Showing 267001 words to 270000 words out of 411050 words

Chapter 90 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

19991

zan iya haɗiye ki ma baki ɗaya da na haɗiye ki Fatima , da kuma hakan shine kaɗai zai fiddani daga zullumi

Bata ce kome ba sai murmushi kaɗan da tayi , cikin ran ta tana aiyana , "ina ma da zata iya shigewa cikin jikinsa ta fake wataƙila da rabuwar su baza ta kasance ba ,

Cigaba tayi da ciyar da shi abincin , kafin ta ji ya riƙe hannun ta ,

"na ƙoshi Fatima , buɗe bakin ki na baku ke da Baby ,

Bata musa ba ta buɗe baki ya shiga ciyar da ita , ita ma kaɗan ta ci tace ta ƙoshi ,

"kaɗan kika ci Fatima , ki ƙara saboda Baby ,,

"Na ƙoshi , ai kaima kaɗan ka ci ,

Bai ce kome ba , sai jawo ta da yayi jikinsa ya haɗe ta da ƙirjinsa tsam-tsam ,

Cikin kunnen ta yace

" ina sonki Fatima Zahra ,

Lumshe idanun ta tayi , wasu siraran hawayen da bata san dalilin sauƙar su takamaimai ba suka silmiyo suka sauƙa a fatar ƙirjinsa , runtse ido yayi yana jin tausayin ta mai tarin yawa yana mamayarsa a wajen sa babu abar tausayi sama da ita ,

Sun ɗan yi mintoci kaɗan a haka kafin ya zare ta daga jikin sa , "Fatima , magarib tayi muyi Sallah ,

****

Bayan sun idar da Sallah sun yi addu'o'i shiru ne ya ratsa tsakani kafin Falmata tace

" ina so na shiga wajen Yakaka ,

Shiru Youssouf ya yi bai ce ƙala ba , saboda har ga Allah bai son su dunga kaɗaicewa saboda bai san da wacce manufa Yakaka take tafe ba , sai dai koma menene yana fatan kar Allah ya bata damar fayyacewa Fatima kome .

Jin yayi shiru ya sa Falmata sake cewa

"zance wajen Yakaka muyi hira kaɗan , ga shi Mama ma tana ta bacci ba abun na tayar da ita ba ta je Maman ta ta gan ta ,

"ki rabu da ita , mu je na raki ki kiyi mousu sallama ki dawo nan ki kwanta ki huta , gobe kun yi hira ,

Youssouf yace haka yana kama hannun Falmata cikin zuciyar sa dan babu yadda zai yi ne , da ba zai bari ta fita ba ,

Tare suka shiga har falon , basa nan dan haka Falmata ta ƙarasa ƙofar ɗakin Hajja , shi kuma ya dakata daga tsakiyar Falon ,

Ƙwanƙwasa ƙofar tayi ,

"Yakaka , na dawo .

Zuruf Hajja ta miƙe daga kishingiɗar da tayi tana jaan chasbaha , ta buɗo kofar tare da leƙowa ,

"uwarɗakina ai Yayar ki tayi bacci tuni , ki koma kiyi kwanciyar ki ki huta kun haɗu gobe da safe ko kuwa ,

Murmushi tayi , "kai Yakaka har tayi bacci ikon Allah ,

Ɗan jim tayi sai kuma ta sake cewa ," Hajja to ko cikin dare idan ta farka ki faɗa mata na zo muyi hira tana bacci , ai ta ci abinci ko ?

"ta ci abinci sosai ta cika cikinta dam ,

"to Hajja sai da safe ,

" yauwa uwarɗakina maza a je ayi bauta a huta ,

Har ta juya sai kuma ta sake dawowa ,

"amma , un, un Hajja nace da dai kin taso ta ta koma ɗakina , ina da filo mai laushi irin wanda take so , Yakaka bata son filo mai tauri irin naki Hajja ,

Wani kallon yatsu-tsu Hajja tayi mata ,

"aifa Lalle , ita Yakaka jaririya ce kenan ?  To ai wannan surutun da kike ba kai ba ƙafafu ya isa ya tayar miki da ita daga baccin da na lallaɓata da kyar take yin sa , ni wuce Dan Allah ki tafi Allah ya tashe mu lafiya ,

Ƴar dariya Falmata tayi jin yadda Hajja take yi mata shaguɓe akan Yakaka , juyawa tayi ta kama hanya cikin ranta ba haka ta so ba , so tayi su raba dare suna hira da Yakaka , bata so Yakaka ta ga kamar ta kyale ta ta maƙalewa mijin da bata da tabbacin cigaban zaman su ,

Youssouf da sauri ya taryeta a cikin ransa yana hamdala da rashin ganawar su ,

Hajja tana komawa ɗaki ta dubi Yakaka da take zaune akan sallaya riƙe da Alkur'ani tana karatun ta hankali kwance , duk zantukan Falmata a kunnen ta , tausayi gami da ƙaunar 'yar uwar ta suna bin jinin jikinta da gudu ,

Hajja ta mokaɗe baki , lokacin da take komawa ta zauna a wajen da ta tashi ,

"ai a wani ƙaulin irin wannan ƙaryar tana iya zama makaruhi , ko kuwa ba haka ba Babba uwar Mama ?

Yakaka bata kulata ba ta cigaba da karatun ta , can ƙasan ranta diramar Hajja ta fara bata dariya , 

**

Youssouf , Yakaka , da Falmata kusan kowannen su raba dare yayi bai yi bacci ba musamman Youssouf da ƙiran sallan farko na ƙarfe uku da rabi a kunnuwan sa a hankali ya zame Falmata daga jikinsa wacce itama bata jima da samun bacci ba , ya miƙe tare da shiga banɗaki ya ɗora Alwala , jallabiya ya zira yazo ya tada sallah

Nafila yayi tayi har zuwa lokacin da masallatan unguwar suka sa Assalatu , sai ya sallame ya miƙe ya ɗau turare ya fesa tare da ɗaura agogon sa ,

Fita yayi ya nufi masallaci , bayan ya ja ƙofofin gidan gabaɗaya ,

Yana bada baya , mutumin da yake maƙale da jikin katangar , ya siɗaɗa kansa tsaye ya shiga gidan ,

Yakaka wacce ta shiga banɗaki domin ɗaura Alwala sallah ta ga inuwar mutum ya gifta ,

Tsam tayi tana tunanin waye ?

Haka kawai ta ji zuciyarta ta tsinke , sai ta juya da sauri ta fito , sannu-sannu take tafiya , hasken lantarki ya game ko'ina , gabaɗaya unguwar ƙiran sallah ne ta ko'ina ,

Mutum ta gani a tsaye ya bada baya yana nufar ƙofar falon Youssouf ,

"Waye ne ta ce

Idanunta ƙyar akansa ,

Chak aka tsaya ba tare da an jiyo ba ,

Matsawa tayi ta sake cewa waye ne nace ?

Ba'a amsa ba ,

Taku ta fara yi tana kusantar sa , ta zo kusa da shi bata ankara ba ta ji an kifa mata marin da ya gigitata ,

Tayi taga-taga tana jin wani tsuu a kunnuwanta saboda ƙarfin marin , ta ji takun gudunsa sai dai ta kasa watsakewa daga zafin marin da yayi mata dan haka bata yi wani yunƙuri ba ,

Lokacin da ta watsake babu kowa a wajen ,lokacin an idar da sallah gari har ya ɗan yi shaa ,

Yawatawa ta fara yi a wajen tana raba ido ko Allah zai sa ta ga azzalumin da ya mare ta haka ?

Ƙarar buɗe ƙofar gidan ya sa ta juyowa a tsorace , wanda ta hango ya shigo ya sa zuciyarta bugun uku-uku ,

Da sauri ta gyara zaman hijabinta , ta fara tattaro duk wata dauriya da ƙarfin halin da take da shi ta kuma shiga harhaɗa manyan kalmomi masu kaushi da take son yin amfani da su domin su taya ta tunkarar sa ,

Tirus , Youssouf yayi yana hangota , sarai ya gane ta , wani ɗan guntun yawu ya haɗiye lokacin da tunaninsa ya gama ba shi dalilin tsayuwar ta anan ,

Gyagijewa yayi a matsayin sa na soja bai kamata ya tsorata har haka ba .

Kai tsaye ya nufi ƙofar falonsa yana yin kamar ma bai san tana wajen ba ,

bai ƙarasa ba ya ji tashin muryarta ta ƙira cikakken sunan sa ,

" Youssouf Abdul-Aziz Baskore ,

Sai ya juyo a hankali ya fuskantota da takunsa mai girma , fuskar sa babu alamun ɗaukar wargi ,

"Gani

Yace da ita muryar sa a kwance tamkar fuskar sa ba a murtuke take ba ,

Cikin zallar ɓacin ran da yake tunkuɗo kansa daga ƙasan ranta da ta wanzu tana ɗauke da shi tsawon shekaru , ta ƙaraso daf da shi da taimakon hasken Alfijir da ya ƙeto ya dusashe hasken lantarkin wajen suke iya kallon fuskokin juna ,

" Nasan baka san wannan ranar zata zo ba , baka san cewa zan dawo ba , shiyasa har ka samu damar kutsawa cikin rayuwar ƙanwata,  ka cuceni ka yaudareni , ka ɓata min rayuwa , ka lalatamin Asalin 'yata , ka sa rayuwata ta shiga garari  kuma ka zo kana sake cutar min da ƙanwata , a karo na biyu kana sake gurɓata mata rayuwa , Allah zai saka mana abunda kayi mana , kai wanne irin marar imani ne macuci Azzalumi , Mayaudari kuma fasiƙi mazin ....

" KI MIN SHIRU .

Baisan lokacin da ya daka mata tsawa ba saboda kalamanta da yaji suna tayar masa da hankali , take jijiyoyin kansa suka fito ruɗu-ruɗu , idanunsa suka sauya launi , jikinsa har tsuma yake yi , irin tashin hankalin da yake ji , da akwai bindiga a hannunsa zai iya kai harbi .

Tsawar da yayi ita ta farkar da Falmata wacce taji tashin muryar sa a tsawace , shafa ɓangaren da yake tayi ta ji baya nan ,

Sassauta murya Youssouf yayi yana kallon Yakaka da take masa kallon sheƙeƙe kallon tsana kallon baka isa ba , , zata yi magana ya sake katse ta ,

"Nace kiyi shiru ,

zuciyar sa ya ji tana kai kawo wajen tuno masa da girman kuskuren sa , girman laifin da ya yiwa Yakaka , sai ya shiga ƙoƙarin sassauta fushin sa tabbas kome Yakaka zata faɗa masa ya cancanta  , shi ɗin ai ya cutar da its dayawa kamar yadda tace ,

"ki yiwa Allah kiyi haƙuri , kiyi shiru mu bar kome a tsakanin mu ko dan saboda Albarkacin Fatima da Mama , ki faɗa min duk abunda kike buƙatar nayi miki zan yi ,

Ya furta hakan muryar sa a ƙasa yana satar kallon ƙofar falonsa,

Cikin rashin sanin sa Falmatan tana tsaye daga jikin ƙofar ta bayan labule kalmomin sa na ƙarshe kuma sun cigaba da sauƙa a kunnuwanta tarwai .

"Abunda nake so shine kawai ka sakar min ƙanwata , ka sake ta Youssouf ka kuma bani 'yata , Falmata baza ta taɓa cigaba da zama matarka ba muddin ina raye , ka auri Falmata Alhlin babu sanina ba kuma tare da amincewar wani nata ba , ya zama dole ka saki Falmata , ka sake ta nace .

Ganin yadda ta birkice masa tana ɗaga sauti tamkar bata cikin hayyacin ta yasa Youssouf ruɗewa yana gudun kar Falmata ko Hajja ɗayar su ta ji maganar , dan haka cikin yanayi na lallaɓa yace ,

" to naji naji , zan SAKE TA ,

Wani irin kallon kar ka raina ni Yakaka tayi masa ,

" yanzu nake son ka sake ta anan idan kuma ba haka ba wallahi zan je masarautar maraɗi a yau ba gobe ba ,

Da tashin hankali Youssouf yake kallon Yakaka , wacce ta tsattsare sa da ido babu alamun shakku a tare da ita ,

Gani yayi gabaɗaya ta rikiɗe masa tamkar ba yarinyar nan da ya rainawa wayo , ya kuma yi wasa da rayuwar ta a shekarun baya ba ,

Falmata wacce hawaye suka riga suka wanke mata fuska kamar ruwan fanfo, ta sanya tafukanta duk biyu ta rufe bakinta ta hana sautin kukan da take yi fitowa , a hankali ta silale ƙasa ta durƙusa tana jin yadda marar ta ta wani irin curewa guri guda ..


Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kun wuni lafiya ?😍❤

Wai-wai , kai-kakai , yau wacce rana ?? 🤓😂

Uhmmm ai idan har baku daina sakar min bama-baman Comments da likes din ku irin na jiyan nan ba ( ko ma fiye da haka )  Nima kuwa ba zan yi k
ƙasa guiwa ba wajen cigaba da sasukar rubutu ba,  "Ah to meye? Ai tuwon girma miyar sa nama,  sannan kuma yaba kyauta tukuici. ❤😍

Amma kuyi hakuri da yadda bana samun damar maida muku da martanin sharhin ku,  idan nace zan dunga daukar waya ba zan kammala aiyuka na da wuri har na samu damar typing ba , duk da haka nayi alkawarin zan bibiyi comments din ku baki daya na bada amsa inshaallah .

Nagode.




Na manta ko da wacce take buƙatar hayar ɗan Biri saboda tsaro ?! 🐒😂
[12/16, 1:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)





Umm'muaz




42











Wani ɗan kuka ciki-ciki da Mama ta fara daga can cikin ɗakin kwanan su mai haɗe da nishi shi ya sa Falmata miƙewa daga inda ta durƙushe tana rishin kuka ,

A duƙe ta ƙarasa ɗakin saboda mararta da take ji ta riƙe , da taimakon hasken lantarki ta hango Mama a ƙasa ta faɗo daga kan ɗan gadon ta da yake dakin ,

Da sauri ta ƙarasa ta ɗagota tare da rungume ta a jikinta, tana tattaɓa jikin da ta ji yayi zafi rau , muryar ta na karkawa tace ,

" Mama meyasa kika faɗo daga gado ? Ina ne yake yi miki ciwo faɗa min , ? Kai ne ko ƙafar ki ko hannu ? Ko Bayan ki ne ??

Mama wacce take wani irin nishi ta riƙe hannun Falmata tare da ɗorawa akan cikinta ,ƴar muryar ta da kyar take fita tace ,

"ciki na ne ,Mama cikina yana ciwo sosai , ki bani magani zan sha ,ina so nayi bacci Mama ,

Wasu sabbin hawayen ne suka silmiyo daga gurbin idanun Falmata ,

"sannu Mama ,sannu kin ji zan baki magani yanzu ,

Bata amsa ba sai nishi da ta cigaba da yi , a hankali Falmata ta dafa cikin nata ta ji yadda ya kumbura yayi ƙem-ƙem ko numfashi da kyar take fitarwa, wani irin tausayi ne ya kamata tare da tashin hankali a lokaci guda ta nemi ciwon marar da take ji ta rasa ,

Tana dafe da cikin Mama ta fara yin addu'ar samun lafawar ciwo kowanne iri ne ,

Tashin hankalin da zuciyar ta ke ciki a lokacin yana neman kayar da ita , saboda rikicewa da jikin Mama yake neman yi da ƙarin ƙarfin nishinta ta fara ƙiran Baban ta ,

"Papa , Papa ,

Youssouf wanda shigowar sa kenan falon jikin sa a sanyaye ya zauna a kan kujera zuciyar sa cike da tashin hankali kan iƙirarin Yakaka na ya saki Falmata ko kuwa ta je ga iyayensa  , sam bai yi zaton abubuwa zasu rinchaɓe masa ya irin haka ba ,

Yasan cewa shi mai lefi ne a wajenta amma ko meyasa baza ta saurara su bi kome a sannu ba ?

Ƙiran sunan sa da Mama take yi ya sa ya miƙe ya nufi ɗakin zuciyar sa ɗauke da sabon zullumi kan tashin ciwon ta ,

A kiɗime ya ƙarasa kan su ya tsugunna ta bayan Falmata yana zagaye su duk biyun da hannuwansa da ya kai ya ɗora a cikin Mama inda ya ga Falmata ta riƙe ,

" Meye ya same ta ? Ciwon ciki take yi ,

"Papa ,

Mama ta ƙira sunan sa tana ƙokarin buɗe ido ,

" na'am princesse ina yake miki ciwo ?

'papa ciki na ka bani magani ina so na kwanta ,

"Mama ai a kwance kike , bari na kawo magani kisha kafin mu tafi hospitalisé, 

"Fatima yaushe Mama ta fara ciwon ciki ?

Ya tambaye ta yana kallon fuskarta ,

Sunkui da kai tayi tana kaucewa ganin Fuskar sa , muryar ta a ɗan dishe tace "Yanzu ne ,

Bayan ya kawo maganin ciwon ciki ya bata ta sha , ya janyeta daga jikin Falmata ya ɗora ta akan gado , " Fatima kin yi sallah kou ?

Girgiza kai tayi tana miƙewa ,

'kiyi sallah mu tai da Mama hospitalisé ,

Bata amsa ba ta ɗau hijabinta ta zura tana barin ɗakin da take jin sa a ƙuntace tunda shigowar sa ,

Ta kama hanyar da zata sada ta da ciki sashinta , sannu-sannu take tafiya tamkar wacce aka zarewa laka ,

damuwa yayi mata yawa bata taɓa zaton zuwan wannan ranar ba , saki a tsakaninta da Baban Mama ?

Da kowanne daƙiƙa guda tunawa take da kalaman Yakaka , da Baban Mama taƙi yarda wani sashin zuciyar ta da yake bijiro mata da rashin kyautawar Yakaka tare da son kai da take ganin ta nuna ƙuru-ƙuru ya rinjayeta ,

Ƙoƙari take ta haɗiye tashin hankalinta ta haƙurƙurtar da ranta ta kuma ƙarbi duk wani hukuncin da su biyun da a yau duniya bata da kamar su zasu kai ga yankewa akanta ,

So take ta rufe ta binne duk wani sirrin dake zuciyar ta a can ƙasan ranta .

Sai dai zuciyarta rawa take tana tantamar anya zata iya ??

Hannu ta sa ta tura ƙofar falonta ta shiga , tamkar baƙuwa haka take sanɗa a falon , aiyanawa take nan da ɗan wani lokaci kaɗan kome na gidan zai tashi daga matsayin mallakinta , to ya koma na wa ??

Taƙi yadda ta hasaso ƙarshen lamarin saboda bata jin zuciyar ta zata iya jurar yadda ƙarshen kome zai zama bata son tuno da makomar Rayuwarta .

Har ta nufi ɗaƙin ta sai kuma ta dawo da baya ta yi ɗakin da Yakaka take ta ɗan ƙwanƙwasa ƙofar ,

Yakaka wacce take zaune akan sallayar da ta idar da sallah tana lazumi ta tashi ta buɗe mata ƙofar ,

" Falmata kin tashi ?

  "un bari nayi sallah , ta amsa mata tana ratsawa ta gefenta ta wuce banɗaki ,

Bayan ta idar da sallah ta ɗaga hannuwanta duk biyu tana addu'a ,

Ta kwashe fiye da mintoci sha biyar tana addu'o'i , har zuwa lokacin da zuciyar ta tayi rauni gaba ɗaya hawaye ya taho mata , sai ta fashe da kuka mai sauti ,

Yakaka wacce take azkar ta tsahirta , a hankali ta ɗago kai tana kallon ta , sai ta tashi daga inda take ta dawo kusa da ita ,

Dafata tayi fuskar ta na bayyana damuwa tace mata
  'Falmata meyasa kike kuka ? Wani abu aka yi miki ? Ko baki da lafiya ne ?  Ki daina kuka Falmata ki faɗa min abunda ke damun ki kin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login