Showing 270001 words to 273000 words out of 411050 words

Chapter 91 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14341

ji ?

Idanunta suna zubar hawaye ta riƙe hannun Yakaka , muryarta ɗauke da sautin kuka tace ,

" Mama bata da lafiya Yakaka , Tunda ta tashi tana da ciwo har turai mun je saboda lafiyar Mama amma ba'a dace ba , yanzu ma bata da lafiya zamu tafi da ita asibiti , ki mata addu'a Yakaka .

Wani irin tashin Hankali Yakaka ta shiga , zuciyarta na tsananta bugu tace ,

"Mama tana da ciwo tunda na haifeta ? Aina ciwon yake ?

" a cikin jinin ta , idan ciwon ya tashi tana shan wahala sosai Mama abun tausayi ce ,

Shiru Yakaka tayi cike da tausayin ɗiyar ta ,

A hankali tace" kije ki shirya ku tafi Falmata , Allah ya bata lafiya , Allah ya warkar da ita babu ciwon da bashi da Magani  ,

Miƙewa Falmata tayi ta fita zuwa ɗakinta , tana fita kukan ta ya sake dawowa sabo , can cikin ranta neman hanya take da zasu yi magana da Yakaka , so take ta tambayeta meyasa ta ji suna hayaniya da Baban Mama ? Ba tare da ta nuna mata ta san zancen da suka tattauna ba , a sanin ta Yakaka kaifi ɗaya ce wataƙila ta fayyace mata dalilinta ,

Sai dai rashin samun ƙafar maganar da Yakaka ya sa tayi shiru da tarin damuwarta da ciwon Mama ya zo ya ninka mata ,

Bayan fitar ta kukan da Yakaka take dannewa ya taho mata, nadama marar iyaka ta sake rufe ta ,

"Ashe Mama ba ma mai lafiya bace amma ta tsallake ta tafi ta barta ? Haka ta dunga rayuwa da ciwo tun tana jaririyar ta ? Babu tausayi da kulawarta a matsayinta na uwa a gareta ? Ita kuwa anya Mama zata yafe mata idan ta girma labari ya iske mata ? Alƙawartawa kanta take yi tana sake jaddadawa bazata sake yin nesa da ɗiyar ta ba kome runtsi .

Kasa zama a ɗakin tayi ta fito falon da babu kowa sai kwarafniyar Hajja daga cikin kitchen ,

Zama tayi akan kujera tayi jugum cikin allhini ,

A sukwane ya turo ƙofar ya shigo yana saɓe da Mama wacce tayi luruf , bai lura da Yakaka ba , ya ɗaga sauti dake bayyana tashin hankalin sa ,

"Fatima ki fito mu tai asibiti jikin Mama ya matsanta kada ta shiga hatsari ,

Miƙewa tsaye Yakaka tayi tashin hankali bayyane bisa fuskarta , jikinta har rawa yake ,

Yi tayi kamar zata taka taje inda suke sai kuma ta jaa ta tsaya , idanunta baki ɗaya akan Mama , ba ko dubi fuskar Youssouf ba ,

Muryar sa ya sa Hajja fitowa da take kitchen tana aiki , turus tayi tana raba ganinta tsakanin Yakaka da Youssouf ,

"Babban soja barka da asuba ,

"Barka Hajja yaya hidima ? Mama batta lafiya yanzou zamou tai da itta asibiti ,

Take fuskar Hajja ta sauya daga mamakin da take yi zuwa Alhini ,

"Allah sarki kai wannan yarinya kina shan wahala , sannu Mama Allah ya baki lafiya , Babban soja Allah shi baku ladan jinya da hidima da ita ,

"Amin Hajja ,Amin

Ya furta dai-dai fitowar Falmata cikin hanzari  , idanunta hawaye shar-shar suna zuba , da kyar take ganin gabanta ,

"Hajja ina kwana , tace cikin muryar kuka ,

Cike da tausayawa Hajja ta amsa ,

"Sannun Falmata bari kuka haka nan , Allah dai ya bawa Mama lafiya kin ji ? Ai ke kece uwar Mama duniya da lahira .

Tana ƙarasowa Youssouf ya riƙe hannunta suka kama hanyar barin Falon ,

Sai dai taku biyu suka yi , Falmata ta waiga ga Yakaka wacce take tsaye idanunta cike da ƙwallar son sanin halin da Mama take ciki ,

Inda take hango alamar Yakaka ta nufa , tana zuwa ta lalubo hannun ta ,

" zo muje asibitin tare Mamar Mama ,

Babu musu Yakaka ta biyo ta , ganin haka ya sa Youssouf nufar waje bai ce ƙala ba ,

" Hajja mun tafi ,

Yakaka tace ,

bata amsa ba har suka ƙarasa barin falon tana bin Yakaka da kallon mamaki , nisawa tayi bayan wucewar su ,
    "o ni Hauwa'u naga abunda yafi ƙarfina , ji bi dan Allah yadda ta bi su ƙobare-ƙobare babu ko 'yar kara ? Geme-geme da ita ta shiga tsakanin su ,   Da ta san tana son ƴar tayi tafiyarta dandi ta bar ta ?? Tawa ta sameni nikam sai nayi da gaske zan hana yin ɓatatciya a gidan nan ,

***

Dukkanin su biyu a baya suka zauna , yayin da suka shimfiɗar da Mama a tsakanin su , kanta yana a ƙirjin Falmata ta rungume ta , ƙafafuwanta kuma suna kan cinyar Yakaka , Youssouf shi ke jaan motar ,

Hawayen su duka biyun yana ɗiga akan Mama wacce zuwa lokacin bata a haiyyacin ta , kowaccen su tana tofa mata addu'o'in da ya sawwaƙa gareta ,

Da gaugawa Likitocin bada taimakon gaugawa na yara suka amshi Mama wacce ta riga ta suma a lokacin , suka rufu akanta suna ƙoƙarin ceto ranta ,

Bayan kuka da addu'a babu abunda Yakaka da Falmata suke yi , Youssouf kuwa ya kasa tsaye ya kasa zaune , idanunsa sun kaɗa sun yi jaa , bakinsa ya bushe ƙemas , sai kai kawo yake yi yana addu'a Allah ya dawo da lafiyar Mama ,

Suna nan cikin halin juyayi likita guda ya sanar da su an samu nasarar dawo da numfashin Mama da mummunar mura ta tokarewa kirji sakamakon kwayoyin cuta ,

Sai dai ana neman jini saboda ƙarancin na jikinta da shine musabbabin kawo hargitsin ciwon nata ,

duk da cewa ba wannan ne karo na farko na sanya mata jikin ba kamar koyaushe a yau ma sun shaida masa sun fi son wani cikin dangi ya bada jinin fiye da na saye da ake sawa ,

Shi jinin sa bai zo dai-dai da nata ba haka ma na Falmata tuntuni sun san haka ,

Bayan likitan ya bar wajen Falmata wacce ta ji duk abunda likitan ya faɗi da faransanci tace ,

" ko za'a nemo wani to wanda ya yarda zai bada jinin a gwada jinin ko Allah zai sa a dace ?

Yakaka wacce ta rafka tagumi kanta a sunkuye , jin haka sai ta ɗago kai ,

" muje a auna jini na ko zai zo ɗaya da nata ,

Kallonta Youssouf yayi kamar zai ce wani abu sai ya fasa ,

"tasso muje , yace ,

Da sauri Yakaka ta miƙe , kallon Falmata yayi ,

"Fatima yanzou zamou dawo kinji kou ?

A hankali ta gyaɗa kai ba tare da ta waiga sashin da yake ba.

Cikin sa'a da aka auna jinin Yakaka yazo dai-dai da na Mama jinin su B+ ne ,

A take aka yi duk wasu gwaje gwajen da suka dace zuwa lokacin da aka jaa jikin Yakaka leda guda ,

Bayan jiran tsawon awanni fiye da hudu ,zuwa ƙarfe biyu na rana aka ɗaurawa Mama jinin bayan an kaita ɗaki na musamman da suka saba zama muddin aka riƙeta a asibiti ,

Baki ɗayansu gajiya tare da damuwa sun bayyana a siffofinsu , tun safe babu wanda ya ci abin kirki a tsakanin su , duk kuwa da cewa Hajja ta kawo musu abincin kari  tare da kayan da zasu iya buƙata anan, kuma ta koma yin abincin dare ,

Ko maganar kirki basa tsawaita yi kowanne yana ji da damuwar sa da ta masa katutu ,

Da lallaɓa Falmata ta iya cin abincin kaɗan wanda Youssouf ne ya bata da kan shi , ba tare da ya lura da Yakaka ba , da ita ma baya ta basu tana zaune akan kujera daga gaban gadon ta riƙe hannun Mama da aka ɗaura mata jini .

Ba da son ranta ba ta ɗan ci dankalin da yake sanya mata a baki tare da ƙwai, sam bata so mu'amalar su ta tsawaita a gaban Yakaka da take iya hango bayanta ,

" Na ƙoshi .

Tace tana ture hannun sa da yake sake kawo mata dankalin ,

Shima bai ce ƙala ba ya janye farantin gefe , sai ta miƙa hannu ta ɗauka , ta cika shi da dankali da soyayyen ƙwai ta yunkura ta ɗauka , gaban gadon ta kai ta ja wata kujera ta ɗora akai ,

"Yakaka biri3 bui3 , ( Ki ci abinci )

Kallon abincin tayi , ko kusa bata jin yunwa , ganin irin yanayin da Mama take ciki ya tsinka mata zuciya , yasa zuciyarta tayi rauni , so da tausayin 'yar ta ya ci ƙarfin zuciyar , tsoron rasa ta kuma ya mamaye ta ,Sama-sama ta ci abincin .

Ƙarfe biyar da rabi Hajja ta kawo abincin dare sai ta ce , "Falmata da Youssouf su tafi gida saboda halin da itama Falmatan take ciki na buƙatar kulawa da samun isasshen hutu , 

"Ita da Yakaka kuma su zauna tare da Mama a asibitin har zuwa gobe ,

Shawarar ta yiwa Youssouf daɗi dan haka basu jinkirta ba yace su tafi gida , ganin jikin Mama da sauki kaɗan akan zuwan su,

likitoci sun ta kai kawo a kanta kuma babu laifi zazzaɓin ya sauƙa , cikin ne dai har kawo yanzu a kumbure ,

Falmata wacce da farko ta so tirjewa taƙi tafiya , sai da Yakaka tace mata ta tafi ta huta tunda ita ma Hajja tace bata da lafiya,

Sannan fuskarta babu walwala tayi musu Sallama idanunta na kan Mama ta bi bayan Youssof wanda tun bayan da ya matsa gaban gadon Mama ya yi mata addu'a tare da sumbatar goshinta ya shafa kanta yayi ficewar sa ya tsaya daga waje yana jiran fitowar ta ,

Bai ce kome ba ya riƙe hannunta suka tafi , ita ma har suka shiga mota bata ce masa ƙala ba sai tunanin zuci da take yi ,

Bayan fitar su Yakaka ta kai kallon ta ga Hajja ,

"Hajja meye yake damun Falmatan ita ma ? Naji kin ce bata da lafiya amma ita bata faɗa min ba , ?

Sasakai Hajja tayi tana kallon ta ,

"au sai ta faɗa miki tukun zaki gane ? Ji min rashin kan gado , yanzu ke Babba uwar Mama Allah baki Fahimci ƙanwar ki tana da yaron ciki ba ?

Dukkanin wata nutsuwar ta Yakaka ta  tattaro ta juyo sosai ta fuskanci Hajja , muryar ta a nutse tace ,

" Menene yaron ciki kuma ? Ki min bayani mai kyau ni Hausa ba yare na bane Hajja ,
 
Kallon gefen ido Hajja tayi mata , sannan tace ,

" Au haka fa , to abunda nake nufi shine ƙanwar ki tana ɗauke da juna biyu , ciki na haihuwar ɗan mutum , nan da wasu watanni idan Allah ya kaimu zaki sake samun wata ɗa ko 'ya , yanzu kin gane ko Babba uwar Mama ??

Tun da ta ambaci ciki a jikin Falmata , Yakaka ta daina Fahimtar a halin da take ciki dukannin sauran bayanan Hajja bata fahimce su ba ,

"  Ciki a jikin Falmata ?  Kuma Youssouf ne ya yi mata ?  A lokacin mantawa tayi da cewa aure ne ya gifta tsakanin su , tashin hankalin da take ciki ji take tamkar abunda ya faru ga rayuwarta ne ya afku ga Falmata ,

Wani irin Kuka ta fashe da shi ta haɗa kanta da ƙarfen gadon ,

Shin Youssouf wanne irin mutum ne haka Mai cike da zalinci da sharri ?

Bata san lokaci ya ƙure mata ba sai yanzu da tasan kome da take gudu ya faru , ƙanwarta kuma ta afkama tarkon Youssouf a karo na biyu , Youssouf yayi nasara akan ƙanwarta kamar yadda ya ci galaba akan ta ,

Kukan ta ya tsananta da yasa jikin Hajja yin laƙwas , karkata kai tayi tana ƙifta ido

" Ikon Allah Babbar uwar Mama menene abun kuka haka ga abunda yakamata ayi farin-ciki da Samuwar sa ? Ni har jikina yayi sanyi wai kaza ta taka wuƙa ,

Yakaka bata kula Hajja ba , hasalima hankalinta baki ɗaya baya jikinta , ya tafi tunanin neman mafita , ita yanzu yaya zata yi ? Wanne mataki ne yafi dacewa da ta ɗauka ?  Anya tana da mafita a yanzu ?

Ganin ta cigaba da kuka yasa Hajja yin shiru , hasashe take akan dalilin kukan Yakaka daga jin labarin cikin Falmata , to ko dai kishi take ??

***

Duk yadda Youssouf  ya so ya samu Falmata ta kula shi su yi ko ƴar maganar kirki ne taƙi ,

Tunda suka zo wanka tayi ta shige ɗakinta ta rufe ta kwanta , sai dai duk yadda ta so ya ƙyaleta ta kwana a sashinta ƙi yayi a ƙarshe ma hankalin sa ne ya tashi ya fara tambayar dalilin sauyawar ta ? Cike da fargabar ko dai Yakaka ta mata wani zance ne

Amma tace masa babu kome kawai rashin lafiyar Mama ke damunta , nan ya lallaɓata suka tafi sashin sa ,

A nan ɗin ma zama suka yi babu wata  hirar kirki , shima da ƙarin damuwar sa da ƙira yake ta shigowa wayar sa daga Matansa waɗanda suke zuba idon ganin sa tun jiya ,

ya rasa kuma takamai-mai uzurin da zai basu kome ya kufce masa sau biyu yana ɗaga ƙiran su a mabanbantan lokuta yana cewa "yana uzuri ne zai ƙira daga baya ,"

Daga Maimounatu har Siyama sun gaza gane kan mijin nasu tun gabannin tafiyarsa turai , ga shi ya dawo ɗin ma ya zo su gan shi abu ya ta'azzara , ga shi sun gama yin duk wani shiri na tarɓar sa ,

Musamman Siyama da kewar sa ke walagigi da ita , tun tana daurewa har ta kai yanzu kowa ya ganta zai iya fahimtar damuwar da take tare da ita ," duk tsoronta kar wata ce ta ɗauke masu hankalin miji , 

***

Ƙiran Tafeeda ya sake shigowa karo na biyar a yau ,

Yana kallon wayar ta gama ƙara , kiran na katsewa ya ɗau wayar ya kashe , ya miƙe tare da kashe wutar ɗakin ya zo ya kwanta daga bayanta yayi rigin-gine .

Falmata wacce duk tana jin ƙiransa da ake yana ƙin ɗauka , ta kuma fahimci wata sabuwar damuwar da shima yake ciki ,

sai ta ji tausayin sa ya kamata , ko babu kome a gurinta shi mutumin kirki ne , managarci Mai kyaun hali da kyakkyawar zuciya ,  sai ta juyo a hankali ta ɗaura kanta akan ƙirjinsa ta rungume shi da hannun ta guda, tana jin lokacin da yayi ajiyar zuciya mai ƙarfi .

Cikin dare bacci ya ƙauracewa idanun Youssouf tunaninnika sun masa yawa , yana son ya san halin da Mama ke ciki yasan kashe wayar da yayi ma a halin yanzu kuskurene tunda yana da marar lafiya a asibiti ,

Dan haka ya miƙe zaune ya ɗau wayarsa tare da kunna ta , kan layin Hajja ya danna ƙira yana kallon agogo wayar da ya gwada masa ƙarfe ɗaya saura mintuna biyar ,

Yasan cewa dare yayi sosai amma ya zama dole ya san halin da ɗiyar sa ke ciki tun bayan barin su wajen ta , da kuma yadda zata kwana ,

A can wayar ta ɗau ƙara , yaji alamun shigar ƙiran ,

Muryar da ta doki kunnuwan sa ya sanya shi miƙewa tsaye , yayi taku kaɗan , yana waiwayen Falmata ,

" Mai wayar tana bacci ,

   cewar Yakaka da ita ta ɗau wayar Hajja saboda ƙarar wayar kar ya tayar da Mama da ta samu bacci da kyar bayan kukan ciwo da take yi , tare da rikicin neman Iyayenta .

  " Yaya jikin Mama ?

Yace , yana fitowa daga ɗakin zuwa falo domin kada ya tayar da Falmata daga bacci ,

Miƙewa tayi daga kujerar da take kai , tana jin tsanar sa na sake bijiro mata da jin sautin muryar sa  ,

" Youssouf
    Ta ƙira shi , bata sauƙe mumfashi ba ta ɗora da cewa , "ina batun mu ? Kar ka manta da abunda na faɗa maka muddin kana son cigaba da ganin farin-cikin iyayen ka sannan....

Katse ta yayi ,

" yaya jikin ɗiya ta nake tambayar ki ? Ke baki da tounani ne ? Baki ganin halin da Mama take ciki ? Ba yanzou bane lokacin yin wannan maganar kiyi hakuri don Allah .

" Yanzou ki tada Hajja daga barci ki bata wayar zan tambaye ta kan lafiyar  ɗiya ta ,

Ƙit !

Yakaka ta kashe wayar har ita yake ƙira marar tunani ? Akwai marar tunani da ya wuce shi ? Duk sanadin waye suke cikin halin da suke ciki a yanzu ? Da bata haɗu da shi ba zata haifi Mama ne ? Ko kuwa yana nufin shi da ya gudu ya barta da cikin Mama ya fita ƙaunar Mama ɗin ne ? Yana da sani ne ko kaɗan akan irin wahalar da ta shiga na kwana a rumfar kasuwa tare da cikin Mama a jikinta ?

Guntun tsaki tayi tana komawa ta zauna a kujerar da ta tashi ,

  ta shafa kan Mama wacce take baccin zoma tana ɗan nishi kaɗan-kaɗan , duk da cewa an ƙara mata jini leda guda amma har yanzu ƙafa da hannunta fari sol alamun rashin jini

tausayinta yana sake kama ta , ko runtse bata runtsa ba , tun lokacin da Hajja ta faɗa mata cikin jikin Falmata damuwarta ta sake ninkuwa ,

Duk dogon nazarin nema mafita da tayi hankalinta yaƙi amincewa da ta ƙyale Youssouf ya cigaba da zama da ƙanwar ta ta gwammace ya saki Falmata su koma Nigeria tayi rainon cikin ta haihu idan yaso su ɗauko abunda aka haifa a kaiwa iyayensa tunda shi da Falmata aure suka yi ,

Dole iyayensa zasu riƙe abunda ta haifa , ita kuwa Mama 'ƴar ta ce da suka haifa ba tare da aure ba ta san iyayensa baza su riƙe Mama ba , Mama zata kasance tare da ita .

**

Youssouf ya ji yadda ta katse ƙiran ba tare da ta bashi amsar da yake son ji ba , sauƙe wayar yayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login