Showing 63001 words to 66000 words out of 411050 words

Chapter 22 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14364

ɗan uwar ki wane ɗan iskan ne yace ki kawo min ƙanin ki nan ? Ko nace miki ina bukatar almajiri ne ? Oya kama hanyar ka kayi tafiyar ka kwa haɗu a mahaɗar ku kar na sake ganin ka a gidan nan ,"

Gaba ɗayan su sun firgita da tsawar da tayi musu musamman ma falmata wacce kalma korar da aka yi mata ta sanya ta jin ruwan hawaye ya fara taruwa a gurbin idanun ta ,"

Madam kiyi hakuri , shima na kawo shi ne ko akwai aikin da zai dunga yi miki ,?
        Aikin ubanki wannan ɗan tatsitsin yaron zai min ? ,"
    Kai tashi kayi naka guri nace ," ta furta hakan tana zazzarowa falmata ido ,wacce dirin muryar madam saly cikin faɗa duk ya bi ya diririta ta tare da dasa tsoron ta cikin ran ta anan take har ma ta ji ta fara nadamar zaɓar gidan ta a matsayin wurin mafakar ta ,

Cikin muryar kukan da ya bayyana kansa yakaka tace ,"

     Makaho ne madam dan Allah ki taimaka mana ki bamu wurin da zamu dunga kwana wallahi zan dunga yi miki aiki daga safe har dare koh baki biyani ba ni dai kawai ki taimake mu ni da ƙani na ki bamu wurin kwana ,?

Kallon hadarin kaji madam saly take yi ma ta ,"

    Yau ji min gantalallun yara ke yanzu ni ce zan baku masauki ke da musaƙin ƙanin ki ?? Dan uban ki yaks kin ga gida na yayi kama da masaukin baƙin ƴan gudun hijira ?? Ciki ma har da muskinai ? Ke ma ai kin sa wanan abun bazai yi yu bane "auren mage da ɓera " an faɗa miki nan gidan sarkin unguwa ne koh kuwa gidan mai gari ?? To bari kiji ni bani da wurin ajiye ke kan ki bare miskinin ƙanin ki , toh na ci uwar me da ku ??gayyar na ayya gayyar tsiya gayyar ƙwarƙwata da tsumma, dan aikin da kike min daga na ɗaga murya nayi cigiya zan samu madadin ki , dan haka tun wuri ki maida ƙanin ki inda kika ɗauko sa ,ki zo ki kama min aiki na , kina cin lokacin aiki kin kuma san dai doka ta ban yadda da asara ba ,"

Ɗan liti wanda tun shigowar su yake tsaye a gefe ya kafe yakaka da falmatan da idanu ,yana nazarin ɗan dirarren yaron mai ƴar kyakkyawar zagayayyar fuska da yakaka ta kira da kanin ta ," yayi charaf ya chafe zancen jin ana shirin korar masa hanyar samun abebaɗan arziki !

Haba haba madam saly tayaya arziki yana bin ki kina guje masa ," kuma ai a so kare har bindin sa !
     Ya furta hakan yana farfari da ido

A harzuƙe madam saly wacce ta koma daga bakin kofar ɗakin da ƴan matan ciki ke tattataro ƴan kayayyakin su suna fitowa ta juyo
,' waɗan nan ne hanyar arzikin liti bana son ƙazamar kalma," wai me kuke jira ne ?? Ta wurga tambayar ga yakaka wacce zuwa lokacin kuka take yif-yif suna durkushe cikin rana ,"

  Ke dai mutuniyar mu sanya labule ki ji bayani , kiji nufi na kar ki yanken hukunci baki ji hujja ta ba ,!"idan ban da abun ki ai Abun da ke ga amarya shi ta kan ba ango "  Ya furta hakan yana jan hannu madam saly wacce take wurga masa harara ,tamkar idanuwan ta zasu faɗo ,"

  Bayan shuɗewar mintoci sha biyar madam saly da ɗan liti suka dawo ,"

    Ke yaks na yadda ki zauna anan tare da su larki a ɗakin su , zasu ɗan matsa miki wajen kwana domin wannan babban ɗakin kulle sa zan yi , ƙanin naki kuma zai bi ɗan liti su dunga kwana tare idan ya so kullum da safe ya dunga zuwa nan yana min wanke-wanke kafin ya tafi barar sa ," daga yanzu bazan biya ki ko sisi ba domin zan dunga ciyar da ku sau uku a rana da ke da ƙanin naki ,idan kin yadda toh idan kuwa baki yadda ba sai a bi wani sarkin ,!
Ba tare da tunanin kome ba yakaka da falmata suka amince bayan sun bi ɗan liti da madam saly da doguwar godiya tare da addu'o'i ,

Toh sai ƙanin naki ya biyo ni yaga ɗakin kwanan koh ? duk da dai ba gani yake yi ba amma ya ɗan tattara wajen da zai sa ƴan haƙarƙarin sa ," ni ya ma sunan sa ne ??
   sunan sa kachalla !
    Ah kachallari ne toh tashi zo mu tafi mikon hannun ka ,"

Tare da rashin sakewa falmata ta jefa hannun ta cikin na ɗan liti , wanda ɗumi tare da laushin fatar hannun falmata tuɓus-tuɓus , suka nemi ruɗar da shi a karon farko ,"

Da ido yakaka ta raka su cikin ranta tana fatan Allah ya sa madam saly ta zamto gatan su ,!

Kichibus yagana suka yi ita da su falmata wacce ɗan liti ya matse mata hannu gam cikin nasa yana ɗan luguiguitawa , a ɗan fisge ta dube su tare da gaishe da ɗan liti sai dai kuma fuskar falmata da ta gani a fisge ya sanya ta sake waiwayowa da zabari sai dai bata ci nasarar sake kallon fuskar yaron ba sai bayan sa ',

Tana shigowa ta ci karo da yakaka cikin mamakin ganin ta a wurin aikin tare da alhinin abun da ya faru da su a daren jiya wanda duk a zaton ta har yanzu su yakaka suna asibitin ne ta kamo hannun yakaka ,
    Yakaka ya jikin falmata ??tana ina ? Ta samu sauki da fatan babu abun da ya same ta ??

Sai da yakaka ta ɗan hah-hanga ta ga babu kowa a cikin rumfar da suke saida burkutu wanda a halin yanzu take kan tattarawa tare da goge gujeru da teburan da masu saye ke zama ," tace
     Yagana jikin falmata da sauki , kuma a halin yanzu tana gidan nan mun taho tare , yagana dan Allah ki rufa mana asiri domin a saboda abun da ya so faruwa ga falnata jiya mun bar sansanin mu mun dawo nan gidan da zama sai dai a matsayin falmata namiji , zaki ganta cikin shigar maza da askakken kai tana amsa sunan kachalla , domin Allah kar ki faɗawa kowa ita mace ce kin ji ? Ki rufa mana asiri !

      Tare da maɗaukakin mamaki yagana take kallon ta ,
  falmata ta koma namiji kuma ??kuma kun dawo nan gidan da zama ? Anya yakaka wannan hanyar mai billewa da kyau ce ? Kin san fa gidan nan cike yake da ƴan iska da ma unguwar baki ɗaya , ke da kan ki hatsari ne kwanan ki cikin gidan nan kina dai ganin yadda da ƙyar muke kwatar kan mu a hannun ƴan iskan nan idan suka sha kunun madam saly , ni a ganina gwara mazan sansanin mu basa shan wannan ruwan da ke fitar da mutum a hankali ya sa hauka, ni dai idan har kin ɗauki shawara ta ku koma sansani duk lalacewar sa yafi nan ,

Yagana falmata tace baza ta koma ba , ta riga ta tsorata , sanin halin mazan gidan nan ya sa na ɗauki matakin mayar da falmata namiji domin kare ta daga idanun su ,"
    Katse ta yagana tayi ,"
   Toh idan kin kare falmata ke kuma fa ?? Bakya tsoron su cutar da ke ??
    Ɗan murmushi yakaka tayi ,"
   Zan iya sadaukar da kome nawa domin na bada kariya ga falmata , falmata miskiniya ce bata da kowa daga Allah sai ni ,"  ki mana addu'a kawai yagana kuma ki rufa mana asiri ,'
     Kallon ta yagana tayi na ƴan dakikai ,

shikenan dan ta ni kam baku da matsala koh cewa kika yi kar na nuna na san falmata  bazan nuna ba ,  me ma kika ce sabon sunan ta ??
    Kachallah
    Kachallah , ta maimaita
Suka haɗa ido gami da kwashewa da dariya , ga alama zuciyar yakaka ta samu ƴar nutsuwa a karon farko tun bayan barowar su garin su .

          Niamey Niger

Yau kwanakin su siyama da gnala goma sha huɗu wanda kuma a gobe ne suke da niyyar komawa maraɗi saboda hutun da ta ɗauka a wurin aikin ta gobe yake ƙarewa ,

Zaune suke a ɗakin ubboh wacce ta kama kan siyamar tana kitsewa kamar yadda ta saba yi mata tun siyamar tana ƙanƙanuwa ,har ɗan tasawar ta kafin a aurar da ubboh ,"

      Ho addah ke kouwa yaushe ne zaki bar mini kitson hittoɓe ? Haba mana adda baki ganin na girma da wannan kitson ??
     Ɗan murmushi ubboh tayi tana me kallon fuskar siyama da ta shagwaɓe fuskar ta ta jikin mudubi ,"
      Kauna ta kin kouwa san yadda kitson hittoɓe yake fidda kyauwou tare da cikar surar ki ?? Na kou jima ina faɗi miki babu kitson da ke haska ki yaa shi ina mai tabbatar miki akwai wani sirri cikin kitson ga ki riƙe shi da kyawou har gidan amren ki,"

Shiru siyama tayi domin ubboh ta fama mata ciwon da ke nuƙurƙusar ta cikin rayi ," da nazarin sauyin da ya bayyana akan fuskar ta ubboh ta tsaida kitson da ta fara yi ,"

     Ban san yauhe ne munka fara ƴar haka da ke ba kaunata ,?? Yauhe ne kin ka fara boye mini damuwar da ke a zuciyar ki ? Yanzu duniya da gaskiya siyama kina da ƴar uwa da ta fice ni ?? Tuno da kusancin da ya wanzu tsakanin mu tun tsawon lokacci shin kou kuowa dai matsayi na ya sauyu gare ki ?

  Juyowa siyama tayi ta fuskanci ubboh , fuskar ta da alamun rashin jin daɗin maganganun ubboh ,"

Kou kussa adda matsayin ki gareni wallah basshi sauyuowa , ke kou me zai sanya ki wagga irin tounani adda amm ??

   Shafar fuskar ta ubbo tayi ," cikin ranta ƙaunar siyama na sake linkuwa,

Tun zouwar ki nan wurina na fahimci kina tare da damuwa amma juyin duniya nayi da ke ki faɗi min me ke ad damun ki kin ki faɗi mini toh ƙaƙa kike so in yi da rayi na ? Shin kou kuwa dai a chan gida an ka bata miki rayi ??

     Ajiyar zuciya siyama tayi domin ta ga wannan ce damar da zata yi amfani da ita wurin fidda abun da ke boye cikin ran ta , sake marairaice fuska tare da shagwaɓe ta tayi bayan ta karya wuya ,"

    Adda amm ni kam ban san dalili guda wadda ya sa hamma youssouf ya ƙi jini na ba , tun tasowa ta nake hangen ƙiyayyar da ke mini cikin idanouwan sa
 
    Da sauri ubboh ta kai hannu ta ɗan make bakin siyamar , tare da maɗaukakin bacin rai akan fuskar ta tace ,"
    Wanne irin kalami kike haka ga ɗan ouwan ki siyama ? Shi youssouf ɗin ne basshi ƙamnar ki ? Ƙaƙa kin kai ga fahimtar hakan ,?  Ƙou kouwa shi da baki nay ya furta hakan gare ki ? yi samri ki sanar da ni ƙaƙa anka yi wagga mummunan tounani ya kai ga ɗarsuwa cikin rayin ki ?

  Hawayen da daman suna kurkusa sune suka samu dalilin ballowa da gudu akan kumatun siyama ," cikin ranta tana faɗin "ayi a ƙare yafi a bari sai gobe ,"

    Hamma youssouf bai ɗaouke ni matsayin kauna gare shi ba , har ya gaza boye hakan a gare shi Shi ɗai , sai da ta kai ya bayyana ga bayun masarauta agades , inda ya danganta ni da baƙuwa garai a gaba gare su ,"sun ka maishe ni marar muhimmanci ga har ta kai bayun sun nemi taka ni ,'

   Cikin takaicin jin abun da youssouf ɗin ya aikata ga ƴar lelen ta ubboh tace ,"
     Yi shirun ki kaunata ki kuma daina wagga mummuna tounani , youssouf yana dawouwa ya iske ni nan cikin gida na zan kuma yi masa magana , yo a rabe magirbin yakuwa ne da na rama ?? Bar ni da shi ,"
    Cikin sanyin murya da cikin ran ta ba haka ta so ba , tace
    Adda kar ki masa faɗa bissa dilili na bani son ko ƙaƙa ran sa ya baci a sanadiyya ta , bacin ran sa ba zaya dadaɗa mini ba ,"

      Cikin son fahimtar abun da ta hango tattare da siyamar ,"ubboh" tace
     Ke ko ƙauna ta faɗi min gaskiya ƙou kouwa dai son hamman naki kike ?? Kou amren dangin kike so ?

    sunkui da kan ta tayi a lokaci guda tana wani ɗan kyakkyawan murmushin da tun zowar ta ubboh take son ganin irin sa a fuskar ta , kamo haɓar ta tayi ta ɗago fuskar ta ,tana dariya tace
     "ni ƴar uwa nake gare ki bai kyautu ba ki boye min kome idan Allah ya yarda youssouf sai ya zama miji gare ki , ina bayan ameren ku ɗari cikin ɗari , ai ba domin lamurran sa da wagga ɗiyar buzouwa ya kankama ba ai da ba'a bawa dawa ba gida ba ta ƙoshi ba ," ki kauda wagga mummunan tounani naki , youssouf ɗan ouwan ki ne kuma zai zamto miji gare ki bisa yarda Allah , ki samu kusanci da shi , kin ji kou ? Ni zan yi maganar ku da hajiya umma ,"
     Cikin matsanancin farin cikin da siyama ta gaza boye shi ta miƙe bisa kan guiwar ta tare da rungume ubboh wacce ke zaune bisa bakin gadon ta na alfarma ," zuciyar ta cike da farin cikin da ta daɗe rabon ta da jin irin sa tamkar dai ubboh ta riga ta ɗaura mata aure ne da biyamuradi youssouf ɗin ,"
         Nagode nagode nagode , kawai ita ce kalmar da take fitowa bakin ta saboda ta gaza doguwar magana

Cikin sanɗa saɗaf-saɗaf gnala ta koma da baya wacce ta taho domin kawo wa siyama lamurjen da ta sanya ta haɗa mata , ta zo bakin kofar ta tsinkayi tattaunawar su da ta jaa hankalin ta har ta tsaya daga bakin kofar ta ji kome ,"
     Sai dai kan ta ya ƙulle ashe daman siyama ba ƙanwa take ba ga biyamuradi youssouf ??ashe kishiya take ga uwargijiyar ta ? To amma ya aka yi gimbiya maimouna bata kai ga sanin hakan ba ??
   Jikin ta har rawa yake lokacin da ta mayar da lamurjen ɗakin girki tare da komawa cikin ɗakin da aka yi mata masauki ta murza ɗan makulli , cikin ujila ta fiddo wayar ta tare da danna kiran uwargijiyar ta tana me zumuɗin sanar da ita wannan labarin , domin tun zuwan su sau uku gimbiya maimouna na kiran ta a waya tana tambayar ta ko akwai wani labari koh sun koma maraɗi ??ita kuma Tana shaida mata har yanzu suna niamey ɗin kuma bata ci karo da wani abun da ke bukatar fashin ɓaki ba ,"sai tsantsar ƙaunar da ta fahimci tana tsakanin ƴa da ƙanwar, wanda gimbiya maimouna ta gwatsale ta tare da cewa bata tambaye ta wannan ba ta kuma sake gargaɗin ta tare da jaan kunne akan ta kula da abun da ya kai ta kaɗai ,!

Sai dai har wayar ta gama karaɗin ta daga chan wurin gimbiyar bata ɗaga ba , "tana kuma jin tsoron sake kiran ta kar tayi laifi , dan haka ta maida wayar tare da dasa zaman jiran kira daga gimbiyar ,!

        Maraɗi

Lokaci yayi  kusa da zaki iddasa aykin da kin ka faro shi saratu , koh kin manta cikin watan ga mai kamawa youssouf yake cika shekarun sa talatin cif ne ? Kou kouwa dai kin manta da abun da zai faru a ranar zagayowar haihuwar sa na cikon shekarun sa talatin ,

    Ban manta ba hajiya uwa ba kuma zan manta ba tou ƙaƙa ma za'a yi na mance wannan lokaci ?bayan shi zai zamto shiri na na karshe akan tarwatsa rayuwar safiyyah tare da duk wasu masu ƙaunar ta ??

Ke dai Allah shi kai mu karfe 23:59h na ranar goma ga wattan biyu ,"

Ni ma nace Allah ya bani ikon ɗorawa !
     Kar ku manta da nunan ƙauna !

#umm'muaz
#comment
#vote
#share*©Fikrah Writers Association*


*MAFARI*
(hargitsin rayuwa)


*Umm"muaz*


*17*

Cikin sati biyu da tarewar su yakaka a gidan madam saly ,sun zama ƴan gari a da'irar ta yadda yakaka ta san ɗakunan manyan kilakai da ƙananun karuwan da suke unguwar saboda aiken ta da madam saly take wurin su , a gefe ɗaya kuma ta zama ƴar ɗakin samy baby , wacce bayan dawowar yakaka gidan madam saly ta gama nazarin yarinyar tsaf , ta gane bata san ma mai kalmar bariki take nufi ba kamar yadda da tayi zaton yakakar ƙaramar karuwa ce , sai ta fahimci ashe yakakan neman abun sawa a bakin salati take tare da wajen da zata sanya haƙarƙarin ta , dan haka sai ta jaa ta a jiki ta maida ta mai gyara mata ɗaki tare da yi mata ƴan kananun aike da aiki , ita kuma tana bata ƴan kuɗaɗe bayan jibgin suturun ta da ta fitar ta bata kwance , tun yakakan tana ɗari-ɗari ganin abun da samy baby tayi mata a farkon haɗuwar su , har dai ta zo ta saki jiki da ita , sosai take kyautatawa samy baby da ta riƙa a matsayin uwarɗakin ta , wacce take samun alheri tare da sakewa a wurin ta , domin a lokuta da dama har ƴar hira samy baby take zama su yi da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login