Showing 237001 words to 240000 words out of 411050 words
Chapter 80 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
,
Daga haka ya wuce yana satar kallon madubin motar sa inda ya hango Bayan Yakaka tana tafiyar ta a hankali dogon hijabin jikinta da yake kusan taɓa ƙasa bai boye salon takun tafiyar ta irin na barewa ba ,
Ɗauke kai yayi lokacin da yake dai-daita kan motar sa ya hau titi ya cilla zuciyar sa cike da zullumin tunani kan inda ya nufa ,
Kai tsaye ya tasamma unguwar da aka bashi tabbacin anan gidan da matar nan da yake zaton innar sa ce take aiki , duk kuwa da cewa duk cikin binciken da ya gabatar na tsawon satika biyu bai samu wani abu da zai bashi tabbacin cewa ita ce ko ba ita bace ? Amsa guda ɗaya ta tabbata a gare shi , shine matar kurma ce kuma ƴar gudun hijira ce daga yankin Bama , da take rayuwa tsakanin gidajen masu kuɗi tana yin aikace-aikace da ita da tilon ɗan ta mai kimanin shekaru takwas .
Yana shiga unguwar ya bi kwatacen gidan da aka ce tana aiki da su , ya tsaya daga bakin babbar ƙofar gidan ya nemi iznin shiga daga dattijon dake gadin gidan ,
Ganin sa da dattijon yayi cike da haiba da alamun wadata ya sa shi yin tunanin ko ire-iren mutanen da suke mu'amala ne da masu gidan , dan haka kai tsaye yayi masa iznin shiga da motar sa harabar gidan ,
Bayan ya fito daga motar sa ya miƙawa dattijon hannu suka yi musabaha ,
"Baba ina neman Mamar Bulama ne ance nan gidan take aiki ?
"To oho Kurma Mamar Bulama ƙwarai kuwa nan take aiki idan ka miƙe wannan yar hanyar ka ƙure sashin su yana nan daga hannun ka na dama nan za ka ga wata ƙaramar ƙofa ,
" toh sannu Baba nagode sosai .
Har ya fara taku , sai kuma dattijon da yake bin bayan sa da kallo ya dakatar da shi ,
" Amm bawan Allah nace ko dai lafiya kake..
Wata bangazar da ɗan yaron da ya kwaso da gudu yana gara gare-garen sa ya yiwa dattijon shi ya hana shi ƙarasa zancen sa yayi taga-taga , hular kan sa ta faɗo ,
Da sauri Doctor Hamza ya kama masa yana masa sannu ,
A fusace ya ɗago kan sa ,
" wannan akwai hatsabibin yaro , Bulama , Bulama , ai ko dan kai nayi fatan a kori uwarka daga gidan nan kafin ka kassara ni ko ma ka kar ni baki ɗaya ,
" wallahi bawan Allah a rana Bulama bai kuskureni ba ya kuskureni sau takwas , ka ga nan "
ya nuna masa dai-dai muƙa-mukin sa da ya ɗan kunburo
" jiya-jiyan nan iwar haka Bulama ya auno min jifan wani mulmulelen dungur , haba me ake da giggiwa irin ta 'ya'yan sansanin gudun hijira ,
Da tausayawa Doctor Hamza yake ba shi haƙuri tare da yi masa sannu , kafin ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro gudar dubu ɗaya ya miƙa masa ,
"Sannu Baba ga wannan ka saya manzafi ka shafa a wajen ka kuma dunga sa ruwan ɗumi ,
Da sauri dattijon ya wafci kuɗin yana ƴar dariya ,
"Kai to madalla , Madalla bawan Allah nagode , ai ka gane kwatancen da nayi maka ko ? Ko na raka ka ne ?
"Nagane Baba zan shiga da kaina ,
Kai tsaye ya doshi sashin , a ƙofar ya tsaya yayi sallama bai ji an amsa ba , baki uku yana sallama ba amsa ,
Cike da nutsuwa ya tura ƙofar da take ta ƙarfe ya shiga faffaɗan filin da yake ɗauke da wasu ɗakuna uku daga kan wata yar baranda ,
Yawata idanun sa yayi a filin wajen , daga gefe ya hangon ta a zaune , tana soka allura da zare a jikin hular da take hannunta tana ɗinkawa ,
Yayi mata kallon mintuna biyu masu kyau kafin ya fara taku yana kusantar ta , zuciyar sa cike da yaƙini kan kasancewar ta innar sa ,
Kamar daga sama ya faɗo haka ya gan shi tsil a tsaye a gaban shi yayi banga-banga ya riƙe kunkumi ,
Duban sa ya mayar kan sa yaro ne da bai wuce shekaru takwas ba fari kal da shi irin mamar sa , launin idanun sa yayi masa yanayi sosai da na wata da ya sani da a lokacin baida damar zurfafa tunanin ganota,
Girar sa ya ɗaga yana kallon yadda yaron ya ƙanƙance ido yana wani kumburi kamar mai shirin dambace sa'an sa , ya gane shi sarai yaron nan ne dai da ya bangaje dattijon nan a waje ,
Murmushi yayi tare da miƙa masa hannu ,
"Salamu Alaikum abokina , ni sunana Dr .
Tsuke baki ya sake yi , kafin ya amsa cikin dakiya
" Ni kuma sunana Bulama , waye kake nema ? Wancen mamata ce sunan ta Mamar Bulama , nan wajen mu ne masu aiki , can babbar ƙofar can nan ne wajen ku 'yan gayu ,
Mayar da hannun sa aljihu yayi ya gyara tsayuwa yana murmushi tare da mayar da hankalin sa kan yaron domin sosai yanayin wayon sa da tsaurin idon sa ya burge shi ,
" wajen Mamata nima na zo ba wajen yan gayu ba ,
Da sauri Bulama ya katse shi
"waye mamar ka to ?
Da baki Doctor hamza ya cuna masa Mamar Bulama da take nesa da su ta duƙufa ɗinkin ta babu alamun ta san da tsayuwar su a wajen.
' Ga mama ta can ,
Da sauri ya waiga ya dubi Mamar sa , sai kuma ya dawo da ganin sa kan Doctor Hamza .
" Mamata ce Mamar ka ?
Ya furta hakan yana bin shi da kallon mamaki daga sama har ƙasa ,
"unhun ,
Doctor Hamza ya amsa masa yana ɗaga kai alamun tabbatarwa
Da gudu ya juya wajen Mamar sa yana dariya ,
Da murmushi ya bi bayansa zuwa inda take
Yana zuwa faɗawa yayi a kanta , zabura tayi da ya sa allurar da take ɗinki da ita ta soki hannun ta ,
Dungure Bulama tayi tana harararsa .
Bata lura da kasancewar sa a wajen ba , sai da ya kamo hannunta da ta riƙe tana duba wajen da allura ta soke ta da har yake jini ,
Da firgici take kallon sa da ya sa ɗan hankici yana naɗe mata hannun , sannan yana ce da ita ,
"A iya sanina Uwa bata gudun ɗan ta kome muni ko tsananin Lamari , a matsayin da muka ajiye juna tun farkon-fari mun fi shaƙiƙan abokai kusanci , ina zaton kin manta da kika ce ke zaki fara rakani taɗi wajen budurwata ranar da zan fara tsayawa da ita , sai kuma ga shi shekaru sun tafi sun yi nisa cikin wani irin bauɗaɗɗan lamari marar daɗi , da har ɗan nan naki yayi aure baki sani ba , ba kuma kya son sani ,
Ya ɗago kan sa bayan ya gama naɗe mata hannun , ya kalli ƙwarar idanun ta da suke sake bayyana masa tare da tabbatar masa ita ɗin ce dai ,
Da wani irin yanayi yace ,
"khaalty nasan kina ji na , kin kuma gane ni , idan baza ki magantu domi na ba , ki magantu dan Amne Amina , ki dubi girman Allah ki waiwayi 'yar uwarki , ki koma mata ko rayuwar mu zata dai-daita gaba ɗaya ,
"kar a tuno da kome da ya riga ya faru ya wuce , yanzu lokaci ne yayi na gyaruwar kome ,
Hawayen da suke sauƙa a idanunta ne suka ɗigo akan bayan hannun sa
Hannun sa ɗaya ya kai da nufin goge mata ,
Bulama wanda idanun sa suka kaɗa suka yi jaa yana daf da fashewa da kukan shima , ya ture hannun Hamza , ya sa 'yan tafukansa biyu ya share mata hawayen , kafin ya waigo gareshi ,
" Kai ba yaron ta bane tunda ga shi ka sa ta kuka ka tashi ka bar gurin mu ,
" ka fita
Ya ce yana tura Doctor Hamza
Doctor hamza ya miƙe a hankali ganin taƙi cewa kome ga kuma hayaniyar Bulama da take ƙara damun sa .
Yayi taku biyu yaji tayi magana da sautin da baya fita mai kyau irin ns bebaye ,
Juyowa yayi sai ya ga ta miƙo masa hannuwanta irin yadda take yi masa tun suna yara ,
Da murmushi a fuskar sa ya koma yana sassarfa ya harɗe yatsun sa cikin nata da zuwa lokacin kuka take haiƙan ,
"la bas , ki daina kuka khaalty ,
Yake cewa ga ita da sigar rarrashi .
Hawayen ta ta goge Bulama yana taya ta kafin ta sunkuya ta share rairayin da yake ƙasa ta rubuta masa da yaren su ,
kayf hal 'ukhti ? (Ina yar uwa ta ?) kayf tamakanat min aleaysh bidun ily? ( yaya tayi rayuwa bayana ? )
Kafin ya amsa mata ta sake rubuta masa wata kalma
" aftaqadaha kathirana , ( nayi kewar ta sosai )
A takaice ya bata labarin Amnee da mafi yawa yafi karkata ga halin damuwar da take ciki akan rashinta , ya ɗora da sanar da ita rabuwar auren iyayen sa , da haifar da ruɗani tare da ƙaruwar zubar hawayen ta ,
Ƙarshe ya roƙi da ta zo ya kai ta wajen 'yar uwar ta .
Nan ya ga sabon ɓacin rai akan fuskar ta kafin ta tirje ta nuna ƙin amincewarta da batun ,
Duk yadda yake zaton lamarin zai kasance ya wuce haka , domin kuwa a ƙarshe ta sanar da shi muddin ya matsa kan batun komawar ta gida zata bar inda ya sani ta sake maɓoya ita baza ta taɓa komawa gida ba .
Rochester New York
Cikin kwanakin da suka biyo bayan zuwan Falmata asibiti tare da fara shan maganin ta , sosai aka samu cigaba ga lafiyar idanun ta inda cikin satin ta na biyu da fara shan maganin ya zamana tana iya ganin alamun haske fayau amma bata ganin hoto , hasken ma wasu lokutan yana zama babu ,a wasu lokutan kuma yana mata yawa sosai ta yadda har take gagara buɗe idon ,
Hakan ya sa da ta yiwa likitan ƙorafi sai ya bata shawarar ta nemi tabarau da ake amfani da su wajen rage ƙarfin hasken rana , watau tabarau masu duhun launi , bayan haka kuma ya sake shawartar su akan amfani da sandar makafi , ( white cane )
Domin zai taimaka mata wajen gudanar da al'amuranta na yau da kullum a sabbin wuraren da bata kai ga sani ba , zai kuma bata kariya tare da zama garkuwar a gareta .
Dan haka Biyamuradi ya tafi kanti da kan sa ya zaɓo mata tabarau masu kyaun suffa na mata , tare da sayo mata sanduna har guda biyu .
Falmata wacce tun ranar da ta saurari hirar Biyamuradi da Maimounatu duk ta zama wata iri , damuwa tayi mata yawa sannan 'yar sakewar da ta fara yi da shi ma duk ta bi ta daina ta koma takura kan ta kamar farkon auren su .
A hankali ta lura da yawan yin waya da mata biyu da yake yi daga barandar gidan ta waje ,
ta gane su biyu ne ta yadda daga ya gama waya da ɗayar yake ƙiran ɗayar , sai dai ko kusa taƙi yadda ta sake saurarar hirar sa da ta lura shima bai son ta ji tunda fita yake yi idan zai yi wayar sannan ko Mama bai yadda ta bi shi .
A ɓangaren Biyamuradi shima shirun Falmata tare da damuwar da take ciki ya fara damunsa , sai kaffa-kaffa yake yi da ita yana ta bin hanyoyin ganin ya dawo mata da walwalarta kamar farkon zuwan su ,
A yau ma yana zaune tare da su a falo Mama tana wasan ta a gefe da tilin kayan wasan da ya sayo mata su tari guda tarkace iri-iri .
Wayar sa tayi ƙara alamun shigowar ƙira , hannun sa da yake dafe da kan sa da ke ɗan masa ciwo sama-sama ya janye daga kan shi tare da yunƙurawa ya zauna sosai ya ɗau wayar sa ,
Ganin wanda yake ƙiran nasa ya sa shi tattaro duk wata nutsuwar sa ,
" Assalamu Alaikum Maimartaba barka da war haka da fatan alheri .
Daga can Maimartaba ya amsa masa , suka gaisa , kafin ya jefo masa tambaya da ta so ruɗa shi da farko
" Youssoufa wake tare da kai nan ƙasar Amurka ? Kacce bisa ga aiki ka tahou nan kou ?
Satar kallon Falmata yayi wacce take zaune daga gefe a ƙasa ,
Sai ya miƙe ya fita
Bata ganin sa amma taji takun barin sa wajen , ajiyar zuciya ta sauƙe tana jin damuwar ta na sabunta ,
" wayar zai je yi da su ,
Ta aiyana haka a cikin ranta .
"Ranka ya daɗe bissa aiki na zou nan kouma tare mukke da abokan aiki na kamar yadda na faɗi tun farko ,
Daga ɓangaren Maimartaba sarki Abdoul-Azizou yayi shiru yana nazari , kafin ya amsa
" Madalla Allah shi taimaka yaushe kake dawouwa ?
Cike da jin daɗi Youssouf ya amsa da
"ƙasa da watanni huɗu ko biyar ranka shi daɗe ,
"Allah shi dawo da ku lafiya , ka tsayar da gaskiya cikin dukkanin lamuran ka , sannan ka tsananta addu'a .
Ya amsa da
" to nagode sosai Ranka shi daɗe .
Suka yi sallama , ajiyar zuciya ya sauƙe yana nazarin Kalmomin Maimartaba kamar akwai dalilin yin su ,musamman ma tambayar da yayi masa a farko.
Nisawa yayi kana ya dubi fuskar wayar sa ya ga agogo ƙarfe uku na yamma ta kusa , can gida Niger yanzu tara na dare ne kenan Maimartaba yana sashin sa suka yi waya ? Bai tare da hajiya Umma domin da zai haɗa su su gaisa .
Kawar da tunanin yayi ta hanyar lalubo layin wayar maimounatu bata jima tana ƙara ba ta ɗaga cike da salonta na ƙwarƙwasa wanda yake da tasiri sosai agare shi ,
Yana nan a tsaye a wajen ya kwashi fiye da rabin awa yana hirar da ita ke tsawaita masu ita ta hanyar amfani da daɗaɗan kalmomin ta ,
Da suke ɗumama masa zuciya da jiki daga barin jin matsanancin sanyin da ke farfajiyar wajen .
Da kyar suka rabu kafin ya ƙira Siyama sama-sama suka yi hirar da yafi karkatata ga tambayar lamuran da suka shafi 'yar sa ita kuma siyama tafi damuwa da lafiyar sa tare da lamuran sa na yau da kullum .
Bayan sun gama wayar ya maida ta aljihu ya ɗaga kai yana kallon yadda garin yake lulluɓe da tsananin sanyi .
juyawa yayi ya koma ciki nan ya tarar da irin ɓarnar da Mama take yi ta gan-gama wuta sosai a ɗan wajen hura wuta har wutar ta fito waje tana gaf da kama 'yan ƙananun kayan wasan ta da ta riga ta jefa wasu cikin wutar da hakan ya sa wutar ƙara ruruwa sosai .
" Mama me kike haka ?
Yace da maɗaukakin sauti da ya sa daga Mama har ita kan ta Falmata suka firgita , da sauri Falmata ta yunƙura tana laluben Mama cikin tambayar me take yi ?
Biyamuradi da takaicin yadda Falmata take yin jugum kamar mutum-mutumi ya fara isar sa ya dube ta a fusace ,
"Tayaya zaki iya sanin me take yi bayan baki da wani aiki sai tunanin wofi tamkar kin fi kowa damuwa a duniya ,
Saitin da yake Falmata ta maida ganin ta da kalamansa suka tunzuro ta ƙari da takaicin hirar da yake da matan banza a zaton ta ,
Muryar ta babu ƙarfi sosai tace ,
" ai ni miskiniya ce marar ido da bata wuce mabaraciya ba , da zai fi dacewa a cikin matan da kake taɗi da su kullum ka auri ɗaya da zata dunga kula da gida sosai ,
Chak ya tsaya daga tattara kayan wasan Mama , ya maida ganin sa kanta , yanzu ya samu ƙarin haske akan yadda ta sauya yake ganinta koyaushe cikin fushi da ɓacin rai ashe kishi ne ke cin ran ta ,
Murmushi yayi ya bar abunda yake tare da dawowa gefen ta ya zauna ya riƙo hannun ta , tausasa muryar sa yayi yana me tsare ta da ido yace ,
" Fatima ki saurareni , ki ji abunda zan faɗa miki a yanzou domin shi zai amfanar mouna ni da ke , matan da kike ji ina waya da su su biyu ba matan banza bane Matana ne su ma kamar yadda kike Matata .
Kamar ya caka mata wuƙa sai ta zame hannun ta daga cikin nasa , bakin na motsi a hankali ,
Bai kula da yanayin ta ba saboda ya shirya faɗa mata gaskiya a yanzu , ya sake riƙo hannun ta tare da cigaba da magana ,
" Fatima kiyi haƙuri amma yau zani faɗi miki doukkanin haƙiƙanin gaskiya bisa kaina .
Bai jira amsar ta ba ya shiga bata labarin ko shi wanene tiryan-tiryan , tundaga sunan sa na gaskiya, kasancewar sa ɗan sarki , aikin sa zuwan sa Nigeria auren sa da matan sa , abu guda ya ɓoye mata haƙiƙanin dangantakar sa da Yakaka .
Tamkar a mafarki haka Falmata ta tsincin wasu kalmomin nasa , cikin wani irin yanayi da ta gaza tantance wanne iri ne , muryar ta can ƙasan maƙoshi , tace da shi
" Duk cikin labarin da ka bani baka faɗa min lokacin da kuka yi aure da 'yar uwata ba ?
Mukut ! Youssouf ya haɗiye busasshen yawu tambayar ta zo masa a bazata ta yi masa dirar mikiya bai kuma shirya amsar bata ba a yanzu ,
" Fatima zan faɗi miki wannan labarin a gaba cikin lokaci na mussaman ba yanzu ba ,
Cikin rashin yarda da ya mamaye tunanin ta ta fara girgiza kai ,
" a ah yanzu nake so ka faɗa min muddin kana so na yarda da duk labarin da ka bani yanzu ,
zaro ido yayi yana duban fuskar ta da ƙwayar idanun ta da suke cike taf da rikici da tashin hankali