajja itama ta fara shiri ko ?

"Eh zan sanar da ita idan ya ragge kwanaki goma mu tafi sai tayi shiru cikin kwanaki biyar , idan ya rage kwanaki biyar da tafiyar mu sai direba ya ɗaukota daga Nigeria ,

"To Allah ya kaimu ,

****

Wasa gaske cikin 'Yan kwanakin Youssouf ya gaza samun kwanciyar hankali tsoro ne cike taf a ransa , duk kuwa da cewa babu wanda ya sake neman sa kan wani batu sai dai yana tsoro ne kar ko tana ƙasa tana dabo .

Falmata har ta gaji da tambayar sa akan yadda ya zama koyaushe cikin tunani babu nutsuwar kirki , 'yar soyayyar da yake gwada mata mai sanyi da shiga zuci duk ya rage a wasu lokutan ma raba dare yake tunani , da juye-juye ,

Kasantuwar daman ita mace ce marar hayaniya mai kammalewa sai bata tsananta shisshige masa ba ta ɗan janye jikinta itama ta maida hankalinta baki ɗaya kan Mama ,

da kuma fama da kanta da take yi saboda wani ciwon kai marar daɗi da yake addabar ta tare da bugun zuciya fiye da ƙima duk tayi wata 'yar hidima sai ta ji mummunar gajiya da bugun numfashi sun taso mata ,

Mama da kanta ta san cewa Babanta ya rage kula da dararrakin ta sosai saboda duk ta dame shi zai samu ya zameta ya shiga ɗaki ya rufe ,

Ya rage sati biyu tafiyar su da ya ke tsawon kwanaki kusan goma da yin wayar sa da Tafeeda , wanda duk yadda ya so ya samu damar da zasu sake yin wata magana , Tafeedan yaƙi ba shi haɗin kai idan ya ƙira wayar sa ba bai ɗauka saƙonnin sa kuwa ya tura su babu adadi ta kan yanar gizo da kai tsaye ta hanyar saƙon karta kwana , nan ma ga shaidar an karanta sako amma babu amsa , dan haka shima ya zuciya ya daina neman sa .

Ya fito wanka da safe ya tarar da miss call ɗin Tafeeda , da hanzari ya ɗau wayar bai ko tsaya shafa mai ya sanya kaya ba ya ɗau wayar ya shiga neman layin sa ,

Sai dai kakarun Amai da ya jiyo daga Falon su ya sanya shi sauƙe wayar daga kunnen sa ba tare da ya kashe wayar ba ya fito falon hankalinsa a tashe ya ƙaraso ga Falmata wacce take durƙushe daga ƙofar kitchen ɗin su tana Amai ,

Da hanzari ya ƙaraso wajen ya riƙo ta zuwa jikin sa bayan ya ajiye wayar sa a ƙasa da aka riga aka ɗaga kiran daga ɗaya ɓangaren ba tare da ya sani ba ,

"qu'est-ce qui ne va pas avec toi chérie, es-tu malade? ( me yake damun ki ? Baki da lafiya ne ? )

Bata amsa ba illa yunƙurin Aman da ta cigaba da yi duk kuwa da babu kome a cikin nata ,

Shafa bayanta ya shiga yi yana ɗan bubbugawa tare da jero mata sannu ,

Mama wacce tashin ta kenan daga bacci ta jiyo muryar su ta fito , itama ta tsaya tana kallon su fuskar  ɗauke da alhini da 'yar muryar tace

"Papa qu'est-ce qui ne va pas avec Mamma ?

"Princess Maman ki bata da lafiya ne, dauko min papier mouchoir dagga ɗaki na goge mata baki ,

"To ,

Ta juya da ɗan gudu zuwa ɗakin su ,

"Sannu Fatima ,

Yace cike da tausayawa , 

Daga can ɓangaren Hawaye masu ɗumi suka silmiyo daga idanun Hajiya Umma , ta zare wayar Tafeeda daga kunnen ta tare da miƙa masa wayar ,

Karɓar wayar yayi ya duba wayar yaga ba'a katse ta ba dan haka cike da tashin hankali ya kara a kunnen sa yana fargabar ko wani abu ne ya faru da Youssouf ɗin ,

Sai dai ya ƙarashi Maganar sa bai ji Youssouf ɗin ya amsa ba , sai muryar wata mace yake ji ƙasa-ƙasa , dan haka ya katse wayar waigo ga Hajiya Umma ,

"Umma Lafiya Yarima yake kou ?

"babu shakka lafiya yake ,
ta amsa da wata irin murya ,

Ganin yanayin ta ya sa Tafeeda miƙewa yayi mata sallama zuciyar sa cike da tunanin meye haka Youssouf ya faɗi wanda ya sa Hajiya Umma ƙwalla ?

Shi daman zouwa yayi ya gaishe ta tare da cigaba da kwantar mata da hankali bayan tashin hankalin da ta shiga a kwanaki sakamakon wani Al'amari mai girma da ya taso game da Youssouf ɗin ,

wanda shi yayi tsayuwar daka wajen ganin lamarin ya dai-daita da a yanzu yake mataki na ƙarshe na gyara kome wanda kuwa hakan ba zai samu ba sai da haɗin kan Youssouf ɗin ,

tunanin ko zai yadda da lamarin da zai je masa da shi a matsayin shawara ko ba zai yadda ba ya sanya shi yin jinkiri yana nazari dan haka nema yaƙi yarda suyi magana da Youssouf ɗin

Sai fa yau da Hajiya Umma ta sa ya ƙira sa a gabanta ta warware masa labarin mummunan ƙullin da aka so yi masa ,

Sai kuma ya ga Umma ta ƙare wayar ba tare da ta ce kome ba sai ƙwalla , lamarin da ya ƙulle masa kai kenan , koma menene zai ƙira Youssouf ɗin ya ji .

A ɓangaren Su Youssouf bayan Falmata ta gama Amai ya gyara wajen ya ɗau wayarsa bai lura da Shaidar an ɗaga ƙiransa ba saboda hankalinsa da yake kan Falmata wacce sai numfarfashi take saboda ƙaruwar bugun zuciyar ta tare da ciwon kai da ya haɗu mata ,

Ko sannu da Youssouf yake yi mata da kyar take amsawa ,

"Fatima ko mu tahi hospitalisé ne ?

Jikin ta babu kuzari ta gyada kai ,

Cikin hanzari ya shiga ya shirya ya wankewa Mama jiki tare da goge mata baki , ya dawo ya tarar da ita tana baccin zomo ,

"Fatima mu je ki shirya ,

Shi da kansa ya taya ta ta gyara jikinta yana riƙe da hannun ta suka fito

" za ki iya tafiya da kan ki ko kuwa na ƙira taxi ,

"zan iya tafiya ,

Basu sha wata wahala ba kasantuwar daman tana kan ziyartar likita , dan haka suka samu ganin likitan ta inda shi kuma bayan tambayoyin da yayi mata da duk bayanan da ta ba shi , ya miƙa su ga wata likita daban , wacce ta sake yi mata tambayoyi ,

Daga haka ta yi mata gwaji , bayan bayyanar sakamako ,

da fara'a likitar take miƙa musu sakon taya murnar cewa Falmata tana ɗauke da ciki na tsawon sati huɗu ,

Duk da cewa Falmata tana jin yaren faransanci babu laifi , Amma a yau ji tayi sam bata Fahimci me likitar ke nufi ba , tamkar ta manta ma'anar kalmar ,

Sai da ta ga Biyamuradi Youssouf ya rungume ta , yana bayyana farin-cikin sa da lokaci guda Albishirin da likitar tayi masa ya wanke masa zuciya tare da yin awun gaba da duk wata damuwa tasa , "Ya'ya ai arziƙi ne .

"Fatima Tu es enceinte, tu portes mon bébé , Alhamdulillah

Ya ɗago fuskar ta ya sumbanci goshin ta ,

Hannunta ta kai kan nasa hannun da yake tallafe da kumatun ta , kyawawan idanun ta na bayyana farin-cikin dake maƙare da zuciyar da

"Baban Mama da gaske ina da ciki ? Zan haifi jariri daga cikina Mama Zata samu dan uwa , Mama zata wa....

Katse ta yayi ta hanya ɗora laɓɓansa akan nata ya sumbace ta ,

"Mama da Yumna zasu samu ɗan ouwa ko ƴar ouwa insha Allah nayi Farin-ciki Fatima .

Mama da take tsaye tana kallon su ba tare da ta san me suke yiwa murna ba , sai ita ma ta sa dariya ta taho ta rungumo su ,

Hannuwansa ya sa ya zagaye a jikinsa yana jin waɗannan rayukan guda biyu sun zama wani ɓangare na daga rayuwar sa ,

Da wannan farin-cikin me tarin yawa suka baro asibitin zuwa gida , bayan likita ta basu shawarwari tare da  'yan magungunan da zasu taimaka a matakin farko na zaman ciki .

Falmata Ji take babu wata rana da take kai wannan ranar farin-ciki a wajen ta , minti kaɗan zata kai hannu ta shafi cikin ta , farin-cikin ta biyu ne ,

Tana ganin cewa lokacin warkewar Mama yayi tunda gata ɗauke da ciki ,

Da shigowarsu gida wayar sa tayi ƙara  Tafeeda ne ya sake ƙiran farin-cikin sa bai ɓuya ba a muryar sa suka gaisa da Tafeeda ,

Kafin Tafeeda ya ɗora da cewa ,

"Yarima magana nake so muyi kou ka bani dama ?

Jin haka sai ya miƙe daga jikin Falmata ya fita zuwa 'yar barandar gaban gidan ,

"ɗan ouwa na baka dama faɗi ina jin ka ,

Yace masa a taƙaice ,

"Magana ce zamu yi game da lamarin yarinyar nan da kake boyen sa gareni tsawon wannan shekaru , na riga nasan koume kan zaman ka tare da su da amren innan ita yarinyar da kake har gidan da kun ka tare a Niamey na shina Yarima ,

"To munin Al'amarin ba dagga gareni yake ba , sai fa dagga maƙiya waɗanda sunka dunga bin lamarinka , a cikin binciken da nai kai tamkar da sanya hannun su kome da ya faru ya kai ga faruwa  ,

"Lamari ya munana ta inda zance ya taho ga Fada ya iske kunnen Maimartaba da Hajiya Umma bai tsaya nan ba har sai da ya iske mutanen cikin Fada baki ɗai ba'a kouma san waye ya fiddo maganar ba ,

"cewa Yariman Maraɗi yana da ɗiyar banza bata Amre ba , tare da yin zaman banza da Mahaifiyar ta zaman dadiro , tun dagga Nigeria ,

"Yarima nayi duk bakin ƙoƙarina wajen ganin anbi daddigin masu yaɗa maganar nan an dakile bazuwar ta , kouma anyi nasara ,sannan na ƙaryata batun gaban moutanen cikin fada tare da Maimartaba ,

"Amma nasan wannan yunƙuri nawa ai bai isa ba ya kawo ƙarshen maganar nan tunda kouwa akwai ta da gaskiya , maƙiya ba za su bar lamarin nan ba .

"Menene mafita a yanzou ?

Youssouf ya katse dogon bayanin da Tafeeda ke yi masa ,cikin miƙa wuya

'Mafita gouda ce ,ka rabu da ita wannan yarinyar da kake amre , ka sallame su su tafi tare da ɗiyar nan ,

"ka rabou da ita domin tsarkake kan ka dagga zargin al'umma ,tare da aibatawa ,

"ka rabou da ita domin tsira da mutuncin tare da ƙimar ka ,

"ka rabou da ita doumin gujewa russa alaƙar ka da iyaye da 'yan ouwan ka ,

"ka rabou da ita doumin gujewa samar da bakin-ciki a zuciyar Mahaifiyar ka ,

"ka rabou da ita domin gudun samun galabar maƙiya a kan ka ,

"ka rabou da ita domin tsarkake masarautar ku tare da kaiwa ga matakin nasarar zama sarkin maraɗi a watarana .

"ka nesanta kan ka daga wannan ɗiya da innarta doumin tsallake ramin maƙiya , muddin ka ƙiya ? Za ka gamou da dariyar maƙiya da baƙin-cikin iyayen ka .

"cigaba da zama da itta yana nufin rassa kowa tare da kai ciki kouwa har da ni kaina .

"Tafeeda ,

Youssouf ya ƙira shi da wata irin murya mai cike da tashin hankali ,

"Yarima shawara ce ni na baka zaɓi yana dagga gare ka , ni na barka lafiya ,

Wani iri yake ji tamkar an zare masa laka , menene yake shirin Faruwa da rayuwarsa ne ?

Kalmar Rabuwa da Fatima tayi masa nawin saurara ko a kunne kawai ,

To amma kuma shi ya zai yi ne? Ji yake kamar an raɓa ƙwaƙwalwarsa da duk wata tunani .

Cigaba yayi da tsayuwa a wajen ya gaza motsawa

Hannuwan ta ya ji sun ratsa kirjin sa daga bayan sa ta rungume shi , tare da kwantar da kan ta a bayan sa ,
Cikin sanyin muryar ta tace

"Baban Mama tun ɗazu nake jiran ka , kazo muyi Sallah mu godewa Allah , akan wannan babban arziƙi da ya bamu .

Hannu ya kai ya zagayo da ita ta gaban shi ,

Kallon fuskarta da take ɗauke da tsantsar farin-ciki yayi , suɓul da ita sai ƙyalli take tare da wani irin haske na musamman da ta ƙara a 'yan kwanakin nan,

Ji yayi tsikar jikinsa ta tashi dawowar kalaman Tafeeda cikin kunnuwan sa yasa jinin jikin sa tsinkewa ,

"Fatima ina son ki dayawa , je t'aime tellement Fatima

Yace da wata irin murya lokacin da yake rungumeta tsam a jikin sa , yana fidda ajiyar zuciya a zahiri .

Ji tayi riƙon da yayi mata yayi tsanani da kyar take fidda numfashi  , dan haka ta motsa da kyar ,

"Baban Mama mu shiga ciki na zauna ,

Tana jikinsa suka taka zuwa cikin gidan ya zaunar da ita akan kujera , amma shi ya gagara zaman saboda tashin hankalin da yake ciki ,

"Baban Mama ...

"Fatima ku zauna a gida ke da Mama ku jiraye ni zan fita na sayo mana abubuwan buƙatu kadan yanzu nake dawouwa da gaugawa ba zan daɗe ba kin ji kou ?

A sanyaye ta amsa da "to , tana gyaɗa kai ,

Daga haka ya juya ya fita , ba tare da ya san inda zai tafi ba , kawai so yake ya zama shi kaɗai bai san ɗanɗanon shakuɗuwar farin-ciki da baƙin-ciki a lokaci guda ba sai yau ,

Bai san girma da tsoron da yake cikin rasa abunda kake so ba sai yau da layi yake shirin shatuwa tsakanin sa da abubuwa biyu mafiya soyuwa agare shi ,

Bai san da irin wannan tashin hankalin da yake sa ɗimuwa ba sai da ya tsinci kan sa can nesa da unguwar da yake ba tare da ya sani ba ,

Tsayuwa yayi a ƙarƙashin Doguwar bishiyar (Pinus taeda) da duk ganyayyakin ta suka gama zubewa saboda sanyi ,

Hannun sa ya zira a aljihun rigar sanyin jikin sa cikin rashin sanin makomar rayuwar sa ,

Waye zai tallafa masa ya fahimce shi ? Tayaya zai yi bayani a fahimce shi cewa kome da ya faru gare shi ya faru ne bisa ruɗin shaidan da kaddara maigirma , kaddarar haihuwar Mama da Auren Fatima ?

Waye zai faɗawa ya saurare shi cewa Fatima ta riga ta zama mahaɗi na cikamakin farin-cikin rayuwar sa ?

Mama ɗiya ce jini daga cikin jinin jikin sa dake gudana ,ta yaya zai iya tsame ƙwayar jinin sa daga jikin sa ?

" daga gefe ya hango wani brewery ( wajen sayar da giya ) ya tsallaka ya shiga wajen ya zauna , akan ɗaya daga cikin kujerun gurin , ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ta zo da tare da gaishe shi ,

Kan sa yana kallon teburin gaban sa ya ce mata

Please bring a bottle .

bata tafi ba ta fara lissafo masa sunayen giyar da suke da ita, ya katse ta ,

  Bud Light

Bata jima da sai gata ɗauke da kwalbar giyar da ya buƙata da ɗan kofin gilashi , tare da farfasassun ƙanƙara cikin wani ɗan mazubi na gilashi .

Tsirawa kwalbar ido yayi yana jin ƙaruwar damuwar sa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login