Showing 273001 words to 276000 words out of 411050 words

Chapter 92 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14350

bai sake ƙira ba ya juya ya koma ɗakin ,

Zama yayi a bakin gado , cikin ransa rikicin da Yakaka ta zo da shi ya kai matakin ƙure shi, ya fara neman mafitar yaya zai yi da Yakaka domin kuwa ko a mafarki ba zai yi mata yadda take so ba , ya saki Matarsa akan wanne dalili ? Aurensa da Falmata aurene da sai mutuwa ce kaɗai zata raba su ,

Yana son matar sa , yana ƙaunar ta ,yana tausayin ta , ya kuma shirya tsaf domin zamar mata bango abun jingina , idan ya rabu da ita taje ina ? Waye zai jiɓanci lamarin ta ? Wa suke da shi a duniya jigo ?  Daga ita har Yakaka masu rauni ne domin kuwa mata ne  tayaya zai sau aurenta ?  Alhalin ga zuri'a a tsakani Allah ya fara basu ,

dangantakar su ba mai yankewa bace har abada ba zai rabu da ita ba ko da kuwa ace ita da karan kanta ta nemi da ya sake ta ba zai aikata hakan ba ,

bare wasu mutane daban da ba sune suke riƙe masa da igiyoyin auren sa ba  , Fatima Zara matar sa ce har a lahira baya fatan rabuwar su .

Zai roƙi Yakaka da tayi hakuri ta yafe masa duk wani laifi da take zaton ya yi mata , tare da Alƙawarin kula da hidimar Rayuwar ta muddin zata yadda ta cigaba da rufe asirin tsakanin su daga sauran mutane , ciki har da Falmata da Mama idan ta girma .

sannan tayi haƙuri ta koma Nigeria ta samu miji tayi aure shi zai tsaya mata a wannan gaɓar .

muddin kuwa taƙi yadda da tayin salama , bai iya hasashen yadda ƙarshen lamarin su zai ƙarƙare , bai san ba gurin hukuntata akan yunƙurinta na raba shi da matar sa ko zai iya yi mata sassauci Albarkacin Mama ba?

abunda ya riga ya sani ne tun a ranar farkon ganin sa da ita ba soyayya ce ragamar tarayyar su ba illa musiba tare da sharrin shaiɗan da shi ya faɗawa a ciki , ita kuma ta gagara tsamo sa a madadin haka ma sai ta zama abokiyar taya shi ,ashe idan haka ne itama da nata laifin ,

Zai yi kome zai kuma jure kome domin ganin ya cigaba da rayuwa da matar sa da 'ya'yan sa ,

A hankali ya hau gadon ya rungume ta tsam a jikinsa , runtse ido tayi hawayen da suka taru mata suka zubo , tun daga tashin sa ta ji shi , ta ji wayar sa da Yakaka ,

Wanne irin sirri ne a tsakanin su da suke ɓoye mata basa so ta ji ? Jikinta yana bata rabuwar su da ita da Youssouf ta zo kusa.

Washegari


Tunda tayi sallar asuba gari yayi haske ta shiga kitchen duk kuwa da Youssouf ya so hana ta amma ta dage ,

"bai kyautu ba kuma Hajja ta dawo daga asibiti tayi mana girki zan iya ba abu mai wahala zan dafa ba kawai pasta ne zan yi , tace da shi .

Ba yadda ya iya saboda gaba ɗaya ta koma mishi kamar farkon auren su , sai janye jiki take da shi ,tana ƙin kallon sa , bata tsawaita zance da shi

Bayan ta gama girkin ta zuba ta rufe , ta zo ta wuce shi a falon yana zaune ba tare da tace masa kome ba ,

Da ta shiga ɗaki wanka tayi ta koma ta kwanta a gadon ta saboda tun ƙarfe ɗayan dare rabon ta da baccin kirki , lokacin da ta ji wayar da suka yi , tana kwanciya bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta

Youssouf  da ya gaji da jiranta ta zo suyi karin kumallo , tashi yayi ya leƙa ɗakin nata ,

A gado ya hangota tayi luf tana baccin ta , ransa yayi sanyi da yaga tana bacci sosai haka , a hankali ya taka zuwa cikin ɗakin ,

Zama yayi a bakin gadon yana ƙarewa fuskarta kallo , ƙaunar ta na sake fisgar shi , gani yayi ta fi yi masa kyau idan tana bacci ,

Kamar motsi ya ji an taɓa ƙofar falon , dan haka ya miƙe ya fito yana dube-dube , sai dai bai kai ga ganin kome ba , tsayuwa ya cigaba da yi a harabar gidan ya zura hannu a aljihu yana tunanin zuci ,

"yana son zuwa Maraɗi ko domin iyayensa , amma tsoron abunda zai tarar a can ya hana shi samun ƙarfin zuwa ,

Ciki ya koma inda ya tarar wayar sa da ya ajiye akan kujerar da ya tashi tana ƙara ,

Zuciyar sa ta buga da ƙarfi ganin Mai ƙiran nasa da ba kasafai ta cika yin ƙiran waya ba , sai fa da Babban dalili ko kuma idan shi ya ƙira domin gaishe ta ,

"Adda Ammi ce Babbar yayar su baki ɗaya da take aure a jahar Damagaram ,

Har wayar ta tsinke bai ɗauka ba saboda fargaba , amma bai jinkirta ba ya bi bayan ƙiran da hanzari ,

**

Daga cikin motar ƙirar Honda Accord  da take tafiya da matsakaicin gudu akan titin Boulevard Mali Véro ,

Hamshaƙan matan su biyu masu kamanni ɗaya suke zaune , ɗaya tana daga gaba Babbar tana baya , ta gaban ta ɗan waiga kaɗan , lokacin da direban ya karya kan motar zuwa cikin unguwar da take gefe da su ,

"Adda Ammi kadda kice mini ke ma Youssoufa bai ɗau ƙiran ki ba ?

Zata yi magana wayar ta ta ɗau kiɗan shigowar kiran sa ,

" ga shi ya biyo sawun ƙiran ,

   Tace ba tare da ta ɗaga ƙiran ba ,

Tafeeda wanda shi yake jaan motar ya juyo kaɗan kafin ya maida hankalin sa ga tuƙin yana cewa "ai ga gidan can ma mun iso Adda Ammi ,

Duk suka zubawa gidan ido ta cikin gilashin motar suna kallo ,bayan ya dai-daita tsayuwar motar , suna shirin fitowa lokacin da suka ga an buɗo ta ƙaramar ƙofar gidan a hankali an fito ,

Su dukkanin su wara ido suka yi suna kallon sa da Mamaki ,

" Mouhammadou ?

Tafeeda ya ƙira sunan sa da mamaki a muryar sa  ,

suna ganin yadda yake dube-dube yana sauri , ya miƙa kan titin unguwar da babu kowa shal , sai fa giftawar motoci jifa-jifa , ba tare da shi ya gan su ba saboda gilashin motar da yake da duhu ,

Shiru ne ya gifta tsakanin su , kafin Ubbo ta ce

"Tafeeda ka ce mouna babu wanda ya san da tabbatuwa lamarin nan sai kai ɗai ?  Sai kouma mu da yanzou ka taho da mu , to Yaya anka yi mouhammadou ya iso nan ? Ko kouwa shi Youssoufa ya ƙiraye shi ?

Cike da nazari Tafeeda ya nisa ,

"Adda ni bansan kome game da wanzuwat shi ba , wataƙila Youssoufa ya ƙiraye shi , sai dai nafi zaton zuwan kan sa yayi ɗauke da wani ƙudiri nashi na daban ,

Duk suka sake yin shiru a motar , bayyanar Mouhammadou a boyayyen gidan Youssoufa na sirri ya sanya su a ruɗani ,

Bayan iyayen su da suka san maganar zaman Youssouf da mace har ma da ɗiya ba ta aure ba a ta bakin wasu mutane ,

Tafeeda shine mutum ɗaya tal da yasan haƙiƙanin gaskiyar lamuran , shine kuma ya yi ta ƙoƙari wajen ganin ya wanke Youssouf , ya dunga neman Youssouf da ya dawo su fuskanci matsalar su maganceta tun kafin duniya ta ɗauka .

Amma daga baya  sai Youssouf yaƙi ba shi haɗin kai , wannan dalilin ne ma ya sa shi dole ya samu yayun Youssouf ɗin Adda Ammi , da Ubbo da su ma suke cikin tashin hankali jin cewa ɗan uwansu yana can America tare da karuwa da 'yar su ,

Shi yayi musu bayanai na haƙiƙanin gaskiyar kome cewa ba fa zaman dadiro Youssouf yake yi ba amren yarinyar yake yi daga ƙasar Nigeria wacce kuma ƙanwace ga ainahin uwar yarinyar da ya yiwa ciki ba ta hanyar aure ba ta kuma rasu a wajen haihuwar 'yar .

Ba ƙaramin baƙin-ciki suka shiga ba da jin irin ta'asar da ɗan uwan su ya aikata , har kuma yake da tsaurin idanun cigaba da yin yadda ya ga dama ,

Dan haka suka tsaida shawarar muddin Youssouf ɗin ya dawo su zasu yi takakkiya zuwa gidan da ya ɓuya yake yin rashin gaskiya ,

su kuma sanya dole ya saki amren yarinyar da yake riƙo tare da haɗa ta da ɗiyar su koma da ita can ƙasar su ,

su basa yadda ya gurɓata musu sunan zuri'a da masarautar su , ba kuma zasu amince ya kawo musu baragurbin ɗiyar sa ba , bare wata matar da bata da masauƙi a tsakanin su ,

wacece ita da zata zama sanadin ɓacin ran iyayen su , ta kuma samu damar zama matar ɗan uwan su Yarima sarkin watarana ??

Adda ammi ta ɗau wayar ta tana sake ƙiran layin Youssouf dai-dai lokacin da taxi ɗin da Yakaka tayi shata , ya ajiyeta a ƙofar gidan ta bashi kuɗin sa ,

Ta kama hanyar shiga gidan hannun ta riƙe da kulolin abincin da ta dawo da su daga asibiti , da kyar take taku saboda tsabar gajiya da bacci da ya cika mata ido ,

Adda Ammi tana jin Youssouf ya ɗaga wayar bata tsaya amsa gaisuwar sa da yake yi mata ba cikin dakakkiyar muryar ta tace da shi ,

"Youssoufa ga munan ƙofar gidan ka , ka hito ka yi mouna jagora ,

Da 'yar ruɗewa cikin muryar sa lokacin da yake miƙewa yana barin abincin da ya fara ci yace

"Adda ai bani gida maraɗi ba kouma na tahoue , ina Niamey ne wajen aikina ,

"Na sani ƙofar gidan ka na niemey ɗin nake magana ko kouwa baka hitowa ka mouna jagora sai mu shiga da kanmu ?

Fitowa yayi hankalin sa a tashe ya nufi ƙofar gidan ko takalma babu a ƙafarsa  ,

A harabar gidan ya ci karo da Yakaka wacce take shigowa , kallon juna suka yi kowannen su ransa a ɓace , ya gota ta kai tsaye ya buɗe ƙofar gidan idanunsa suka sauƙa akansu duk ukun suna fitowa daga motar ,

Yawun bakin sa ya ji ya ƙame , ya rasa halin da yake ciki takamaimai  , ,

da murmushin yaƙe ya ƙaraso gaban su , ya ɗan sosa ƙeya bayan ya rage tsawo ya shiga gaishe su ,

Sama-sama suka amsa suna binsa da kallo ganin yadda duk yake a firgice da alamun rashin gaskiya ,

"Bismillah,
yace da su yana yin gaba , ba tare da ko sau ɗaya ya dubi sashin da Tafeeda yake tsaye ba saboda gudun yadda zata kaya a tsaƙanin su da ya riga ya san cewa shine ya haɗo masa wannan gangamin ,

Da shigar su harabar gidan yayi nufin kai su sashin sa , sai dai tsintar maganar Adda Ammi yayi tana tambayar sa ina matar gidan ?

Cikin dakiya ya waigo , "tana ciki , yace a takaice yana kallon ta ,

"to ai wajen ta yakamata mu shiga duk muyi maganar da take tafe da mu  ,

Ɗan jim yayi yana kallon ta , cikin shakku , sai dai yadda tayi maganar cikin lumana ya sa ya wuce gaba zuwa sashin Falmata suna bin bayansa ,

Zuciyarsa cike da fatan samun masalaha akan koma menene , fatan sa Allah yasa zuwan su ya gyara kome ,

Suna shiga falon suka tarar da Yakaka a zaune daga ƙasa tana hutawa tare da jiran shigowar Falmata da take zaton ko tana wajen Youssouf zuciyarta ɗauke da ƙudirin fara sanar mata da kome a yau ,

Shigowar su ya sa ta miƙe , fuskarta kadaran-kadahan ta gaishe su ,

Shi Tafeeda bai amsa ba , Ammi da Ubbo ne suka amsa a taƙaice suna ƙare mata kallo sama da ƙasa , zuciyar su na shaida musu wannan me kama da asbinawan ce ta sa ɗan ouwan su kaucewa hanya ??

Ratsawa tayi zata wuce ta bar su Ubbo ta dakatar da ita ,

"baiwar Allah dawo nan , kou ba ita ce  matar gidan ba ?
   ta juya akalar tambayarta ga youssouf

Da sauri Youssouf ya girgiza kai ,
   "Ba itta ce ba ,

To ita wannan wace ?

Adda Ammi ta tambaye shi

a ciki ya amsa ,
"yal ouwatta ce ,
.ubbo tace
"itta ina tai ?
" bacci take , adda domin Allah muyi duk maganar da zamu yi ni da ku ,

"Ke

Adda Ummi ta buɗe murya wajen ƙiran Yakaka wacce har lokacin take rakaɓe daga gefe a tsaye ,

"ki tai ki tado mouna da 'yal ouwakki ku taho tare ,

Yakaka bata san me suke nufi ba hausar tai mata nisa dan haka ta tsaya tsam tana kallon su ta ƙasan ido ,

Youssouf da yanayin Ammi ya fara ɗarsa masa tsoro a rai , ya nunawa Yakaka ɗakin da Falmata take ciki ,yace

" Fatima tana ciki ki ƙira ta ,

A hankali Yakaka ta tura ƙofar ɗakin Falmata da har kawo yanzu baccin ta take yi ,

Ta ƙarasa bakin gadon a hankali ta dafa ta ,

"Falmata , Falmata , ta ƙira sunan ta tana ɗan jijjigata ,

Buɗe idanunta da suka yi mata nawi tayi , sai kuma ta ware su da sauri ta miƙe zaune tare da riƙe hannun Yakaka da take hango ta dusu-dusu ,

" Yakaka kece ? Ina Mama ? Ya jikin nata ? Ta samu sauƙi ? Tayi bacci ? Bata yi kuka ba ko ?

" jikin Mama da sauƙi na baro ta tana bacci , Yanzu muje falo kina da baƙi ,

" Baƙi ?su waye  ? mu babu wanda yake zuwa wajen mu ai ?

"wasu mata ne ina ga ƴan uwan sa ne ,

Yakaka tace tana miƙewa tsaye ,

A hankali Falmata ta kai hannu ta laluɓi gilashinta ta sanya a fuskar ta , bayan ta ɗora hijabi akan doguwar rigar jikinta ,

Tare suka fito falon yatsunsu cikin na juna  ,

Har ƙasa Falmata ta durƙusa ta gaishe da matan da ta tarar da ƙamshin su ya cika falon , sannan ta gaishe da Tafeeda ,

Sai tayi shiru jin yadda suka amsa mata a cike da ginshiri ,

"wannan ce matar taka ? Uwar 'yar taka ? Wannan kuma 'yar uwarta ?

Adda ummi ta tambaya tana nuna Falmata da Yakaka da hannun ta a walaƙance ,

"Eh , ah ah , eh ita ce Matata Fatima ,

Kallon sa su duka biyu suka yi jin yace "eh ya kuma ce "Ah ah ,

Gyara zama tayi ta matso kusa daga kan kujerar ,

" ke yarinya kina jina ?

  Falmata wacce ta fahimci da ita ake , ta gyaɗa kai a hankali bayan ta fuskanci inda take iya ganin Matar da take mata magana sosai ,

" daga ina kike ? Su waye iyayen ki  ?

daga Falmata har Yakaka zuciyoyin su suka buga , Sai Falmata ta sake matso Yakaka tana riƙo Hannun ta ,

A hankali Yakaka ta sauƙe ganin ta akan Adda Ammi ,

" Mu 'yan gudun hijira ne a ƙasar Nigeria, kuma iyayen mu duk sun rasu ,

Ƙutawa tayi tana gyaɗa kai cikin buɗaɗɗiyar Muryar tace " kin san Youssouf wanene ?

Girgiza kai  Falmata tayi alamun "ah ah ,
   " shekarar ku nawa kuna amre ?

Youssouf wanda ya fara hango tsoro a fuskar Falmata tare da hasasho inda Adda Ammi zata ƙarƙare maganar ta ya yunƙuro da nufin katse ta

" Adda Ammi  ....
Da hannu ta dakatar da shi , "Youssoufa ba kai nake tambaya ba ,

"yarinya shekarun ku nawa nace da Amre ?

"shida ,
   Falmata tace cikin siriryar muryar , zuciyar ta cike da son sanin yau wacece agaban ta ko dai mahaifiyar Baban Mama ce ??

Muryar ta ya katse mata tunani,

"kin taba ganin wanni daga cikin dangi nashi ya zou inda kuke ? Ko kouwa ku ya taɓa sada ku da dangin sa ?

Shiru Falmata tayi ,

"kin san dalili ??  Bata jira amsar Falmata ba ta ɗora da cewa ,

"sabadda kama dagga kan iyayensa da mou 'yan ouwansa har zouwa kan dangin da masarautar mu zouwa kan mutanen jahar mou baki ɗaya ba mou san da amren kou ba ,

"Youssoufa ɗan Sarki ne , Yarima ne shi , yana da iyayen sa suna raye mu yayyensa ne , yana kouma da ƙanne , sannan yana da matan amre har biyu da ɗiyar sa ,

"duk baki san mou ba , a yadda ɗan'ouwansa kuma abokinsa ya buncika mouna ya amre ki ne tare da ɗiyar yal ouwakki da ta haifa ba tare da sun yi amre da shi ba shigiyar ɗiya, ya zo nan ya ɓoye kou , yana rayuwar sirri da kou , kin raba tsakanin sa da matayensa , kin ɗauke hankalin sa daga aikin sa , bashi da watta hidima sai taku ke da ɗiyar da gurɓatatciya ce shin yarinya baki gudun jefa rayuwarki ga hargitsi maigirma ?

Cikin wata irin murya Falmata ta ɗamƙi hannun Yakaka ta jijjiga ta tare da cewa

" Yakaka kiyi magana mana , kina ji fa an ƙira Mama shegiya ,

shiru Yakaka tayi tana jin yadda wani abu ya zo mata ƙahon zuci ya takore , ko motsa laɓɓanta ta gaza ,

Juyawa tayi wajen da Youssouf yayi suman zaune akan shamtar sa da Adda Ammi tayi ,

"Baban Mama ka ji wai Hajiya yayar ka tace Mama ba 'yar aure bace , ka faɗa musu gaskiya yadda ka faɗawa Baba prof lokacin auren mu dan Allah,

Hawayen da suka cika gurbin idanunta suka sauƙo , ta matso gaban su ,

" Hajiya dan Allah ko da ni baza ku karɓeni ba kuyi haƙuri ku karɓi Mama kar ku ɓata mata asali , Mama yarinya ce marar lafiya dan Allah kar ku ....

Tsawar da Ubbo ta daka mata ya sanyata yin shiru ,,

"ke yarinya raba mu da ƙazanta ,yadda kuka zou tare hakka zaku kouma tare , mu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login