Showing 33001 words to 36000 words out of 411050 words

Chapter 12 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

20114

ba ya fara taku cikin sassarfa lokaci ɗaya yana sauke idanun sa akan tagar ɗakin sa wanda hasken rana ya riga ya hudo ta tsakanin labulen .

Bayan tsawon mintoci fiye da talatin da biyamuradi youssouf ya ɗauka yana addu'a da neman gafarar mahaliccin sa bayan ya idar da sallah ,

sadda kansa ƙasa yayi yana me jin kunyar ɗago kansa ya dubi aminin nasa wanda ya tabbatar idanun sa a kafe suke a kan sa , yayin da sashi guda na zuciyar sa yana me son tuno da wani abu .

A firgice ya dago kan sa a sakamakon tunowa da yayi dawowar sa daren jiya da faduwar da yayi a harabar lambun sa wanda daga nan bai sake sanin inda yake ba a sakamakon kakkarfan baccin da yayi awon gaba da shi a wurin a yashe , da hakan baya rasa nasaba da sabuwar sumfurin dahuwar burkutun da ya sha a jiyan wanda gaba ɗaya ta hargitsa masa ƙwanya .

Aina ka tarar da ni ?

Shine kawai tambaƴar daya jefawa tafeedah bai koh kula da irin kallon da tafeedan ke jifan sa da shi ba mai cike da tarin ma'anoni .

A jefa a inda kaga yafi dacewa da kai cikin kuma irin yanayin da ka zabarwa kan ka ."amsar da tafeedah ya bashi kenan " yana me miƙewa cikin yanayi na nuna alamun tafiya yake da niyyar yi ,"

Wani boyayyar ajiyar zuciya biyamuradi youssouf ya sauke a sakamakon fahimtar da yayi cewa tafeedah ne ya kawo sa ɗakin nasa ,"

Da misalin karfe nawa ka shigo gidan ? Su wa ka tarar a haraba ta ina nufin ma'aikata na sun yi chanji ?

Mts! Idan kasan kana gudun zubewar mutuncin ka me zai sa ka jefa kan ka cikin rayuwar da kake youssouf ," tafeedah ya furta hakan cikin ƙufula yana me komawa ya zauna a inda ya tashi ,"

Cigaba yayi da cewa karfe uku na asubah na shigo sashin ka bayan tasowata daga wurin taron mu (meeting) ,inda masu tsaron gidan suka tabbatar min kana ciki tun farkon dare ,"

Amma abun mamaki nazo na gama neman ka ƙasa koh sama baka nan har nayi niyyar fita na sanar da masu tsaron ka , sai nayi tunanin zagayawa har cikin lanbu inda na tarar da kai kwance a ƙasa , da farko na tsorata amma daga baya na fahimci abun da ka min alkawarin ka daina sha kayi min rantsuwa da Allah akan baza ka sake sha ba ita ka sha youssof , ƙarin abun takaicin ma a cikin gidan nan , bayan ka san duk cikin ahalin gidan nan babu wanda ya taɓa sanin kana ta'amali da barasa ," kafi kuma kowa sanin masifun da fallasuwar wannan mummunar ɗabi'ar taka zata iya jawowa a garemu baki ɗaya ,"haba youssof , haba youssof , duk cikin tarin ababen zubda mutunci da jawo tozarta ka rasa wanda zaka zaɓa sai BARASA ? Bayan kasan itace shugaba ummul'aba'isi na jaan ɗan adam ga aikata kowanne irin sabon ubangijin mu ,"

tsagaitawa yayi lokacin da yaji muryar sa ta fara karkarwa alamun gaf yake da fara kuka sakamakon ƙona masa zuciya da wannan ɗabi'ar ta abokinsa ,amininsa kuma ɗan uwan sa youssouf da ya jefa kansa a ciki tun yana da ƙarancin shekaru sosai domin shi da kan sa ba zai iya cewa ga lokacin da youssof ɗin ya fara shan barasa ba , kawai dai ya farga ya gane ne shi da kan sa a saboda kusancin da suke da shi da juna ta yadda wasu lokutan dayawa zai taradda da youssouf ɗin cikin maye ,"

wanda tun yana ƙaryata kan sa cewa youssouf giya yake sha ,a dalilin tsawaita bincike da yayi bai taradda alamun barasa ba a duk inda youssouf ɗin yayi bigire da kuma boye masa tare da waskewar da ya dunga yi , har dai ya zo ya yadda, kuma yayi amanna aminin sa mashayin giya ne , ya kuma tabbatar lokacin da ya bi shi har zuwa wani tsohon kuchakin gidan saida burkutu wanda yake chan tsakiyar unguwannin talakawan gari inda anan youssouf yake zuwa yayi tatul , amma baya guzurin ta .

A ranar yayi kuka har kan sa yayi ciwo ,kuma ya girgiza matuka musamman da yayi duba ga matsayin youssouf a garin na kasancewar sa ɗan sarki mai jiran gado , wanda ake sa ran watarana shi zai jagoranci dubannan al'ummar yankin ya zama shugaba a gare su abun koyi ,

Yaya hajiya umma (mahaifiyar sa) da mai martaba ,haɗi da ƴan uwan sa zasu ji a lokacin da suka farga , uwa uba yaya al'ummar gari zasu dubi lamarin yayin da labarin ya bazu ga kunnuwan su , haƙiƙa maƙiƴan sarari da na boye zasu ji daɗi suyi murna , sannan kuma da akwai yiwuwar subucewar samuwar mulkin jahar maraɗi daga hannun sa domin rashin chanchantar sa ta wannan fuskar ! Wane irin mulki ake zato ga mashayin sarki ????

Tun daga lokacin tafeedah ya nuna cikar amintakar dake tsakanin su da biyamuradi youssof ta hanyar yi masa faɗa da nasiha mai tsanani a kullum, gami da boye masa sirrin sa tare kuma da toshe duk wata hanyar da zata iya sa asirin youssof ɗin ya tonu , sosai yake koƙarin kare masa martabar sa da mutuncin sa , ta inda har ta kai yasamu nasara a wani dare shekaru biyu da suka wuce ,biyamuradi youssouf ɗin yayi masa alkawarin daga ranar ya daina shan barasa bayan fada da suka yi kacha-kacha inda tafeedah har yayi wa youssouf ɗin barazanar daina shiga sabgar sa idan har ba zai daina ta'amali da barasa ba .

Farin ciki tare da kwanciyar hankali suka wadata ga tafeedah bayan jin alkawarin da youssof yayi masa ",cikin rashin sanin tuban muzuru youssouf ɗin yayi ya kuma ninke sa a baibai domin daga ranar ya sauya lokutan shan barasar sa muddin yana cikin garin maraɗi , ta yadda ya maida tsakanin sulusin dare lokacin fitar sa ya sha abar sa , yayin da idan yana wata ƙasar koh wata jahar a duk lokacin da ya samu sarari yake zuwa ko'ina ne ya nemo barasar gargajiya da aka fi sanin ta da " *BURKUTU* " zazzafa ya sha iya shan sa babu abun da ya fasa .

Janye idanun sa da suka ciko da ƙwallar takaici tafeedah yayi , cikin rashin kuzari ya sake miƙe jin youssof ɗin ya rasa abun faɗa , toh me ma zai faɗa masa ? Soke hannayen sa yayi cikin wondon sa ,"ni zan shiga na gaishe da hajiya umma daga chan zan wuce ,sai kuma Allah ya kaddara saduwar mu , ina mai fatan Allah ya kiyaye ka ya baka nasara akan waɗanda zaka tunkara ,"

Daga haka ya sanya kan sa gaba da sauri youssof ɗin ya miƙe daga kan dardumar da ya idar da sallar sa ,"Jira ni nima babu abun da zan yi da wuce wanka sai mu fita tare ," bai jira amsawar sa ba kamar yadda shima tafeedah bai tsaya domin saurarar sa ba ya sanya kai yana me ƙarasa barin katafaren ɗakin youssouf ɗin .

Yana shiryawa yana tunanin maganganun aminin sa tabbas duk wasu kalmomin da ya ɗauki shekaru yana furtawa agare shi gaskiya ne ," kuma shima a karan kansa yana mai bakin cikin halin da ya wayi gari ya tsinci kan sa a ciki sannan yayi iyakacin kokarin sa dan ganin ya daina shan burkutu amma hakan ya gagareshi duk kuwa da addu'o'in da yake yi a koyaushe yayi sallah akan Allah ya yaye masa, amma abun kamar tiri ,

ji yake idan bai sha burkutu ba a kowacce rana , yana iya rasa numfashin sa , burkutu ta zama jinin jikin sa , mahaɗin rayuwar sa kuma abar dake samar da nutsuwa da farin ciki a rayuwar sa ( a ganin sa kenan )

Ajiye matajin hannun sa yayi bayan ya kammala taje ƙwantatciyar sumar sa wanda yake yawan yi mata saisaye luf-luf da ita ," yayi yawo da idanun sa a ɗakin cikin son gamsuwa da bai bar wani abun sa mai muhimmanci ba ,"duk da cewa tun a daren jiya sojan dake kula da shirye-shiryen tafiyar tasa ya kammala haɗa masa kome cikin umarnin sa da yake zaune a gefe yana gwada masa abubuwan da yake bukatar tafiya da su ,"ya shirya su tsaf tare da kai su motar da aka shirya zai yi tafiya zuwa Niamey inda daga nan zasu daga zuwa Nigeria.

Cikin takun sa na ƙasaita wanda yake bayyana cikar jarumtar sa irin na gwarzon soja , jaan tunga yayi ya tsaya "ɗan mitsitsin murmushi yayi ganin tafeedah da yayi a zaune cikin ɗaya daga cikin kujerun falon fuskar sa kadaran kadahan ya dago ya dube shi gami da miƙewa tsaye yayi gaba ," da sauri ya bi bayan sa suka jera .

Cikin nutsuwa suka yi sallama a babban falon hajiya umma , da ya jawo hankalin siyama da merama aisha da suke zaune bisa wadatattciyar darduma suna ƙarin kumallo ," gefe guda masu hidimar zuba musu abincin da tsaftace wurin ne suke durƙushe zaman jiran su kammala , zumbur aisha ta miƙe

Da ɗan gudu da tsalle ta ƙaraso gare su dai-dai lokacin da suke yiwa kan su mazauni akan jerun kujerun falon ,"zama tayi a gefen biyamuradi gami da ɗaura kan ta bisa kafaɗun sa ",barka da safiya hamma nah ,
nayi kewar ku sosai na same ku lafiya . ?

Shafa kan ta yayi lokaci ɗaya fuskar sa tana sake faɗaɗa da yalwatatcen murmushin da yake bayyana tsananin  ƙaunar sa ga ƙanwar tasa yace ",

lafiya lau meramar mai martaba yaya karatu ?
Yaushe kika zo ?
anyi muku hutu koh ?

Anyi hutu hamma jiya da yamma nazo .

Ɗan gyaran murya tafeedah yayi ,

Murmushi ta sake yi tana me sunne kanta a jikin hamman nata tace ,"ina kwana hamma tafeedah na same ku lafiya ," ?
    Bazan amsa ba tunda abun ma wariyar launin fata ce ,"

    Leƙo shi tayi ta bayan biyamuradi tana ɗan murmushi tace yi hakuri hamma tafeedah kasan nayi kewar hamma na watanni uku fa ,"

    Kallo yake mata me kama da harara amma kuma fuskar sa ɗauke da sassayan murmushi wanda sai shi ya san ma'anar sa , sai kuma ita da duk lokacin da yayi mata irin wannan murmushin da kallon take tsintar kanta cikin wani irin yanayi na fargaba da mutuwar jiki ,"

Cikin sanyin jiki siyama ta ɗago idanun ta tana mai sauke su akan abun ƙaunar ta ," hamma youssof antashi lafiya ,? Hamma tafeedah barka da asuba ,?

Ciki-ciki ya amsa mata da "lafiya" saɓanin tafeedah da suka gaisa sosai cikin sakewa har ma yake tambayar ta akan lamarin aikin ta inda ta tabbatar masa da ta ɗauki hutu na tsawon sati uku ,"

cigaba tayi da satar kallon biyamuradi da aisha wanda suke hirar su ƙasa-ƙasa cikin tsantsar shaƙuwa da kulawa da junan su da alama wata matsala ce da aishan wanda ta ƙagautu ta haɗu da yayan nata ta faɗa masa kasancewar ta rainon sa kuma abokin shawarar ta ,

cikin nazari take kallon sa bata samu ƙwanciyar hankali na sosai ba sai da ta fahimci faɗuwar sa ta jiya da dare bata haifar masa da wani rauni ba ,"ta sauke boyayyar ajiyar zuci , tana me Ƙwaɗaitawa a ranta ina ma ita ce maƙale da kafaɗun biyamuradin yana sauraren ta cike da kulawa da ƙauna kamar yadda yake yi wa ƴar ƙanwar ta sa ,"

lokaci zuwa lokaci suna sakarwa juna murmushin yaƙe ita da tafeedah da rabin hankalin sa yake kan wayar sa domin idan da sabo yaci ace ya saba da yadda yake zama saniyar ware a duk lokacin da biyamuradi da aisha merama suka haɗu .

Da yalwatacciyar fara'ar ganin ƴaƴan nata ta ƙaraso falon , cikin hanzari bayun suka yi jerin gwano suna masu isar da gaisuwar su ɗaya bayan ɗaya , kafin cikar mintuna biyu sun cika babbar dardumar da suka shimfiɗa da kawatattun kwanukan abinci na alfarma ,ficewa suka fara yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun sake kai gaisuwa .

Da murmushi take amsa gaisuwar yaran nata tare da tambayar su yaya suke ,"

Umartar aisha tayi da ta zubawa yayun nata abinci ," ita kuma tuni siyama ta zuba mata abubuwan da take tunanin zata so ,"ta ɗebo ruwa a wani kyakkyawan mazuɓi tare da kamo hannun umma ta hau wanke mata su ," cike da so da kauna take sanya mata albarka ," tana me sunkui da kai take amsawa da ameen umman mu .

Bayan sun kammala cin abincin ne tafeedah ya miƙe bayan amsa wayar da yayi wanda saƙo ya iso gare shi ana neman sa ," ƙarasawa gaban umma yayi tare da yi mata sallama addu'a tayi masa tare da ɗaurawa da nasiha ta ƙare da gargaɗin sa akan idan har yana cikin garin maraɗi kar ya yanƙe zuwa wurin ta kullum koh da bayan tafiyar aminin sa ,

Tare da ladabi yake amsa mata da yi mata alkawarin ba zai ɗauke ƙafar sa daga sashin ta ba koh da youssof baya nan , sallama yayi mata tare da miƙewa ya fice bayan sun yi musabaha da aminin nasa .

Bin sa yake son yi domin ya shawo kan sa amma bashi da kuzari koh kuwa bai tanadi kalmomin da zai yi amfani da su wurin wanke fushin da yake hangowa a idon tafeedan ba , dan haka ya bar shi ya sarara zasu  shirya a waya , domin sanin da yayi cewa shi da aminin nasa basa iya wani dogon fushi da juna , duk saɓanin ra'ayin su bai taɓa jawo musu fushi da junan da ya wuce awanni ishirin da huɗu ba , dole daya zai nemi daya koh da ta waya ne koh ta hanyar sakon kar ta kwana su shirya ," kaunar junan su daga Allah take ,"

Cikin son fahimtar samun saɓani a tsakanin su umma take bin su da kallo har lokacin da tafeedan ya bacewa ganin ta ," tasowa biyamuradi youssouf yayi gami da dawowa daf da ita tamakar zai hau cinya ,"riko hannayen sa tayi tana me murmushi tace ,"yarona tun kafin ka tafi ka fara bani kewa ƙwarai zan yi kewar ka bani kaɗai ba har mai martaba ma jiya ya ɗauki lokaci yana mitar nisan da zaka yi mana alamu sun nuna kiris yake jira ya janye alfarmar da yayi na barin ka tafiyar nan ,"

Tare da tsananin ƙaunar iyayen nasa da yake taso masa yana kokarin dannewa yace "umma na shekara tamkar kwana ce kamar yau zaku ga Allah ya dawo muku da ni ,'kuma a jiya mai martaba ya sanar da ni cewa duk lokacin da yaga dacewa zai dunga tashin mutane daga nan musamman suna zuwa dubo masa ni ,ko da shi da kan sa bai samu damar zuwa ba ,"

umma na nima zan yi kewar ku ya karashe zancen sa yana me "ɗaga tafin hannunuwan ta ya sunbata tare da sanya kumatun sa a tsakanin hannun ta ,"ya cigaba da cewa addu'ar ku ita nafi bukata domin ita zata min jagora zuwa kan dukkanin wasu matakan nasara akan tafiyar da na sa gaba ,"

Murmushi tayi tana jin yadda kowacce ɗakika ɗaya take ƙaruwa da yawan kaunar ta ga gudan jinin zuciyar ta ", baza mu gushe ba muna masu yi muku addu'a har sai lokacin da mai rabawa ta raba tsakani ," ta furta hakan tana me kokarin maida ƙwallar da take son cika mata gurbin idanu ," yi maza kayi harama yarona .

Waiwayawa tayi ta dubi sashin da siyama take zaune wacce a zahiri take shafa fuskar wayar ta da ta jiƙe sharkaf da ruwan hawayen da yake ta ɗiga a bisa fuskar wayar ,"a dalilin matsananciyar kewar biyamuradi tare da wani karfin son sa da yake hanƙoro a cikin zuciyar ta , uwa uba damuwar ta da halin da biyamuradin zai iya kasancewa a ciki bayan tafiyar sa zuwa wata ƙasar , duk da cewa ba wannan ne karon sa na farko ba ,amma ita a gareta a duk lokacin da zai yi nesa da yin tozali ga idanun ta rauni ne sabo zuciyar ta take yi .

Siyama ta kira sunan ta ,"na'am umma ,!

Yi maza ki sa a fito miki da kayan naki a kai mota ku zo ku kama hanya kar rana tayi sosai ,"

Ta juya ga biyamuradi youssof wanda bai kai ga fahimtar kalaman mahaifiyar tasa ba , tace ", koh zaka yi magana ga hadiman naka "sojojin sa" tun da su suka san shirin motocin tafiyar ta ku , zu zo su ɗauki jakar siyama zata bi ka ku tafi tare zuwa niamey ɗin , ku kaita har gidan "ubbo"

Cikin jirkituwar fara'ar fuskar sa yake kallon bakin mahaifiyar tasa lokacin da take rattabo masa bayanin , amma kuwa lalle yarinyar nan tayi bala'in raina sa , watau ma da shi zata haɗa hanyar ta duk tarin direbobi da motocin da suke jibge a gidan nan ta rasa waye zata nema haɗa hanya da  sai shi ? A fusace ya waiwaya bangaren da yake zaton take da niyyar gargaɗin ta da idanun sa amma wayam yaga bata nan .

Cikin kwantar da kai yace ,"amma umma ni ba kai tsaye zan tafi zuwa niamey ba zamu tsaya a wasu wuraren me zai hana direba ya kai ta ?

Cikin ɗan ɗaure fuska umma tace ,"ko ma ina zaka biya tun da dai niamey ɗin ka nufa tare zaku tafi hankalina zai fi kwanciya sanin tana tare da kai cikin tsaro fiye da idan direban gida ne zai kai ta ," kayi musu umarni a zo a fito da kayan ta ,

Bai samu zarafin amsa mata ba ya hango fitowar siyama wacce ta sauya shigar ta daga doguwar rigar da take jikin ta a ɗazu ,zuwa wani sassalkan leshi ruwan madara wanda aka yi masa ɗinki riga buba da zane ta ɗaura ɗankwalin ta ya zauna mata ɗas akan tarin bakin gashin ta irin na fulanin usul , sosai kayan suka haska mata fatar ta me dauke da matsaicin haske ,zanen kuwa ya zauna ɗabas a cikakken kunkumin ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login