Showing 309001 words to 312000 words out of 411050 words

Chapter 104 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14279

sawun mu ba ko da da ƙiran waya , ni kuma na ƙira layin nasa da nake da shi bai tafiya , ai kin ga sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha , idan zaman gidan daɗi ne ki zauna ga waje kiyi ta zama har mahadi ya bayyana .

Daga haka ta jaa bakin ta ta tsuke tana kawar da kai .

Rai a ɓace Falmata ta miƙe ba ko sai anjima ta fice a ɗakin , Hajja ta bi bayan ta da kallo , cikin ran ta cike da tausayin ƙuruciyar dake ɗiban ta tana shirin sanyata yiwa kanta sakiyar da ba ruwa , ita a karan kanta ba ƙaramin damuwa tayi ba da rashin ji daga wajen Youssouf kamar yadda yace kafin rabuwar su zai ƙira domin jin labarin halin da suke ciki , rashin ƙiran nasa ya ɗaure mata kai , tsoron ta ɗaya kada ace ya sau auren Falmata , ko kaɗan bata fatan hakan , tayi ƙiran wayar sa aƙalla sau goma bayan tahowar su amma bata shiga fatan ta Allah yasa lafiya .

Haka kawai ta ji damuwa tana mamayar ta kan cewa da Hajja tayi tunda suka taho wai bai ƙira ba , ita a nata zaton su na gaisawa da Hajja ta waya , kawai bai neme ta bane sanin da yayi tana fushi sosai da shi dan haka ko an kawo mata wayar ma ba karɓa zata yi ba kamar yadda ita ma ta kuɗurce a ran ta ,

To ashe ma ita take zaton haka shi yana can ko tunawa da sha'anin da ya shafe ta baya yi , ya riga ya yada da ita da abunda ke tare da ita , duk sai jikin ta ya sake yin sanyi ƴar hirar da suke yi ma ita da Yakaka da Rahima ƙarama kafin tashin ta zuwa ɗakin Hajja,  sai ta gagara cigaba da sa baki tayi lamo a kwance tana jin yadda abunda ke cikinta yake dunƙulewa waje guda ,

Yakaka ita ta lura da shirun da tayi dan haka ta kai hannu ta jaa yatsar ƙafar falmata tare da cewa ,

  " Maman baby yaya ne ? Akwai damuwa ne ?

  Janye ƙafar ta tayi ba walwala a muryar ta tace ,
   " Maman mama kin san dai na ce ku daina ƙirana da sunan nan bana so ,

Rahima ta kwashe da dariya "  to Yakaka mu daina cewa Maman Baby , mu koma ƙiran ta da Matar soja yafi daɗi ko Hajja Falta ?

Kuka ta fashe da shi da a farko suka yi zaton na wasa ne , sai da suka ji har tana jaan hanci tukun suka tsahirta daga dariyar da suke duk kuma sai hankalin su ya tashi jikin Yakaka har rawa yake ta tallafo Falmatan zuwa jikin ta suna rige-rigen tambayar ta " me ya same ta take kuka ??

   Ba tare da ta daina kukan ba tace ," Nace muku bana so  , bana so bana so , kun ƙi dainawa .

  Da sauri Rahima tace , " Yi hakuri ba zamu sake ba dan Allah ki daina kuka daga wasa ? Haba Fatima-zahra Maman Baby ,
   Da sauri Yakaka ta ɗago tana hararar Rahima ,
   Dariyar da Rahima take bata tuƙe ba ta dafe baki tare da cewa
   " Au So nake nace Mamar Mama ta biyu , yi haƙuri ba zamu sake ba kin ji ƴar ƙanwata ?

Batare da ta amsa ba ta zame daga riƙon da Yakaka tayi mata ta koma ta kwanta a inda ta tashi , wani irin yanayi marar daɗi na sake mamayar ta baki ɗaya bata jin daɗin kome , abu kaɗan sai ya ɗaga mata hankali ya ƙara mata damuwa .

  Fuskar Yakaka cike da damuwa take kallon ta , damuwar da ta hango tare da ita ya ɓata mata walwalar da take ciki mai daɗi , cikin ran ta ta haƙiƙance akwai abunda ke damun Falmata haka kawai ba zata yi kuka ba daga ɗan wannan wasan , ji tayi ta damu da son sanin damuwar ƙanwar ta  .

Tun daga ranar sai duk walwalar ta ta ragu damuwa ta bayyana a cikin suffa da mu'amalar ta , kome take yi babu nishaɗi duk kuwa da cewar basu taɓa tsintar kan su a cikin gata da riritawa irin na wannan lokacin ba , daga kan Mamar su har zuwa Amnee da Baa , Rahima da kusan kowa na gidan nan-nan ake da su ,

Sai dai damuwar ta mai zurfi ce , kullum cikin kasa kunne take ta ji ko Hajja zata ƙira ta tace ga Youssouf ya ƙira su yi magana ko kuwa ma tace ya ƙirata ita sun gaisa amma ko alama ta yin ƙiran nasa bata ji ba , ita kuma tsoron surutun Hajja ya sa ta kasa tambayar ta .

***

Yau tana zaune a tsakanin mamar su da Amnee suna ƴar hira , su ukun ne kawai a wajen , Rahima da Yakaka sun tafi amso sabbin ɗinkunan su da Baa ya bayar da kuɗi aka kawo musu atamfofi da lesika aka kai ɗinki domin su yi amfani da su wajen bikin auren Rahima da yanzu bai fi kwanaki goma sha biyu ba suka rage .

Amnee ta ɗan dube ta tana murmushi tace ,
   " Fatima zahra , cikin nan naki wata nawa yake ciki ne ? Anya bai kamata ki fara zuwa awo ba ?

  Da sauri ta ɗago kai ta dubi Amnee sai kuma ta sunkui da kai batare da tace kome ba ,

Khaalty Rahima ta ɗan dube ta , tace Fatima ba dake ake ba ?

  A hankali tace , " Nima ban sani ba Amnee ,

Jimm Amnee tayi kafin ta ce , " to ai ya kamata ki fara zuwa awo banda ma dai shirme irin naki Fatima cikin fari da ake ɗokin sa da yi masa ƙirgen ƙwaƙwaf amma ke kyace baki san watannin sa ba ?

Hajja wacce take ƙarasowa falon daga waje inda ta gyara shanyar alkamar da ta wanke ta yin kunun Baa , sarai ta ji wasu daga kalaman Amnee , tace
   " Wallahi uwar masu gida ke ma dai kya faɗa , wannan uwarɗakin tawa da kike gani kome nata daban ne bata ajiye kome ba sai wauta , cikin nata yana gaf da cika watanni huɗu a yadda lissafi na ya nuna min , sai dai kuma kin san cikin fari ɓuya ce da shi amma lokacin da suka dawo dai daga can turai cikin bai wuce watanni biyu ba da ƴan ɗoriya , daga can ta yo cikin ,  yanzu kuma kin ga dawowar tasu kusan kwanaki talatin .

Dariya ce ta so kama Khaalty Rahima jin wannan ƙokari na Hajja na ƙididdige kwanakin cikin Falmata da ko ita kakar ɗan ko ƴar ba ta iya haka ba ,

Ran ta cike da jin daɗin tsantsar ƙaunar da ta lura Hajja na yiwa ƴa ƴan ta tace ,
  " Hajja baki da dama ke da Uwarɗakin ki ba mai shiga tsakanin ku , wannan zuwa awon ma ai ke zaki dunga raka ta  .

  Ƴar dariya Hajja tayi kafin ta harari Falmata tace ,
    "  can dai su ƙarata ita da Babba Uwar Mama ita zata raka ta bana iya miskilancin fatima ba .

Dariya Amnee tayi kafin tace,
  " zan yi maganar da Baa Alaji idan ya so sai ya nema mata iznin mijin nata , kan fara zuwa asibiti saboda kuwa zuwa awo abune mai matuƙar muhimmanci ga mata masu ciki , yadda duk muka yi sai ki shirya a fara kai ki kin ji ko ƴata ?

A hankali ta gyaɗa kai kurum , tausayin abunda ke cikin ta kan yadda Mahaifin sa yayi banza da su ya fara kamata .

Daga haka Amnee da Mama suka cigaba da yin hirar su , a hankali ta miƙe ta nufi ɗakin su , domin kuka da take jin yana taso mata ,

Tana shiga ɗakin ta sanya tafukan ta duk biyu ta rufe fuskar ta tana fashewa da kuka marar sauti .

Tana tsakiya da yin kukan ta tsinkayo Sallamar Doctor Hamza , shuru tayi tana saurarawa jin tashin muryar gaisawar da suke shi da iyayen su ,

Jin sun gama gaisawa sai ta miƙe tan share hawayen ta , Doctor Hamza yana sawun gaba na mutanen da ba zata manta alherun su ba a rayuwar ta ,dan haka ya zama dole duk inda ta ji shi ta je ta gaishe shi ko da kuwa babu ƴan uwantaka a tsakanin su bare yanzu da suke ƴan uwan juna makusanta ,

A hankali ta fito , ta tako zuwa tsakiyar falon ta zauna tana gaishe shi ,

Da murmushi yake amsawa yana jin daɗin ganin ta samu lafiya , yace
   " Fatima ƙanwata ke ce haka kika girma ? Alhamdulillah lafiya ta samu .
Ƴar dariya tayi , kafin tace " Ni ce Yaa dakta ,

  Dariya shi ma yayi yace " lalle girman 'ya mace ba wuya , Al'amarin Ubangiji kuma ya zarta yadda duk muke zato , Khaalty lokacin da na kawo yaran nan gidan nan ko kusa bani da masaniyar muna da wata alaƙa tsakanina da su , kawai nayi niyyar taimakon su ne domin Allah , ashe kin ga ma abun farin-ciki ƙannena ne su , lokacin da Amnee take sanar da ni ba ƙaramin mamaki nayi ba da farko ma ni na shiga ruɗani ne su waye Amina da Fatima ? Sai da ta min bayani sosai ,

Ya nisa kafin ya cigaba da cewa , " Khaalty nayi murna da Allah ya haɗa ki da ƴaƴan ki , Allah ya kuma kare ku baki ɗaya , ya sa bakin wahalar ku kenan .

  " Amin Amin ɗana , tace da sigar zolaya ,
  Shima dariyar yayi da sauti sanin cewa ta ƙira shi da ɗanta ne dan tasan bai son haka tun yana ƙaramin sa a cewar sa tayi ƙanƙanta ta ƙira kanta Mamar sa ina ma laifin tace ita yayar sa ce  ?

  Khaalty Rahima ta cigaba da cewa , " kawai sai muka gan ka babu sanarwar zuwa ? Ko wani aikin ka zo yi ?

  Jingina kansa yayi da kafaɗun kujerar da yake kai , yace
  " Baa ne ya ƙirani tun shekaran jiya , yace lalle na zo cikin kwanaki biyun nan , to nima daman kuma ina shirin zuwa saboda shirye-shiryen bikin nan ban sani ba ko akwai abunda za'a iya buƙata mai muhimmanci ayi a gama akan lokaci tunda ga ku , kar ya zama irin na bikin su zainab kome a hagunce , aiki ne ya tsare ni ban iso da wuri ba .

  " Na fara shiga wajen Baa ɗin amma na tarar da shi da mutanen nasa kin san sai kuma ya sallame su da abunda suka saba , kai mutanen mu sai a hankali , wai kawai sai ku mayar da wani mutum ɗaya wajen zuwa ku faɗi buƙatun ku da damuwar ku kamar wani shi ɗin injin buga kuɗi gare shi ? To wai wanene bashi da buƙatu da damuwowi ?

Sallamar Rahima da ta shigo da ɗan gudun ta , ya sa shi mayar da ganin sa kan ƙofar , dai-dai da shigowar Yakaka , wacce tunda ta ji Rahima na murna tana cewa ga motar Company ya zo , ta ji jikinta yayi sanyi duk taku ɗaya na kafafun ta da jin ƙarin hauhawar bugun zuciyar ta ,

Idanun ta ta sauƙe kansa da shigowarta falon , karaf suka haɗa ido ,

Kowanne su yayi saurin janye ido Doctor Hamza ya haɗa da kawar da kai ita kuma ta sunkui da kan ta , cikin raggon taku ta ƙaraso ta bayan kujerar da Amnee take kai , tayi durƙuso da kyar ta haɗo kalmomin ,
   " Ina wuni ,
  Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da zolayar Rahima da yake cewa " ke little idan ana shirye-shiryen aure ramewa ake yi ke kuwa ga ki sai sake kumbura kike , me takwarar ki take baki haka hala ɗure take miki ??
   Dariya Khaalty Rahima da Rahima ƙarama suka sa a tare , kafin Rahima ta zagaya ta kujerar da Amnee take ta saƙalo hannuwanta a wuyan ta , tana haɗa fuskokin su tace ,

   " Khaalty kar ki faɗa masa , abun sirri ne ko ?
 
Amnee wacce ta lura da yadda yayi watsi da Yakaka , kuma bata ji daɗin hakan ba sai ta ce ,
   " Takwarata tana gaishe ka fa ?
Wani wur-wur yayi da ido , sai kuma yace " Ok Lafiya , ba tare da ya dube ta ba illa haɗe girar sa da yayi , ya zaro wayar sa daga Aljihunsa , kaf fara'ar fuskar sa ta ɗauke .

A hankali Yakaka ta miƙe tana murmushin yaƙen akan wasan da Mamar su da Rahima suke yi , sum-sum ta wuce ɗakin su .

Ƙiran wayar Amnee da aka yi yasa suka ɗan tsahirta daga hayaniya , bayan ta ɗaga wayar sai ta saurara ,
  " to Baa Alaji tace. 
Duban Khaalty Rahima tayi , tace
  " Ukhtee , da ke da Ɗan ki ku zo muje Baa alaji yana ƙiran mu .

***

Bayan sun sake gaisawa a tsakanin su ,a ƙagauce Amnee da take zaune daga gefen sa tace
  " Baa Alaji lafiya dai ko ? Wannan ƙiran Allah ya sa Alheri ne. 

Prof ya dube ta da ɗan murmushi , yace " inshaAllah Alheri ne Aminatu ,
ganin ya mayar kan Hamza da Khaalty Rahima da suke zaune a ƙasa kafin ya fara cewa .

" Dalilin da yasa na ƙira ku ba kome bane sai kan wata magana ko kuwa nace shawarar da na yanke tun watanni baya , amma ban sake haƙaƙewa akan abunda nake niyyar yi ba na haɗa Aure tsakanin Ƴaƴa na biyu kai Hamza da kuma ƙanwar ka Amina ba , sai da tabbatuwar yaran nan ƴan uwan ka ne ba wasu bare ba da ba'a san asalin su ba , hakan ya sa na sake ganin dacewar lamarin fiye da farko ,

" Duk da cewa batun ƙarin auren da nace kayi ba sabon abu bane a wajen ka , tun kwanaki na sanar da kai ka kuma yi na'am kawai wacce nake burin ka aura ɗin ne baka kai ga sani ba , sai a yanzu nake sanar da kai Aminatu ƴar Rahima ƙanwar Mahaifiyar ka ita ce matar da nake son ka aura a matsayin matar ka ta biyu , da fatan ba zaka yi gardama ba ??

Daga Khaalty Rahima har Doctor Hamza baki ɗaya idanu suka zuba suna kallon sa , a hargitse sosai ƙwaƙwaƙwar Doctor Hamza take , meke nan yake ji ? Yaya Baa zai masa haka ?

A hankali ya sauƙe ganin sa daga kan prof ya sunkuyar da kansa ƙasa , ta wutsiyar ido yake hango yadda Khaalty Rahima ta dawo da ganin ta kan sa , zuciyar sa na shaida masa cewa amsar sa kowa a wajen yake jira , kan ya amince ko kuwa a ah  ?

abunda ya bi duk wasu gaɓɓai na jikinsa ya kassara bai wuce kaifin idanun Khaalty Rahima ba , matar da tunda ya buɗi ido ya gansu tare da Mahaifiyar sa a matsayin shaƙiƙan juna , ƙaunar ta a gare shi kuma mai tarin yawa ce , jin daɗin wasannin ƙuruciyar sa duk ya yi tare da ita , shi kuwa ta yaya zai iya cewa yaƙi ƴar da ta haifa daga cikin ta a tsatson idanun ta ?  wallahi ba zai iya ba , Baa ai bai kyauta masa ba da ya titsiye shi da wannan batun a gaban idanun Khaalty Rahima ,

Satar kallon Amnee yayi yaga yadda ta nutsu fuskar ta da wani irin yanayi na nuna  zaƙuwa tana kallon sa .

Yawan ƙaunar da Amnee ke yiwa Rahima ya san kuskure kaɗan idan yayi kan lamarin nan zai matuƙar sanyata a ɓacin rai , shi yaya zai yi ne ?

Muryar Khaalty Rahima da ta ratso shirun  wajen ya katse masa tunani ,

  Da wani yanayi cikin muryar ta da ya sha banban da murmushin yaƙen da yake fuskar ta a lokacin tace ,

  " Yaya , mun ji daɗi mun kuma yi farin-ciki da wannan haɗin da kayi niyyar yi , Sai dai Yaya , Hamza ai tuni ya riga ya zaɓi abokiyar zaman sa har kuma tafiyar su ta fara miƙawa cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna ba tare da yana da niyyar  ƙara yin wani auren ba , dan haka ni ina ganin Yaya da dai an bar yarona ya zauna da matar sa ɗaya kar a ɗaura masa nawin mata har biyu da bai shirya ba .

Prof da yake kallon duk su biyun , ya gyara zama , yana mayar da ganin sa gaba ɗaya kan Khaalty Rahima .

" Rahima wannan ba hujja bace da zata hana auren Hamza da Aminatu , sai dai idan kin nuna min Aminatu ba ɗaya take da sauran 'ya'yan da na haifa da nake da ikon zaɓa musu abokan rayuwa ba, ko kuwa har yanzu baki huce daga abunda ya gabata ba shiyasa zaki gwada hakan ta hanyar hana wannan al'amarin tabbatuwa ko Rahima ?

Da taruwar hawaye a idanun ta muryar ta cike da tashin hankali , ta shiga girgiza kanta tana cewa " Haram ko kusa ba haka bane Yaya , dan Allah kar kace haka , a tun kafin bayyanata Aminatu da ƴar uwarta suna da wani majiɓanci da ya wuce ka tsawon wannan shekarun ? kayi haƙuri ba nufina ba kenan , ni shi nake...

"  idan ba haka bane to ki barni nayi abunda nake da manufar yi inshaAllah alheri ne a garemu baki ɗaya ,

Bai saurara ba ya juya ga Doctor hamza da zuwa lokacin gumi ke tsattsafo masa a goshi , da murya dake cike da gargaɗi Prof yace ,
   " Likita kai nake saurare kai kuma me kace ?

   Ɗago da kan sa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login