Showing 312001 words to 315000 words out of 411050 words
Chapter 105 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
yayi ya dubi iyayen sa , yanayin da ya gani a kan fuskokin su, su duka biyu ya razana shi musamman ma Amnee dake masa wani kallo mai kama da harara , da sauri ya mayar da kansa ƙasa kafin muryarsa cikin rashin amo sosai ta fito ,
" Na'amince Baba , Na Amince Baa .
Daga haka yayi shiru yana jin wani irin ɓacin-rai da ya taho masa tare da Amincewa auren yarinyar da ta gama yawon ta shekara da shekaru dan kawai tana ƴar uwar sa ,
Daga sama ya tsinkayo muryar Prof yana cigaba da cewa ,
" To Alhamdulillah Allah ya maka Albarka , ya baka 'ya'yan da zasu maka biyayya fiye da yadda ka min , Ubangiji Allah ya jiɓanci lamarin ka ya raba ka da sharrin duniya, Allah ya sa Albarka a zaman ku ya baku zuri'a masu yawa da Albarka , ka faranta min rai sosai .
Ya nisa lokacin da Amnee wacce haƙoranta ke washe tana ƴar dariyar dake nuni da zallar farin-cikin da take ciki take amsa addu'o'in sa ya cigaba da cewa ,
" za'a haɗa auren naku da na Rahima ayi shi duk a rana ɗaya dan a rage hidima idan ya so ko bayan sati guda ne idan ka samar mata muhallin da ya dace da ta zauna a can Abujan kusa da kai sai ka taho ka ɗauke ta hakan yayi ko ?
Yace yana mayar da ganin sa kan Amnee , wacce ta gyaɗa kai da sauri da maɗaukakin fara'a a fuskar ta tace , "Yayi sosai ma Baa Alaji , cikin sati uku masu zuwa ai su zainab sa iya zuwa Dubai yiwa takwarata kayan ɗaki .
Da wani irin bahagon yanayi Doctor hamza ya ɗago yana kallon su ,
Khaalty Rahima da duk hankalinta ke kan sa ta yi gyaran murya kaɗan , cikin ƙanƙan da kai tace ,
"Yaa ka min izni nayi magana wannan karon a matsayina na innar ango madadin uwa ,
Murmushi Prof yayi , "An miki izni , yace
" Yaya Dan Allah a mana alfarma , bayan an ɗaura auren a bamu ko da watanni biyu ne ya kammala shirin sa , kamar samar da wajen zama a tsanake , ya kuma sanar da uwargidan sa cikin kwanciyar rai , ya ɗan samu ya dai-daita lamuransa ,tunda nawi ne zai ƙaru masa kar a tsawwala yafi kyau yayi kome cikin lumana tunda indai ta zama matar sa ai kome ya kammala .
Cike da amincewa Prof yace , " To shikenan tunda kun nemi wannan Alfarmar an muku , amma ya tabbar kafin cikar watanni biyun ya kammala duk wasu shirye-shirye tunda ɗan naki ai Babban likita ne albashin sa ya kai wani mizani amma duk da haka na ɗauke mar nawin sadaki da duk wasu hidindumu da suka shafi biki na shi hidimar shine ya samar mata da muhalli mai kyau tare da ɗaura aniyar kulawa da duk wasu hakoki nata da suke kan shi daga ranar da zata shiga gidan sa har zuwa ranar da mutuwa zata ɗauki ɗayan su , kaji ko ?
Ya ƙarasa zancen yana juya akalar tambayar sa ga Hamza ,
" Gyaɗa kai yayi nagode Baa Allah ya ƙara girma ya furta hakan yana miƙewa yayi hanyar ficewa daga falon , Khaalty Rahima ma godiyar tayi musu sosai kamar zata zubda ƙwalla dan farin-cikin gatan da ake shirin yiwa ƴar ta ,
Tafe yake baya sanin ina yake ajiye ƙafar sa , Jacket ɗin sa riƙe a hannun sa saboda zafi da yake ji yana damunsa kota'ina cikin jikin sa tsabar tashin hankali , abunda ya faru yanzu a falon Baa so yake ace wani rarraunan mafarki ne daga cikin jerin shuɗaɗɗun mafarkan da ya dunga yi a shekarun baya , domin tuntuni ya wanke tabbatuwa hakan daga zuciya da tunanin sa .
Har ya kusa sashin sa ya tsinkayo muryar Khaalty Rahima tana ƙiran sa , juyowa yayi yana ƙirkiro wani rarraunan murmushi ya ɗora a fuskar sa ,
Ta ƙaraso idanun ta akan fuskar sa tana nazarin sa , muryar ta cike da nutsuwa tace
" Hamza kada fa ka damu kan ka wajen yin duk wasu hidindimu ko da gidan da zata zauna ɗin ma ka kama muku mai sauƙi idan ma ba hali ko ɗaki guda sai a bata a cikin gidan da kuke zaune nasan 'yata safiya ba zata ƙi ba , idan kuma duk hakan bata samu ba , zan sa Ukhtee ta roƙi Yaya ko anan sashin naka na gidan nan ai sai a barta tayi zaman ta ba ma sai ta tafi can Abujan ba , shi zaman aure ai bautar Ubangiji ce wurin Mace da Namiji baki ɗaya .
Tausayin ta ya kama shi , bai bar murmushin da yake yi ba yace " kar ki damu Khaalty yadda duk Baa ya ce haka za'a yi inshaAllah babu abunda zai gagara ,
Murmushi tayi , sannan ta cigaba da cewa , "Nagode, Nagode , yadda ka rufa min asiri kaima Allah ya rufa maka, ya baka 'ya'yan da zasu maka fiye da abunda kayi ga iyayen ka , nagode nag...
Hannunta ya riƙo ," haba Khaalty godiyar me kike min haka , ai ni...
Da sauri ta katse shi , tana cewa "Godiyar kome ma , ka yi kome da yakamata nayi ta gode ma Hamza Allah ya ma Albarka ,
" Amin ya amsa yana sakin hannun ta ya juya ya nufi sashin sa ,
A hanya komawa ciki Khaalty Rahima da Amnee suka haɗu , cike da farin-ciki suka rungume juna ba sai bakunan su sun furtawa junan su ba babu makawa sun san zucoyoyin su cike suke da farin-cikin faruwar wannan lamari.
" Baa Alaji yace a tambayi takwarata ita ma, ko ta amince ? Ko kuwa tana da wani wanda take so ya shirya yin aure , dan fa ba za'a mata dole ba ,
Ɗaure fuska Khaalty Rahima tayi , " wanne irin ma a nemi amincewar ta Ukhtee ? Shi namiji ma aka masa dole bare ita mace ?ai koma waye take so dole ta haƙura tunda Yaya ya yanke hukunci .
Murmushi Amnee tayi , " wa yace miki dole aka yiwa ɗan ki ? Ba soyayya bace ya sa ya ɗauko ta ya kawo ta gidan nan lokacin ma bai san ko suwaye su ba ? Ai kawai dan dai kaddara ta gifta tsakani badan haka ba da auren su ma zaki gan su ,
Ƴar fara'a Khaalty Rahima tayi , " duk da haka Ukhtee kin san fa irin aibun da yake tare da takwarar taki , ni gani nayi kamar an tauye shi da aka liƙa masa auren ta , kuma a yadda ma na lura yanzu ɗan nawa baya yi da takwarar taki ko da a baya ya nuna ra'ayin sa akan ta ,
Wucewa gaba Amnee tayi tana cewa " koma menene dai idan aka yi auren ai sa shirya kan su , so na gaskiya ai baya kankaruwa sai dai wani abu ya dusashe tasirin sa , ni bari naje na samu takwarata na shawo kanta ta amince ayi abun nan ranta na so , ba zan so ba a takuramin ita da auren dole ,
Ƴar ajiyar zuciya Khaalty Rahima tayi tana murmushi ta bi bayan Amnee zuciyar ta cike taf da ƙauna tare da farin-ciki marar misaltuwa da rabon ta da irin sa shekarun dayawa .
***
A ɗaki Amnee ta tarar da su ukun suna gwada ɗinkunan su , Falmata tana mitar burguza-burguzan riguna da siket ɗin da telan ya yi mata , " mai sunan Mama dan Allah ki ga wannan siket ɗin yadda ya min yawa ba ko fasali ni ɗai gaskiya a mayar ya rage min , naku ke da Yakaka cas-cas irin na ƴan mata amma ni shine ya min haka siket kamar buhu ?
Dariyar da tuntuni Yakaka take riƙewa ita ta ɓurtso kanta , cikin dariyar take cewa ,
" Kai Falmata gaskiya ba'a iyar miki , ke kome aka miki bai yi ba, yanzu da matsattsu aka miki cewa za ki yi sun matse ki sun hana Baby sakewa yanzu kuma anyi wanda Baby zai wataya kince an miki buhu , Allah kana gani dai , ka shirya min Falmata ,
" zunɓuro baki Falmata tayi dai-dai da shigowar Amnee da Mamar su ,
" Maama kin ga ku faɗa musu su daina tsokana ta kullum Rahima da Yakaka basu da abun yi sai tsokana ta, yanzu ku ga irin ɗinki da suka kai aka min ,
ta ɗaga siket ɗin ta ,
"ku ga kuma nasu ,
tace tana ɗaukar siket ɗin Yakaka ta nuno , ta ɗora da cewa " dan Allah Amnee za'a ce tela ɗaya ya ɗinka ? Nawa kamar wata gani garau , nasu kuma na yayi ?
Karɓar kayan Amnee tayi tana ajiyesu gefe , tace " sun yi girma kam , kiyi haƙuri za'a mayar ya rage miki wannan ɗinki ai ko a Niger ayi wanda ya fi shi tsari bare anan Nigeria gidan cancara ɗinki ,
Ganin ta ta mayar kan Yakaka da take kallon su tana dariya da haƙori ,
" Zo nan ki zauna takwara ta magana nake tafe da ita mai muhimmanci , duk ku nutsu ku bar shirmen nan ,
Amne ta furta hakan lokacin da take zama a bakin gadon , tana yiwa Yakaka nuni da gefen ta kusa .
A nutse Yakaka ta taho kusa da ƙafafun Amnee ta zauna a ƙasa maimakon gefen ta da ta nuna mata ,
Cikin nazari Amnee tace ,
" Takwara akwai wanda kuke tare ne ? Ina nufin akwai wanda kuka yi wata magana ta aure da shi ??
Dumm Yakaka tayi , zuciyar ta na sauya bugu , a lokacin ba wanda ya faɗo mata sai wannan mutumin da yayi ta nacin bibiyar ta shekaru kusan biyu tana zille masa a abuja , kafin barinta Abuja dai Lubna tace ta ba shi number ta Amma ko sau ɗaya bata taɓa riskar ƙiran sa ba , wataƙila daman wasa yake , ita kuwa bayan shi ai ba wanda ta taɓa saurara mafi yawan masu cewa suna son ta duk gani take fasiƙanci zasu yi da ita , domin tunda tasan illar zina da zunubin ta take jin tsoron maza ma gaba ɗaya .
Tunanin ta ya katse lokacin da taji Amnee na maimaita mata tambayar , a hankali ta girgiza kai , " Babu kowa Amnee ,
" kin tabbata ? Ki fa faɗa min idan akwai ,
Amnee ta sake furta haka domin haƙaƙewa ,
Zuciyar Yakaka ta fara shiga ruɗu da son sanin dalilin da ya kawo wannan maganar ta sake cewa , " Allah babu kowa Amnee ,
" To Alhamdulillah , Aminatu kina jina ko ?
Bata jira ta amsa ba ta cigaba da cewa , " Baa Alaji , Baban ku na gidan nan ya yanke shawarar haɗa aure a tsakanin ku ke da Yayan ku Hamza , muna fatan ba za ki bijirewa Umarnin mu ba ?
A razane ta ɗago kan ta saboda yadda zancen ya zo mata baga-tatan , ta shiga raba ganin ta tsakanin Mamar su da Amnee cikin wani irin jirkitatcen yanayi ,
Ganin yadda fuskar ta ta nuna yasa Khaalty Rahima hanzarin tare ko wanne irin sakamakon da zai biyo baya ta hanyar cewa ,
" kuma har an riga an gama yanke magana za'a haɗa bikin ku rana guda da na takwarata nan da kwanaki goma sha biyu , babu sauran wata magana .
Ihun da Rahima ta sa tana tsalle ta taho ta rungume Yakaka shi ya katse zancen khaalty Rahima ,
" Alhamdulillah burin Big bro zai cika , Masha Allah Baa mun gode sosai wallahi , sai ta sake ta da gudu tana barin ɗakin tana cewa , " bari naje na taya bro murna wayyo Allah ,
Shiru ne ya ratsa ɗakin sai tashin sautin murmushin Falmata da farin-ciki mai tsanani ya bayyana kan sa a fuskar ta ,
" Takwara baki ce kome ba ? , Amnee ta sake katse shirun ,
A hankali Yakaka ta ɗago kan ta ta ɗan dubi Amnee muryar ta can ciki tace , " Shi ya yarda ?
Tambayar da ta karya zuciyar iyayen nata biyu har ma da Falmata , kafin Amnee ta amsa ta sake cewa , " Idan har shi ya yadda shikenan Amnee ni ai koyaushe mai muku biyayya ce Baa kuma nima Babana ne , nagode da duk abunda kuka min .
Hannuwanta duk biyu Amnee ta sanya ta ɗago ta , ta zarce da rungumeta a jikinta ,
" Allah ya miki Albarka takwarata Allah ya baku 'ya'yan da zasu muku fiye da irin biyayyar da kuka yi mana ,
Addu'o'i ta cigaba da yi mata Falmata na amsawa da ƴar muryar ta dake bayyana amon murna ,
Miƙewa Amnee tayi tare da cewa ," bari naje na sake sabunta tsari da shiri bikin ya zama biyu , kai wannan shekarar ta zo min da ɗinbin Alheru Alhamdulillah Allah nagode ma ,
Bata jira cewar su ba ta fita ta bar su , su ukun ,
Yakaka ta ɗago idanunta dake cike da ƙwalla damuwa ɓaro-ɓaro a fuskar ta take kallon fuskar Mamar su tana son ko yaya ta bata damar da zata ce wani abu ,
A hankali Khaalty Rahima ta tako ta zauna a inda Amnee ta tashi , bata yadda sun haɗa ido ba tace " Naji daɗi da kika nuna halacci baki yi butulci ba , abu na gaba shine ki ɗauko haƙuri da juriya akan duk wani ƙalubale da za ki fuskanta a gaba ki riƙe su a matsayin makamin ki , sannan a ko'ina kika tsinci kan ki cikin kowanne hali ki ji tsoron Allah , Allah ya miki Albarka Amina .
" Amin, Yakaka ta amsa hawayen idanun ta na sauƙa bisa ƙuncin ta ,
Miƙewa khaalty Rahima tayi saboda zuciyar ta ba zata juri ganin irin wannan damuwar mai tarin yawa da take hangowa daga Yakaka ba , abunda ta riga ta sani inshaAllah cikin auren nan nasu akwai alheri mai tarin yawa ,
Tasan abunda Yakaka take tsoro bai wuce illar dake tare da ita ba akan irin abunda ta aikata , ita ta ɗau hakan a matsayin kaddarar Yakaka, kuma inshaAllah a wannan gaɓar ta ƙudurci aniyar yakice kunya irin wacce iyaye mata ke nunawa ƴaƴan su , zata ɗauri ɗamarar gyara ɗiyar ta ciki da bai tare da mata darussa masu inganci cikin ɗan zaman da ya rage musu tare , da zai taimaka wajen sauƙaƙa mata duk wasu ƙalubalen da ka iya taso mata a gidan aure .
Kayan gyara kuwa daga nan har N'Djamena, zata ɗau hanya ta tafi domin ta ga ta yiwa ƴar ta gyara mai kyau da zai taimaka ko kaɗan ne wajen samar mata da ɗan matsayi ko yaya a wajen Mijinta, sanin da tayi tana da abokiyar zama ko kusa ba zata so ƴar ta ta walaƙanta ba . ( Khaalty Rahima nima ina da saƙo zuwa N'Djamena nan amma ni turaren wuta nake so 🙄🤐 )
Tana bada baya daga ɗakin Falmata ta taso da sassarfa ta isa inda Yakaka take zaune kamar an dasa ta ko motsin kirki bata yi , tana zuwa ta rungume ta tana ƴar dariya-dariya tace , " Yakaka na Alhamdulillah , kin ga Al'amarin Allah ko ? Allah baya bacci Yakaka nayi murna , nayi murna , a kunne ta ta raɗa mata ,"Félicitations Mme Hamza Mustapha Dilmari,
Kukan da tun-tuni ke cin Yakaka a rai shi ta saki lokacin da tashin hankali yayi nasarar lillisa zuciyar ta , " Aure ? Aure tsakanin ta da Doctor hamza mutumin da ya tsani kallon ko fuskar ta ? mutumin da yake zargin ta da tafiya yawon banza ? Mijin sofi ƙawar samy Baby ? Anya Mamaa ba zasu kaita inda za'a kashe ta bane tun kwananta bai ƙare ba , a gareta wannan ba gata bane ba .
****
Duk yadda Rahima ta dunga ƙwanƙwasa ƙofar falon Doctor Hamza bai taso ya buɗe ba duk kuwa da cewa yana zaune dirshan a ƙasa a falon sai dai damuwar da yake ciki ta toshe masa kunne daga jin hayaniyar Rahima , ya zurfafa cikin tunani .
Wani irin yanayi marar daɗi ya tsinci kansa a ciki , ko kusa da yasan abunda zai riska kenan a garin da bai zo ba ,
Yarinyar da ta gama yawon banzan ta bai sani ba ma ko ta maƙalo wata cutar ita ce dan kawai Baa yana son gyara wani shuɗaɗɗan kuskure sai ya laƙa masa auren ta ?
Wannan da bata ajiye kome ba sai tarin ƙarairayi da yaudarar banza , har ita ce ake so ya gatata ? To wanne gata zai mata da bai nuna mata sumfurin sa ba a baya ?
Shi ya sani a da ya so ta amma yanzu ko alama baya jin ɗigo na son ta sai ma baƙin-ciki da yake ji a duk lokacin da ya gan ta .
Babu yadda zai yi , bashi da wata mafita shiyasa ya amsa auren ta da aka liƙa masa , da ace ba Khaalty Rahima bace uwar ta da Wallahi da ko ta halin ƙaka sai ya cisge wannan liƙin da ake son yi masa ,
To amma kasancewar ta 'ya ga Khaalty Rahima ya sa dole ya amince , zai aure ta , su zauna a yadda yanayi ya zo musu shi da ita ..!
Assalamu Alaikum masu karatu
Da fatan kun wuni lafiya ? Ina miƙo saƙon gaisuwa tare da fatan alheri agare ku baki ɗaya .
To ga fa abun yazo , wai inji mai tsoron wanka , Ina nufin bikin Yakaka da Hamza 😂
sister J , da Raly Garba , ku ne fa masu rabon anko , sai dai kuma ga lokaci ya zo a ƙure kwana goma sha biyu kachal ai ya muku