Showing 186001 words to 189000 words out of 411050 words

Chapter 63 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14335

mahaifin yaron anyi musu tsakani ba ,
    Faɗa take yiwa lubna tamkar zata doke ta , a karshe ta gargaɗe kan ko kusa ta da shi bata yadda ta sake tsayawa ba kuma zata faɗawa baban su ya sanar da mahaifin yaron su ja kunnen ɗan su , ya fitar harkar ƴar su ,

  Sororo ! Yakaka tayi cikin jin mamakin malama maryam menene abun tashin hankali haka ?
  Da son kwantar mata da hankali tace ,

   Anty ai hannun ta fa kawai ya riƙe , kuma fa cewa yayi ta taimaka masa ,

wani irin kallo malama maryam tayi mata ,

   Yakaka ,

Namiji baligi ya kama hannun mace baliga haramun ne a musulunci , muddin ba muharamman juna suke ba domin tafarki ne na samar da ZINA a tsakanin mace da namiji  ,

Zina kuma haramun ce a musulunci, kuma tana daga cikin manyan laifuka wanda ake kira Kaba'ir.
Allah ya fada cikin Qur'ani
و لا تقرب الزنى
Wato kada a kusanci zina.
Hikimar fadin hakan shine ba aikata zina kadai ba, aikata abunda zai janyo zinar irinsu rungumar juna , taɓe-taɓen juna da shafe-shafen jikin juna tsakanin namiji da mace dukkansu Allah yayi hani domin hanya ce ta kusanta kai ga zina ,

cikin sanyin murya yakaka tace

Anty menene ZINA  ??

Zina ita ce Saduwa a tsakanin namiji da mace ,( ina nufin mace da namiji su kasance cikin abun rufuwa ɗaya jikin su na cikin na juna , azzakarin namiji yana cikin farjin mace ) ba tare da hukuncin aure ya shiga tsakanin su ba , duk mace da namijin da suka yi tarayya irin haka ba tare da an ɗaura musu aure kamar yadda addinin musulunci ya koyar ba to babu shakka sun aikata zina ,

kamar yadda na faɗa miki ita zina tana cikin manyan laifukan da Allah yayi hani da su sannan kuma ya tanadi hukunci ga duk waɗanda suka aikata ta ,

Hukuncin Zina a shari'ance ,  ita zina ba'a tabbatar wa da mutum ita dole sai da hujjoji, hujjoji guda biyu ne ko dai mutum ya yarda da kanshi ya aikata , ko kuma mutane huɗu su ganshi turmi da taɓarya a wannan hali ne ake tabbatar da zina,

Amma ko mutune uku ne suka ce sun ganshi turmi da taɓarya sai ɗaya yace shi dai ya gansu a tube suna shafe shafe to baza a karbi shaidun su ba, za'ai musu bulalar ƙazafi tamanin tamanin ,


Amma idan shaidu sun kammala ko mutum ya amsa da bakin sa yayi zina Hukuncin sa a shari'ance shine bulala ɗari ga waɗanda basu taba aure ba. Kamar Yadda Allah ya faɗa"

الزانية والزانى فاجلدا كل واحد منهما مأة جلدة، ولا تأخذكم بهما رأفة فى دين الله إن كنتم تؤمنون بالله واليوم الآخر.
Wato mazinaci da mazinaciya ayi wa kowanne su bulala ɗari, kada tausayi ya kama masu dukan idan har sun kasance masu imani da Allah da ranar lahira.



Sai wanda yayi aure akwai hadisin da yace duk mai aure ko wanda ya taɓa aure idan ya taɓa zina za'a jefe shi, amma sai idan shine da kanshi yazo yace yayi zina yana so a jefe shi, amma idan bai yadda a jefe shi ba ba za'ayi mishi dole ba za'a barshi ne.

Wani irin tsoro da tashin hankali me tsanani ne ya dirar mata , cikin wata irin muryar da ke bayyana tsantsar firgicin da ruhin ta ke ciki , tace

   Anty ko da mutum taimako yayi ,

Malama maryam cikin tsanaki tace ban fahimce ki ba yakaka wanne irin taimako ne yake zuwa ta hanyar aikata zina ??

Anty ina nufin ko shi namijin cewa yayi mace ta taimaka masa , sai ita ma ta taimaka masa , suka yi , shikenan tayi zina ??

Su dukan su sun aikata zina , saboda babu biyayya ko temakekeniya tsakanin bayin Allah wajen saɓa masa , su dukkanin su basu da hujjar kare kan su , suyi gaggawar tuba ga ubangiji domin zina babbar musiba ce ,

Sannan kuma yakaka ai duk namijin da zai cewa mace ta taimaka masa ta bashi kan ta suyi zina , ai wannan babban maƙiyi ne a gare ta , bata da maƙiyi sama da shi , mugu ne kuma macuci domin na farko zai ɓata tsakanin ta da ubangiji , yasa ta aikata abunda Allah zai yi fushi da ita , da zai hana ta samun ganin Alkhairi da dacewa cikin rayuwar ta duniya da lahira har sai idan ta tuba ,

Na biyu duk ranar da mutane suka san me suke aikatawa, mutanen kirki zasu guje ta , za'a dunga mata kallon fasiƙa, mazinaciya ƴar iska , karuwa .

Na uku idan ta hanyar zina da suka aikata ta samu ciki ta haihu , abun da ta haifa idan ya girma shi ma da kan sa zai tsane ta , ƙimar ta zata zube a idanun abunda ta haifa , saboda ta zamto sanadin da mutane zasu dunga ƙyamatar sa da ganin sa wani mutum da aka samar da shi ta haramtatciyar hanya ,

Bayan haka illolin zina suna da yawa , daga ciki akwai ɗaukar munanan cututtuka da zasu iya kai me su ga mutuwa ,

A ƙarshe namijin da duk zai yi zina da mace abu ne me wuya ya aure ta , ko da ya aure ta kuma bazai taɓa ganin ƙimar ta da mutuncin ta ba , sannan ƙanƙanin kuskure zai iya haifar da zargi a tsakanin su da zai lalata musu aure ,

Kuma duk macen da tayi zina kafin tayi aure bata da wata martaba a idanun duk wani namijin da zai zo ya aure daga baya saboda ta rasa ƙima da mutuncin ta na ƴa mace tunda tayi zina .

Ki gujewa abunda duk zai kai ki ga aikata ZINA yakaka cikin ta akwai tarin masifu kin ji ko ??

Bata amsa ba illa miƙewar da tayi bata tsaya ba ta taka da gudun gaske tana barin gidan ba ta ko tsaya ta sanya takalman ta ba bare ta saurari ƙiran da malama maryam take mata ,

gudu take bata ko dub Inda take jefa ƙafar ta ,
   Da ƙarfi ta tura ƙofar ɗakin tana shiga ta zuɓe a tsakiyar ɗakin tana sakin wani irin kuka marar sauti da yake tuƙowa daga ƙasan ruhin ta ,

   Cikin wata irin murya ta fisgo kalmar ,

   ALLAH NA TUBA , NA TUBA ALLAH , BAZAN SAKE BA ,ALLAH NA TUBA KA YAFE MIN ,

  Kuka take tana maimaita kalmomin nan jikin ta har tsuma yake ,

Ashe haka ne girman laifin da ta aikata batare da ta sani ba ? Ashe ita ɗin me tarin zunubi ce ? Ashe baza ta samu wani alkhairi ba arayuwar ta tunda tayi zina ,

Ta jima a zaune a wajen tana kuka har duhun dare ya shigo , zuciyar ta ta tsorata iyaka , neman yadda zata yi Allah ya yafe mata take yi , sai dai bata san yadda zata yi Allah ya karbi tuban ta ba , ji take kamar zata mutu ,

Tashi ta sake yi tana gama hanya saboda kukan da ta ɗauki lokaci tana yi yasa kan ta sarawa tare da fara jin jiri ,

tana gama hanya ta fito , bata ko dubi ɗakin samy baɓy da kiɗa ke tasowa ta cikin sa alamun da ke nuna ta dawo gidan ba , ta sake fita ,

hanyar gidan malama maryam ta sake  ɗauka ,

  tana so ta san yadda zata yi Allah ya yafe mata , tana so ta san yadda zata yi ta gyara kuskuren ta ,

a falo ta tarar da malama maryam tare da iyalan ta suna cin abincin su na dare ,
   Babu sallama ta rakaɓe daga bakin ƙofar gami da sakin kuka me ciwo ,

hankali tashe malama maryam ta tsame hannun ta daga abincin da suke ci ta miƙe , ta zo ta kama yakaka ,
    Tambayar ta take lafiya ?meye ya same ta ? Ko wani abu ya samu antyn ta ? Daman yanzu take so idan ta gama cin abinci lubna ta raka ta gidan nasu ta duba ta domin ɗazu ta fita bata cikin nutsuwar ta yanzu kuma ta dawo tana kuka , shin menene yake damun ta ??  

   Cikin muryar ta da kuka ya fara disarwa , tace nayi ZINA malama maryam , ki taimake ni ki faɗa min yadda zan yi Allah ya yafe min , ban sani ba malama maryam wallahi ban sani ba ,

  Ta shi , ta shi mu shiga ɗaki ki nutsu ki min bayani yadda zan fahimce ki ,
   Ta kama hannun ta zuwa ɗaki ta zaunar ta bakin gado , ina sauraran ki me kike son faɗa min yakaka ?

Tiryan tiryan , yakaka ta fara bada labarin tun daga farkon haɗuwar ta da yarima har yanayin yadda abubuwa suka kasance har zuwa yadda alaƙar ta da samy baby da yadda ta yaudare ta ta zo da ita garin  abuja ta baro ɗanyar jaririyar ta tare da makauniyar ƙanwar ta,  bata idasa ba malama maryam ta katse ta ,

Kin yi kuskure yakaka , kin yi kuskure , kin yi kuskure ,! Kaicho  
    wani irin tausayi chakuɗe da bacin rai take ji cikin ran ta , tamkar wata makusanciya a gareta ce ta aikata abubuwan da yakaka ta aikata ,

tun farkon fara koyar da yarinyar ta fahimcin tana da raunin sani sosai da sosai game da addini , kusan ma bata san kome ba , shiyasa ta ɗaura aniyar ganin ta kawo sauyi ta fidda ta daga duhun jahilci , cikin rashin sanin ta ashe jahilci tare da rashin wayon yarinyar har ya kai haka ( Bata san menene zina ba ) ? Ta yadda aka yi amfani da jihilcin aka cutar da ita cuta mai tsanani irin haka ?

Kukan da yakaka take ya tsansnta ganin shirun malama falmata ya ɗau lokaci tare da bayyanuwar matsanancin tashin hankali bisa fuskar ta ,

  ALLAH zai yafe miki yakaka , muddin kika nemi yafiyar sa tare da niyyar baza ki sake komawa ga aikata saɓo irin wannan ba , ALLAH me yawan gafara ne ga bayin sa ,

Duk da cewa akwai bayanai daga malamai game da mutumin da ya aikata saɓon Allah alhalin bai san cewa sabon nan me girma bane da zai iya kai me shi ga shiga wuta ,ko kuwa bai ma san saɓo bane baki ɗaya, akwai hukunce hukunce , hukunci na farko shine , Shi JAHILCI ba'a uzuri da shi, sai dai cikin wannan hukuncin akwai bayanai da suke nuna akan karbi uzurin JAHILI , idan ya kasance gurin da ka tashi babu addini , babu malamai masu koyarwa ,ko kuwa an hana ka damar fita neman ilmin kuma ba'a koyar da kai ba a gida ,  to za'a iya yi maka uzuri da wannan , amma idan gurin da kake akwai addini akwai malumma , sai kaƙi fita ka nemi ilmi kasan hukunce hukuncen addini kayi zaman ka cikin jahilci to wannan baka da uzuri a addini , jahilcin ka ba uzuri bane ,

to amma idan ka rasa damar samun ilmi ne , akwai hadisin manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da yake cewa :
     Allah ya ƙetarar da Al'umma ta abu uku , ma'ana ya yi musu afuwa akan abu uku , na farko shine mutum yayi abu cikin rashin sani , na biyu mutumin da ya aikata wani kuskure akan mantuwa , sai na uku wanda aka tilasta ma sa aikata saɓo, !


To idan aka yi duba ga wannan hadisin za'a yiwa mutumin da duk ya aikata wani saɓo cikin rashin sani , uziri a sassauta masa , sannan shi kuma yayi tuba zuwa ga Allah , tsarkakaken tuba ,

Manzon Allah yana cewa : duk wanda yayi tuba na gaskiya to zai kasance kamar bai taɓa aikata wannan Zunubin ba , amma wanda yake tuba alhali yana komawa ga aikata zunubin sa to tamkar yana yiwa Allah izgili ne .

kiyi Tuba na gaskiya yakaka tare da niyyar baza ki sake kusanta kan ki ga aikata ZINA ba a rayuwar ki , Allah zai yafe miki ya wanke ki a idanun Al'umma domin Laifin shi kika yiwa ,

Sannan , ki tashi ki nemi ilmi ki kuma yi aiki da shi idan dama ta samu gare ki kome ƙanƙantar sa ki koyar da ilmin da yake gare ki domin sauran Al'umma su amfana ,

shiriya ta zo miki hasken ilmi ya zo miki ki sa hannu biyu ki karɓe su ƙwarai akwai falala tare da samun dacewa a cikin su , ki manta da rayuwar baya ki himmantu wajen neman gafarar ubangiji akan saɓon da kika wanzu kina aikatawa , da fatan kin fahimce ni ??

bata amsa ba illa hannu da ta kai ta rungume malama maryam , idanun ta na zubar ƙwallar da ita kaɗai ta san dalilin sauƙar su a daidai wannan lokacin

Godiya ta dunga jerowa malama maryam har lokacin da ta sanya ƙafar ta tana barin gidan lokacin dare ya fara shiga karfe goma saura ,

kan titi babu kowa garin ya sake ɗaukar sanyi , a hankali take tafe iska yana ɗaga hijabin ta , tayi zurfi cikin tunani , daki-daki take tuno kome da ya dunga faruwa a rayuwar su ita da ƙanwar ta ,

tana so ta zargi iyayen su akan killace su a gida da suka yi suka hana su neman ilmi , sai dai so irin na tsakanin ɗa da iyayen sa ya mata dabaibaiyi yaƙi bata dama , ji take suna da wata hujjar su , babu shakka akwai dalili ,

tunanin falmata da baby mama yayi mata dirar mikiya , wata irin kunyar falmata ta ji tana nuƙurƙusar ta , yaya zata Ji ranar da duk ta san irin kuskuren da tayi har ta samar da baby mama ta gudu ta bar mata ita ? Wataƙila daga ranar zata fara tsanar ta ,

tsoro take ji tsoron girma ya zowa baby mama ta samu sani akan irin ta hanyar da aka samar da ita , ? Me zata cewa waɗannan bayin Allah biyu ??

Lalle wajibi ne a gare ta ta nemi ilmin addini ko domin ta samun ƙarfin guiwar da zata iya fuskantar su tare da tarin hujjoji da bayanan da addinin ya tanadar domin ta gamsar da su ta kuma wanke kan ta a idanun su su san cewa ta aikata kome ne cikin DUHUN JAHILCI ,!

Ko zasu fahimce ta ? Ko falmata zata yadda ta cigaba da riƙe ta a matsayin ƴar uwa masoyiya ? Ko baby mama zata yadda da ita a matsayin uwa ?? Yaushe wannan ranar zata zo ? Zata zo nan kurkusa , ko sai bayan shuɗewar tsawon wani lokaci ? Abun da ta riga ta sani muddin su na raye wannan ranar zata zo ,

YARIMAN MARAƊI ,

Zuciyar ta ta auno mata da sunan sa da kome da ya wakana cikin rayuwar ta a wannan gaɓar shine sanadi ,

bata gan shi ko kusa tare da duhun jahilci makamancin nata ba , kome da shi yayi mata yayi ne cikin ilmin sa ,da sanin sa ya aikata Zina da ita ,

zuciyar ta take ji tana wani irin buɗawa da sabon yanayin da yake shigar ta akan sa da sabon matsayin da ya kamata ta ajiye shi tun farko a ran ta ,

Tunowa ta fara yi filla filla da farkon haɗuwar su har zuwa ranar ƙarshe da ya kore ta daga motar sa a tsakiyar titi  tana kuka , yayi tafiyar sa ya bar ta har yau bai sake waiwaiyar ta ba ,

tabbas shi macuci ne azzalumi agare ta bai chanchanta da samun soyayyar ta ba ko kaɗan ,

bai taɓa son ta ba , kawai amfani yayi da jahilcin ta ya ribaci gangar jikin ta ya yasar da ita tare da cikin da yayi mata , wani irin yanayi mai ƙarfi da kaifi ta ji yana keta zuciyar ta a game da shi , hannun ta ta kai ta tattaro bakin hijabin ta ta riƙe tare da cije gefen leɓen ta na ƙasa da ya zo daidai da zubowar hawayen ta da yake nuni da mummunan ƘULLACIN da tayi masa .... !!!!!!
[10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Fikrah writers association

MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )


umm'muaz


31





Ba ƙaramin kaɗuwa Youssouf ya yi ba lokacin da Maimartaba yake shaida masa zancen auren sa da Siyama , da har an riga an miƙa dukiyar auren ta ga mahaifin ta dake niamey , za'a yi ɗaurin auren sa da ƴan matan duk biyu a rana guda kamar yadda ya buƙata ,

Ya jima a zaune gaban Maimartaba yana jin yadda zuciyar sa take cunkushewa da tarin takaici ,

Ba tun yau ba ya gama lura da take-taken yarinyar , shi yasa sam baya sakar mata fuska ashe bai sani ba har tayi girman da zata iya yin tsaurin ido irin haka a matsayin ta na mace ta doshi iyayen sa da buƙatar son a haɗa su aure ? Babu shakka zata ɗanɗani kuɗar ta a hannun sa , sai tayi danasanin wannan mummunan shisshigi da tayi ta kutso kan ta cikin rayuwar sa da take a hargitse a halin yanzu ,

Ganin shirun sa ya tsawaita ba tare da ya amsa da amincewar auren ba , ya sa me maimartaba yin gyaran murya

  Da fatan ba zaka bijirewa oumarnin mu ba ? Bisa ga wannan haɗi da munka yi na amre tsakanin ka da ƴar ouwar ka , saboda ba muyi haka ba face sai da munka hango tarin alkhaire tare da dacewa sannan munka so ƙulla igiyar amre a tsakankanin ku , wannan ɗiya ɗiyar ƴar uwa ta ce , kai ma kuma ƴar ouwa take gare ka , ina yi maka oumarni ka karɓi amren nan da hannu biyu da ikon Allah gaba kai zaka yi farin ciki .

Kalmar 'Umarni, ta daƙile dukkanin wani yunƙuri da zai iya yi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login