Showing 180001 words to 183000 words out of 411050 words
Chapter 61 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
inn da yake cikin garin na sokoto zuwa wayewar gari sun huta sun kuma sake shiri sai kuma su faɗa yankin niger ta," ilela ," su ɗau hanya ta birnin N'konni da zai ɗaura su kan kodoben da za su sadu da birnin Niamey ɗin niger ....!
Ba su suka samu isa Niamey ba sai ranar Asabat da misalin ƙarfe bakwai na dare duk kuwa da gudun da direban ya dunga shararawa tun da suka faɗa yankin niger kasancewar sun shigo ƙasar su , kowa yaga gilmawar motar su basu hanya ake ,
Kai tsaye direban ya wuce da su ( Radisson Blue hotel,) ƙarƙashin umarnin youssof , kasancewar shahararren hotel ɗin mafi yawan lokuta nan ne wajen sauƙar sa idan wani aiki ya kawo shi Niamey ɗin kasantuwar hotel ɗin kusa yake da manyan ma'aikatu masu muhimmanci na ƙasar da ke babban birnin Niamey ,
Babu ɓata lokaci ya kama musu ɗakuna inda hajja me wurya da falmata zasu zauna a ɗaki guda , (one bedroom Residence ) dake ƙasa shi kuma ya Kama nasa ɗakin a sama ( royal suite ) inda ya saba zama idan ya zo otel ɗin yayin da direba yayi tafiyar sa inda sauran abokanan aikin su suke , ya bar masa mukullin tare da motar , '
Bayan yayi wanka ya sallaci isha'i , misalin ƙarfe takwas da rabi ya sauko ƙasa , ɗakin da suke ya tasamma , ƙwanƙwas musu ƙofa yayi ,
Hajja me wurya tana sallar isha'i lokacin , falmata kuwa ta idar tana kwance bisa faffaɗan gadon ta sanya baby mama a gaba wacce take ta baccin gajiya bayan an cika mata ciki da madarar ta me ɗumi ,
Sake ƙwanƙwasa ƙofar yayi a karo na biyu yana sake kallon number ɗakin da take rubuce a jikin wani ɗan katako dake sakale a jikin ƙofar ,"nan ne dai ɗakin nasu ,"
Miƙewa zaune tayi
Hajja kamar ana buga ƙofa ko ?
Ƙyat ! Ƙyat
Hajja ta mata alama da hannu
Oho sallah kike ?
Sake bugun ƙofar aka yi da ɗan ƙarfi da ya sanyata miƙewa a hankali bayan ta zura hijabin ta ,
Ƙasantuwar ɗakin ba wani babba sosai bane taku kaɗan tayi ta isa jikin bango , dan haka ta fara shafawa bata sha wahala ba hannun ta ya sauka jikin ƙofar,
Waye ne ?
Ni ne buɗe min ƙofa
Ta shaida muryar sa
kama mariƙar ƙofar tayi ta murɗa sai dai bata ji alamun ƙofar ta buɗu ba ,
Ban iya ba
tace da shi cikin ƴar ƙaramar muryar ta ,
,'Bata iya buɗe ƙofa ba ? Ya tambayi kan sa ,"
Hajiya batta cikin ɗakin ??
Tana sallah ,
ta ce masa
Bai ce kome ba ya gyara tsayuwa gami da jingina da jikin bangon ɗakin ,
Cigaba tayi da tsayuwa tana ɗan laluba jikin ƙofar ko zata ji wajen buɗewa ,
Ba'a ɗauki lokaci ba hajja ta idar da sallah ,
Ke kam wannan yarinya anyi bagidajiya , yanzu ace buɗe ƙofa ma kin kasa ? Ni gusa ki ban guri ,
buɗe masa ƙofar tayi ya shigo suka gaisa ,
Hajja akwai abunda kuke buƙata ne ?
Babu abunda muke buƙata ɗan nan , mun gode ƙwarai da hidima ,
Idon sa ya ɗora kan baby mama ,
Ta daina rigimou kou ? Ba ku buƙatar kome kou ?
Shiru falmata tayi domin bata ma san da ita yake ba ,
Hajja ta ce
fatima maigidan na magana
Wanne maigida hajja ??
Wata ƙatuwar harara hajja ta wurga mata , tamkar falmatan tana ganin ta a ƙufule tace
Baban jaririyar ta ki
A sanyaye ta ce me yace ? Wai zai tafi da baby ?
Da sauri youssouf yace
Ban faɗi hakka ba fatima cewa nayi ba ku buƙatar kome ?
Eh !
Ta bashi amsa tana zama bakin gado ta shiga laluben baby mama, hannun ta ya sauka bisa kan ta ta shiga shafawa a hankali ,
Ya juya ga hajja , ni zan shiga gari wajen aiki na , akwai yiwuwar gobe sai yammaci zan shigo , duk idan kun buƙaci wanni abu ku ƙira ma'aikatan otel ɗin ta kan wayar tarho ,
Ga ta nan ,"
ya nuna mata telphone ɗin dake ajiye daga saman ƴar durowar gefen gado "
madallah hajiya ina sake godiya
Mune da godiya ai ɗan nan mune da godiya , to to babu kome Allah shi taimaka muna nan muna addu'a
Ameen hajja sai gobe
Ya juya yana barin ɗakin
Da sauri hajja ta zunguri falmata ,
Ke baki san ki gaishe da miji ko kiyiwa miji addu'a bane ? yau ni hauwa'u na ga abunda ya fi ƙarfi na me zan gani haka ? Yanzu ashe haka za ki dunga gwada rashin hankali a gidan auren na ki ? Ko kuwa taƙamar yarinta kike ? To bari ki ji na faɗa miki ni lokacin da aka min auren fari ma ban kai ki cika ba , kin fini ƙugu da ƙirji da sharaɓa da kome ke har shekaru ma domin ni lokacin da aka min aure ma sha huɗu nake ko nonon arziƙi bani da su , amma billahil azeem ban yi irin wannan haukar da na hango somi-somin ta a tare da ke ba ,
Ke kenan sai ƙwalafacin ƴa , alhalin kina gwadawa uban ta halin ko in kula , idan taƙamar ki son ƴaƴa ai sai ki kwantar da kai kema ki samu ki tara naki ba ki dunga gwada naci akan ƴar wasu ba ,
Falmata wacce ta fara jin haushin hajja akan takurar da ta ke mata, muryar ta a cunkushe tace ,
To a ta ya zan tara nawa ƴaƴan ??
Sororo hajja tayi ,
Ah lalle abun naki na yi ne, 'an biyawa bazaura hajji , to sai ki cigaba da tambaya ta , ranar bada amsa tana zuwa , aikin banza yarinya sai sokonci kika iya ,.
Washegari biyamuradi youssouf bashi zaune bashh&
har sai da ya samu wani ɗan madai-daicin gida irin wanda yake so a unguwar ,(Banifandou 2) ya kamawa su falmata hayar sa ya biya kuɗin shekara guda cif ,
Ƙarfe hudu tayi masa a shahararren company ƙera kayan katako da shirya gida ,(sunwe) inda ya faɗa musu buƙatar sa na son a kai masa kaya dai-dai da tsari da fasalin gidan sa ,
Basu yi ƙasa a guiwa ba suka tashi ma'aikatan su har su huɗu suka je ganin gidan ,
Hotunan gadaje , kujeru da sauran kayan adon gida aka dunga nuna masa tare da kuɗaɗen su ,
Bai yi zari ba ya zabi dai-dai kudin sa , tare da matsayin Falmata a wajen sa ,
Ma'aikatan da kan su suka kwashi kayan a motar su zuwa gidan inda gobe zasu je su shirya kayan da safe ,
Sai sha biyun dare Youssouf ya koma hotel ɗin saboda tun ƙarfe takwas na dare yana tare da manyan su suna wata ganawa ta musamman da lieutenant-Gènèral da Major Général , waɗanda sune ƙashin bayan samun ɗaukakar sa a fannin aiki ,
Ya so ya je ya ga ɗiyar sa da yadda suka wuni amma ganin yadda dare ya riga yayi sai ya yi wucewar ɗakin sa kai tsaye , da zummar gobe zai gana da su cikin rashin sanin sa yini baby mama tayi da matsanancin zazzabi tare da mura , banda kuka babu abunda take , tun falmata na rarrashi ita kaɗai har hajja ma ta karɓa , duk da haka ta ƙi shiru , zuwa dare har shiɗewa take gaba ɗaya hankalin su ya gama tashi banda kuka babu abunda falmata take ko abinci sun gagara ci ,
Ganin duhu ya sawo kai ga youssouf bai zo ba ya sa hajja me wurya fitowa daga ɗakin ba tare da ta san takamaimai ina zata nufa ba , Allah ya taikaita mata wahala ya gama ta da ɗaya daga cikin ma'aikatan otel ɗin da ya kawo musu abincin rana ,
Nan ta tsaida shi ta tambaye shi ina ne ɗakin wanda ya kawo su ? Suna buƙatar taimakon sa , bai gane inda ta dosa a maganar ta ba saboda haka ya yi mata jagora zuwa gun manyan su , inda cikin kwatancen hajja me wurya tare da duba sunan ainahin wanda ya kama musu ɗakin da suke suka fahimci colonel youssouf take nema ,
basu da number wayar sa dan haka suka shiga ƙiran layin telfo na ɗakin sa nan ma basu ci nasara ba domin wayar tana ta ƙara ba'a ɗauka alamun da ke bayyana babu mutum a ɗakin .
Ganin yadda hajja ta damu tare da sanin matsayin wanda ya kawo su ya sa suka tambaye ta matsalar su ?
Nan ta shaida musu ƴar shi wanda ya kawo sun ne jaririya bata da lafiya suna neman a kai ta asibiti ,
Nan take ma'aikatan hotel ɗin suka jagorance su zuwa wani asibiti me zaman kan sa mafi kusa duba da halin da ƴar jaririyar take ciki na wahalar numfashi,
bayan sun haɗa su da likitoci da nan take suka karɓi baby mama suka fara bata taimakon da ya dace ,
Sai suka dawo suka cigaba da ƙiran layin ɗakin youssouf lokaci-lokaci ko ya dawo ?
Dan haka da shigar sa ɗakin bai rufa mintoci goma ba fitowar sa daga wanka kenan , kan wayar ɗakin ta fara ƙara ,
Nan ya ɗauka bayan sun gaisa suka sanar da shi halin da ƴar sa ke ciki tare da asibitin da suka kai ta ,
A gigice youssouf ya sanya kayan sa gami da ɗaukar ɗan mukullin motar sa , kai tsaye ya tasamma asibitin da ba baƙon sa bane domin fitatcen asibiti ne da duk ƙasar aka san sunan sa ,!
Bai wani sha wahala ba illa tashin hankalin da yake ciki lokacin da ya samu ganin babban likitan da aka tabbatar masa shi ya kula da jaririyar a daren ,
A kiɗime youssouf ke tambayar sa ina ƴar ta sa take ? Kuma a wanne hali take ciki ? Nan likitan ya kwantar masa da hankali inda ya shiga yi masa bayanin abunda ke damun ƴar sa tana da ,( single pneumonia ) wanda kuma shi ya kawo mata wannan wahalar numfashin tare da zazzaɓi me tsanani , sanadin shaƙar ƙura me ɗauke da ƙwayoyin cuta da tayi,
Dan haka likitan yayi ƙira da a kiyaye sosai a kula da ita , a ƙarshe ya sanar da shi an shawo kan matsalar ta a halin yanzu har ma ta samu bacci zuwa gobe idan aka ga yanayin jikin ta ana iya sallamar ta ,
Tare da likitan suka nufi ɗakin da aka kwantar da baby mama ɗaki ne na musamman ( side room ) inda falmata da hajja suke tare da ita ,
Lokacin ƙarfe ɗaya saura na dare dan haka nuna masa ɗakin ya yi , ya juya ,
A hankali ya murɗa kofar ɗakin ya shiga , da haske wal a ɗakin dan haka ya hango falmata daga kan gadon tana zaune ta jingina bayan ta da jikin ƙarfen gadon tana riƙe da baby mama a hannun ta , ga alama bacci take ,
Hajja kuwa tana kwance akan ƴar shimfiɗar da ma'aikatan asibitin suka bata sai sharar bacci take saboda gajiya da tayi da kuma jikin girma !
A hankali ya tako cikin ɗakin ya ƙarasa bakin gaɗon gami da rage tsawo ya leƙa fuskar baby mama , ya yi haka ne saboda baya son tashin su a bacci,
Falmata kuwa tun taɓa ƙofar da yayi ta ji sa , hasalima ba nisa baccin na ta yayi ba saboda sam yanayin wajen da yayi shiru sosai yana bata tsoro , tun tana ƙiran sunan hajja lokaci zuwa lokaci tana amsa mata har dai ta ji hajjan tana mitar ta dame ta da ƙira cikin magagin bacci dan haka ta haƙura ta ƙyale ta , Tayi shiru tana sauraran sauƙar numfashin baby mama da take yin sa cikin nutsuwa alamun sauƙi ya samu gare ta ,
Hannun sa ya kai a hankali da nufin ƙara rufe jikin baby mama da ya ɗan buɗu kaɗan ba tare da sanin falmata ba ,
Yana ajiye hannun sa ta maida nata akan nasa ,
Ɗago kan sa yayi ya dubi fuskar ta , manyan idanun ta da suka ɗan yi jaa kaɗan sun kafe fuskar sa da kallo tamkar tana ganin sa ,
Haɗa baki suka yi wajen yin magana ƙasa-ƙasa
Ita tana tambayar wanene ?
Shi kuma yana cewa ni ne fatima !
A hankali ta ɗauke hannun ta daga kan nasa ,
Shi kuma ya gyarawa baby rufuwa tamkar yadda yayi niya cikin ran sa yana mamaki tare da girmama nisan kunnen ta tare da yadda take kaffa-kaffa da ƴar baby , da ɗai bai taɓa cin karo da uwa irin ta ba , duk da ƙarancin shekarun ta
Komawa yayi ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun wajen yana duban fuskar ta cikin nazari , kallon ƙurr yake mata tsaf yana wasu tunaninnika masu nissa ,
A jikin ta take jin idanun sa suna yawo saboda tsikar jikin ta da ta ji tana mimmiƙewa,!
ya tsinkayi muryar ta da ɗan karfi tace .
Ka ɗaina kallo na haka bana so !
Ware idanu yayi da ɗan mamaki a fuskar sa ,"ya aka yi tasan ina kallon ta ,"? kafin yayi murmushi kaɗan ganin yadda ta turɓune fuska ,
,'Ƴar baiwa ce," ya aiyana haka cikin ran sa , a sarari kuwa cewa yayi
Ki kwantar da itta ke ma ki kwanta dare yayi ,!
Yayi baya da kan sa tare da miƙe dogayen kafafun sa ya ɗan zame kaɗan akan kujerar yana jin yadda tunanin lamura suke yi masa rubdugu tamkar yadda ya saba duk dare tunda abubuwa suka fara haɗe masa !
*****
Stade Général Seyni kountchê ( SGSK ) nan ne babban filin da gwamnati ta shirya gudanar da bikin karamma sojojin ta waɗanda ta tura nigeria tare da yi musu ƙarin girma , har ma da kyautuka ga waɗanda suka chanchanta , !
Mai martaba sarkin Maradi tare da Mommoudou , 'wanda hajiya mama ta tilasta masa zuwa taron ƙarin girman ," sai Tafeeda ƙarƙashin rakiyar tawagar maimartaba , suna cikin mutanen da suka halarci wannan taron da suka samu isowa a yau ,
sai kuma Ubbo tare da Siyama wacce ita ma ta iso Niamey tun ranar asabat tayi zango a gidan ubbo tare da cigaba da tsara yadda zata fara bin matakin farko na kusanta kan ta ga Biyamuradi muradin zuciyar ta !
Da wasanni irin na soji , kiɗe-kiɗen su zuwa faretin su , aka fara buɗe taron da kai tsaye ake watsa shi a gidajen tv dake baki ɗayan ƙasar Niger ,
Kafin a bada dama ga maigirma Shugaban ƙasa yayi jawabin yabo da jinjinawa ga sojojin ƙasar sa , sannan shugaban rundunar sojojin ƙasa na ƙasar ma yayi nasa bayanin , har zuwa kan wasu manyan kusoshin gwamnatin ƙasar da manyan soji da duk dai yabo ne suke yi ga sojojin su da suka dawo daga bakin daga ,
Youssof Abdul-azizou shine wanda aka fara ƙira domin martaba shi tare da yi masa ƙarin girma ,
Da faretin su na soji ya fito filin ya ƙarasa har zuwa gaban shugaban ƙasa ya sara masa ya juya gaban manya-manyan sojojin su na ƙasa nan ma ya sara musu kafin ya ƙarasa kan ɗan tudun da aka tanada domin tsayuwar sa inda shugaban sojin su na ƙasa yake tsaye , daga gefen sa wasu sojoji biyu ne a ƙame da ƙwali rike a hannuwan su ,
Sara masa yayi ya ƙame ,
cikin takun sa na soja lieutenant General ya ƙaraso gaban youssouf tare da kai hannun sa ya warware ɗan yadin dake ɗauke da tambarin girman matsayin youssouf ɗin a soja , ya miƙa sa ga ɗayan sojan dake hannun sa na hagu ya sa a kwalin hannun sa ,
lokaci guda ya waiga ga ɗayan sojan ya ɗauki sabon rank ɗin da ke ɗauke da zanen yellow layi huɗu wanda yake ninke cikin kwalin hannun sojan ya maƙala a gefen kafaɗar youssouf ɗin dai-dai inda ya cire na farkon ,
Da hakan yake nuni da sabon matsayin Youssouf Abdul-azizou Baskore da ya tashi daga colonèl ya koma MAJÓR YOUSSOUF ABDUL-AZIZOU BASKORE ,
A take gurin ya ɗauki tafi tare da sarewa da gangunan su na soji , wani irin yanayi ne ya bayyana a fuskar mommodou da take kirtiɓ ya haɗe girar sama da ta ƙasa , idanun tafeeda da ya sauƙa cikin nasa shi ya sa shi gyara yanayin fuskar sa tare da haɗa hannunwan sa biyu cikin yanayi na dole ya ɗan tafa su ,!
Da fareti major youssouf ya dunga bin su ɗaya bayan ɗaya tun daga kan shugaban ƙasa har zuwa shuwagabannin sa wajen aiki yana sake sara musu , masu camera na aikin haska shi da masu ɗaukar sa a video , ƙarshe ya dire a gaban mahaifin sa da yake hakimce cikin shigar su ta sarakuna , idanun sa da suke sakaye cikin farin gilashin ƙarin ƙarfin ido suna bayyana tsantsar farin cikin da yake ciki , yayin da bakin sa da yake rufe ta cikin rawanin sa yaƙi daina murmushi ,
Ƙamewa yayi ya sarawa mahaifin sa , ga jin daɗin sa sai maimartaba ya miƙe gami da miƙa masa hannu suka yi musabaha idanun su na musayar zallar ƙauna , ya rungumo shi zuwa jikin sa ,
Bakin sa na furta kalmar
MADALLAH DA KAI MAJOR YOUSSOUF KAI KA KASANCE ABUN ALFAHARI NA ,
Kunnuwan youssouf kaɗai suka jiyo me mahaifin nasa ke cewa .
Yayin da fuskar mommodou tayi jaa tana tsattsafo da gumi .
Ware idanu sosai hajja me wurya take cikin son tabbatar da fuskar wanda take gani tarwai a fuskar ƴar tv da take kunne cikin ɗakin