Showing 171001 words to 174000 words out of 411050 words
Chapter 58 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
here? Go back to your class now ,"
Ƙifin-ƙifin da ido yakaka take yi tana kallon sa , tare da wasa da bakin ɗan madaidaicin hijabin ta,
I say Go back to your class,!
Ya daka mata tsawar da ta firgita ta
Dariyar da mafi yawan yaran ajin suka kwashe da ita shi ya sa malamin mayar da hankalin sa gare su ,
Hey what's wrong with you class ?
Uncle she is our classmate , she's a new comer,
Wasu yara kusan su hudu suka haɗa baki wajen faɗi , suna cigaba da dilliƙar dariyar da tun shigowar yakaka suke son yin ta ,
Ya buɗe baki da nufin sake yin wata maganar shigowar malama Maryam ta katse shi ,
Ɗalibai suka miƙe domin gaishe ta ta dakatar da su ,suka koma suka zauna tana jefa musu tambaya cikin harshen larabci tace
Aina huwa ɗalib jadid Yakaka Gali ?
Da hannun su suka yi mata nuni da inda yakaka take zaune ta sunkui da kai idanun ta taf ƙwalla , tana jin yadda idanun malamin nan ke yawo akan ta da kallo mai ɗauke da ƙasƙanci ,
Ɗan takaitatcen bayani malama maryam tayiwa malamin nan akan yakaka a ƙarshe ta nemi alfarmar tana so tayi magana da yakaka a wajen class ,
Ya bata izni yana shaida mata shi ya gama da ajin ma , lokacin sa ya fita , sai na malamin darasin gaba ,
Da hausa malama maryam tayiwa yakaka tausasan kalamai tare da gabatar mata da kan ta a matsayin malamar ta da zata dunga koyar da ita inda ta nemi da ta jajirce akan duk wani ƙalubale da zata fuskanta a yayin neman ilmi , ta kuma dage ta buɗe kwakwalwar ta ya zama tana maida hankali tana koyon duk abunda ake koyar da ita , har ma tayi mata albishir a gaba idan ta dage ta iya karatu za'a mata chanjin aji zuwa na manya sa'annin ta , a ƙarshe kuma ta gargaɗe ta akan ko kusa kar ta bada ƙofar da yaran nan zasu raina ta , ta tsayar da karfe 7am na safe zuwa 8am a matsayin lokacin da zata dunga koyar da yakaka darussan da suke cikin yaren English , karfe 4pm zuwa 5pm kuma ta koyar da ita Arabic da littatafan addini ,
Godiya mai tarin yawa yakaka tayi mata tana share ƙwallar idon ta da hannuwan ta biyu ,
Kafin ta juya ta koma cikin ajin ƙarƙashin umarnin umarnin malama maryam !
Cikin kwanakin da suka biyo baya yakaka ta kafa naci ta ƙarfi da yaji so take ta ga tayi ilmi ," bata da wani lokaci sai na karatu ta tattara duk wasu al'amuran da suka shafi rayuwar ta na baya ajiye shi a waje guda cikin zuciya ta ta killace su gefe , da gaske so take ta yaƙi jahilci , so take ta ci gajiyar ilmi so take ta goge kalmar wawanci da aka mata laƙabi da shi , so take lokaci yayi saurin juyawa wanda zai zo mata da sauyi daga JAHILA ZUWA MALAMA .
Gidan malama Maryam bayan layin gidan samy baby ne , ɗan madaidaicin gida ne inda suke rayuwa ita da mijin ta da ƴaƴan su uku , babbar ƴar ta lubna zasu iya zuwa sa'anni da yakaka , sai maza biyu faruq da sadiq , a halin yanzu Lubna tana ss2 , faruq yana ss1 sai sadiq da yake jss3 , mahaifinsu ƙaramin ma'aikaci ne da yake aiki da wani company ,"
Rayuwar gidan Malama maryam abun sha'awa ce duba da yadda suke masu ƙaramin ƙarfi amma rayuwar su cike take da wadatar zuci , soyayya da shaƙuwa gami da tausayin juna a tsakanin iyayen da ƴaƴan su ya yawaita , da hakan ya zama abu mafi muhimmanci da ya haifar da ingantatciyar tarbiyya a wajen ƴaƴan su ,
tare da taimakon tsayayyar uwa da suka samu , malama maryam mace ce wacce ilmin addini ya wadace ta , take kuma aiki da shi, a yanzu matakin karatun ta degree ne a fanni Arabic And Islamic Studies , sai dai mai fadadawa tare da zurfafawa cikin neman ilmi ce musamman ma na addini, a bangaren bokon ma ba baya bace ,
Yanayin ɗabi'un ta su ke sanya take birge duk wasu mutanen da suka mu'amalance ta , komen ta cikin tsari da nutsuwa take yin sa , bayan wadatatciyar tsaftar da ta bayyana kan ta agare ta a duk inda ta kasance ,
A tun ganin farko da Malama Maryam tayiwa Yakaka yadda ta tarar yara na yi mata dariya , ta ji tausayin yarinyar ya tsirga mata , ta san babu shakka wani shamaƙi mai girma ne ya tauye yarinyar ya hana ta samun ilmi akan kari , dan haka ta ƙudiri aniyar jan ta a jiki , ta yadda zata tunga taimaka mata tare da ƙarfafa mata akan harkar karatu ,
Ganin suna kaiwa har kusan magariba kafin su dawo gida idan ta tsaya yiwa yakaka lesson saboda nisan dake tsakanin makarantar da unguwar su , yasa ta cewa yakaka su dunga komawa gida tare idan kowaccen su ta je gida tayi sallah ta ci abinci , sai yakaka ta zo har gidan ta suyi lesson ɗin , wanda lokacin da take ɗauka tana yi mata lesson ɗin ma ya zarce awa ɗayan da makarantar ta sharɗanta mata ,
Sannu sannu saboda nacin karatu irin na yakaka da kuma samun fuska da tayi wajen malama maryam da take kira ,"anty," wacce ta sake mata sosai babu tsangwama ko kyara a yayin da take koyar da ita , ya sa har ranakun da babu makaranta ma yakaka zuwa take su ɗauki lokaci ana mata lesson ko na arabi ko na boko , wanda malama maryam ta lura yakakar tafi kafa naci akan na bokon tamkar dai tana da wani lulluɓaɓɓen burin da take son cikawa ta hanyar karatun bokon , babu laifi ƙwaƙwalwar yakaka tana da saurin fahimta hakan ya sa take jin daɗin koyar da ita ,
A hankali sabo ya fara shiga tsakanin yakaka da lubna wacce take yarinya mai tsananin wayo , hankali da manyance , cikin abunda bai fi sati uku ba da fara zuwan yakaka gidan su ƙawance ya ƙullu tsakanin su kasancewar halin su na nacin karatu da ya zo ɗaya , saboda lubna mai naci da ƙwazon karatu ce duk kuwa da cewa makaranta mai sauƙin kuɗi suke karatu ita da ƙannen ta , amma saboda kaifin ƙwaƙwalwar su , da kuma tsayuwar iyayen su akan fannin karatun su ya sa ko yaran da suke karatu a shararrun makarantu kuɗi baza su fi su ilmi ba ,"
Nacin karatu biyu ta haɗu dan haka bayan lesson ɗin malama maryam , lubna ma ta na koyawa yakaka wasu abubuwan da suke ma sunfi matakin karatun ta , a cewar lubna lokacin da yakakar zata kai matakin ta riga ta koya baza ta ji wahalar karatu ba ,
A wani yammaci lubna da yakakar suna zaune kan ƴar darduma a tsakar gida bayan lubna ta gama koya mata karatu , suna ƴar hirar su kafin malama maryam ta gama ƴan aikace-aikacen da take yi a ɗakin baban su ,
Lubna ta dubi yakaka wacce ta duƙufa tana kwafar rubutu daga jikin textbook ɗin ta ,
Yakaka ku ƴan wanne gari ne ? Naga zane a fuskar ki , kuma hausar ki ma wata iri ?
Ba tare da ta ɗago ba tace
Ni ƴar maiduguri ce !
Su maman ku da ƴan uwan ku duk suna maiduguri ne , ? Kin ce nan da antyn ki kike zaune ,
Tsam yakaka tayi ta bar rubutun da take ,"
Ganin shirun ta ya ɗauki lokaci ya sa malama maryam fitowa daga ɗaki da duk hirarrakin nasu daman a kunnen ta yake ,
Lubna tashi maza ki ɗora girki , yakaka kawo textbooks ɗin ki mu fara karatu ,
Babu kuzari tare da walwala a gare ta suka yi karatun suka gama da bata wani fahimta ba ko kusa , da malama maryam ta lura da kyau ma sai ta ga taruwar hawaye a gurbin idon yakakar lokacin da suke yin sallama zata tafi gida , bata ko jira rakiyar lubna da take raka ta kofar gida ba , tayi tafiyar ta ,
Tana fita malama maryam ta ƙira lubna ta zaunar da ita tayi mata faɗa sosai akan bincikar mutum game da abunda ya shafi rayuwar sa kai tsaye ba tare da shi wannan mutumin shi yayi ra'ayin kan sa , ya bata labari ba,
Nan tayi ta ba wa mamar ta hakuri tace baza ta sake ba, malama maryam tace ita ba ita zata bawa hakuri ba , yakaka zata ba wa ,"
nan tayi alƙawarin gobe idan yakaka ta zo zata bata haƙuri ,
Tun a hanya yakaka take kuka shaɓe shaɓe da hawaye har ta ƙarasa gida , tana shiga kai tsaye ta wuce samy baby tare da ƙawayen ta da suke baje a falo suna hirar su , kowacce ta bararraje kai ba ɗankwali sai tilin izgar roba da aka yi musu kitso da shi a ka ,
Chan lungun gado ta samu ta Zauna gami da haɗa kan ta da jikin gadon ta fashe da kuka me fidda sauti , kukan tausayin rayuwar da ta bari a baya , kukan ƙewa da famuwar ciwon da ke binne a ƙasan ran ta , kukan tunowa da iyayen ta , ƴan uwan ta ,garin ta , asalin ta , kukan rashin kowa na ta da tayi ,
Yaks kukan me kike haka ? Cewa nake yanzu lokacin kuka ya wuce a wajen ki ? Ashe har yanzu baki san cewa kuka baya maganin kome ba ? Baya sawa bare ya hana ?
Ko kuwa wani abun malamar ta ki tayi miki yanzu na je na ci mata mutunci ? Ki min magana mana ?
Idanun ta jazur ta ɗago kai , anty samy na tuno da su mama , baba , falmata da baby mama , bani da kowa anty samy , ni bani da kowa !
Da wata irin murya mai ɗauke da tausayi , samy baby tace ,
Kina da ni yaks , ni zan cike miki gurbin su , har zuwa lokacin da zaki koma musu ,
Wasu sabbin hawaye ne suka zubowa yakaka ,
Falmata fa ? Waye zai zama madadi na a wajen ta ? Falmata bata da kowa ita ma idan gidan su rahima suka gaji suka kore ta ina zata je ita da baby mama ? Anty samy ina son komawa na zo da su ,!
Babu wanda zai kore su a gidan su doctor , doctor da baban sa mutanen kirki ne , ki kwantar da hankalin ki , ba yanzu bane lokacin da ya kamata ki ɗauki nawin su lokacin na nan zuwa kin ji ko ?
Naji anty samy ,
Yauwa ko ke fa ? Yakaka matar Yarima ta furta hakan tana juyawa ga barin ɗakin ,
Da wani irin kallo yakaka ta bita ,
Yarima
Ta maimaita !
****
Kwanakin kammaluwar aikin Biyamuradi Youssouf Tare da komawa ƙasar sa suna sake kusantowa , aiki yana sake zafafa a gare su , inda cikin ƙasa da wata ɗaya aka samu asarar fiye da sojoji hamsin cikin rundunar sa , wanda hakan ko kusa ba abu ne mai dadi ba wajen su da ma gwamnatin ƙasar su baki ɗaya , duk kuwa da cewa aikin soja daman ya gaji haka , sadauƙarwa ne a bakin rayukan su ,
Dan haka duk yadda ya so ya samu damar zuwa sake ganin ɗiyar sa abu ya gagara dole ya haƙure har zuwa nan da kwanaki goma da wa'adin su yake ƙarewa ,
Baby mama sai girma take tana daɗa wayo , har ta wuce kwanaki arba'in tana neman cika watanni biyu , kome ƙin ka da jariri idan ka ga baby mama sai ta burge ka , ka ji kana son ɗaukar ta , idan kuwa ka ɗauke ta ji zaka yi ina ma a baka ita , ina ma ƴar ka ce ? Yarinya ce mai tsananin ruwan kyau bayan kyaun kan sa da take da shi , ƴar bul-bul da ita fara tas gwanin sha'awa madarar jariran da ake bata ta karbe ta ba'a ce jaririyar da ta barranta da shan nonon uwa bace ba ,
Bugu da ƙari kulawa da lelen da Falmata take yi mata domin duk da kasancewar falmata makauniya , tsafta yana daga halittar ta ce , dan haka ko yaya ta ji wani yanayi da bai gamsar da ita ba a tare da baby mama , take zata tuɓe ta ta goge mata jiki da wiper , ko ruwan ɗumi da tawul ta sauya mata diaper da kaya , bayan wanka sau biyu da hajja mai wurya take mata safe da yamma ," dan haka koyaushe baby mama cikin ƙamshi take da wankakkun kaya tsaf-tsaf ,
So da ƙaunar baby mama a bayan kowacce daƙiƙa sake ninkuwa yake cikin ran falmata , ta ɗauki duk wani so ƙauna da tausayi na duk wasu mutanen da ta taɓa so a rayuwar ta rashin su ya sa ta juye su akan ƴar jaririyar , tamkar ran ta aka taɓa haka take ji idan tace 'uhun' da sautin kuka ,
bata taɓa gajiyawa da hidimar baby mama , ta kan manta da yunwar cikin ta ko ƙishirwa idan ta shagaltu cikin tarairayar ta , son baby mama haɗe yake da bugun zuciyar falmata !
Waƙoƙi iri iri take rera mata da ƴar daddaɗar muryar ta cikin yaren su , sai kuwa ƴar jaririyar tayi luf , ƙulus a kwance tana kallon fuskar falmata da tunda ta fara kallon abubuwa ta himmantu gurin tsare fuskar falmatan da idanun ta a duk lokacin da take farke , ga alama bada jimawa ba zata haddace kamannin ta tare da ɗaukar yanayin ɗumin jikin ta , ta kuma gane warin jikin uwar goyon ta da ta buɗi ido tun ranar farko ta gan ta a matsayin UWA a gare ta ,"
******
Duk abunda aka sanyawa lokaci aka zana iyakar sa to fa babu shakka zai zo ya wuce tamkar da ɗai ba'a taɓa fara farkon sa ba ,
Yau shabiyu ga watan goma sha biyu ita tazo dai-dai da ranar kammaluwar aikin tawagar rundunar sojojin niger da suka kawo tallafi wurin yakar ƴan tawayen Boko Haram zuwa cikin yankin nigeria ta kan boda inda yankunan biyu suka haɗu na niger da nigeria ,
ƙarƙashin jagorancin Colonel Youssouf Abdul-Azizou Baskore , a kuma yau gwamnatin ƙasar su ta bada umarnin su fara janyewa daga filin daga inda waɗanda aka turo su maye gurbin su zasu samu isowa bakin dagar a yau , ' dan haka baki ɗayan sojojin gurin idan ka dubi fuskokin su a yalwace suke da fara'a , inda dayawa daga cikin su suke ta ihu da wasanni a tsakiyar dajin domin bayyana murnar su a fili kan komawar da zasu yi ƙasar su cikin dangi da iyalan su , bayan kwashe fiye da tsawan watanni goma sha biyu da suka yi cikin daji ,
Colonel Youssouf ya bi jerin ƴan uwan sa soji wajen bayyana farin cikin sa bisa ga wannan nasarar da suka samu na tsallake hare-haren ƴan tawayen boko haram ɗin da suka sha far musu , da kuma nasarorin da suka samu wajen fatattakar ƴan tawayen boko haram ɗin ta hanyar kashe wasu tare da kama wasu da dama , hakan a gare su babban nasara ne da dukkanin su suke sanya samun ƙarin girman matsayi daga gwamnatin ƙasar su ,
Gefe guda kuma zuciyar sa cike taf da murnar sake ganin ɗiyar sa da zai yi a yau , sosai ya zaƙu yake kuma ɗora idanun sa akan fuskar ta , dan haka duk wani abunda yake cikin ƙuzari da karsashi yake yin sa ,
Sha biyun rana tawagar sojin da zasu karbi aiki suka iso ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba bayan musayar gaisuwa da wasu bayanai na sirri irin na tsaro da ya shiga tsakanin manyan sojojin gurin da zasu tafi da sabbin da zasu maye gurbin su ,
Motocin da suka kawo sabbin sojin suka fara juyawa da tawagar masu komawa inda zasu ajiye su a babban barikin garin maiduguri zuwa gobe da zasu wuce ƙasar su ta jirgi da zai tashi ta abuja !
Biyamuradi Youssouf bai jira rana tayi sanyi ba , da isar su barikin maiduguri , wanka kawai yayi ya sauya kayan sa daga uniform ɗin soji ,
Ɗaya daga cikin direbobin su ya ja sa zuwa unguwar da ƴar sa take ,
Ƙarfe ɗaya na rana ta gota suka isa gidan nan ya tadda prof tare da wasu baƙin sa ,dan haka ya jira su har suka gama ganawa sannan ya shiga falon ,
Bayan gaisuwa da suka yi prof bai bari ya ɗora kome ba yace bari suyi sallah su ci abinci ,
Bayan sun ɗan taɓa abincin da ba sosai Biyamuradi Youssouf ya ci ba ,
Prof ya tattara hankalin sa ga Youssouf yana saurarar sa inda yake sanar da shi ,
Yana so gobe ya zo ya ɗauki ɗiyar sa saboda a goben yake son komawa ƙasar su domin aikin sa ya kammala ,'
Shiru prof yayi yana ɗan nazari
yayin da zuciyar yarima ta cika taf da taraddadi tare da fatan kar wata matsala ta taso domin zuwa yanzu ya gama tsara kome game da makomar rikon ƴar sa a tare da shi , ya gama tsara inda zai kai ta tayi rayuwa irin wacce yake so ƙarƙashin inuwar kulawar sa da kuma kariyar sa ,
dan haka baya jin akwai wani abunda ya isa ya hana shi ɗauke ɗiyar sa daga hannun waɗannan mutanen da bai kai ga sanin su ba basu kuma da kowacce irin alaƙa da shi da har zai iya barin jinin sa tare da su , ya shirya tsaf ko