Showing 390001 words to 393000 words out of 411050 words
Chapter 131 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ki na amre ki har mun ka haihu ? Ina son ki mana Siyama...
Zame hannun ta tayi tana girgiza kai lokaci guda tayi wani murmushi mai ciwo muryar ta da 'yar dariyar baƙin-ciki tace .
"Kar ka jefe ni da kalmomin aro domin shi kayan aro ai basshi rufe katarar mai su , wannan kalmar ta so ba tawa ce ba ban taɓa samun ta ba ga gurin ka kai tsaye sai ko dan alfarma bani son jin ta domin ba'a halicce ta a zuciyar ka a domin ni ba .
Saƙare yayi yana kallon ta wata irin kunyar ta ya ji a lokacin tana tasowa tana danne shi har yana jin kamar bai iya numfashi mai kyau .
Ganin yayi shiru ya sa ta miƙewa bayan ta kashe laptop ɗin ta ta tura gefe , wani irin ciwo zuciyar ta ke yi so take ta samu waje tayi kuka yadda ya kamata .
Sai dai kafin ta ɗaga ƙafa ta bar gurin ya jawo hannun ta da ƙarfi ta taho gaba ɗaya ta faɗa masa yayi mata kyakkyawar runguma a ƙirjin sa .
Kukan da yake cin ta a rai shi ta samu damar yi ta shiga rairawa har jikin ta na tsuma .
Biyamuradi Youssoufa ya kasa cewa kome illa rungume ta da yayi tsam yana jin yadda kukan ta ke ratsa jijiyoyin jikin sa suna tsinka masa gudun jini tare da ɗarsa masa wani irin yanayi mai kama da tsoro-tsoro a cikin ran sa "tsoro yake ji na ɗaukar hakkin ta , tsoro yake kar Allah ya kama shi da laifin rashin adalci a tsakanin Matayen sa .
Sai da tayi kukan ya ishe ta har ta fara lafawa dan kan ta sannan ya kai hannu a hankali ya riƙo hannun ta ya ɗora shi a saitin ƙirjin sa muryar sa can a ƙasan maƙoshi yace .
"Kin ga nan , kin ji yadda zuciyata ke tsanan ta bugu a halin yanzu ? Akan ki ne Siyama tuhuma ta take yi meyasa na ɓata miki Siyama ? Zuciyata na ganin GIRMAN ki ke ABAR GIRMAMAWA kike a gareni , ina jin Kunya idan na ga na ɓata miki Siyama a nan duniya cikin 'ya'ya mata wace ta samu ƙima da girman matsayi kwatankwacin naki a gurina Siyama ? Amsar ita ce babu.'
" Yakanar ki ta sayo miki mafi ɗaukakuwar daraja a gurina shin ba za kiyi alfahari da hakan ba ?
A hankali ta ɗago kan ta daga cikin ƙirjin sa tana jin yadda ruwan hawayen ta ke ƙafewa zuciyar ta ke tsantsamewa kunnuwan ta ke buɗewa .
Kallon da take masa kallo ne na irin " sake faɗa na ji ? Da gaske kake ?
Da hannunwan sa biyu ya riƙo fuskar ta yana jin yanayin da yake ji a game da ita na sake ninkuwa har yana neman fin ƙarfin sa so yake kawai ta yarda da abunda yake faɗa mata .
"Siyama zuciya ta na girmamaki gangar jikina kuma na buƙatar ki ke ɗaya ce ke da wannan matsayin a guri na da alƙawari na miki watta ba zata samu gurbi ya irin na ki ba , watta ba zata ɗau wannan matsayin ba ki yarda da ni .
Ɗan bakin ta da ya faɗaɗa da murmushi yake motsawa da son cewa wani abu shi ya rufe domin a lokacin baya buƙatar tace wani abu .
"So , ƙauna , haƙuri , Yakana da kawaicin da ta kwashi shekaru tana gwada masa sun riga sun masa gamsarwar da bai buƙatar ta sake furta kowacce kalma a gare shi a domin wai ta maida masa martanin kalmomin sa lokaci ne yanzu yayi da ita ma zai kyautata mata gwargawdon girman da zuciyar sa ke bata .
"Ta gaza tantance a halin da take ciki tsawon lokaci ji take kamar mafarki take za ta farka , kalmar girma ta mata nawi wajen ɗauka kamar yadda zuciyar ta ta gaza wajen jurar irin farin-cikin da take ciki wanda da ɗai a rayuwa bata taɓa samun makamancin sa ba dan haka ta dunga maida masa martanin Soyayyar da yake gwada mata cikin nishaɗi da basu taɓa samun makamancin sa ba a duk zaman auren su .
"Shin me ya kai hakan martaba a ce Mijin ka wanda Allah ya umarta da ka girmama shi , da bakin sa yace shi ke girmama ka ?
"Ashe ba soyayya ce kaɗai abun nema a wajen Miji ba akwai abunda yafi soyayyar girma da martaba .
"Babu shakka daga yau za ta iya tutiya da matsayin da Mijinta ya ɗora ta akai matsayin da bata taɓa tarayya da wata akan sa ba nata ne mallakin ta ita kaɗai .
"Ina ma da mata zasu fahimci hakan a duk lokacin da hagu ta ƙi su a gurin Miji suyi amfani da Dama su samarwa da kan su ramin kan su ba tare da sun nace da suyi kafaɗa da kishiya ta fanni ɗaya ba.? Da kuwa gidaje da yawa an zauna lafiya a tsakanin kishiyoyi .
Siyama ke ayyana hakan a cikin ran ta bayan bacci ya ɗauke Biyamuradi Youssouf da ita kuma zallar farin cikin da take ciki a yau shi ya hana ta bacci .
A karo na biyu ta ɗaga kan ta duk da cewa da duhu a ɗakin so take ta sake ganin hasken fuskar sa ko da sau ɗaya ne kafin bacci ya ɗauke ta .
A daren yau son da take masa ya sake ninkuwa ne akan na daa har tana jin kamar ba zata iya ɗauka ba .
Cikin bacci ya mayar da kan ta jikin sa ya kwantar tare da sumbatar goshin ta kafin ya cigaba da baccin sa cikin nutsuwa .
Ɗan murmushi tayi ta sumbanci ƙirjin sa kafin ta rufe ido baccin da yafi daɗi da kan sa daɗi ya ɗauke ta.
****
Abuja
Cikin satika ukun da suka biyo bayan barin Sofi Gidan Doctor Hamza wata irin Soyayya mai daɗi da shaƙuwa mai girma ne ya ƙullu tsakanin ma'auratan biyu Doctor Hamza da Yakaka .
Musamman da ya kasance daman 'yan uwan juna ne dan haka sai aka yi dace wasu daga cikin halayen su suka zo ɗaya kamar yanayin buƙatuwar halittar su da matsananciyar tsaftar su , yawan ibadar su , da rashin son hayaniyar su dan a wasu lokutan ma shiru gidan yake ɗauka suna gudanar da soyayyar su a aikace ko kaɗan basa gajiya da junan su kusan koyaushe cikin ƙoƙarin farantawa juna suke muddin dai suna tare .
A satika ukun har wata 'yar sirantatciyar ƙiba Yakaka tayi ta sake fari tayi fes da ita , yawan gyaran da take yiwa fatar ta kamar yadda Amnee ta koya mata bayan ta haɗo ta da kayan gyaran yasa kullum jikin ta kamar bayan ƙwai luwai-luwai .
Ga ƙamshi na musamman da ya zauna mata saboda turara da take yi gaba ɗayan jikin ta da hakan shi yafi kome sa Doctor Hamza ya liƙe mata kasantuwar sa ma'abocin son kamshi.
Ga girki da kullum take yi musu masu gamsarwa da ƙara lafiyar jiki saboda har ajin koyan girki ta shiga a whtsapp na musamman da shahararriyar ƙwararriyar mai koyar da girke-girken nan kuma Marubuciya Maryam Talba ta bude take kuma jagorar azuzuwan musamman domin koyar da mata girke-girke masu gamsar da Maigida,
Tare da goyon bayan Doctor Hamza da shi ma yake jin daɗin girkin ta dan haka ya amince ta faɗa ajin Koyan girki Na chef Maryam Talba
(wacce duk take da ra'ayin shiga ajin girkin Chef Maryam Talba duba da cewa Azumi ya gabato Uwargida kina bukatar sabbin darasi kan girke-girke domin gamsar da Maigida da iyalan ki , to kar ki ji kome yi maza ki min direct message insha Allah zan sada ki da Chef din da na san sai kin min godiya a gaba sannan babban abun farin-cikin da za ki tadda shine a kudi mai rahusa za ki fada ajin 👌sai kun zo👍)
*****
Yau ta wayi gari cike da burin gwada wani daddaɗan girkin da a jiya Chef Maryam ta gwada musu da yayi matuƙar burge ta .
Kamar yadda Chef Maryam ta kware a girke-girken mu na nan gida Nigeria har da na ƙetere ma ba'a bar ta a baya ba ta ƙware a girkin larabawa dan haka yau Yakaka tayi aniyar gwada dafuwar Maqluba wadda dafuwar shinkafa ce da kaza, dankali, ganyayyaki haɗi da sauran sinadaran girki .
Maqluba girki ne na mutanan gabas ta tsakiya wanda yake da matuƙar daɗi .
Cike da nishaɗi take aikin ta tana yi tana bin ƙira'ar Alkur'ani da ta sa a wayar ta.
Kafin ya bayyana ƙamshin sa ya sanar mata da wanzuwar sa a gurin zuwa lokacin da ya shigo kitchen ɗin ta ɗago kan ta a hankali tana jifan sa da wani tsadaddan murmushi .
"Habibi barka da tashi , gaskiya ka sha bacci.
Ta furta hakan ba tare da ta janye murmushin ta ba
Ƙarasowa yayi ya rungume ta ta baya yana ɗora kan sa a kafaɗar ta yace .
"Wafaa kin saɓa doka ta meyasa ?
Wara ido tayi tana ƙoƙarin juyowa ya hana ta a hankali ta ce
"Kayi haƙuri cikin rashin sani ne.
"Ba laifi kika yi ba Wafaa , amma ban ji daɗi ba da kika manta cewa na hana ki kiyi aiki ke kaɗai idan har ina gida ko da bacci nake ki dunga tashina muna yi tare .
Murmushi mai bayyana haƙora tayi ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya lokacin da ta kashe gas saboda girkin ta ya kammala .
Tana ƙoƙarin juyowa ya sassauta riƙon da ya mata ta juyo tana fuskantar sa.
"Hannun ta ɗaya ta ɗora a ƙirjin sa tana ɗan bubbugawa a shagwaɓe tace "wallahi har hankali na ya tashi ko wani laifin na yi ban sani ba.
Dariya yayi yana riƙe hannun ta yace "laifi kika yi mana meyasa za ki wahalar min da ruhina da kika san koyaushe yana nan ne a tare da ke , meyasa baki tada gangar jikin ba ? Anyi aikin tare da shi ?
Murmushi tayi tana kallon sa irin waɗannan kalaman nasa su suka ta dilmiye a cikin ƙaunar sa ba tare da ta ankara ba ko kaɗan baya mata ƙouron kalaman sa na soyayya kamar yadda baya ƙasa a guiwa wajen gwada mata ƙauna a zahiri bai kuma jinkirtawa wajen yaba mata a duk lokacin da tayi wani abun a yaba kome ƙanƙantar sa kuwa '
Maza irin sa sukan sauya akalar zuciyar kowacce mace cikin sauƙi .
Sauƙe idanun ta tayi ƙasa tana murmushi saboda wani irin narkakken kallo da yake mata , ita irin salon Soyayyar sa nawi take mata kunya take sa ta har ta dunga jin wani yarrr a jikin ta.
Ko kaɗan bata iya masa martanin kalaman sa , kuma bata jin daɗin hakan so take ita ma ta koya su dunga musayar ƙauna kamar abun zai fi armashi .
Sautin dariyar sa ta ji da yasa ta ɗago kanta da sauri tana kallon sa sai ta ga idanun sa bayan ta yake kallo .
Juya ta yayi yana mata nuni da wasu tattabaru Mata da Miji (aure ) , da suka sauƙa ta gaban tagar kitchen ɗin suna soyayyar su .
"Wow look at them Wafaa so lovely.
Ya furta hakan muryar sa kasa-kasa yana rungumeta ta baya.
Zuba musu ido tayi tana kallon yadda suke sumbatar junan su kamar sa cinye bakin juna, sun matukar birgeta tsuntsaye kenan ma suke wannan soyayyar ? Ba shakka soyayya aba ce mai daɗi.
Daga shi har ita shagala suka yi da kallon soyayyar tattabarun mai ban mamaki da Sanya sha'awa tare da nishadi a zuciyar ma'abota soyayya.
Basu Ankara ba Matar ta gayyaci Mijin dan Su cimma maƙurar soyayyar Su ganin haka yasa da sauri Yakaka ta ɗaga tafukan ta biyu tana rufe fuskar ta .
"Habibi mu bar su hakan nan zasu yi sirrin Su.
Ta furta hakan tana ƙoƙarin janye jiki daga wajen .
'Yar dariya Doctor Hamza yayi yana sauƙe mata hannun ta da ta rufe fuskarta da shi
Cike da zolaya a muryar sa yace "ki buɗe ido ki kalle su darasi za mu ɗauka mu ma anjima sai mu gwada.
tana buɗe idanun ta ta gan su a halin da ita bata so da sauri ta sake rufe ido ta juya tana shigar da kan ta kirjin sa har a cikin ranta kunya ta ji .
Rungume ta yayi yana dariya ƙasa-ƙasa kunyar ta na ɗaya daga cikin abunda yasa yake ƙara son ta ,kunya alamun imani ce bayan haka tamkar ado take ga ma'abota ita.
Ƙiran wayar sa da aka yi shi ya katse shirun nasu ya sassauta riƙon da yayi mata kafin ya zaro wayar sa daga aljihu.
Cikin ransa cike da addu'ar Allah yasa ba ɗaya daga cikin waɗan da yake zato bane .
Addu'ar sa kuwa bata karɓu ba domin kamar yadda ya zata dai Baba Prof ne da kan sa yake ƙiran sa.
Cike da ladabi ya ɗaga kiran suka gaisa kafin ya tsinkayi Baa yana masa maganar da yake gujewa tsawon sati guda .
"Hamza ka kuwa je kun taho da iyalin taka ?
Shiru yayi saboda ya san kawai ya tambaye shi ne ba wai dan bai san cewa bai je ba sai dan ya ba shi damar shigar da uzurin sa.
"Ban tafi ba Baa amma yau dai nake son na je Insha Allah .
"To ka daure dai ka je saboda kullum sai Mahaifiyar ta ta ƙirani bana son kayi wani abunda zai taɓa mana zumuncin mu na dai faɗa maka ina kuma sake maimaita ma shi aure daman haƙuri ke jagorantar sa sannan ba zaka gina gidan ka ba sai ka zama jajirtatcen Namiji tsayayye sannan gidan ka zai zama yadda ake so .
"Ina umartar ka da kaje anjima ka dawo da Matar ka ka kuma cigaba da haƙuri da su su duka biyun aure ibada ne .
"To Baa insha Allah zan je Allah ya ƙara girma.
"Madallah Allah ya muku Albarka baki ɗaya.
"Amin
Ya amsa yana sauƙe wayar ya kashe.
Ba sai ya faɗa mata ba daga cikin maganganun sa ta fahimci akan me ake zance da lokacin da ta fahimta ba ƙaramar juriya tayi ba wajen ɓoye razanar ta ta juya tana ƙoƙarin zuba musu abincin a farantin da ta ɗauko .
"Wafaa ya ƙira sunan .
"Na'am ta amsa tana ƙin kallon sa .
Ɗan jimm yayi yana juya zancen da yasan dole ya taɓa mata rai kafin ya tattaro juriyar sa yace .
"Baa da Amnee sun ce Sofi ta dawo , dan haka anjima zan je mu dawo tare.
Wata 'yar fara'ar da take tsakanin laɓɓa ta sakar masa da 'yar dariya tace "Yeehh Anty Sofi Oyo-yo gaskiya naji daɗi Yaya Dacta .
Matso ta yayi yana mata rumfa fuskar sa babu walwala yace "me kika ce ?
"Cewa nayi naji daɗi .
Ta sake faɗin hakan da siririyar murya ganin yadda ya haɗe fuska .
"Ba wannan ba da wanne suna na ji kin ƙirani yanzu ?
Dariya tayi tana tura shi baya ta ce "Anty zata dawo sunan ka na baya ma zai dawo..
Abincin da ta fara zubawa shi ya hana ya sake riƙe ta amma muryar sa bata ɓoye halin da zuciyar sa take ciki na rashin jin daɗi ba yace "Wafaa kar ki rage ko ɗigo na daga yadda muka saba al'amuran mu dan wai Sofi za ta dawo idan kika yi hakan za mu ɓata ni da ke , umarni ne wannan nake ba ki .
Bai sake cewa da ita ƙala ba ya fita daga kitchen. zuciyar ta taji ta ƙuntata "to ita meye laifin ta dan ta ce zata janye sunan da take ƙiran sa da shi a gaban matar sa ? Ita a ganin ta kiyayewa take son yi sanin da tayi Sofi tayi nisa a fagen kishi.
Hawayen da suka cika gurbin idanun ta ne suka zubo , wani irin tsoro take ji kan dawowar Sofi ko yaya zaman su zai sake kasancewa ?
Jikin ta duk a sanyaye ta gama zuba abincin ta ɗauko ta nufi falon , a kan kujera ta hango shi kafin ta ƙaraso ya taryo ta ya karɓe farantin hannun ta , sai ta koma kitchen ta ɗauko masu kayan sha da ta haɗa .
Ɗan shiru ya ratsa tsakani kafin lokacin da ta fara zuba musu haɗaɗɗiyar Maqluba da ƙamshin ta ya ɗau wajen ya tado wa da Doctor Hamza muguwar yunwar da yake ji .
"Wow what a delicious ? a complete meal containing, carbs, protein, fats, fibre, essential vitamins and minerals.
Da murmushi take kallon sa lokacin da ya kai loma ta farko ya haɗiye ya sake ɗiban wata yana lumshe ido ya cigaba da cewa .
"Wafaa do you know Basmati rice has higher fibre content and is a great option for various meal plans, prevents against Cancer cell formation and prevents constipation against heart health risk.?
Tana ɓoye dariyar ta ta ɗan girgiza masa kai alamun bata sani ba.
Kazar da ya ɗauka ya gutsira ita ya nufo bakin ta da sauran .
Noƙewa tayi tana dariya tace " ni fa ba kaza zan ci ba kawai shinkafar raina ke so.
Wara ido yayi yana mata kallon mamaki kafin yace "Come on ki ci kaza Wafaa chicken is a great source of lean protein and has abundance of selenium, phosphorus, niacin.
Haka ba dan ta so ba ta gutsiri kazar ta ci kafin ya cigaba da bata abincin Suna cikin ci tace "Habibi kai baka cin tumatir Sosai ni kuma shi nafi so ka dunga bani sosai.
Bayan ya haɗiye abincin bakin sa yace "eh kuma kina da gaskiya domin shi tomato is a great source of vitamin C, potassium, vitamin k1, folate which are great for normal tissue growth and cell function.
Dariyar da take ta riƙewa tuntuni ita ce ta kufce mata ta shiga ƙyalƙyalawa har tana kwanciya a jikin kujera , shiru yayi yana kallon ta da murmushi a laɓɓan sa daman burin sa kenan ya ga fara'ar ta farin-cikin sa yana tare da walwalar ta.
****
Kamar yadda Doctor Hamza ya alƙawarta A daren ranar bayan Sallar isha'i ya tafi gidan su Sofi domin su dawo tare lokacin da ya ɗora idanun akan ta sai da ya razana saboda ramar da yaga tayi cikin 'yan satika.
Yadda yake zaton za ta masa hauka sai ya ga akasin haka sai nan-nan take yi da shi daga ita har Mahaifiyar ta da hakan yasa dole shi ma ya sau jiki suka ɗan