Showing 144001 words to 147000 words out of 411050 words

Chapter 49 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14352

yana tsastsafo da jini , "

Bani da lafiya Falmata , yakaka tace da ita da wata ƴar murƴa chan ƙasa , tana mai zamewa ta kwanta gami da ɗaura kan ta akan cinyoyin Falmatan

Wani irin ciwo take ji marar misaltuwa tana jin kamar wani abu ya tokare ta , da zata iya zata sanya hannun ta zaro shi ,"

Ta gaza rarrashin falmata wacce ruwan hawaye ya ɓalle a idanun ta , tana iya hango tsoro tare da matsanancin firgicin da ya cika ƙwarar idanun Falmatan , nan take taji wani yanayi ya karci ran ta marar daɗi ,

A gajiye ya shigo falon bayan fitowar sa daga sashin mahaifin sa inda ya fara yada zango a tun shigowar sa gidan ,
   Tana maƙale a ran sa shiyasa ya gaza wucewa yaje ya kwanta ya huta kamar yadda gangar jikin sa ke muradi , sai da ya biyo domin ganin fuskar ta ,
       Nishin ta tare da sautin kukan Falmata ya fara ji kafin idanun sa su hango masa su a tsakanin kujera ,

da wani taku da yafi dacewa a ƙira sa gudu ya ƙaraso wajen , kallo ɗaya yayi mata ya fahimci halin da take ciki ,

  Rahima , da hafsa har ma da zainab waɗanda basa gidan su ya fara kwalawa ƙira , saboda ruɗewar ganin ta a ciwo , "

   Bai ƙarasa jin Falmata wacce take mar bayani cikin muryar kuka akan , su Rahima basa gidan fa ,"

ya fita da gudu yayi sashin sa ya sanya mukulli ya buɗe , kai tsaye wardrobe ɗin da ya nufa ya ciro manyan ledoji ukun da suke ɗauke da tambarin ,"Today's,'  da suke shaƙe da kayan haihuwa zuwa kayan baby da duk wani abun da za'a iya buƙata a yayin sabuwar haihuwa ya tanada ,hatta dogayen riguna biyu da mai jego zata sa a jikin ta bayan haihuwa , zuwa dogon wondo har da panties  duk ya saya ya adana , da babu wanda ya san hakan daga Allah sai shi ,,'

Da gudu ya koma gidan bayan ya zuba kayan a bayan mota , Fatima kama ta mu tafi asibiti , 

   Toh
tace tana mai kamo Yakaka da kyar suka miƙe tsaye , , da kyar Yakaka take cira ƙafa jin yadda cikin ya dunƙule guri guda , baya da ƙugun ta kuwa , ta tabbatar sun ɓalle, bakin ta ya rufu gum , ba un ba un-un .

Da gudu ya jaa motar kasancewar akwai rangwamen ababan hawa ya sa basu ɗauki dogon lokaci ba suka iso asibitin yayi parking kusa da wata brown ɗin mota matrix,"

Da sassarfa ya shiga ciki , sai ga shi sun dawo tare da nurses biyu da wasu ma'aikatan asibitin su ma biyu ,

Suka kama yakaka suka ɗora ta akan wheelchair , suka tura ta zuwa cikin asibitin da matuƙar sauri , Doctor Hamza da Falmata suka bisu a baya da hanzari ,"

Duk abun da suke akan idon samy baby wacce take cikin motar da take gefen ta Doctor Hamza , ta riga su zuwa wajen kamar yadda ta al'ƙawar ta , sake gyara kishingiɗar ta a jikin kujerar motar tayi , cikin ran ta tana addu,"ar kome ya tafi yadda ta tsara ,!

Da hawa gadon ɗakin haihuwa da haihuwar Yakaka duk abune wanda ya faru a tsakanin mintoci talatin ,"

Haka kuma baza ace anyi haihuwa a ɗakin ba saboda jaririyar kukan farko da tayi na zuwa duniya tun daga nan ta lalubi ɗan yatsan ta ta danna a baki tana tsotsa a hankali , tayi luf kamar mai bacci ,

Har aka ɗauke ta aka shige da ita wata ƴar kofa inda aka tafi duba lafiyar ta ,

Yakaka kuwa wacce take jin ta sawai kuma garau , tamkar ba ita bace wacce take jin ciwo kwatankwacin na mutuwa mintoci talatin da suka wuce , sai tsokanar ta tare da jaan ta da hira likitar da ta ƙarbi haihuwar ta take yi , tana kuma ƙara jinjina mata akan namijin ƙoƙarin da tayi wurin haihuwar , sam Yakaka bata da raki irin na wasu matan musamman haihuwar fari ta yadda za'a ji idan sun zi haihuwa suna ta faman ihu tare da sambatu marasa alfanu ,!

Hankalin ta baki ɗaya baya ksn likitar , ys tafi ga son sanin ya suke akan tsarin su , ita dai babu wayar a hannun ta a halin yanzu bare ta kira samy baby , bata fatan ace shirin su ya ruguje domin ta riga ta ƙwallafa son cikar burin ta a ran ta , shiyasa take ƙoƙari gurin kaucewa duk wani abun da zai sa mata tarnaƙi ya sa ta fasa nufin ta , hakan ya sa ko jaririyar bata duba ba,  da tun da ta iso duniya bakunan nurses tare da likitar da ta karɓi haihuwar bai gajiya ba gurin faɗin ",Masha Allah , Tubarakallah ," Tana jin yadda suke amfani da mabanbantan kalmomi gurin koɗa kyaun jaririyar , "
   Har ɗaya daga ciki take faɗin ita tun da take karbar haihuwa bata taɓa ganin mai kyaun wannan babyn ba Tubarakallah ,"
   
Likitar tana gama gyara ta da tabbatar da lafiyar ta , ta wanke hannuwan ta ta leƙa waje , inda  Doctor Hamza yake ta kai kawo Falmata kuma take zaune daga kan kujerar da aka tanada domin zaman jira ,"

  Yana ganin Doctor ta nufo shi shima ya ƙara taku zuwa wajen ta ,"

Da murna da fara'a take sanar da shi cikin harshen Turanci , matar sa ta haihu lafiya ta haifi kyakkyawar ɗiya mace , a halin yanzu bazai jima ba za'a fito da uwar zuwa ɗakin hutu daga bisani kuma idan an gama duba Lafiyar jaririyar za'a kai ta wurin mahaifiyar ta , "

Wani irin farinciki yake ji yana huda shi tamkar dai matar sa ce ta haifa masa ɗiyar sa da gaske bakin sa yaƙi rufuwa sai kalmomin godiya yake jerawa ga ubangiji, "

Juyawa yayi lokacin da likitar take komawa ciki , ya nufo Falmata wacce bata kai ga fahimtar me suka tattuna shi da matar da ta ji tashin muryar ta ba ,"

  Kallon ta yayi yana aina ya zama dole ya samo mai taimakawa yakaka a halin yanzu da ya san jikin ta ba ƙwari ,kuma haihuwar farko ce tana bukatar wani babba a kusa da ita  Falmata , yarinya ce kuma miskiniya baza ta iya bawa yakaka taimako ba a wannan gaɓar ,"

   Amne ita ce ta faɗo masa a rai , ya lura tana son yaran musamman ma Yakakar , kusan koyaushe suka yi waya sai ta tambaye shi game da yaran , dan haka ya san baza ta ƙi ba idan ya nemi ta kula da yakaka ,"

   muryar sa wasai yace da ita ,
      Fatimah , ki jira ni zan je na zo da Amne yanzu , Yayar ki ta haihu , kar ki je ko'ina ,
   bai jira cewar ta ba ya wuce da sauri yana duba agogo , saboda gudun lokacin juma'a ya shigo , "

ya bar Falmata da tarin farinciki cike fal da zuciyar ta , tare da son sanin a wanne hali yayar ta da jaririyar su suke ciki a halin yanzu??

samy baby tana ganin tashin motar Doctor hamza , da fitar shi daga asibitin ta fito daga cikin motar ta gami da gyara zaman hijabin kan ta bayan ta ɗauko wata babbar leda baƙa da flask ɗin ruwan zafi ta nufi cikin asibitin da ta riga ta zo shi sau dayawa ta yawata a ciki ta san kan shi tare da hanyoyin cikin sa ,"

Ta gaban Falmata ta zo ta wuce ta ƙarasa daf da kofar ɗakin haihuwar ta tsaya , tsayuwar mintuna uku tayi jal , aka buɗo kofar ɗakin gami da turo Yakaka akan kujerar ɗaukar marasa lafiya ,"

   kallon kallo suka yiwa juna kafin su sakarwa juna murmushin da yake bawa nursese ɗin tabbacin sanayya a tsakanin su biyun , Yakaka ta sunkui da kan ta ƙasa

  Ba tare da sun cewa juna ƙala ba aka cigaba da tura Yakaka samy baby na take musu baya suka zo suka gitta ta gaban Falmata dai-dai lokacin hawayen da suke idanun Yakaka suka fara sauka yif-yif , tana hango ƴan kyawawan kafafun falmata dusu-dusu , sakamakon ruwan hawaye da ya cika idanun ta ,

Aka wuce da ita zuwa ɗaKin hutun ,samy baby da sai da suka shiga ɗakin tayi magana ,"
   ta kama yakaka ta kwantar ta a kan gado tana ta faman jera mata sannu ,"

   Sannu ƙanwa ta , sannu kin yi kokari ,!
   Ah tayi kokari sosai cewar nurse ɗin da take ƙoƙarin ɗaurawa yakaka  ƙarin ruwa ,"
    Ƙanwar ki ce ko ? Ina mijin nata ?
   ai ga shi kuna kama , farar fatar ku ɗaya , ki kula da ita zan je na zo da baby , ki haɗa mata tea mai kauri sosai !
    a jimlace samy baby ta amsa da
  Toh
  Lokacin da nurse ɗin take barin ɗakin ,"

  Tana fita samy baby ta miƙe ,

Tashi tashi mu tafi Yaks , bamu da isashen lokaci ,"
  Da wani irin yanayi a fuskar yakaka ta miƙe zaune lokacin da samy baby take cire mata ƙarin ruwan da aka maƙala mata ,"

   FALMATA

tace tana mai share ambaliyar ruwan hawayen da ya zubo mata ,"
  Meye haka yaks ? Zaki ɓata mana shirin mu ne ?

Anty samy Dan Allah ki bari mu tafi tare da Falmata ,

    No no no yakaka kar ki ɓata mana tsari idan kin  haƙura kin fasa zuwa wajen yarima ɗin ne ni sai nayi tafiya ta , daman taimakon ki zan yi kamar yadda na faɗa miki tun farko , shi yace na zo na kai ki gurin sa ," idan kin fasa sai na koma na faɗa masa ke yanzu bakya son shi kin samu wanda ya fi shi ,
   share hawayen ta tayi da bayan hannun ta ,"
   Toh ki barni naje na faɗa mata kome , na faɗa mata kar ta damu zan je muyi aure da baban baby na dawo na ɗauke su ita da baby , bana son Falmata ta samu matsala sakamakon barin ta da zan yi ba tare da sallama ba , nasan zuciyar Falmata baza ta ɗauki rashi na irin haka ba , Falmata Bata da kowa bayan ni ,

  mtss samy baby ta jaa tsaki lokacin da ta sunkuya ta ɗau ledar da ta zo da ita ,"
    yaks ni kin ga bari na tafi tun da duk tsawon lokacin da muka ɗauka muna tsara yadda kome zai kasance yau da ranar ta zo kin rusa kome da kan ki , sai kiyi ta zama , cikin rayuwar da gaba kaɗan zaki yi danasanin taɓa wanzuwar ki cikin ta idan kika haɗu da kaidi tare da masifar da take yanyame a cikin ta ,

  Ni kin ga tafiya , tace tana nufar bakin kofa ,"

Wani irin tsalle zuciyar yakaka take , auren Youssouf babban nasara ne tare da cikamakin duk wani farin ciki na rayuwar ta ,"
   Ki tsaya anty samy , na YARDA ZAN BIKI KI KAI NI WURIN BATURE KAM SULUM ,"

  Wani shu'umin murmushi samy baby tayi kafin ta dawo cikin hanzari ta buɗe ledar hannun ta tare da zaro wasu manyan hijabai har ƙasa guda biyu ,
     Ta zurawa yakaka ɗaya ita ma ta sauya na jikin ta ta kamo hannun yakaka , wacce duk take a ruɗe a gigice , cikin rasa gane takamaimai a yanayin da take ciki , "
   ki saita tafiyar ki mai kyau kin san ta gaban a ɗakin haihuwar zamu zo mu wuce  , samy baby tace da ita haka lokacin da suke barin ɗakin ,"
  
    Ta gaban ɗakin haihuwa suka wuce da ya kawo su har gaban Falmata wacce take zaune jugum har lokacin idanun ta kafe guri ɗaya ," duk jikin ta yayi sanyi haka kawai take jin bugun zuciyar ta na sauyawa tare da tsikar jikin ta da take ta tashi akai akai , kwalla na taruwa a gurbin idanun ta ,

   Da hannu Yakaka ta toshe bakin ta domin hana kukan da take yi fitowa sarari yayin da ta runtse idanun ta gam ,  da taimakon hannun ta da samy baby ta matse tsam suka wuce ta gaban falmata ,
    Wucewar su ya zo dai-dai da zubowar ƙwallar idanun Falmata , sannan kunnen ta na jiyo mata tamkar takun kafafun Yakaka suna nisa da ita ,"

    Yakaka ki fito na gan ki

   ta furta a sarari , tana mai saita idanun ta inda kamar take jiyo takun kafar Yakakar

Sun kusa fita a kan doguwar hanyar suka tsinkayo kukan jaririyar da ya karaɗe wajen ,
     Chak yakaka ta tsaya ,
A sarari ta furta MAMA , tana mai waigawa da sauri , daga inda take tana hango jaririyar a naɗe cikin wani ɗan kyakyawan baby pink ɗin mayafin da aka naɗo ta ciki , sai wutsil wutsil take da hannu , ga alama hakurin ta ya ƙare ,tana neman abincin ta

idanun ta ta sauke akan Falmata wacce ta kafe hanyar da suke da ido , idan ba gizo idanun ta ke yi ba tana iya hango kyallin hawaye a idanun falmata ,

Wani abu ta ji ya yanki zuciyar ta , cikin ta ya ƙarta , ta ji kamar ta zura da gudu , ta rungumi waɗannan bayin Allah guda biyu da take shirin bari cikin maraici ,"

   bata yi aune ba ta ji samy baby ta fusgi hannun ta lokacin da ake shigewa da babyn hanyar ɗakin da aka bata , Falmata tana mai juyar da kan ta inda take jiyo tashin kukan jaririyar da take jiyo shi da wani yanayi mai girma da yake huda zuciyar ta yana taɓo ƙasan ran ta,"

Da wata irin dusashiyar muryar da kuka yaci karfin ta take kiran sunayen su su biyu lokacin da samy baby take jaan hannun ta zuwa gurin motar ta ,"

  FALMATA , MAMA ,

Tana zuwa ta buɗe mata gidan baya da taimakon ta ta shiga , ta zagayo ta buɗe mazaunin direba ta shiga , tana jin yadda tata zuciyar ma take yin rauni da matsanancin tausayin rayukan da yake lulluɓe ta ,tana tuhumar kan ta Anya Anya kuwa ita SAMIRA ta kyauta ???

Da gudu ta bar hsrabar asibitin ta fito kan babban titi , ta miƙa hanya sosai ta nufi kwadaben barin gari , kasantuwar daman da shirin ta tsaf , sai kawai ta ɗaɗɗaga gilasai lokacin da ta hau kan babban titin da ya nausa ya nufi wajen gari , sashi na ran ta na ƙarfafar ta akan ƙudirin ta ,

a hankali yakaka ta sauke hijabin da ta ja ta rufe fuskar ta baki ɗaya da shi ta ɗaura jajayen idanun ta da suka rine suka kumbura hatta fuskar ta tasa ta saita ganin ta akan titi tana kallon manya bishiyoyi da ƙananun dazuzzukan da suke kusa da gari ,"

zuciyar ta na wani irin ƙuna , ƙuna mai tsanani , tana jin ta empty , tana jin ta kamar tana kan guguwa tana walagigi da ita tana jin tamkar ta rasa kome da kowa , tana jin tamkar tayi KUSKURE MAFI GIRMA A RAYUWAR TA .!

A hankali ta maida kan ta jikin tagar motar ta kwantar tare da runtse idanun ta , zuciyar ta na dawo mata da hoton Halin da ta bar FALMATA DA MAMA a ciki , kunnuwan ta na amsa kuwwar kukan JARIRIYAR TA ...

WAI
    Wai
       Wai

Assalamu Alaykum kowa da kowa , ina gaishe ku tare da fatan Alheri , nasan kun yi dogon jira na tsawon sati biyu cif yau ' da fatan zaku dunga min uzuri , domin da ace ɗaya daga cikin ku ya san tarin aiyukan dake jibge akai na wallahi da babu mai yin ƙorafin rashin ganin cigaba akai akai ,

duk da haka zan ji daɗi idan ku ka cigaba da min uziri , ɗan adam a koyaushe yana buƙatar ɗaga ƙafa tare da bada dama !!

  Nagode kwarai da yadda ku ke bibiyar rubutuna , tare da ku da taimakon ku rubutun har ya miƙa ya haka ,, ina fatan zaku cigaba da bibiya ta har mu cimma matsaya ,"

kofar shigar da ƙorafi ko gyara tare da ra'ayoyi a buɗe take a gare ku , kai tsaye zuwa gare ni , zan ji dadi kuma zan yi amfani da shawarwarin ku muddin bai saɓawa ainahin tubalin ginin labarin ba .

  Nagode !
  
      
   

   
     
[10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Mafari .....
( Hargitsin Rayuwa )


umm'muaz

27






Da sauri Doctor Hamza yake tafiya ," Amne na bin bayan sa , lokacin da suke kutsawa cikin asibitin , bayan sha da kyar da suka yi a cikin cinkoson ababen hawa da ya fara haɗuwa akan titi sakamakon kusantowar lokacin sallar juma'a ,"

Sai dai tun da ya dosa bakin ɗakin haihuwar taron mutanen da ya gani kama daga likitocin asibitin zuwa kan nurses da securities ya sa shi rage takun sa ,"

  Maganganun da ya ji suna faɗa cikin harshen turanci tare da kama sunan AMINA DILMARI shi yasa shi zabura ya kutsa tsakanin su ,
    What's happening/ Me yake faruwa ?
yace da su cikin wata irin muryar ,

  Calm down sir , Babban likitan da asibitin yake mallakin sa yace yana kamo kafaɗun doctor Hamza ,
Muje office muyi magana ,"  zame kafaɗun sa doctor Hamza yayi lokacin da yake fuskantar likitan ,
   Ina patient ɗina ? Yace da buɗaɗɗiyar murya , "
   Shiru likitan yayi ,"
  Wani irin bugu zuciyar Hamza take kamar zata fito waje ,"

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login