Showing 330001 words to 333000 words out of 411050 words
Chapter 111 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
tare da fargabar rasa shi da ta shiga da har ta kai ta ga kwanciya rashin lafiyar sati guda sai da ta fara samun labarin samun sauƙi a gare shi sannan ita ma ta fara gyagijewa .
Bayan ta kammala haɗawa Hajiya Umma abincin a can ɗakin ta na ƙurya inda ba wani mai shigar sa cikin bayu sai fa su 'ya'yan ta da kuma makusanta na sosai , fitowa tayi daga ɗakin ta dawo ɗan madaidaicin falon da yake tsakanin ɗakin da sauran manyan faluka ta zauna .
Hajiya Umma bayan ta idar da sallah ta ɗan taba abincin sama-sama , sai ta ɗaga waya ta ƙira Siyama , nan take kuwa ta shigo tana rike da hannun Yumna , wacce da shigar su ɗakin ta saki hannun mahaifiyar ta tayi wajen kakar ta da gudu ta faɗa mata akan ƙafafu ,
Da ƴar dariya Hajiya umma ta ɗago ta tana cewa , " ke zainaba ki ɗagga ni kadda ki ƙarasa min ƙafafu ki sa ni ɗingishi dagga dawowa ta daman yaya lafiyar ƙafar ?
Birgima yumna ta sake yi akan ƙafar Hajiya Umma kafin cikin 'yar muryarta mai cike da wayo tace ' Umma na faɗi miki ni suna na ba Zainaba ba suna na Yumna ko Mamaa ?
Da murmushi Siyama ta ɗan yi gurfano daga gefe tana ƙoƙarin janye Yumna daga kan Hajiya Umma tace , " Yumna bakya jin magana ko idan baki ɗagga Umma ba gobe ban tahiya dake unguwa .
Da sauri ta ɗaga Hajiya Umma ta faɗawa uwar a jiki tana cewa ," kin ka ce wajen Baba na zamu tai ba unguwa ba ?
Shiru Siyama tayi bata amsa ba , illa ƙafafun Hajiya Umma da ta fara dannawa a hankali tana mata tausa .
Da tausayi a ƙwayar idanun Hajiya Umma take kallon Siyama , sarai ta fahimci yadda Siyamar take a ƙagauce da ta ji halin da Mijinta yake ciki ta kuma ji wani batu kan tafiyar su da aka tsara har da ita a waɗanda zasu ganin lafiyar Youssouf ɗin , sai dai zuwa lokacin tahowar su da Youssouf ya nanata kan cewa kada a taho da Siyama cikin masu tahowa wajen sa , tayi zamanta kawai har zuwa lokacin da Allah zai sa ya dawo yasa aka fasa tafiyar Siyama .
Hajiya Umma ta so ƙin amincewa saboda ita tafi ganin dacewar zuwan Siyaman da take matar sa fiye da sauran ƴan uwansa , sannan kuma ita ma Siyamar hankalinta zai kwanta muddin ta gan shi da idanun ta saboda tun a india su na da labarin irin mawuyacin halin da ta shiga na fargabar rasa Mijinta .
Sai dai duk yadda ta so Youssouf ya amince da zuwan Siyama ƙi yayi a ƙarshe da ta dame shi ana gobe dawowar su , yana kwance kan gadon sa na asibiti Hajiya Umma da Maimartaba kuma suna daga kan doguwar kujerar da take falon ,
Hajiya Umma ta sake tada batun zuwan Siyaman , da jin haka yasa Youssouf miƙewa a hankali ya zauna yana ɗan cije baki saboda wajen da aka yanka aka masa aiki a uwar hanjin sa har yanzu bai kai ga warkewa ba cikin kwana biyun nan ne ma yake iya miƙewa zaune da kansa
Fuskar sa da tayi fayau ta ƙara yin haske babu walwala , bai yadda ya dubi Hajiya Umma sosai ba yace ," Umma , Dan Allah Siyama kadda ta zou , babu wani alfanu a zouwan na ta .
Da ƙaruwar mamakin ta take kallon sa ,muryar ta da ɗan fushi wannan karon tace , " to wai mene ne dalilin ka ? Ina sane fa tunda ka farfaɗo baka yadda kun yi kou da waya ta kirki da yarinyar nan ba dagga ta gaishe ka sai ka ajiye waya , me zai sa ka dunga yi mata haka , ita ai wankakkiya ce bata da wani laifi cikin abunda ya afku .
Kan shi ya mayar gefe , muryar sa can ciki yace ," kiyi haƙuri Umma , amma Siyama ma ai macce ce , kaidin macce kouwa abun a gudu ne , hatsarin ta mai girma ne baka sanin abounda ke binne cikin ruhin ta , zahirinta cike yake da ƙarairayi da hilata , Allah kaɗai ya san abunda macce take iya ɓoyewa .
A lokacin Maimartaba ya ɗago kan shi daga karatun jaridar Hindustan Times da yake , ya kai duban shi ga Yousouf da yake komawa ya kwanta bayan gama zancen sa ,
Yunƙurowa Hajiya Umma tayi zata sake yin magana , Maimartaba ya dakatar da ita , fuskar ta a marairaice take kallon sa tana son ya ce wani abu ga Youssouf a lokacin , amma sai bai ce kome ba ya komawa karatun jaridar sa .
Ko da suka keɓe shi da ita , ƙorafi ta shiga yi masa kan hukuncin da take tunanin Youssoufa ya yanke wanda bai kamata ba ko kusa laifin da Maimounatou ta aikata ya shafi Siyama .
Murmushi kawai Maimartaba yayi ,kafin yace " Ki kwantar da hankali , a ba shi lokaci zuwa lokacin da zai gama dawowa ga nutsuwar sa daga ruɗanin da ya shiga , Macce ai mahaɗin rayuwa ce ga Ɗa Namiji , shi da kansa zai safko .
Muryar Siyama ta katsewa Hajiya Umma tunanin da ta faɗa , " Umma babu abunda zan sake yi miki ?
Girgiza kai tayi , " babu kome ɗiya ta , sai magana da nake so mu yi da ke ,
Da sauri Siyama ta gyara zama zuciyar ta cike da ɗokin ko zancen tafiyar ta wajen Youssoufa za'a mata ? tace " To Umma ,
Da tausasawa a muryar Hajiya Umma ta cigaba da cewa , " Nasan kina son zuwa ki ga jikin mijinki to amma saboda halin da zuciyar sa ke ciki yasa aka dakatar da zuwan naki har zuwa lokacin da zai dawo dai-dai, kiyi haƙuri kin san dai yadda wannan mamagunciyar ɗiyar ta zuba masa dafi a zuci da gangar jiki, to sai a hankali zai koma dai-dai dan ma Allah yayi kwanan sa na gaba da zouwa yanzou sai tashin zance , Allah ya ƙara ɗaura mu akan maƙiyan mu na fili da na ɓoye , kiyi haƙuri kin ji ko ?
Da murmushin da ta ƙalato Siyama ta gyaɗa kan ta , tana shafar kan Yumna da har ta fara bacci a jikinta idanunta na kallon ƙasa tace ," Umma Allah ya ƙara girma oumarnin kou abun bi ne a gareni shi kouma Allah shi daɗe shi da lafiya .
"Amin ,Amin Siyama Allah shi miki Albarka ya dauwamar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin ku ,
Umma ta amsa tana mata duba mai cike da so da tausayi ,
A zuci ta amsa lokacin da take miƙewa saɓe da Yumna a kafaɗun ta tana barin ɗakin ,
Lokacin da ta shiga ɗakin ta dake falon tsakiya , kwantar da Yumna tayi a kan gado , a hankali ta zame ta zauna a ƙasa ,hawayen da take riƙewa tuntuni ya samu damar shimfiɗowa da gudu , tunanin abu biyu zuwa uku suka fara mata ƙaraƙaina a zuci .
"anya ba jikin Biyamuradin bane babu daɗi shiyasa aka hana ta zuwa ta gan shi amma Umma ke ɓoye mata ? Amma kuma ai ta ji sun yi waya da duk wasu makusanta ta kuma tabbatar musu da samun lafiyar sa .
" ko kuma ba ita yake son gani ba matar sa Fatima yace a kai masa ?
" kadda dai ace abunda Maimounatou ta yiwa Mijinta ya ɗarsa masa tsanar mata da yasa shi gudun su ? idan kuwa hakane babu shakka ba zata taɓa yafewa ɗiyar Agades ba ,da bayan tsawon shekarun da ta kak-kange ta hana ta damar samun gamsasshiyar soyayyar mijinta , ta himmatu wajen hilatar sa da salon soyayyar ta na ƙarya, tsakanin karya da gaskiya har ya aukawa son wata daban ba ita ba ,
Bayan kuma ga ta ita da ta ɗauki shekaru wajen ƙoƙarin ginawa kan ta matsugunni kome ƙanƙantar sa a zuciyar sa , ta haɗiye duk wani ɓacin rai ta kawar da kai ta danne tasirin kishin ta , amma sai da lokaci ya gabato mata da zata girbi ladan haƙurin ta , sai mummunan nufin Maimounato ya nemi mayar mata da hannun agogo baya ?
Runtse ido tayi tana jin ƙauna tare da tausayin Mijinta gefe guda tsoron sake rasa kulawar da ya fara nuna mata take yi .
, tunowa da lokacin rabuwar su taki kaɗan kafin tafiyar sa sashin Maimounatou , yadda ya riƙe ta ajikin sa , irin kalmomin da ya furta mata da suka zama tamkar magani ga wani daɗaɗɗan raunin da take fama da shi a rai , da hakan yasa ta jin kwaɗayin son cigaba da samun makamancin daɗaɗan kalmomin sa ya haka , cikin rashin sanin ta mummunan lamari na gaf da afkuwa musu .
Buɗe ido tayi tana karanto addu'o'in samun nutsuwar zuci .
Washegari da sanyin safiya saƙo ya isowa Hajiya Umma cewa " Hajiya Mama na mata barka da zouwa sannan kouma tana nan tafe zuwa sashin Hajiya Umman ,
fuskar Hajiya Umma bata nuna wani yanayi ba na farin-ciki ko saɓanin sa tace "a je a ce tana yiwa Gimbiya Saratu Maraba .
Zuwa hantsi misalin ƙarfe tara da rabi hajiya Mama ta iso , ƙarƙashin rakiya bayun ta su huɗu ,waɗanda tun daga falon farko suka dakata ,
Ita ɗaya ta taka zuwa Falon gaba inda ta tarar da Mairamar sarki tare da Siyama suna karin kumallo , kallo ɗaya Aisha Mairama tayi mata ta mayar da kan ta gefe , Fuskar Siyama kadaran-kadahan ta gaishe ta , ita ma tata fuskar babu fara'a ta amsa tana mayar da ganin ta kan Aisha da tayi tsam daga barin cin abincin da take , kafin tayi magana Aisha ta gaishe ta lokaci ɗaya ta miƙe zuwa cikin ɗakin Umman .
Ita ta yiwa Hajiya Mama iso ta shiga wajen Hajiya Umma .
Bayan gaisuwa shiru ne ya biyo bayan ɗan taƙaiccen zaman da suka yi kowacce tana saƙa a zuci , kafin Hajiya Mama ta gama auna kalmomin da take tafe da su da zummar ajiye su a muhallan da suka dace tace
," Sai kuma wannan lamari mai cike da sarƙaƙiya ya faru ? Wannan yarinya tayi ƙarƙon kifi , ta ɓata nasabar ta , ai kome kyaun nasabar macce muddin bata da hali kamar zoben zinariya take a hancin alade, shiyasa fa ni ban fiye zaƙewa wajen tsantsame zuri'a tafannin auratayya ba, wannan ƙwarya ta bi ƙwaryar bata cika yin ƙarƙo ba sai ki ga anyi gamdakatar da bara gurbi , amma ɗiyan saraki masu son tsalkin nasaba basu gane ba , ai ga irin ta nan Allah dai shi taƙaita , yaya shi jikin Youssoufa? Ya fa kamata ayi wani abu kan Yaron nan Mammadou sabbada kowa ya shaida sharri ne wannan ɗiya take yi masa .
Tunda ta fara maganar Hajiya Umma bata dubi sashin ta ba tana a kishigiɗe yadda take , ɗaya bayan ɗaya kalmomin Hajiya Mama suke sukar zuciyar ta tare da bijiro mata da mummunan fushin da take ƙoƙarin tausa zuciyar ta ta danne kamar yadda ta saba haɗiye dayawa daga cikin munanan abubuwan da Hajiya Mama ta sha yi mata ko a kanta ko akan 'ya'yan ta .
Fuskar ta na bayyana fushi mai tsanani ta miƙe zaune lokacin da zuciyar ta gama aiyana mata "shi fa maƙaho bai san ana kallon sa ba sai an haɗa da zungurin sa,
" Saratu ki dakata daga waɗannan maganganu naki marasa tushe da makama , shi wawa bai san zuru ba sai ya tsinka , ki sani cewa duk wasu kaidi da makirce-makice hadi da ja'iba da ta'annakin da kike bibiyata da zuri'a ta da shi ina sane , ina sane nasan kome tun kafin yau , na yi miki shiru ne saboda nasan shi munahinci dodo shike , muguntar mutum kuma ita ke kawo hallakar sa har inda yayi zaune yana kitsa sharri, sannan akwai ranar da hadari zai taso tare da guguwar da zata wargaza mugaye .
Cikin tsakar idanun Hajiya Mama da ta tsare ta da ido ta kai duba suka yi musayan kallo ,
Ɗan guntun murmushi tayi kafin ta cigaba da cewa ,
"Saratu kika ce akwai aibu cikin tsantsame zuri'a ? To ai rashin tsantsame zuri'a yasa kin ka kawo matsayin da kike bisan sa a yau , rashin tsantsame zuri'a yasa kin ka zama muguwar uwa mai kitsa sharri , Matar kirki 'yar Nasaba da ita Miji ke fariya yana ado da ita tamkar rigar silki , amma Annamimiya mai haɗa bakin wuta a tsakal gida ita ke saka shi cikin ɗimuwa ta dauwamar masa da shiga kunya da baƙin-cikin da har abada zai kasa samun farin-ciki da ita .
" Ya isa Hajiya Safiyya dan na tako na zou shiyar ki ba shi zai baki damar da za ki ci mutunci na ba , Hajiya Safiyya babu yadda za ki iya da ni , banbancin nasaba da ki ka ɗau shekaru kina ɗaga shi sama kina tutiya da shi bai isa ya sauya mana daidaituwar matsayi ba a cikin gidan nan kuma ko kin ki ko kin so Inkiya ta ita ce Gimbiya Matar Sarki .
Tana huci ta miƙe tsaye ta fara taku tace " na zo nan ne dan na sanar da ke ki sa a gaugauta sakar min ɗa ya dawo saboda ina da masaniyar ke kika sa aka cigaba da garƙame shi ba tare da ya aikata laifin kome ba .
A tsakanin kwanakin da suka biyo baya Bilal da Ubbo tare da Maigidan ta suka tafi india , washegarin tafiyar su kuma Tafeeda shima ya juyo , saboda yanayin aikin sa da bazai bar shi ya cigaba da zama ba a can .
Bayan an gama zaman fada da Maimartaba ya tsawatar akan hana cigaba da batun abunda ya faru da Youssoufa , aka fuskanci abunda ya shafi fada da al'amuran ta kaɗai ,
A daren ranar misalin ƙarfe takwas saƙon ƙira daga Maimartaba ya riski Tafeeda , babu ɓata lokaci ya cimma turakar Maimartaba ƙarƙashin jagorancin jakadiya .
Bayan ganawar da bata wuce mintoci talatin ba Maimartaba ya masa iznin tafiys bayan ya samu duk wasu bayanan da yake son samu daga wajen sa .
Duk da cewa Hajiya Mama ce take da turaka a ranar amma kasantuwar buƙatar ganawa da Hajiya Safiya ya taso yasa Maimartaba aika jakadiya ta masa ƙiran Hajiya Umma .
Lokacin da saƙon ƙiran ya samu Hajiya Umma tayi mamakin Ƙiran nasa sai kuma ta cika da fargabar ko dai wani lamarin ya afku ?
Batun da Maimartaba ya zo mata da shi a lokacin da ta isa turakar sa ya busar mata da maƙwallato , da wani irin yanayi cikin muryar ta tace ,
" Ranka ya dade amma sai nake ganin rashin dacewar Yarima ya cigaba da riƙon amren ɗiyar nan ta Nigeria , wacce ba'a ma kai ga sanin matsayi da tushen ta ba , Ranka ya dade a duba wannan lamarin ayi duba da yadda wannan ɗiya ta agades tazo da ha'inci ita wacce ma take da tsarkin Nasaba ɗiyar girma , ina ga kouma ita wannan da take tsintattar mage a yadda labari ya iske mu ko a can Nigeria basu da wata nasabar da za'a iya haɗa jini da su , ba'a ma san dangin su ba 'Yan Gudun Hijira ne kaddarar rayuwa tare da maƙirci irin na maƙiyan mu ne kawai ya haɗo kasantuwar su tare da ɗan mu me zai hana kawai a raba wannan Amren ?
Cikin tsanaki Maimartaba yake kallon ta har ta gama zantukan ta tayi shiru ,
"Safiyya , ya ƙira sunan ta yana gyara zaman gilashin ƙara karfin gani idon sa .
" Na'am , ranka ya dade ta amsa tana mai kaucewa haɗuwar idanun su , cigaba yayi da cewa
"Yanzou ashe abunda ya faru bai isa zamar miki ishara ba ? Bai isa miki nuni da cewa kyaun nasaba bai nuni da kyaun ɗabi'a da cikar mutuntaka ba ? Bai isa sanar da ke cewa halin ƙwarai baiwa ce da ubangiji ka iya bayarwa ga bayinsa tsakanin talakawa da masu kuɗi , masu mulki da bayun su Iyaye kouma su taya wajen ƙarin gyaruwar halayya da taimakon gwargadon irin kyaun tarbiyyar da suka yiwa ɗiyan su .
"Nasaba ba ita ke tsalkake mutum daga aikata halin banza ba , shi halin Mutum mallakin sa ne daga lokacin faruwar halittar sa da bai da wata alaƙa da wata Nasaba ko ni'imar rayuwar da zai zo ya taras nan duniya .
" Domin ɗiyar Nasaba tayi zalunci bai nufin ɗiyar ƙananun mutane tayi fiye da munin abunda ta aikata mai yiwuwa ne ita ɗiyar talakawan ta bayar da mamaki wajen zuwa da ɗabi'u mafiya kyau wajen ƙwaiƙwayo , wannan ɓangare ne na baiwar Ubangiji kamar yadda na shaida miki , dan haka umarni nake bayarwa kan a tai a zo da ɗiyar da Youssoufa ke amre dagga Nigeria ta kasance ƙarƙashin kulawar mu kafin dawowar Mijinta hakan shine zai nuna cikar ƙima da darajar mu , sam ba dattaku irin namu bane mu bar ɗiyar mutane dauke da amren ɗan mu can a ƙasar su batare da sanin halin da take ciki ba , ba'a kuma sanar da ita halin da Mijinta ke a ciki ba da hakkinta ne ta sani .
Hajiya Safiyya da tayi zugum tana jin sabon damuwa na mamayar ta Allah ya sani bata son cigaba da kasancewar yarinyar nan a matsayin surukar ta ita da son ran ta ne Siyama kaɗai ce zata cigaba da zama a matsayin matar auren Youssoufa , ta ƙuta sannan tace ,
" Ranka ya daɗe a halin da Youssoufa yake ciki yanzou babu tabbacin ko yana son cigaba da zama da yarinyar nan tunda ka ga kou Siyama ai....
" Safiyya ta ban san ki da gardama ba kar kuma ki sakayo ta cikin ɗabi'un ki a yanzou , Youssoufa yana son matar sa duk kouma tunane-tunanen da kike yi kiyi watsi da su domin zai zo miki da saɓanin su , dan haka kamar yadda nace a shirya tafiya a zaɓi mutanen da suka dace