Showing 399001 words to 402000 words out of 411050 words
Chapter 134 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
duk wata jijiyar jikin ta tayi tsayuwa daga barin yin aiki na wucin gadi .
A yau taurin zuciyar ta gaza yin tasiri yayi domin kuwa ruwan hawaye ne ya ɓalle mata kamar an buɗa famfo .
Sai shiƙar kukan ta Doctor Hamza ya ji wanda ya mayar da kan sa ga aikin sa .
Tsam yayi yana jin ɗan guntun tausayin ta na kawo masa , daga can ƙasan ran sa sai ya ji kamar fa bai kyauta ba yadda ya sanar mata da batun cikin Yakaka dole za ta iya jin babu daɗi tunda ita Allah bai bata ba musamman da yakasance Sofi tana da bala'in kishi.
A hankali ya ɗago kan sa yana kallon ta sai dai kafin yayi wani yunƙuri ta miƙe kamar ana tunkuɗa ta ta bar wajen .
Girgiza kai yayi yana mai mayar da kan sa ga aikin sa da yake so ya kammala kafin gobe saboda a gobe da yamma yake so ya bar garin zuwa Kano .
Washegari
D
octor Hamza da kansa ya shiga kitchen domin samarwa Yakaka da abunda za ta ci saboda kusan kwana tayi da zazzaɓi asubar farko kuma ta fara Amai .
Dan haka ya kama ta zuwa falo ya kunna mata tv yace tayi kallo kafin ya gama haɗa mata abun karyawa.
Ba dan ta so ba ta haƙura ta bar shi ya shiga kitchen sai dan ko kaɗan bata jin ƙarfin jikin ta wata irin kasala ce take bin gaɓɓan jikin ta jikin ta babu ƙarfi gefe guda kuma bata son warin Albasa da tasan muddin ta shiga kitchen to kuwa sai ta shaƙa .
Lokacin da ya gama ya kawo mata bata wani ci dankalin da ya kawo mata tare da ƙwai na kirki ba tace ta ƙoshi .
Yana tsakiya da rarrashin ta kan ta daure ta sake ci kaɗan Sofi ta sauƙo bata dubi inda suke ba ta zauna akan kujera ta ɗau remote.
Lokacin da ya dubi fuskar ta sai da zuciyar sa ta doka da karfi ganin yadda fuskar tata ta kumbura suntum idanun ta kuwa har kamar kwanciyar jini.
Da sauri ya baro Yakaka ya juyo gare ta "Subhananlah Sofi me ya same ki haka ? cikin dare ɓarayi sun shigo gidannan ne ?
Ba tare da ta dube shi ba tace "Da aljanu muka yi dambe ko ka manta?
Yadda tayi maganar a cushe ya so ba shi dariya amma sai ya gintse fahimta da yayi so take ta zo da rainin na ta da tayi alƙawarin ta daina '
"Oh i see .
Yace yana barin kusa da ita ya koma ga Yakaka wacce ita ma ta tsorata da ganin yadda Fuskar Sofi ta kumbura tayi jawur kamar wacce ta shiga filin dambe da wanda ya fi ƙarfin ta .
Bayan ya shirya ya fito gargaɗi ya yiwa Sofi kan kada ta yarda ta fita ko'ina ta zauna ta kula masa da Wafaa .
Kafin azahar zai dawo su yi Sallama saboda bayan Azahar zai tafi .
Bai yi zaton samun amsa mai daɗi daga gurin ta ba amma ga mamakin sa sai ya ji ta amsa har tana masa fatan alheri hakan sai ya faranta masa tare da ƙara masa kuzari ya bar gidan cike da nishaɗi farin-ciki goma da ashirin .
Sai dai yana fita Sofi ma ta fice kai tsaye inda suka yi za su haɗu sa Samy baby domin ta bata cikon kuɗin da za'a yi harkokin aiki kama daga kuɗin jirgi da Samy Baby ta bata tabbacin ta samu wanda zai mata hanya muddin ta saki kuɗi cikin kwanaki uku ma za ta ɗaga India, da yake kan Sofi ya kunce ilmin zamanin ta tare da wayewar ta sai suka gaza yi mata amfani saboda taƙi basu dama shaiɗan da muƙarraban sa kaɗai ta sau wa ragamar rayuwar ta cikin tsakanin jiya da yau ko ibada ta daina yi kwata-kwata da daman dai ba sosai take tsayar da Sallah ba amma daga jiya zuwa yau ko Sallah ɗaya bata yi ba, cikar mummunan burin ta kawai take mafarki a bacci ko a farke ita dai burin ta ta ga bayan Yakaka "kaicho Sofi .
Haka ta ɗau kuɗi zunzurutu naira Miliyan biyar da dubu dari shida ta bawa aminiyar ta Samy Baby bayan naira Miliyan huɗu da rabi da su kenan kuɗin da ke account ɗin ta da tun a jiya tayi transfer su zuwa account na Samira.
Wannan farin kudin kuwa kudin duk wasu gwala-gwalan ta ne tare da wani daya na Momy kori da ta amsa Aro bata mayar mata ba duk ta hada su ta sayar ta dankawa Samira kudin.
"Samira dan Allah ki tabbatar kome ya tafi yadda ya dace kin ga Doctor tafiya zai yi to so nake kafin ya Dawo kome ya kammala sai dai ya dawo ya tarar da gawa kawai .
"Kar ki damu ƙawata to meye amfanin ƙawancen mu idan ban miki ba ? Ke ce fa Sofiya ? kar ki damu jibi-jibin nan zan bar ƙasar nan ke dai ki kwantar da hankalin ki bana son yadda duk kika bi kika tada hankalin ki kin ga yadda kika koma kuwa? Kamar wata bazaurar Jaɓa .
Ɗauke kai Sofi tayi tana jin zagin walaƙancin da Sofi tayi mata a fakaice .
Cikin wayencewa Sami baby ta miƙa hannu ta ɗau wayar Sofi da take ajiye a tsakanin su ba tare da Sofin ta hana ta ba tayi wasu 'yan taɓe-taɓen ta a wayar ta ajiye mata daga nan Sallama suka yi saboda Sofi ta ce bata so Doctor Hamza ya dawo bata gida .
Haka kowaccen su ta nufi motar ta Sofi ita ce ta fara barin harabar wajen kafin Samy Baby ma ta tada tata motar ta jaa ta cike da nishaɗi ta kama hanya '
Kome ya tafi mata dai-dai yadda ta tsara yanzu abunda ya rage mata kawai shine ta tattara duk wasu abubuwan da ta mallaka a garin Abuja ta cika motar ta ta bar garin zuwa garin Damaturu inda ta zaɓa domin gina sabuwar rayuwar ta .
Ita da Sofi kuma daga ta ƙarasa rufta ta a rami kamar yadda ta shirya a jibi kafin ta bar jahar Abuja sun rabu kenan haihatan ah to aina Sofi ta san za ta kama ta ? Sannan ma cikin shirin ta na ƙarshe da zata yi ta san za ta ingiza Sofi ta aikata abunda zai sa ta iya ƙarasa rayuwar ta a gidan Yari da ba zata samu damar neman ta ba ma dan haka ita ta sha kenan ta kuma rufe shafin Sofiya a rayuwar ta "kayya Samira .
Lokacin da Doctor Hamza ya dawo gida ya tarar da Sofi a kitchen tana girki ba ƙaramin daɗi ya ji ba dan haka ya saki jiki da ita ya tsaya a kitchen ɗin suka yi 'yar hira yana ta jaan ta da wasa .
Ƙarfe biyu dai-dai ya musu Sallama ita da Yakaka bayan ya haɗa su ya musu 'yar nasihar kan su zauna lafiya kafin dawowar su sannan ya ɗau kuɗi masu kauri ya danƙawa Sofi ko za su buƙaci wani abu sai suyi amfani da shi duk da ya san a store da kitchen akwai kome na daga kayan abinci
Dauriya Sosai Yakaka ta nuna lokacin da suka masa rakiya bata yi kuka ba sai Sofi ce ma ke zuba masa shagwaɓa wai za tayi kewar sa shi kuma gaba ɗaya hankalin sa yana kan Yakaka
Ko kaɗan ba son ransa bane yayi nisa da ita a dai-dai wannan lokacin sai dai dan ba yadda zai yi aikin sa aikin ceton rai ne dan haka bashi da zaɓi na lokacin da zai yi tafiya a bakin aiki inda za shi ma ceton rai zai tafi dan haka tilas ne tafiyar sa.
Haka suka yi Sallama cike da alhini ya jaa motar sa da zai tafi da ita zuwa gidan Doctor Suleiman wanda shi ne zai kai shi airport ya koma da motar tasa gidan shi .
Yakaka ita ta bada hanya Sofi ta fara wucewa cikin gidan suna shiga Sofi ta rufe ƙofar ta murɗa ɗan makulli , ta ƙasan ido Yakaka ta dube ta Kallon nan da take tsoro shi ta hango a idanun Sofi idan ba gizo idanun ta ke mata ba ma ta ga kamar tana mata wani guntun murmushi.
Zuciyar ta ta doka da ƙarfi sum-sum ta wuce ɗakin ta ta bar Sofi a wajen .
Kitchen ta shiga a gur-guje tayi girki ta zuba a kula ta bar sauran a tukunya sannan ta jidi ruwan gora da juice ɗin da take ɗan sha ta kai fridge na ɗakin ta ta sa ta dawo ta ɗau abincin tazo fitowa daga kitchen ɗin ta ga Sofi ta tare hanya har yanzu dai wannan kallon ne a idanun ta sannan bata janye murmushin mugunta da take mata ba .
Muƙut Yakaka ta haɗiye yawun tsoro .
"Mai ciki girki aka yi ne ?
Sofi ta tambaye ta fuskar ta a yanayin da bai yi dai-dai da kalmomin da ta furta ba.
"Eh nayi girki ne Anty Sofi , naki ma yana tukunya daman yanzu zan zuba miki '
"Bari na kai nawa ɗaki .
Sai da Sofi ta mula sannan ta ɗan matsa da kyar Yakaka ta wuce tana shiga ɗaki ta murza ɗan makulli tana jin nutsuwa na safko mata daga nan bata sake fita daga ɗakin ba har dare komen ta a ciki take yi tsakanin banɗaki da tsakar ɗakin
Sai wayar ta take yi da Falmata da kuma Lubna da su duka biyun suke cikin watan haihuwar su .
Washegari
Kamar yadda tayi a jiya haka yau ma tayi girkin ta ta kai ɗaki ta rufe tsawon yinin bata bari sun haɗu da Sofi ba duk kuwa da cewa ta ji motsin ta daga falo .
Sau biyu ta samu damar yin waya da Doctor hamza wanda ya shaida mata cewa a gobe zai dawo idan Allah ya yarda dan haka ta ƙarasa yinin ranar cikin nishaɗi da jin daɗin dawowar sa duk da cewa tsakanin jiyan da yau laulayi sosai ya taso ta gaba gadan-gadan kawai dauriya take yi .
A washegari da safe Bayan tayi wanka taso fita ta haɗa abin karyawa amma jin yadda Sofi ta ƙure muryar tv tana jin kiɗa ya bata tabbacin tana falon ita kuma cikin kwanakin nan kamar Allah ya ƙara mata tsoron Sofi ne wani irin matsanancin tsoron ta take ji ta yadda ko haɗuwa bata so su yi dan haka ta fasa fita tayi zaman ta kawai a ɗakin da daman ba jin cin abincin sosai take ba yau ta tashi da matsanancin ciwon kai ne .
Can kamar hantsi haka tana ɗan taɓa bacci ta ji wayar ta ta ɗau kiɗa , da kyar ta miƙa hannu ta ɗau wayar ganin ƙiran daga masoyin ta ne yasa tayi azamar ɗagawa .
Cike da ƙauna da kulawa suka gaisa kafin Doctor Hamza ya shiga rarrashin ta a ƙarshe ya shaida mata cewa dawowar sa a yau ba zata yiwu ba sai nan da kwanaki biyu watau ranar juma'a
Wannan karon bata ɗaure ba sai da ta sanya masa kuka da kyar ya iya shawo kan ta tayi shiru da alƙawarin zai dunga ƙiran ta akai-akai duk dai idan ya samu dama .
Ba dan sun so ba suka yi sallama saboda jiran sa da ake yi., duk da cewa ya so yayi magana da Sofi ma domin ya sanar da ita ɗaga dawowar ta shi amma sau uku yana gwada ƙiran ta yana nuna masa cewa tana amfani/waya da layin nata dan haka ya haƙura ya tura mata saƙo kafin ya kashe wayar sa .
Sofi da take baccin asara ƙiran waya ne ya tada ta lokacin da ta ɗau wayar wasu numbers ta gani haka irin na ƙasar waje idan idanun ta sun gani dai-dai ma numbers ɗin na ƙasar india ne dan haka cike da ɗoki ta ɗaga kiran
Kamar yadda ta zata ne Samira ce take ƙiran ta daga ƙasar india kamar yadda numbers ɗin suka shaida mata kafin ma ta ji daga bakin Samy Baby .
Bata jira sun gaisa ba a ƙagauce ta fara tambayar "Samira kada dai har kin isa india ?
Nan Samy Baby tace mata ai ma tana karnataka har kuma ta gana da Boka yanzu haka ma da take jin hayaniya a cikin jirgin ƙasa take kan hanyar ta na komawa masauƙin ta ta kasa haƙura dai dole ta ƙira ta fara mata albishir Boka yace nan da awa biyu zai kammala aikin ta .
Wani irin ihun jin daɗi Sofi tayi tana jin kamar an mata bishara da gidan Aljanna.
za ta sake yin magana ɗif Samy Baby ta kashe wayar ta .
Tana wani murmushin mugunta ta buɗe gidan sim ta zare sim card ɗin ta gutsittsira shi da haƙorin ta ta watsar a gefen hanya ajiye wayar tayi a gefe kafin ta ɗaura seatbelt a hankali ta daga glass na motar kafin ta tayar da motar da bala'in gudu ta cilla ta a titi .
Yadda take gudu a titi ba'a ce Mace ce ke jaan motar ba har dai tayi nisa da ainashin garin Abuja tana tuƙi tana bin waƙar da take tashi ta sifukun motar ran ta fes a dai-dai lokacin ji take duniya ta mata daɗin da bata taɓa jin makamancin sa ba ta samu duniya abunda ya rage kawai sai ta miƙe ƙafa domin cin ta .
Kafin kamar walƙiya ta ga ɓullowar wasu motoci biyu da gudu da suka yanko daga cikin daji suka yi banga-banga akan titi da yasa ta cikin matsanancin tashin hankalin da ya maye gurbin nishaɗin da take ji ta taka birki ƙuuuuuuu da ba domin Allah ya kiyaye ba da babu abunda zai hana motar tayi ƙundumbala da ita .
Samy Baby bata tabbatar yau ita ce rana mafi muni a tarihi rayuwar ta ba sai lokacin da ta fahimci hannun ko su waye ta faɗa'
Masu yin garkuwa da mutane ne kidnappers da take jin labarin su wai-wai sune yau take ganin su a gaban ta kamar a mafarki .
Kwakwalwar ta taƙi samun kwanciyar hankalin yin tunani ɗaya kamar yadda idanun ta suka ƙafe ƙaf daga samun damar zubar hawaye duk wasu kalmomi kuma suka ɓace suka shafe daga bakin ta har zuwa lokacin da suka ɗora mata bakin bindiga suka tasa ƙeyarta bayan sun kwashe kome da yake cikin motar suka nausa da ita cikin daji .
***
Sofi ji tayi farin-cikin da take ciki ya mata yawan da bata jin za ta iya jurar sa bata ɗan wataya ba dan haka ta ɗau wayar ta da sai lokacin ta lura da saƙon Doctor Hamza .
Wani tsallen jin daɗi ta sake yi jin cewa ba zai dawo ba ma a yau sai nan da wasu ƙarin kwanaki wanda hakan duk alamun nasara ne a gurin ta domin kuwa dama ce ta sake samuwa a gare ta .
Kiɗa ta kunna a wayar kafin ta buɗe wata 'yar karamar loka da take jikin gadon ta ta fara zaro kwalabe da sauran kayan mayen ta '
Sai da ta tara su jibgi a gaban ta sannan ta shiga ɗaga su ɗaya bayan ɗaya tana tuttulawa a cikin ta tayi ha'in tana jin ta tamkar tafi kowa farin-ciki a duniya tana tangaɗi ta shiga juya jikin ta tana rawa .
Daga can ɗakin Yakaka da ta ji shiru babu alamun motsin sofi a falon sai ta lallaɓa ta fito kai tsaye ta tafi kitchen saboda yunwa da ta fara sasuƙar ta har jiri-jiri take ji .
Cikin awa guda ta gama irin girkin da take jin sha'awar ci ta kwashe ta kai ɗakin ta ba tare da ta rufe ƙofar ba sai kawai ta faɗa banɗaki tayi wanka ta ɗauro alwala saboda azahar ta gabato.
Tun tana wanka take jin ana ta ƙiran wayar ta har sau uku dai-dai da fitowar ta wayar ta sake ɗaukar kiɗa da sauri ta ƙarasa ta ɗaga ta lokacin da ta ga sunan mai ƙiran Falmata ce .
"Hello Falmata na kina lafiya ko ? Ko haihuwar ce ? Ko kin haihun ne ?
Ta jero mata tambayoyin ba tare da ta ajiye numfashi ba saboda koyaushe cikin bin haihuwar Falmatan take a rai musamman da yake ita ta taɓa haihuwa ta ɗana ta ji yadda haihuwar ke da zafi duk sai take jin tausayin ƙanwar ta kullum cikin addu'ar sauƙa lafiya take mata musamman da cikin na Falmata ya kusan shige kwanakin haihuwar sa da hakan sabon abu ne a haihuwar fari .
"Hello Falmata kina jina kuwa ? Ta sake furta hakan cikin damuwa
Dariyar da Falmata ta cika mata kunne da ita yasa ita ma ta murmusa tana sauƙe ajiyar zuciya ta ce "meye abun dariyar kina jina ina miki magana wallahi duk kin ɗaga min hankali ganin yadda kike ta ƙirana ina wanka na zo kuma na ɗaga kin yi shiru.
"Yakaka bani nake ta ƙiran ki ba wallahi ni yanzu nan na ƙira ina ƙira kuma kika ɗauka .
Ɗan jimm Yakaka tayi "to waye yake ƙirana ? Ta tambayi kan ta , sai bata wani damu ba kawai ta zauna a bakin gado suka shiga hirar su ita da Falmata .
Sun ɗau tsawon lokaci suna hirar da take sanya su duka biyun a farin-ciki tare da sake ƙaunar juna '
Kafin kamar daga sama Yakaka ta ji an damƙi kafaɗar ta da yasa ta matuƙar tsorata ta saki wayar ta ta faɗi .
Jikin ta yana rawa ta miƙe tsaye tana kallon Sofi wacce take tsaye kiƙam hannun ta ɗaya a ɓoye a bayan ta.
An-anty Sofi in-ina wuni.
Wata irin shashashar dariya Sofi ta saki da hatta Falmata da bata kai ga katse wayar ba ta ji ta .
Zuciyar ta ta fara sauya bugu daga lokacin da ta fara saurarar duk wasu zantukan da Sofi take yi cikin maye murya sama-sama .
"Kin yi zaton na kyale ki ko ? A tunanin kin shaa da ni kenan ? Ƙaramar kwakwalwar ki ta baki tunanin kin yi nasara ? Ni Safiya na bari ki rayu da Mijina ki haihu ?
"Wacce irin cusashiyar ƙwakwalwa ce da ke ? Ta kifi ? Kin taɓa ganin an yi haka ? Ba zai yiwu ba , ba zai faru ba ba zai taɓa faruwa ba ki zo ki gina rayuwar ki a kan tawa Hamza nawa ne ni Kadai.
"Dole na rusa rayuwar