Showing 147001 words to 150000 words out of 411050 words
Chapter 50 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
kasancewar sa cikakken likita yasan yanayin da suke yi a duk lokacin da suke son sanar da mutanen marar lafiya wani mummunan labari game da marar lafiyan su,!
Ta mutu ?
Ya tambaya yana jin yadda zuciyar sa ke matsewa da tasowar ɗacin kalmar har akan harshen sa ,"
Da sauri likitan yace
Bata mutu ba amma zai fi kyau idan muka je nayi maka bayani a nutse.
A sanyaye Doctor Hamza ya bi bayan likitan bayan ya nunawa Amne wurin zama a gefen Falmata wacce tayi zugui idanun ta sun yi jaa sakamakon hawayen da take ta gogewa kan rashin sani halin da ƴar uwar ta ke ciki har kawo wannan lokacin ,
Mun rasa gane yadda akayi ko dalilin da yasa matar ka tare da ƴar uwar ta suka bar asibiti kuma suka bar ƴar jaririyar ta ba tare da mun sallame ta ba , sannan Alamu suna nuna kai ma baka san sun tafi ba ,"
Ɗan tsayirtawa likitan yayi yana nazarin fuskar doctor hamza wanda yayi saƙare yana kallon sa , kamar dai bai kai ga fahimtar bayanin da yake masa ba ," ɗan ƙwanƙwasa bakin biron hannun sa yayi akan ƴar takaddar gaban sa,"
Idan har an tabbatar tana gidan zamu iya sallamar ku tare da jaririyar domin ayi gaggawar sadata da mahaifiyar ta domin ta shayar da ita nonon farko ,"
Cikin jirkitattacen kallo Doctor hamza yace wacece ta gudu tare da ƴar uwar ta suka bar jaririyar ?
Tamkar dai sam bai ma fahimci bayanin da duk likitan nan ya masa ba ,"
Ba kai ne mijin AMINA HAMZA DILMARI BA ?
Maimakon ya amsa sai ya miƙe tsaye ,
Kana nufin ita ce suka gudu tare da ƴar uwar ta ?
A taƙaice likitan yace
Haka muke zato domin an duba duk inda yakamata cikin asibitin nan ba'a gan su ba , sannan masu tsaro/securities sun tabbatar mana da sun ga fitar mata biyu farare sanye da hijabai sun hau.....
Ankarar da yayi doctor hamza ya juya daga ofishin ya sanya shi miƙewa ya biyo shi ,
Wurin da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo ,"
Fatimah , kun haɗu ke da yayar ki ?
Da sauri ta ɗago kan ta !
Bamu haɗu ba Yaya dakta har yanzu ba'a kai ni inda suke ba ita da baby , ko basu da Lafiya ne ? Dan Allah ka kai ni wajen su ,'!
Wani gumi yaji yana tsatsafo masa daga illahirin ƙofofin gashin jikin sa ,"
Amne ta taso ta matso kusa da shi ,"
Ina mai jegon ne ?
wai ba'a gan ta ba yace da wata irin murya chan ƙasa , Amne dake kusa da shi kaɗai ta iya jin mai yace
Wanne irin ba'a gan ta ba inji amne ,'
Lokacin da likitan ke sake ƙarasowa tare da wasu nurses da wasu securites ,
Kuyi haƙuri sir , a fara duba gida ko suna chan , domin tare da ƴar uwar ta suka fita ,"
Wata kakkarfar tsawa doctor hamza ya yiwa likitan ,
Ka daina cewa tare da ƴar uwar ta suka fita , "
Ga ƴar uwar ta nan , ya juya yana nuno musu Falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye tana rarraba ƙwayar idanun ta da son sanin meke faruwa?
Ita kaɗai ce ƴar uwar ta , ya zama dole ku nemo ta , ba gudu tayi ba sace ta aka yi , Yakaka baza ta gudu ta bar Fatimah ƙanwar ta ba baza ta gudu ta bar baby mama ba , noorie baza ta min haka ba , ya ƙarashe da rawar murya yana jin yadda zuciyar sa ke cika da tsoron tabbatuwar hasashen mutanen asibitin ,"
Sir kayi haƙuri amma matar ka ba sace ta aka yi ba ita da ƙafafun ta suka fita tare da wacce tace sister nata ce , bayan tafiyar ka matar ta zo , tanan muka wuce da ita , wannan yarinyar da kace ita ce ƴar uwar ta tana zaune a wajen bata nuna ta san yarinyar ba basu mata magana ba su duka biyun , sai da muka je ɗakin , suka yi magana , kuma lokacin da nake fitowa da baby domin kai ta wurin mamar ta naga bayan wasu mata biyu suna fita , ina hasashen su ne , domin su ne kaɗai matan da aka ce an gani sun fita da hijabi tsukin awannin nan ," ka zo ma na nuna maka shaidar flask ɗin ruwan zafin da matar ta kawo , har yanzu yana ɗakin !,
Cewar wannan nurse ɗin da ta kai yakaka ɗakin hutuwa ,"
Bai ce ƙala ba ya bita a baya zuwa ɗakin , anan ya tadda flask ɗin da ta ambata tare da wata ɓakar leda da sauri ya ɗauki ledar ya buɗe ,
Babu kome a ciki sai hijabin yakakar wanda ta zo da shi asibitin ," hajabin da yayi wa farin sani domin shi da kan sa ya saya mata su guda biyar mabanbantan launika .
Shiru ne ya ratsa ɗakin ,"
Doctor hamza yayi shiru kan sa a sunkuye da alama ya zurfafa cikin tunanin me yake shirin faruwa ne ? Da gaske ta gudun ne ? To meyasa zata yi haka ?Anya tana cikin Hankalin ta ? Ko dai gida suka koma tare da RAHIMA ? Idan ba haka ba yaran wa suka sani ? Ina za ta ? Basu da kowa ƴan gudun hijira ne .
Ina baby ??
Da sauri babban likitan yace a je a zo da baby , yana fatan Allah ya sa wutar masifar da take son kunnuwa masa a asibiti kar ta kai ga ruruwa har ta ɓata masa sunan asibiti .
Nurse ɗin ta dawo tare da Baby wacce ɗumin tsaftatatcen ruwan da aka cika mata ciki da shi ya sa ta fara bacci ,"
Miƙa masa ita aka yi ya karɓe ta , bai ce ƙala ba ya jiyo ya fito daga ɗakin ,"
Wajen da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo
Mu tafi gida yace da su ,!
Ita Yakaka ta koma gida ne ? Meyasa ta tafi ta bar baby wanne irin shirme ne wannan ?
cewar Amne ,
Yaya dakta Ina yakaka ɗin ? Bata da lafiya ne ?
Shiru yayi bai amsa musu ba , ya tsinci kan sa cikin ruɗani ,
Kai tsaye gidan Amne ya nufa da su , Amne riƙe da jaririya tare da Falmata suna baya a zaune shi kuma yana jaan motar ,"
Takamaimai bai san tunanin me yake ba , abu ɗaya ne yake fata , shine ya je gida ya tadda ta tara da Rahima sun koma gida , wani tsoro-tsoron tabbatuwar bata gidan ya sa shi kin ɗaga waya ya ƙira rahima yafi so yaje gidan da kan sa ,"
Ku shiga gida Amne zan je na duba ta wataƙila sun koma gida ita da Rahima , ya furta hakan ba tare da ya bari sun haɗa ido da Amne ba wacce take kallon sa
Wai me su likitocin suka ce maka ne ? Cewa suka yi sun tafi gida ita da rahima ?
Waigowa yayi ya dube ta , da hannun ya nuna mata Falmata tare da yi mata Alamun roƙon tayi shiru ta bar maganar tukun , " duba da yadda a halin yanzu ma Falmatan duk a hargitse take tunda suka hau motar bata ce uffan ba sai faman share ƙwalla take tana jaan hanci ,"
Fita yayi ya buɗe mata kofar motar ,
Amne bata sake magana ba ta kamo hannun Falmata suka fito tare da jaririyar zuwa cikin gidan ta ,"
Komawa yayi cikin motar ya zauna ya ɗora hannuwan sa bisa kan Steering motar yayi shiru , zuciyar sa na kai kawo ,"
Ƙwanƙwasa gilashin motar da aka yi shi yasa shi ɗago kan sa ya sauke akan matashiyar yarinyar da ke tsaye a jikin motar sa ,"
Murmushi tayi masa ya ga lokacin da bakin ta ya motsa alamun gaisuwa ,"
Gyaɗa kai yayi kafin ya juyar da kansa ya fara ƙokarin tashin motar ,"
Zaton sa irin ƴan matan unguwar ne take gaishe sa ,"
Ƙara ƙwanƙwasa motar tayi da ɗan ƙarfin ta , tana masa magana ,"
Tsaki ya jaa mai sauti kafin ya sauke gilashin motar ,"
Kalaman ta suka doki kunnuwan sa da yasa ba shiri ya zuro kafafun sa wajen motar gami da miƙewa tsaye ,"
Me kika ce ?
Ɗan matsawa tayi baya kaɗan tana wani guntun murmushi tace
Yakaka ce ta aiko ni , tace na sanar da kai ita ta tafi Abuja wajen Baban Ƴar da ta haifa domin a ɗaura musu aure , dan haka kar ma ka sha wahalar neman ta bayan auren su nan da watanni kaɗan idan sun gama moneehmoon zata dawo kuma tace wai......
Marin da ya kwashe ta da shi ya hana ta ƙasara zancen ta ,sai da tayi taga-taga ta sunkuya , tana ɗagowa ya sake ƙara mata wani ,"
Shoƙo gelen wuyan ta yayi ya maƙure ta , "
Ina kuka kai ta ? Ke da su waye kuka haɗa baki kuka sace ta ? Zaki nuna min inda take ko sai na sada ki da jami'an ƴan sanda sun lallasa ki ,"
Idanun YAGANA sun fiirfito tace wallahi gaskiya nake faɗa , yakaka ƴar uwa ta ce tare muka zo garin nan , tun a sansani muke tare , cikin shege tayi madam ɗin da muke yiwa aiki ta kore ta , shine yanzu bayan ta haihu suka haɗa baki ita da uwarɗakin ta ta gudu zata koma wajen shi suyi aure ,"
Angaje ta baya yayi ,"
Ƙarya kike yi ,"ƙarya ne noorie ƙaramar yarinya ce bata isa shirya wannan wasan ba , ban yadda da ke ba , dole zaki faɗi gaskiya idan kika ji duka a wajen hukuma , wayar sa yake ƙoƙarin zarowa lokacin da ya ji tace ,"
Idan ƙarya nake bari na ƙira uwarɗakin nata ka ji muryar yakakar ma wallahi ,"
Bata saurari amsar da zai bayar ba ta danna ƙiran number samy baby bayan ta saka wayar a hands free , wacce daman jiran ƙiran yagana take , "
Dan haka ta rage gudun motar tare da gangarawa gefen hanya tayi parking sannan ta ɗauki wayar ,
Hello Doctor tace da shi , bata jira amsa sa ba ta juya harshe zuwa turanci ,"inda take cewa
Nasan zaka yi mamakin yadda abubuwa suka faru , wanda a zahiri ba wani abu bane na ban mamaki duba da yadda idanun ka suka makance basirar ka ta toshe , zuciyar ka kuma ta mace akan son yarinya yakaka , ita ma haka tata zuciyar ta mace , ta samu toshewar basira tare da makancewa cikin son wanda zuciyar ta ta zaɓa har ma ta daɗe da mallaka masa ruhi tare da gangar jikin ta baki ɗaya , " ba wani bane wannan illah uban ƴar ta wanda soyayya ta sa ta bashi kan ta , har kuma ta zaɓi rabuwa da ƴar ta tare da ƙanwar ta saboda ta tsira da shi , kana mamaki ko ? Ko kuwa zato kake ƙarya ne ," tunanin ka shiri ne koh ? To bari ka ji kasan daman waƙa a bakin mai ita yafi daɗin sauraro ,"
Juya harshe tayi ta dawo hausa ,
Yaks ,
Yaks ,
Ke yaks
A hankali ta ɗago kan ta da yake bala'in sara mata ta kalle ta da idanun ta da suke cike taf da hawayen tausayin kai ," duk da daman tana jin ta tana waya da turancin da ba fahimtar sa take ba , ba bacci take ba ,
Na'am anty samy ,"
Ga Yariman naki ko kuwa me ma kike ƙiran masoyin naki ??
Cikin sanyin muryar tace Bature kam silum ?
Eh shine akan wayar riƙe kuyi magana ,"
Anty samy kice masa kawai ina zuwa zan zo wajen sa zaki kawo ni , bana jin yin dogon magana , zuciya ta ciwo take min ban san a wanne hali Falmata take ciki ba ,"
Cije baki samy baby tayi tana hararar yakaka da ta lura tana son ɓata mata shiri ,"
Bana son kinibibi bake kika yadda zaki wajen nasa ba ko na mayar ki ne ?
Shiru tayi bata ce e ba ko a ah
Karɓi wayar ki masa magana ya ji ki ,"
Alo Bature kam silum , gani nan zan zo wajen ka , anty samy zata kawo ni , amma gobe nake so mu dawo mu ɗauki su Falmata da mama , sai muyi aure mu zauna tare da su Dan Allah bazan iya zama babu su ba ina son ku ku duka sosai ka yadda koh ?
Ƙarɓe kan wayar samy baby tayi tana murmushin nasara , ta koma turanci
Sauran ƙarin bayanin da zai iya gamsar da kai yana cikin kayan ta tare da wayar ta da ta bari a gidan ku , da fatan zaka rungumi haƙuri , ka nemo matar da zata iya mallaka maka ruhin ta tare da sadauƙarwa irin wanda yakaka tayi ga masoyin ta ," idan kunne yaji .... ? Tace da shi tana sauke wayar a kunnen ta tare da latse ta ta kashe ta tada motar tana fincikar ta da ƙarfi ..
Tun kafin ta gama furto zantukan ta yake jin wani abu mai kama da hayaki yana lullube masa zuciya wani irin ƙaƙƙarfan kishi da tsanar yarinyar suka tarwatsa masa rai da ya sa jin kan sa na juyawa , tabbas ta yaudare shi , yaudara mai girma , ta ha'ince shi ta kuma butulce masa ,"
Amma anya , toh Anya gaskiya ne anya ba tursasa noorie aka yi ba ,! Anya tana da wayo tare da hikimar yin mummunar yaudara irin haka , sashin zuciyar sa da soƴayyar ta tayi ƙarfi ta kafa rassa ke son kawo uziri ke son bata kariya ke son wanke ta , ke son fidda zargi a tsakani ,
Bai bi ta kan yagana ba ya faɗa cikin motar sa ya jaa da ƙarfi gami da nufar gida domin ganin shidar da aka ce akwai ,
Gyara gelen ta tayi wanda ya cukurkuɗe , kafin ta ce
Wannan Banzan har mari na yayi akan wata banzar sokuwar yakaka , oho dai a yau zan yi kwanan farin ciki sanin cewa yakaka tayi nisa da garin maiduguri baki ɗaya , " babu ranar dawowa !
Kai kuma marin nan wallahi bashi ka ɗauka , zan rama shi ta wata hanyar da baka yi zato ba a kuma lokacin da baka yi tsammani ba ,
Wucewa tayi ta kutsa cikin unguwar da daman take ta su , tana hararar gidan Amnee inda take da tabbacin ciki jinin Yakaka suka yi bigire ,"
Cikin ran ta ta fara saƙa da mummunar zaren da zai iya zargewa har da ita ,"
Kusan da gudu-gudu ya shiga sashin su Rahima bai ko tsaya rufe ƙofar motar sa ba ,"
Rahima , Rahima , Rahima yake ƙwalawa ƙira ,
Da gudu ta fito daga ɗakin ta tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin ta ta shirya tsaf domin zuwa asibitin wajen su Yakaka , jin shirun yayi yawa tun hantsi har ga shi ƙarfe uku ta ƙarato.ta tabbatar zuwa yanzu ta haihu ,"
Na'am big bro , ina su Yakaka ya jikin nata ? Ta haihu ,? Me muka samu ?
Ina wajen kayan su yake ? Yace da ita haka idanun sa sun kaɗa ,"
Kayan su wa ?
Fatima .
yace da ita
Wani abu zan ɗauko maka ? Me zan ɗauko maka big bro ta haihu ko ? Me ta haifa ?
Ina wajen kayan su nace miki , ya daka mata tsawar da ta firgita ta ,
Da hannu ta nuna masa ɗakin su
Yana cikin wardrobe ,
Kayan yayar fatima nake nufi
Duk kayan su a haɗe suke big bro , ta furta hakan tana karya wuya , ran ta cike taf da jimamin abun da ya hatgitsa musu ɗan uwa haka ,"
Watsi yake da kayan su yana hautsinawa , har zuwa lokacin da idanun sa suka sauka kan ɗan ƙaramin hoton tare da agogo haɗi da damin kuɗin niger da suke chan ƙasan kayan ta ,"
Zuciyar sa na bugawa ya ɗauki ƙaramin hoton fasfo ɗin gami da kai idanun sa kan fuskar kyakkyawan bamarɗen ingarman saurayin da bai fi sa'an sa ba jikin sa sanye da kakin soji na ƙasar niger , hoton a zamunance yake babu wani alamun tsufa ,"
Tabbas shine ba tantama kome gaskiya ne , ya aina haka cikin ran sa lokacin da yake sake jujjuya agogon da rannan ya gan shi a hannun ta , tace masa na BABAN ta ne , tunowa yayi da ranar da ta nace ya kai ta bakin kasuwa , tace cikin kayan ta akwai hoton BABAN ta , ashe duk ƙarya take masa , ashe yaudarar sa take , ashe ganin yarinya ƙarama yake mata ita kuma tana masa kallon soko ?
Sakin hoton yayi tare da agogon suka faɗi ƙasa kan suturun ta da ya saya mata ya fara taku da nufin barin ɗakin
Lokacin da ya ji kafafun sa sun sauka akan ƴar ƙaramar wayar da take jefe a ɗakin , sunkuyawa yayi ya ɗauka ,
Ya kunna ta ,
Call logs ya shiga nan ya ci karo da number da aka rubuta HUBBY BB a jikin ta ,