Showing 30001 words to 33000 words out of 411050 words
Chapter 11 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ta motar sojojin nan da suka ji ya dumfaro farfajiyar masaukin nasu ,shi ya firgitar da su suka miƙe ba shiri cikin ransu kuwa cike da taraddadin da me jiniyar ta sake zuwa musu a karo na biyu cikin ƙasa da sa'o'in su biyar a cikin birnin na maiduguri ?
Sai dai sabanin tunanin su a yanzu ba daga motar sojojin da suke zato bane ƙarar jiniyar take fitowa ba ," daga wasu jerun gwanon manyan bakaƙen motoci masu daukar ido tare da kyallin sabuntar dake nuni da tsadar su , karar take fitowa ",
Buɗe baki da hanci yakaka,da yagana suka yi suna bin motocin da kallo waɗanda har matukan su suka riga suka sama masu matsaya ,"
Sai dai basu kai ga sauke numfashin farin cikin da suka riƙe na ganin cewa ba waɗannan sojojin da ganin su ba alheri bane a wurin su ,suka dawo ba , idanun su suka yi arangama da jerin gwanon motocin sojojin daga baya da ma na wasu jami'an tsaron masu mabanbantan kayan sawa wadanda basu kai ga rarrabewa da banbancin su da sojojin ba ,"
Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoron da ya cika mata zuciya fal ! Lalubar hannun ta falmata tayi cikin maƙyarkyatar murya take cewa " yakaka, yagana kun ga abun da nake faɗa muku koh ? Ni daman nasan da kyar idan ba gidan bayar da horo sojojin nan suka kawo mu ba ," ai tun daga horon yunwar da aka fara yi mana ɗazu ya ci ace kun fahimci irin kurkukun da muka shigo ," kawai ban faɗa miki bane yakaka , amma tun sanya kafafuna cikin garin maiduguri naji ajikina babu alheri cikin sa , naji cewa akwai wani babban al'amari marar daɗi da zai same mu a cikin sa ,"
Kuwwar mutane tare da dararrakin su da ya cika musu kunnuwa shi ya katse surutun da falmata take yi cikin ɗimaucewa ta koma cewa "menene yakaka ? Harbi ake ? Kashe mu muma zasu yi ? Toh ku zo mu gudu mana tsayuwar me muke ?
Ki nutsu falmata ! Yagana ta furta "cikin ɗan ɗaga murya" a sakamakon surutun da hargowar da falmatan take yi musu cikin ruɗewa ya hana ta , ta gano abun da take hasashe , ganin yadda taga fuskokin kowa a wurin ya yalwatu da fara ,"ta ko'ina bullowa jama'a suke suna tururuwa a harabar wajen ,"
Da gudu yagana ta dira daga kan baranda kafin ta waiwayo cikin tsantsar farin cikin da kamar anyi mata babban bisharara ,"yakaka falmata ga gwamna wallahi gwamna ne yazo ,gwamnan jahar borno ", kuyi sauri ku taho kar wajen tsayuwa ya cika ," daga haka ta kara da gudu kamar yadda taga sauran jama'a maza da mata suna kwasar gudun zuwa gaban dandamalin da jami'an tsaro suka kewaye ta ko'ina wanda da alama anan gwamnan yake tsaye .
Saƙare suka yi a tsaye cikin rashin sanin takamaimai halin da suke ciki na farin ciki koh saɓanin hakan , a zahiri basa jin wani farin ciki a dan saboda zuwan gwamnan musamman ma ga falmata ," wacce ta sauke boyayyar ajiyar zuciyar samun kwanciyar hankali jin ba zuwa aka yi domin azabtar da su ba kamar yadda ta zata ," sai dai ita bata wani farin ciki da zuwan gwamnan domin rashin sanin muhimmancin zuwan nasa .
A hankali yakaka ta fara jaan hannun falmata cikin cewa mu ma muje falmata muga gwamnan kuma muji bayanin sa kin ga duk mutane sun tafi .
Bayan gajeren bayanin da gwamnan ya gabatar musu cikin yaren su wanda duk na ban hakuri ne game da halin da suke ciki tare da yi musu alkawurwukan kyautata musu da ababen more rayuwa , sannan a karshe yayi musu albishirin tarin kayan abinci da suke tafe da shi , gidajen sauro , butoci da kuma bargunan rufuwa , ya kuma ƙara da albishirin za'a ƙara musu matakan kula da lafiyar su da sauran bukatun su na yau da kullum,
a karshe kuma ya basu dama wasu daga cikin su suka faɗi irin matsalolin da suke ciki a sansanin nasu , inda mafi yawan korafe-korafen nasu ya tafi akan ƙarancin abinci da ruwan shaa, uwa uba da cizon da sauro da ƙwarin gurin suke musu wanda cizon sauron yake kawo musu mummunar masassarar da har take iya kaiwa ga rasa rayuka idan ya zo da ajali musamman ga mata masu ciki da kananan yara .
Bankwana yayi musu bayan da ya basu tabbacin za'a samu sauyi daga yanzu inda ya nemi da a naɗa kwamiti da shuwagabanni a tsakanin su kashi-kashi domin lura da matsalolin su .
Nan take aka shiga ihu da kalmomin yabo ga gwamna da tawagar sa har zuwa lokacin da ƙurar motocin su suka bace .
Babu laifi , ziyartar da gwamna ya kawo musu sosai ta saisaita ciwukan da suke cikin rayukan al'ummar sansanin yayin da ya haifar da farin ciki a cikin zukatan kashi tamanin na cikin ɗarin mutanen.
Idan aka ɗauke falmata wacce har kawo yanzu da ake kammala raba musu gidajen sauro tare da barguna, inda ake haɗa mutum biyu da gidan sauro guda bayan an damƙa musu bargunan su ɗai-ɗaya da buta ɗaya ," dukkanin su ba'a haɗa su da juna ba ,an ware su ne daban-daban yayin da aka haɗa yagana da wannan budurwar wacce ta basu kwatancen inda banɗaki yake , yakaka kuwa da wata yarinyar mace mai yara biyu ƙanana aka haɗa ta , falmata kuma da wata mata wacce take yanayi da zaurawa ,"domin ta wuce a sata sawun ƴan mata ƙanana irin su ,"kuma ita bata da ɗa ," babbar budurwa dai .
Babu yadda yakaka bata yi da wannan babbar budurwa da aka haɗa su da falmata akan tayi musu lamini ta bar musu ita da falmata gidan sauron idan ya so sai itama yakaka ta bar mata wajen ta ,"ma'ana suyi musanye wuri," saboda a zahiri ta shiga tashin hankali ganin za'a raba musu wurin kwana da ƙanwar ta ," Amma fir budurwar nan taƙi ,tace ita gaskiya baza ta iya kwana cikin gidan sauro guda tare da mai yara ba , karshe ma ta fatattaki yakaka ta kuma ce idan har ta matsa toh fa sai dai falmatan ta bita su tafi chan su ƙarata "ta bar mata gidan sauron ita ɗaya "
Da farko yakaka tayi tunanin su haƙura kawai da kwanan cikin gidan sauron su haɗu su dunga kwanan su tare, sai dai tunowa da korafe korafen da taji ɗazu sun yi da suke faɗin illar da cizon sauron yake yi da har yake iya kisa , yasa taji babu yadda zasu yi dole ta kiyaye lafiyar falmata , dan haka tana ji tana gani aka raba musu wurin kwana da ɗaki ita da ƙanwar ta .
Dare ya raba tsakiya idan banda juyi babu abun da falmata take yi gaba daya ta kasa bacci saboda tsananin takurar ta da budurwar da ake kira da "ajus" taƴi duk ta bi ta ture ta, tare da janye mata bargonta ta rufu da shi ,sakamakon sanyin damina tare da raɓa irin na tsakiyar daren yanayin damina ,"
sakamakon turo ta da ta dunga yi yasa gidan sauron nasu duk ya buɗe sauro da cinnaku masu fiffike sun samu damar shiga ciki sai faman ɗallara mata cizo suke ,"sau biyu tana yunƙurin jaan bargon ta amma sai ajus ta ɗallara mata mintsini tare da haure ta da ƙafa ,"
Lalubawa tayi ta tashi ta zauna tayi tsumu , gefe ɗaya na zuciyar ta cike taf ! da kewar mahaifan ta da ƴan uwan ta ,"kamar yadda take sake ganin daren na yau ma kamar sauran ukun da suka wuce babu mahaifiyar ta babu mahaifin ta babu ƙannen ta ," duk wani buri da take da shi na samun gamuwa da mahaifiyar ta da sauran ƴan uwan ta taji yana barin ran ta , wani sashi na ranta yana raɗa mata tare da bata tabbacin sun rabu kenan har abada," fashewa tayi da kuka dai-dai lokacin da wata gwarzuwar cinnaka ta sake mallara mata cizo a dokin wuya ,"cikin zubar hawaye take tuno irin kulawar da mahaifiyar su ke basu a irin wannan yanayin na yawaitar muggan kananan kwarin damina sam bata bari su cutar da su ,"toshe kunnuwan ta tayi da hannayen ta biyu a sakamakon rugugin hadarin da taji wanda take da tabbacin ruwan sama gaf yake da tsinkewa
A hankali yakaka ta sauke ɗan jaririn mai kimanin watanni biyu zuwa uku daga kan kafaɗun ta a yadda take durƙushe cikin gidan sauron tana ta faman jijjiga shi ,"tayi niyyar kwantar da shi a gaban uwar sa wacce take bararraje , tayi wawiyar kwanciya cinyoyi duk a buɗe kai ba ɗankwali ," cikin addu'ar Allah yasa kar ya farka domin hakika ta gaji da rainon sa tun farkon dare yake hannun ta lokacin da uwar sa ta dungura mata shi tace ta jijjiga shi yayi bacci, ita ta gaji bacci take ji ,ta jaa ɗayan ɗan nata gaban ta suke shaƙar baccin su ,"sau uku tana ajiye shi amma daga yaji an ajiye shi baya yin minti ɗaya yake sake challara kuka ," cikin gigin bacci da hargowa uwar sa zata ce dallah ta ɗauke sa zai hana sauran mutane bacci .
Cikin sa'a har ta kwantar da shi bai tashi ba ," tsurawa kofar ɗakin ido tayi tana ganin yadda walƙiya take haskawa tare da rugugin hadari nan take hankalin ta ya tashi tunowa da falmata da tayi koh a wane hali take ciki a ɗakin da take ? Ji tayi baza ta iya kwanciya ba idan bata ganta ba .
A hankali ta ɗaga gidan sauron da suke ciki da niyyar fita dai-dai lokacin da aka yi wani tsawa da rugugin tasowar hadari da ya sa jaririn nan ya firgice tare da tsanyara kuka ," a daburce uwar sa ta farka gami da fara cewa ke ke keh kina ina ne kika bar shi yana ta irin wannan ihun ji min ƴar banzar yarinya ,"muguwa ,cikin sanyin murya yakaka tace wallahi yanzu na ajiye shi koh kwanciya ban kai ga yi ba , kuma ma da alama kamar yunwa yake ji ", ta furta hakan cikin fatan Allah yasa uwar ta ɗauke shi ,"mts ta jaa tsaki tare da surar ɗan jaririn kamar ta suri yaro mai shekaru biyu ," ta koma ta kwanta tare da shi tare da ciro abincin sa ta cusa mar a baki ,ɗif yayi shiru .
Sauke ajiyar zuci yakaka tayi ganin uwar da ɗan sun koma bacci ,"ta siɗaɗa ta fita dai-dai lokacin da kakkarfan ruwan saman ya tsinke kamar da bakin ƙwarya ," gudu-gudu ta tsallaka ɗayan barandar ɗakin da falmata take ,'ba tare da ta damu da duhu tare da shirun da harabar wajen ya ɗauka ba ,ga ƙarar ruwan sama ,"
Tana shiga ta fara yawata idanun ta ," a hankali ta fara jin ƴar siririyar muryar ta tana kuka ,"ɗas-ɗas zuciyar ta ta buga tare da taruwar ƙwalla cikin gurbin idon ta, cikin sauri ta fara taku tana kewaye gidajen sauron jama'ah tare da tsallaƙe su cikin taka tsantsan ," tana nufar inda take jin sautin ta domin bata son yin magana kar ta tashi mutane
Cak ta tsaya da kukan jin takun sawayen ƴar uwar ta ,"yakaka ta furta cikin sanyin murya dai-dai lokacin da ta ƙaraso tare da durƙusawa a bakin "shingen"(gidan sauro) .
Ƙasa-ƙasa tace falmata meye yasa ki kuka ? Me aka miki ," da shishiƙar kuka tace babu kome yakaka na tuno da su mama ne ,"yakaka cikin daren nan kika fito kuma ana ruwan sama ? Meyasa ? ki koma ki kwanta dan Allah
cikin ƙura ido tare da taimakon hasken walkiya ta fahimci a dandaryar ƙasa kanwar ta take takure a zaune ," cikin takaici ta maida duban ta ga ajus da take ajiye numfashi ɗaya bayan ɗaya tare da sake duƙunƙunewa cikin jin daɗin barcin ta ,take ta fahimci abun da yake faruwa ,"
Zuruf ta miƙe cikin cewa ina zuwa falmata ," bata saurari amsar falmatan ba ta fita ,
Jim kaɗan ta dawo tare da bargon ta a hannun ta zura hannu ta miƙawa falmatan bargon,"ungo falmata buɗa shi ki kwanta akan rabi ki rufu da rabin duk da ma dai fitsarin yaron matar chan ya taɓa jiki amma ki kwanta a haka ,"
Jin falmatan tayi shiru yasa tace matsa na shinfiɗa miki kin ji ,"? Cikin rawar murya tace yakaka ke kuma ki koma ki kwanta akan me ?
Shittt ," falmata lafiyar ki tafi min kome , bamu da kowa a yanzu daga Allah sai junan mu , menene amfani na idan har ban zamar miki garkuwa ba falmata ," tana furta hakan ne dai-dai lokacin da take gyara mata bargon tana shimfiɗa mata ," kama mata tayi ta kwanta ,"
Yauwa toh bari ruwan ya ɗan tsagaita sai na koma ɗakin mu kiyi baccin ki kin ji ?
Gyaɗa mata kai tayi domin kuwa idanun ta har yaji-yaji suke mata tsabar baccin da ya cika su ,
Sauke sassanyan numfashi tayi , tare da share guntun hawayen da ya cika mata gurbin ido nisawa tayi tana tunanin ƙalubalen da suke a farkon sa yanzu wanda basu da sani akan iyakar sa ,karshen sa babu abun da yafi tsaya mata a zuci irin tausayin ƙanwar ta a yin rayuwa cikin wannan sansanin da ta lura kowa kan sa ya sani kan sa yake so "rayuwar daga ƙawri sai gwaiwa ", zuciyoyin mutane cike take da mugunta da son kai .. Yaa Allah ga ni ga miskiniyar kanwata Allah ka taimake mu .
*Maraɗi jamhuriyar niger*
A karo na biyar ta kama ta sauko daga kan murfin sunduƙin yin "bahaya"( Toilet- Toilette ) da yake cikin banɗakin ta ," kai kawo ta shiga yi tare da duban agogon fuskar wayar ta "
Yau har karfe biyu da mintuna arba'in biyamuradi bai dawo ba kamar yadda ya saba fita sha biyu da rabi na dare ya kuma dawo karfe biyun dare ,"
Meye ya tsayar da shi ? Jin motsi tayi kamar an taɓa kofar sirrin da take bangaren biyamuradin wacce kuma da ita yake amfani wurin fita da shigar sa gidan a dai-dai wannan lokutan da ba wanda ya taɓa sanin yana fita daga Allah sai shi sai ita ,
Cikin sauri ta sake ɗarewa kan sunduƙin tayi ƴar ɗage ta leƙa ta ɗan siririn huɗar da aka yi ta a can saman banɗakin domin ado wanda aka liƙa kwan lantarki a jiki, sai dai a halin yanzu babu ƙwan lantarkin sai dai huɗar da ta fito sarari ake iya ganin abun da ke waje ta wurin ,
Tar ta hango shi a cikin hasken lantarkin da ya ƙawata lambun bayan ɗakunan sa ," yana layi tare da tamɓele jikin farar rigar sa da shuɗin wandon jins ɗin sa dumu-dumu da abun da bata iya tantance shi daga inda take ,"
Ji tayi ruwan hawaye ya silmiyo daga gurbin idanun ta da gudu sun fara tsere akan siriryar fuskar ta ,"
Wani faɗuwar ƴan bori da yayi rigijib shi yasa ta kusa zamewa ta silmiyo daga kan toilet ɗin , da sauri ta ɗiro cikin gudu-gudu ta bullo ɗakin ta tare da fitowa cikin parlour kai tsaye ta nufi kofa ta kama mariƙin kofar ta murɗa , zuciyar ta tana zafi tare da ingiza ta , idanun ta suna hango mata faɗuwar da abun kaunar ta yayi .
Sai dai turus ta jaa ta tsaya lokacin ta tuno da fitar ta a wannan lokacin zuwa bangaren biyamuradi zai jawo , me zata cewa masu tsaron gidan ? Wanda ta san basu san halin da yake ciki ba , basu taba sani ba , idan kuwa har ta fita war haka dole su sani .
Hakan yana nufin fallasuwar mummunar fuskar masoyin ta , hakan yana nufin kunyatar masoyin ta , hakan yana nufin dasuwar bakin ciki cikin zuciyar uwar goyon ta , hakan yana nufin samar da wanzazjen bakin ciki cikin zuciyar uban goyon ta kuma kawun ta , hakan yana nufin tozartuwar ƴan uwan ta ,hakan kuma yana dai-dai da zubewar girma da mutuncin masarautar su baki ɗaya .
Kamar walƙiya ta juya ta koma da sassarfa ta shiga ɗakin ta gami da murza mukulli lokaci guda ta nufi gadon ta gami da fadawa rubda ciki ta sanya kanta tsakanin filo gami da fashewa da wani irin kukan da ya tuƙo tun daga karkashin zuciyar ta , kuka ne irin wanda mutum yake yi idan bakin ciki yayi masa yawa .
*Sorry this is a really short chapter koh? Kar ku damu insha Allah the next one will be longer and more action packed !*
*Things are really starting to heat up now* 😜
*Please comment what you guys think of not just this chapter but every chapter . I really love hearing feedback on my work because these chapters are not easy to write .*
*#Thanks* .
*#son so*
*#mafari Yanzu muka fara*
[6/24, 9:58 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association
*MAFARI.......*
( _Hargitsin Rayuwa )_
*umm'muaz*
7
Juyi ya sake yi a karo na barkatai bisa makeken gadon nasa na alfarma, tare da runtse idanu yana mai sake jin yadda kan sa yayi masa mugun nawi har baya iya buɗe idanun sa sosai , ɗan ƙaramin tsaki ya jaa da yayi sanadin juyowar Tafeedah wanda yake zaune bisa doguwar ƙawatatciyar kujerar da take gaba ƙadan da gadon .
Cikin takaici yake duban biyamuradi yousouf ɗin , kafin ya ɗan yi gyaran murya ! "cikin kowanne daƙiƙa ɗaya da yake wucewa yana sake nisanta ka da lokacin sauke farillah " tafeedan ya furta kalmomin masu nuni da tunasarwa , cikin nuna halin ko in kula ga biyamuradi yousouf , wanda koh kafin tafeedah ya idasa bayanin sa ya buɗe idanun sa tarwai da jijiyoyin cikin suka yi jaa , kammala bayanin nasa ya zo dai-dai da miƙewar sa zumbur daga kan gadon .
Bai yi wani jinkiri