Showing 123001 words to 126000 words out of 411050 words

Chapter 42 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14395

bayyana saman fuskar sa , wanne irin aiki zasu sa ƴar mutane da ciki ?

Har ya taka da nufin shiga gidan sai kuma ya jaa ya tsaya ,
   Ina rahima ?

Ya tambaye su ,"

Cikin rashin jin daɗin yadda falmata ta bayyana masa laifin ƴan uwan sa , yakaka ta amsa a sanyaye

Tun jiya ban gan ta ba yaya !
Baice kome ba ya zaro wayar sa daga aljihu ya shiga neman layin rahima ,"

Bugu ɗaya ta ɗauka

Hello big bro ina kwana ?

Rahima kina ina kizo yanzu ina kofar sashin ku ,"

   Toh ," ta amsa

Ba'a cika mintuna huɗu ba sai ga ta ta fito daga cikin gidan ,"

   Gani big bro ," ta furta hakan tana mai washewa yakaka haƙora gami da kashe ido ɗaya irin na shakiyanci ,"

   Ki je da su ɗakin su suyi wanka su shirya ku zo tare ke da su ," ya bata umarni fuskar sa babu alamun wasa ,"

    Toh ta amsa tana mamakin ɗakin nasu kuma zata raka su ? Kai big bro yana ji da baƙin nan nasa anya anya anya kuwa ,"  tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yace ,"
    Kice ga duk wanda ya nemi hana su yin abun da nace , umarnina ne a bar su suyi wanka su shirya ," nan ta fahimci akwai abunda ya faru ƙila hana su wanka aka yi , to wa ya hana su ?

    Tana shiga ɗakin ta samu amsar tambayar ta domin suna sanyo kafa cikin ɗakin sofi wacce take rangaɗa kwalliya tace ,"
     Kai kai ku koma , wai meye kuke mana sintiri kalen ku baɗa mana ƙwarƙwata ?? Daga kun zo wuri sai kun sauya kalan ƙanshin sa ,"cikin ran ta tana ji haka kawai ta tsani yaran ," ( karfin hali )

Da hannu biyu rahima ta dafe bakin ta kafin ta ce
       lalala anty sofi baƙin big bro ne fa kuma ma daƙin su ne ," yanzu ma shi yace na rako su suyi wanka su chanja kayan su ,"
       Baƙin ƴan gudun hijira ko dai bakin doctor ?
   Wallahi baƙin sa ne shi ya kawo su ,"
Yakaka ku shiga kuyi wanka , ba kowa a bathroom ɗin ko ? Ta furta hakan tare da ɗan kwankwasa kofar banɗakin ,"

 

Falmata shiga ki fara yi ta furta hakan tana mai kaucewa mugun kallon da sofi take watsa musu ,"


    Wata purple and black ɗin atamfa yakaka ta cirowa falmata daga cikin kayan su , sabuwa ce dal falmatan bata ko taɓa sawa ba , ta miƙa mata banɗakin lokacin da tace ta gama wanka , ita kuma ta fiddo wani pink colour ɗin yadi ɗinkin doguwar riga ta riƙe a hannun ta ,

Tsaf falmata ta fito cikin kayan da ɗinkin sun bala'in karɓar ta dinkin riga da siket ne na yayi wanda rahima ta zaɓar mata style ɗin ya zauna ɗas a kyakyawan jikin ta , baki ɗayan ƴan matan ɗakin suka bita da kallo lokacin da take wuce su tana nufar inda ta ji muryar rahima ta ƙira ta ,"

",surar jikin fatima abar kallo ce

  shine abun da rahima ta ambata aran ta lokacin da ta lura da kallon sake bakin da wayayyun ƴan matan suka bita da shi

   Gyara mata ɗaurin ɗankwalin rahima tayi gami da rufa mata bakin mayafin akan kafaɗun ta wanda ta zame daga jikin ta  ,"

Cikin ran ta tana dariyar shirun da ɗakin ya ɗauka ," a hankali ta furta
    Duk ta sumar da su ,!

a gurguje yakaka ta yi wankan ta shirya ta fito , ta sanya ɗan madaidaicin hijabin ta fari mai hannu akan doguwar rigar da ɗankwalin ta fuskar ta fayau ko mai babu ,

Suka bar ɗakin ƙarƙashin rakiyar dogon tsakin da sofi ta bisu da shi ," a sarari rahima ta furta kya ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa , big bro dai kwalelen ki , ko dan wannan mugun halin naki ma zai sa ya tsane ki ,"aikin banza ,

  Yana hango su ya nufi motar sa ya buɗe ya shiga ,"

  Tare da rahima suka ƙaraso jikin motar ,"
  Ta sunkuyo saitin sa ,
  Big bro na cika aiki na , ?
Baki cika ba rahima , ki shigo mu tafi ,
   Ɗan jimm tayi , " bata son fitar domin tare da ƙawayen ta take suna shirye shiryen yadda anjima zasu tsantsare a wurin sisters day ,"
   Shikenan je ki abin ki tunda baki son fitar ,"
   Ta marairaice murya Big bro kayi hakuri ƙawayena zasu je nayi musu walakanci idan na tafi na bar su ,"
   Toh rahima mai jama'a , agaida kawayen ,!
      Ya furta haka yana tayar da motar sa bayan yakaka ta shiga gaba ta zauna rahima ta kamawa falmata ta shiga baya ,"

   Kai tsaye ya nufi tata saloons da bashi da wani nisa sosai da gidan su ,"

Tun da suka tsaya gaban shagon bugun zuciyar yakaka ya sauya ," mikin da yake ciwo cikin ran ta ya dawo ɗanye , hotunan al'amuran da suka gudana a tsakanin su ya fara dawo mata , gata da soyayyar da ya gwada mata na ɗan lokaci suka bijiro mata son da take mishi ya yunƙuro da wani irin ƙarfin da ya sauya bugun zuciyar ta da har hakan ya jawo abun da ke cikin ta ya motsa da ƙarfi ,"

Har abada baza ta so wani namiji makancin son da take masa ba ita ta sani ta kuma haƙiƙance da hakan ," shi ɗin na daban ne cikin rayuwar ta kamar yadda son shi yake da wani irin ɗanɗano na daban a cikin ran ta ," wanda yake bata nishaɗi tare da kashe mata jiki a lokaci guda ,"

A hankali ta ɗaga kai tana kallon ƙaton board ɗin da yake kafe a gaba kaɗan da inda suka tsaya da motar su a gaban shagon ," karon farko da tayi ƙoƙarin haɗa baki ,"tunda aka fara koyar da su
      A hankali leɓen bakin ta suka motsa
        
         TA-TA

sunan wajen da yake ɗaya daga cikin wuraren da baza ta manta su ba a tarihin soyayyar su , wurin da ya sha gwada mata ƙaunar sa batare da jin nawin mutanen da suke kallon su ba , a gaban su ya nuna ita ɗin abar son shi ce abar ƙaunar sa wacce ya zaɓa ,"

kafin zuwa lokacin da kome ya sauya , kome kuma ya ƙare ya tsaya ƙem har zuwa lokacin da komen ya ruguje ,

rugujewar da ta samar da mummunan rauni a zuciya da gangar jikin ta , sai dai tana ji a jikin ta zuciyar ta kuma tana faɗa mata , komen bai ƙare ba kuma kome zai sabunta kan sa a watarana ,

sai dai abunda ta kasa samun tabbaci akan sa shine yau ne ko gobe ne komen zai dawo ?bata da tabbacin dawowar sa alhalin kuma shine komen da zuciyar ta ke ɓida a kowanne daƙiƙa bayan daƙiƙa .

Wani irin farin ciki yaji lokacin da ya fahimci ta iya karanta sunan wurin da ya kawo su ," idan hakane tabbas kwakwalar ta mai saurin ɗaukar karatu ce , ƙwarai zasu shirya shi da ita , wata rana kuma zsi yi alfahari da ita , da alama ƴaƴan sa zasu samu haziƙar uwa ,"
     Yes sunan wurin kenan
   Tata saloons ," ya furta mata hakan da murmushi ɗaure kan laɓɓan sa ,

Da ido ta bishi tana mai jin haushin katse mata ɗan daddaɗan yanayin shauƙin da ta tsinci kan ta a ciki na tunanini abun son ta ,

Rufe motar suka yi bayan sun sun fiffito , yakaka ta kamo hannun falmata ta riƙe cikin nata , ,"

Bissmillah muje
   Yace da su ," yana yin gaba ,"

Kamar yadda suka tsanmata gurin akwai mutane ,amma kasantuwar akwai wadatar ma'aikata nan take biyu daga cikin ma'aikatan suka taso taryar su , ɗaya daga cikin ma ta gane yakaka domin ta sha yi mata gyaran jiki ,"
    Madam sannu da zuwa ta furta hakan tana mai yiwa yakaka murmushin sanayya ,
    Ɗan yaƙe yakaka tayi a ranta tana furta ,'na shiga uku Allah ya sa kar su nuna sun sanni ,"

   Madam kin kwana biyu baki zo ba , ma'aikaciyar ta furta haka daidai lokacin da take basu wurin zama ,"
Shiru yakaka tayi tana satar kallon doctor hamza wanda shi kuma hankalin sa ya tafi ga ɗayar ma'aikaciyar inda yake faɗa mata yana son ganin ainahin ita shugabar su ,"
    Cikin girmamawa tace bari ta shiga ta sanar mata ,"

Ƴar wata ƙofar gilashi da take daga gefe a cikin shagon nan ma'aikaciyar ta shiga ,' bata ɗauki lokaci ba ta fito tace zai iya shiga wurin shugabar ta su ,"

   A cikin mutunci suka gaisa da hajiya Ruma'yassa'u,  nan ya shaida mata kaya yake nema ready made na ƴan mata ,"

    Ta tabbatar masa da suna da kaya masu kyau da inganci domin a jiya ma wasu ɗinkakkun kayan suka iso , dan haka sai wanda ya zaɓa tsakanin atamfa , leshi , shadda , yadi da sauran nau'ikan suturun mata , kawai abun buƙatar a zo da magnitude ɗin mai kayan ko kuwa shi kan sa , ya sanar da ita tare suke da waɗanda zasu sa kayan ," nan tace a shigo da su ,

    Kallon sani take yiwa fuskar yakaka amma kasantuwar its ƴat kasuwa ce da take chuɗanya da mutane da dama ssi ta watsar da laluben inda ta san fuskar yarinyar , ta miƙe gami da cewa su biyo ta su da ma'aikaciya ɗaya dake tare da su ,"

   Har ta ɗsn yi taku ta jiyo da murmushin nan nata mai haiba tana gyara mayafin kan ta tace ,"  akwai iyakacin adadin na kuɗin da keke so su ɗauka ne ?? Kuma shiga nawa zasu ɗauka ,"
    Su ɗauki duk wanda suke so kuma kika ga ya dace da kowaccen su , " ki zaɓa musu ," shiga uku uku ,"

   Toh shikenan ranka ya dade ,"

Ta cikin shagon suka ɓulla ta wata ƴar kofa zuwa wani kawatatcen shago mai zaman kan sa , ta ko'ina kayayyaki ne wasu a rarrataye wasu a cikin closets ɗin gilashi , kaya dai na kece raini tare da ɗaukar hankalin mai kallon su ,

Wurin zama ta basu akan wata doguwar kujera , bayan ta umarci ma'aikaciyar da ta gwada mata su mataki-mataki na jikin su , kai tsaye ta nufi faffaɗar closets ɗin ta shiga zaro wasu tsantsara tsantsaran lesuka masu ƙananun huji duk jikin su da mabanbantan kaloli da aka yiwa  ɗinkin wasu kyawawan dogayen riguna , buɗaɗɗu da tsukakku , gajerun hannu da dogaye ,

Tana daga inda take ta tambayi  size ɗin su nan ma'aikaciyar ta sanar da ita ,"  a take ta zaro huɗu daga cikin lesukan masu size ɗin da aka faɗa mata ,"
        Bayan nazarin da tayi a matsayin ta na cikakkiyar malamar kwalliya wacce kuma ta san takan kwalliya da ado , ta zaɓarwa yakaka wata buɗaɗɗiyar doguwar riga mai rufaffen wuya turquoise color, ( ban San sunan launin a hausa ba  ) mai adon wasu siraran zare silver ,

Falmata kuma ta zaɓar mata ita ma wata doguwar riga da ta tsuke tum daga sama har zuwa cinyoyin ta ta ɓuɗe ta kasa , mai buɗaɗɗen wuya scarlet color, " da adon golden. 

Kowaccen su dai-dai da tsawo da jikin ta , sannan ta zaɓar musu wasu atamfofi da aka yiwa ɗinkin riga da siraran siket sai dai ita yakaka tata rigar har kusan guiwar ta take yayin da ta falmata ta tsaya iyakar cinya ,  ta  yakaka background din ta dark red pattern din kuma aka yi da salmon and moss color , ta Falmata kuma background din fari ne pattern din kuma freesh grass and carnation color, 

Sai yadika da suka ɗauka su duk biyu iri ɗaya see grean  da aka yiwa ɗinkin buba da single zane ,'

Iyakar kyau kayan sun yi kyau , domin shi da kan sa doctor hamza ya yaba ya kuma ji daɗin gani zaɓin da hajiya ruma tayi musu , dan haka bai ji ƙyashi ba ko kadan ya lale makudan kuɗaɗen ya biya kuɗin kayan da ko a mafarki su yakaka basu taɓa hararo kan su a cikin irin su ba ," aka haɗa musu kayan har da gyalalluka bibbiyu da takalma masu kyau kafa biyu da ya sake saya musu aka sanya musu cikin babbar ledar mai ɗauke da tambarin TATA SALONS ,

Har zasu tafi ma'aikaciyar nan da ta gane yakaka tace
  madam yau ba gyaran jiki ne da gyaran kai ??
    Cikin tsanaki doctor hamza ya mayar da ganin sa kan yakaka wacce ta langwaɓe kai tana kifkifta ido duk wasu alamun rashin gaskiya sun bayyana a fuskar ta ,"

  Bai hango kome ba bai kuma fahimci  komen ba illah hasashen sa ya bashi tabbacin tana so ayi mata gyaran jikin ita ma ,'bisa ga kallon da take masa mai kama da roƙo ," ,

Ayi musu gyaran jikin da wankin kai amma kar ayi musu kwalliyar nan ni ban cika son ta ba ,"  yace da wacce ta nace sai ta fasa ƙwan yakaka ,"

    Toh yallabai

ta amsa tana mai shiga rudu ,

da tayi zaton wani ɗan uwan mijin yakakar ne kamar yadda suka yi zaton biyamuradi mijin yakaka ne , sai dai kuma kalaman wannan na yanzu ya sata wasi wasi da chanki-chankin wanne ne mijin tsakanin farin dogon kyakyawan bamarɗen mai cike da ginshiri da ƙasaita irin na saraki , " 

da kuma wannan matsakaicin mutumin wanda tarin nutsuwa da kamala gami da tsantsar ilmi suka bayyana kan su a tattare da shi ," ????? ( toh nima dai tambayar da nake yiwa masu karatu kenan ??? )

Gata dai ta gan ta har da ciki bayan tsawon watannin da suka yi rabo da ganin ta tabbas matar aure ce ,'

Tattara gulmammakin ta tayi ta adana su gefe suka fara goge tare da sumulmule jiki , daga kafafu har kan su yakaka da falmata ,"

Basu suka bar wajen ba sai misalin karfe uku na yamma, iya wankuwa sun wanku fuskar su har sheƙi take , babu wata kwalliya da aka musu a fuskokin su sai fa siraran lallen da aka tsantsara musu yiryir a ƴan hannayen su da ƙafafu karkashin umarnin hajiya ruma a zuwan tukuicin da tayi musu na cinikin da aka mata tare da karrama abokan ciniki irin nata ,"

Kyau kam sun yi shi ƙamshi kuma sai tashi yake a sassan jikin su , falmata jin ta take kamar mai yawo a gajimare saboda yadda iska yake ratsa kowanne sako na jikin ta , yakaka kuwa lumshe ido tayi akan hanyar su ta komawa gida tana tuno wani yanayi irin wannan a tsakanin ta da biyamuradi , da hakan yake sanya ta sakin murmushi lokaci-zuwa-lokaci saboda hotunan fuskar sa da suke ta gilmawa ta idanun zuciyar ta

Yayin da shi kuma doctor hamza yanayin da ya gan ta ciki ya sanya shi nishaɗi har shagala yake wurin satar kallon ta ya manta da tukin da yake yi ,'  sai fa idan motocin bayan sa sun matsa masa ham ,

Sun dawo sun tarar da gidan kamar yadda suka zata a cike danƙam motoci sai fita suke da ƴan matan da mata domin tayi party ,

Ganin cinkoson ya sanya doctor hamza sauke su daga bakin babbar kofar yace su shiga shi zai juya , su bar kayayyakin a cikin mota da daddare zai shigo musu da shi , su tabbatae sun samu wani wuri sun ɓuya daga idanun masu sanya su aiki ,

Duk da kusan kowa harkar gaban sa yake a farfajiyar wurin amma hakan bai hana falmata fahimtar yawan idanuwan jama'ah da yake yawo akan ta ba ta hanyar jin tsikar jikin ta na ta miƙewa , hakan ya sanya ta sake ƙanƙame hannun falmata

Wacce itama ta sunkui da kan ta cikin  jin nawin idanun mutane da ta gani a kan su ,

Tun da suka ratso wurin take bin su da kallon mamaki , tabbas sune toh me kuma ya kawo su yaks gidan bikin zainab ?? Wai daman ashe da yaks ta gudu wani wurin daɗi ta samu ya sanya ta ji ta shiru da a farko ta dunga zaton wahala zai dawo da su da kafafun su ," bata buƙatar a sanar da ita tabbas yakaka da falmata suna cikin kin daɗi domin kuwa ta ga sauyi a tattare da su a zahiri

," shegiya yaks farar mace alkyabbar mata kyakkyawar mace kadara ,' babbar haja da ba'a raba ta da masu tayin saya ," ta furta a zahiri ,"

Kafin ta daddage ta kwalla mata kira daga inda take tsaye a jikin motar ƙawar su

    Yaks Yaks Yaks ,

Chak suka tsaya daga ita har falmata kirjin su yana dakan sha tara ,"didif-didif-didifdif ,......!

Toh fah , ga mafari yanzu ya fara , ga kuma azumin wata mai alfarma watan ninka ibadu ya ƙarato ,!

Zan so na ƙara mana ko da page ɗaya ne kafin na rufe rubutun zuwa bayan ramadan insha Allah ,

menene ra'ayoyin ku ,?  Me kuma zaku ce ??  Nasan cikin shafin nan abubuwa da dama sun faru , a warware su mu tattauna , hakan tukuici ne agare ni ,

Wannan shafin nayi kyautar sa ga duk wasu ghost readers, masu tanɗe romon mafari ba tare da bada tukuici ba , ghost readers acigaba da gashi suya sai ranar da shafukan mafari suka Fara yi muku batan dabo 😂

Nagode muku baki daya!  MAFARI ......
( Hargitsin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login