Showing 285001 words to 288000 words out of 411050 words

Chapter 96 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14391

, ta cikace mata gurbin da Yakaka ta bari ƙarƙashin son zuciyar ta ,

A ganin ta daga Youssouf har Yakaka bata su dace da zama Iyayen Mama ba , mutuwar Mama kuma hutawarta ne daga shan takaicin gori da aibatawan mutanen duniya ,

Ta zaɓi da ta tafi ta barsu tare tunda su biyun babu abunda suka sani sai tsananin son zuciyoyinsu , su zauna tare domin su biyun ai sun dace da juna ,

Ita zata koma Maiduguri , ta roƙi Prof kan ya raba auren su da Youssouf , babu wani sauran zama a tsakanin su tunda wacce ta aure shi a domin ta bata raye a duniyar ,

Abunda yake cikinta kuma ko Mace ko Namiji nata ne , zata riƙe abunta tayi rainon sa ita kaɗai ko da kuwa zata ɗora kwanon talla ne akanta tayi yawo bakin kasuwanni zata kula da ɗiyanta ba zata taɓa barin ɗan ta yayi maraici ba Alhalin tana raye .

***

Duk tafiyarta tsakanin Niger da Nigeria ta yi su ne a halin makanta , ƙarƙashin kulawa da jagorancin Hajja , kuma a motar gida da suke sake babu wata takura ,

Dan haka bata san kome ba game da hanya , ba gani take ba lokacin da aka yi tafiyar , yanzu kuma da take ganin hanyar dusu-dusu ba zata iya fahimtar cewa an nausa da ita wata hanya ta daban ne saɓanin wacce suka saba bi ba ,

Tsakanin Niamey da Diffa tafiya ce ta yini da kwana , kusan awanni ishirin , kuma hanyoyin ba sosai suka cika kyau ba musamman idan hanya ta sauƙa ta tsakanin rairayin hamada ,  ga kuma ranar da ta buɗe sosai take bada zafi .

Dan haka a wahale sosai take ga kiɗa da ya ƙi yankewa a motar tamkar ɗan wani ƙaramin gidan rawa , waƙoƙi daga na Sa'adu bori , sai na Hajiya Sa'adatu Aliyu "Barmani mai-coge"

bayan ƙarar kiɗan ga ta muryar shi kansa Ahmadou gayu da yake bin kowacce waƙa tamkar da shi aka rereta , bakinsa ko gajiya baya yi ,

Tafiyar su tayi nisa kasancewar Amadou gayu ƙwararren direba ne , azahar tayi musu suna wucewa ta cikin garin maraɗi ,

Falmata tayi lamo a motar gajiya gami da yunwa da ƙishirwa sun kai ga jiggata ta , babu kome a cikinta sai ruwa da ƙosai da suka saya tun safe a hanya da ba wani cin kirki ta yiwa ƙosan ba .

Lokacin da Amaudou gayu ya tsayar da motar sa , a gefen titi kusa da wani wajen sayar da abinci , domin a ci abinci , ayi sallah , daga sama ta tsinci muryar sa , yana cewa ,

"Maraɗi muke , cibiyar noma da ciyar da Al'umma to ayi harama , ayi sallah a ci abinci ayi kuma gurinsa , idan da mai laruri , ya tai ya sauƙe , domin idan na danna totur , banni dakatawa nan kussa sai mun dangana da Diffa , dan hakka kowa ya ɗau shiri , yauwa .

Ji tayi tamkar ta cigaba da zaman ta cikin motar , kar ta taka ƙafar ta a ƙasa domin tunda ya ambaci sunan Maradi tashin hankalin ta ya sake hauhawa , domin idan ba ta manta ba , Maradi shine sunan garin su Youssouf , ita fa a yanzu ƙyamatar duk wani abu da ya shafe shi take yi .

ganin idan ta cigaba da zama ita zata kwan ciki , yasa ta yunƙura ta fito , zagayawa ta fara yi neman banɗaki , saboda mararta da take cike .

Bayan ta idar da Sallar da tayi akan mayafinta , sai tayi zaune jugum daga inda take tana iya hango kai kawon jama'a ko ta ina a farfajiyar wajen tamkar ƙaramar kasuwa , masu abinci da masu shayi zuwa kan masu sayar da kayan sanyi sune birjik a wajen ,

Tashin hankalin da take ciki ya hana ta ji wata yunwar kirki tun ranar rasuwar Mama , sai dai tausayin abunda yake cikinta da tasan zai samu ne kaɗai daga abinda ta ci , ya sa ta miƙe ta ƙarasa wajen wata ƴar rumfar sayar da abinci da ta ga mutane na saya sosai , tuwo ta ce a kawo mata miyar yauƙi da kuma kunu bayan ta miƙa kuɗinta ga wata matashiya .

Bata san ita kanta a matse take da son cin abincin ba sai da tayi arba da fari sol ɗin tuwon garin shinkafa da miyar kuɓewa busasshiya da aka ɗan ɗiga mata man shanu a ciki , babu laifi abincin su bai cika tsada ba da ɗan aukinsa , domin 'yan madai-daitan curi/mal-mala ne biyu kuma har da nama yanka biyu .

Da zaƙuwa ta fara cin abincin bayan ta juya baya daga mutanen da suke wajen ,

Tas ta cinye tuwon , ta ɗan sha kunun gyaɗa da ɗanyar shinkafa da yake fari sol shima ba'a cika sugar ba .

Kamar yadda Ahmadou gayu yace su yi guzuri bayan ta gama cin abincin sau kuma ta sayi gasasshen nama da ruwan roba biyu bata jinkirta ba koma mota , nan ta samu duk kowa ya dawo ita ɗaya ake jira dan haka tana shiga , Gayu ya danna totur suka sake ɗaukar hanya .

***

Biyamuradi Youssouf tare da Yakaka da Hajja babu inda basu nemi Falmata ba a tsuƙin unguwar suna haɗawa da cigiya , basu haɗu da ko wanda yace musu ya gan ta ba ,

Iyakar gigita Yakaka ta shige ta , hawaye da gumin zafin rana sun haɗar mata , tsoronta ɗaya ne kada Falmata ta yanke hukuncin tafiya yawan duniya , kamar yadda ita tayi , ta san halin Falmata sarai , tana da zafin rai idan har aka taɓo ta .

Tun a jiyan yadda tayi mata daman ya bata tsoro , sai dai bata yi tunanin zata iya yanke ɗanyen hukunci irin haka ba , meyasa Falmata zata yi mata haka ? Meyasa baza ta yafe mata ba ?

Zuwa ƙarfe goma na safe sun gama cire rai da ganin ta , haɗuwa suka yi a falon kowannen su ya yi jugum ,

Youssouf ya ɗago kansa yana yiwa Yakaka kallon da yafi kama da harara ,

" Ina sake faɗi miki muddin ke kin ka ɓoye ta , ki fiddo ta kafin na kai ga sani da kaina,

A zuciye Yakaka ta katse shi ,

" Ka daina faɗa min maganar da bata da tushe , Falmata ƙanwa ta ce tare ka gan mu idan har ni ban ce sai ka nemo Falmata ba kai baka isa kace na sace ta ba Dan Allah ka barni na ji da damuwa ta .

"Kuyi haƙuri ku duka , lamarin ba na sa'in'sa bane mu ji da tashin hankalin da muke ciki , Babban soja ko za'a kai cigiya kafar watsa labarai ?? Abun yafi kama da sace ta aka yi idan ba haka ba ina Uwarɗakina ta san gari bare har ta fita da kan ta , to ta tafi ina ? Ita da ba lafiyar ido da ta jiki ta cika ba , O Allah gamu gareka , ka iyar muna. 
   Hajja ta ƙarasa zancen ta tana sake rafka tagumi

Tamkar an tsikareta Yakaka ta miƙe tana cewa

"muje tasha , tashar da ake hawa motar barin gari , wataƙila Falmata ta tafi Nigeria ne ,

Cikin ƴan mintoci suka cimma tasha ,  gurin da ake lodin fasinjan zuwa Nigeria suka nufa , suka tarar mafiyawan motoci sun riga sun tafi sai ɗaya ce bata kai ga tafiya ba ita ma mutane biyu ake jira ,

Babu Falmata a cikin su , dan haka Youssouf ya dunga bin ƴan kamashon yana nuna musu hoton Falmata dake fuskar wayarsa tare da tambayar ko ta hau motar zuwa Nigeria ?

Kowa yace bai ganta a tashar ba , zuwa lokacin duk wani firgici da tashin hankali sun zana kansu ɓaro-ɓaro a fuskar sa da tayi jaa , jijiyoyin kansa kuma suka bayyana ruɗu-ruɗu , a sarari ya furta

" Fatima ina kin ka tafi ??

Dattijon ɗan kamashon da ya sa Falmata a motar Mallam Ahmadou shine ya ƙaraso gaban Youssouf da yake tsaye riƙe da kunkumin sa , sai duban gabas da yamma yake cikin rashin samun madafa,

" ance kun taho ne neman watta ɗiya ko ta tai Nigeria kou ?

Cikin sarewa Youssouf ya amsa da "eh , yana share gumin goshin sa ,

"itta ce wata 'yar baƙa kakkaura mai matsakaicin tsawo tana da zanen barebari a fuskar ta ?

Youssouf da Yakaka a tare suka yi rige-rigen amsa masa da cewa "ita ce , tana ina ?
   Youssouf ya dora da nuna masa hoton Falmata domin ƙarin tabbatarwa, ya karɓi wayar bayan ya kashe idanu ya ƙure mata kallo , miƙawa Youssouf wayar yayi da yake ta bin sa da kallo cikin zaƙuwa ,

"Babu shakka itta ce wannan ta zou nan da gefen Alfijir, tana biɗar motar zouwar jahar Borno Nigeria dagga nan kai tsaye , nan nayi mata togaciyar kan nisan dake tsakanin Niame....

   "Baba ina take yanzou ? Ta tahi ne ko kuwa tana ina ?

A kaikaice dattijon ya dubi Youssouf da ya katse masa hanzari , ya ɓantari goron sa kafin yace

  " ta taihi tun motar farko dagga nan kai tsaye zouwa Borno ta yankin diffa zasu ɓulla Nigeria zuwa yanzu wataƙila sun kusan cimma sandamun Maraɗi , ai Ahmadou gayu zaƙaƙurin direba ne ,

  " nufin ka dagga nan Fatima ta tai Borno ta yankin Diffa ? Yankin da yake cike da hatsarin ƴan tawayen Boko Haram suna kama mutane suna garkuwa da su bayan sun kashe wasu ? Bodar da take a rufe , sai ta ɓarauniyar hanya ake bi ? Shine kun ka turata baku hanata tafiya ba , ba kuyi yi la'akari da ƙarancin shekaru gami da rauninta na ɗiya macce ba ?

Wani irin raruma ya kaiwa Dattijon kafin ya ankara ya ɗago shi , cewa yake ,

  "ko waye direban kayi ƙiransa maza ya dawo da matata , kadda ya yarda ya jefa rayuwarta ga wannan mummunan hatsarin da kai da shi da zuri'ar ku baki ɗaya sai na ɗaure ku muddin wani mummunan abu ya afku ga matata ,

Da kyar mutane suka ɓanɓare hannuwan Youssouf daga wuyan dattijon nan da kawo lokacin numfashin sa ya fara ƙaƙarewa ,

Da ban baki gami da lallashi jama'a suka danni Youssouf ya nutsu aka nemo number Ahamdou gayu aka bashi ya shiga ƙira jikinsa sai tsuma yake ,

Da kyar ya samu wayar ta shiga , sai dai ko da aka ɗauka waƙar Barmani Mai-coge ce kawai take fitowa tarwai ta cikin wayar sai kuma iska irin na hanya ,

  Ya dunga "Alo , Alo , Alo ,
Bai ji muryar kowa ba , ya kashe ya sake ƙira nan ma an ɗaga amma "Alo, Alo , kawai ake cewa daga ɗaya ɓangaren , duk maganar da yake yi ba'a jinsa ,

Haka ya dunga ƙira cikin gigita tsawon lokaci ba'a ɗagawa daga baya ma daina shiga wayar tayi , cikin tashin hankali ya ɗago kansa , sai dai duk mutanen da suke tare a wajen ya tarar babu ko guda sun watse, sai fa Yakaka da take durƙushe a ƙasa tana hawaye sai kuma Hajja da take tsaye ta rafka tagumi idanunta da guntayen ƙwalla ,

Rasa wanda zai sake tunkara yayi , dan haka suka jiyo gida idan banda kuka babu abunda Yakaka take yi , jin cewa Falmata ta hau hanya mai tattare da hatsarin ƴan Boko Haram , ya kaɗa ƴan hanjinta ,

Zuciyarta ta cika da tsoron sake rasa ƙanwarta , Youssouf ma tunda suka dawo gida kai tsaye sashinsa ya shiga yana sake gwada ƙiran layin Ahmadou gayu , sai dai har chajin wayarsa ta kai ga sauƙa bai samu nasarar sake samun layin ba ,

Ajiye wayar yayi lokacin da wasu hawaye masu zafin gaske suka sauƙo masa a karo na biyu cikin tarihin rayuwar girmansa , yayi kuka .

***

Su Falmata sun kwana a wani ƙaramin gari dake yankin zinder kusa da garin Diffa , anan suka yada zango , cikin motar ita ta kwana yayin da sauran mazan suka fita ba tare da ta san ina suka yi ba .

Asubar fari bayan tayi Sallah , suka sake damƙar hanya , tafiyar yini guda ta kai su ga kaiwa ƙarshen yankin diffa ta gabashi , inda suka sau hanya tare da nausawa cikin daji  ,

Gudun da motar take alhalin kan tuddai da kwari ne yasa motar take buga tsalle lokaci zuwa lokaci , da hakan yasa cikin falmata ya wani irin riƙewa tare da fara yin ciwo , ga buguwar da jikinta yake yi da motar , gami da warin sigari da bata san yaushe ya gauraye motar ba yana ƙoƙarin sanyata haraswa .

Duk da bata gani sosai ta fahimci dare yayi saboda duhu da ya mamaye ɗan guntun hasken da idanun ta suke iya gani , ya zama dilum bata ganin kome .

Sun kai kimanin awanni biyu a daji suna wannan gudun kafin ta ji motar ta tsagaita gudu , ta tsaya a hankali ,

Hasken da ya dallare mata idanu mai ƙarfi ne da yasa ba shiri ta jaa hijabin ta ya rufe mata idanu , gami da runtse idanun .

Tana jin lokacin da duk na cikin motar suka fita harda shi direban , a hankali ta buɗe idanunta ta cikin motar tana iya ganin mutanen wajen dusu-dusu da taimakon hasken wasu manyan dogayen tociloli da suke hannuwan wasu gungun mutane ,

Abunda ya bata mamaki bai wuce ji da tayi sun juya harshe cikin yarenta ba na kanuri , tar-tar suke magana da Ahmadou gayu da sauran mutanen cikin motar da tunda tafiya ta haɗa su bata ji sun cika hira ba ko da kuwa a tsakaninsu ne , bare har ta fahimci yare su ɗaya ..

Ba sosai ta kai ga Fahimtar maganganun su ba , har kawo lokacin da suka ƙaraso wajen motar , da hausa Ahmadou gayu yace ta fito za'a ɗau saƙo daga ƙarƙashin kujerar da take ,

Cikin sauri ta ziro ƙafar ta waje ta fito , cikin rashin sa'a ta gurɗe ta kusa faɗuwa ,

'yarinya ki kula ,

Cewar Ahmadou ,

Muryarta na ƴar rawa tace

"Baba inada matsalar ido bana gani idan dare yayi wajen babu ramuka ko ?

" Au to to ashe ma musaƙa ce , to babu laifi , ai daman irin ki ake so marasa idon yarinya yau makantar ki ta miki rana , ko kuwa ?

Ya juya ga mutanen da suke bayan sa yana tambayar su ,

amma babu wanda yace ƙala a cikin su , biyu daga ciki suka matsa jikin motar tare da fara ɗaga cikin ramukan kujerun motar suna fito da wasu ƴan madai-daitan kwalaye da basu cika girma ba ,

Falmata da ta durƙusa tana ɗan murƙususu saboda marar ta da take mata ciwo , ta cikin hijabinta tana iya hangen kwalayen da bata san da su ba a motar  kafin zuwa wani lokaci an tara su da ɗan yawa ,

Ɗaya daga cikin mutanen da fuskar sa ke naɗe da mayafi ya sunkuya tare da ɗaukar Ammo box ya buɗe ya zazzago wasu alburusai da suke ciki a jere , hannu ya miƙa na gefen sa ya miƙa masa tocilar hannunsa , ya haska harsashin sosai yana jujjuya shi a hannun sa ,

Cikin Falmata ya bada wani sautin ƙululu lokacin da ta ga an miƙo masa bindiga ya zura harsashin a ciki , wani irin tsoro mai girma ya ziyarceta , meye yaje shirin faruwa da ita ? aina ma wai take ?

Magana suka fara yi bayan sun ɗan yi gaba kaɗan da inda take tsugunne ba tare da wani ya kulata ba daga cikin su ,

Tsantsar tsoro yasa ta daina fahimtar me suke cewa duk kuwa da cewa da yaren da tafi fahimtar sa bisa ga sauran yaruka suke magana  , idanunta sun fir-fito , bindigogin hannuwansu kawai take bi da kallo da zuwa lokacin ta lura fiye da rabinsu suna riƙe da bindiga .

Da ɗaya-ɗaya suka jide kwalayen , tana ganin lokacin da suka ɗaga kujerar da take baya suka maida wata jakar bacco gurbin da suka cire kwalayen ,daga haka ta ga sunyi musabaha tsakanin Ahmadou Gayu da wasu daga cikin tawagar ,

Da gudu-gudu suka hau bayan motocin su ,suka tada tare da nausawa cikin daji .

Amadou gayu ya ƙaraso kanta lokacin da yake cewa ,

" 'yar dindimi sai ki tasso mu tai na sauƙe ki daga bakin hanya inda zaki iya samun motar da zatta sada ki da cikin garin Maiduguri ni iyakatai bakin daji kome da kin ka ji motsi nai anan ki manta da sautin anan muddin kin biɗarwa kan ki lahia , kin ji kou ?

Gyaɗa kai Tayi da sauri , ta shiga motar suka sake nitsawa cikin daji , sai lokacin ta lura babu kowa a motar sai su biyu , ko ina sauran mutane huɗu na bayan motar ? Ta tambayi kan ta .

**

Ƙarfe sha ɗaya na safe yayi mata a cikin babbar tashar garin Maiduguri , bayan Ahmadou gayu ya sanya ta a mota daga ƙaramar hukumar Mobar da ta kawo ta cikin garin .

Duk tayi busu-busu da ita ta fita hayyacinta , yunwa da firgici sun maida ita firka-firka , amma duk da haka .

Hamdala ta dunga yi lokacin da ta samu tabbacin tana cikin garin Maiduguri ne ta samu ƙubuta daga hannun mutanen da tun-tuni ta fahimci ko su waye su .

tunanin inda zata dosa kuma ya rufe ta , domin ita dai bata san takamai-mai sunan unguwar gidan Prof ba , duk rayuwar ta cikin garin ta yi ne a halin tana makauniya ,

Wata rumfa ta hango ana tuyar doya da ƙwai a bakinta,  ta ƙarasa ta zauna daga ƙasa tana kallom mutanen wajen da fiye da rabin su maza ne hatta mai tuyar da mai rabawar duk samari ne ,

Da zamanta a wajen , wani matashi da ya ciko ɗan farantin roban hannunsa da soyayyar doya mai kwai , ya mata duban ƙasƙanci ,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login