Showing 18001 words to 21000 words out of 411050 words

Chapter 7 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14345

a ayarin nasu a bayan mutuwar namijin cikin su tare da mata biyun ba ",

Eh nasan maiduguri yakaka mun taɓa zuwa tare da yaakura na ( yayar mahaifiyar ta )

Sau goma kuka taɓa zuwa koh sau ashirin ," da a yanzu kika ce zaki mana jagora ? cewar falmata wacce take ɗingisa kafar ta gefe-da-gefen rigunan su ita da yakaka a ƙulle da na juna ,.

Sau ɗaya dai na taɓa zuwa tun lokacin ina shekaru biyar na taɓa yin rashin lafiya wai wasu kuraje suka fito min shine aka ce sai a Babban asibitin cikin Maiduguri za'a ban magani ," ta karasa zancen tana me ɗaga zanin ta zuwa gwaiwa ," kin ga taɓon kurajen nan yakaka wannan tabon da kike gani tun ina shekaru biyar a duniya,"

Waiwayawa su ka yi jin Falmata ta jaa ta tsaya lokaci guda suka dawo gefe da gefen ta suka tsaya ," yagana tana cewa kin gaji ne falmata ?
Falmata wani wurin yana miki ciwo ne cewar yakaka ?

Fashewa da kuka tayi cikin shishiƙar kuka ta fara cewa yakaka sai da na faɗa miki kar mu taho kar mu taho kika ce sam sai mun taho ," kika nace ," gashi nan yanzu zamu mutu a cikin daji kura ta samu na kalaci ," ta karashe zance tana jaan majina .

Shiru yakaka da yagana suka yi domin a hakiƙanin gaskiya su dukkanin su biyun karfin hali kawai suke domin kuwa ƙarƙashin rayukan su cike yake taf da tsoron duhun daren da ya riga ya fara shigowa ne,"alhalin suna cikin ƙungurmin dajin da basu san gabas ba bare yamma ,"

Kiyi hakuri Falmata ni bana son yawan kukan nan da kike kin san dai baki da lafiyar idanu ," muyi ta addu'a kawai Allah yana tare da mu ," cewar yakaka

Eh Falmata addu'a ita ce mafita kuma ina jin kamar ma mun kusa isa maidugurin dan ina tunanin lokacin da aka kaini asibitin kamar ance wai bamu kwana a hanya ba wai awanni bi......

Ke ni dallah ki mana shiru ,"ke idan ana zancen waɗan da suka taɓa zuwa birnin maiduguri ma har kya sako baki ?

Wucewa gaba Falmata tayi a fusace tana lalube a ranta kuwa tana ayyanawa kome ta fanjama .
[6/24, 9:58 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association


*MAFARI.......*
( _HARGITSIN RAYUWA_ )



*umm'muaz*


4

Ƙanƙame da juna suke kwance a ƙarƙashin duhuwar bishiyar kukar da duhun ta ya haɗu da duhun dare tare da na damina ya bada matsanancin duhun da ba'a ko iya ganin tafin hannu .

Falmata ce a tsakiyar su yakaka da yagana suna gefe-da-gefen ta ,ko ƙokkwaran motsi basa iya yi saboda tsabar zullumi da tsoron da ya cika musu rai ! Numfashi ma a sace suke yin sa yayin da kunnuwan su suke tarwai a buɗe daga jin motsin abun da yake nesa da su da kusan rabin kilomita .

Babu motsin kome a dajin da ya wuce kukan jemagu da kuma wasu ƙananun ƙwarin da ba'a iya tantance kukan su ," haɗi da wani kuka da suke ji daga nesa ƙadan da su wanda tsananin tsoron da suke ji ya sa suka kasa tantance kukan koh na menene ,"ya dai fi musa kama da kukan bijiman sa (shanu) sai kuma jifa-jifa kukan manyan namun dawa waɗanda suke nesa sosai daga wurin da suke .

Ƙasa-ƙasa muryoyin su suka fara tashi ,"
Umm Yakaka zan yi fitsari ,"
Fitsari kuma falmata dan Allah kiyi hakuri mu jira safe.
Falmata kawai kiyi fitsarin nan anan kwance a jikin mu ," cewar yagana

Motsin da suka fara ji mai ɗan karfi yana doso inda suke ne ya sanya su sake damuƙar junan su kafin jikin su ya ɗau karkarwa kar-kar-kar .
Shikenan muryoyin su sun jawo mu su .

Wani ɗumi yakaka da yagana suka ji a jikin su wanda yake tabbatar musu yawaitar motsin da suke ji tare da ƙarin gabato su da motsin ke yi shi ya sanya falmata sakin fitsarin da tace tana ji saboda tsabar tsoro

Haske suka fara hangowa wanda basa raba ɗaya biyu hasken tocila ne ," kafin su fara jin taƙun kafafun mutum ," tare da tashin muryoyin mutanen da baza su wuce biyu ba sai dai magana suke a cikin yaren da su yakaka basa fahimtar sa ,"

Gani suka yi an ɗan kau da hasken tocilan kafin su ji an taho har kurkusa da su ," karar zubar wani abu kamar ruwa ne ya fara sauka kunnuwan su kafin su ji ruwan mai ɗumi ya fara fallatsuwa akan fiskokin su a zaɓure suka miƙe zaune wanda a tunanin su koh ruwan zafi ake watsa musu ,"

Miƙewar da suka yi shi ya mutumin da yake tsaye shima ya zabura tare da yin eho a take kuma ya buɗe murya gami da yin magana da maɗaukakiyar murya cikin yaren sa nan take sai ga hasken tocila ya dallare fuskokin su yakaka ,"

*****

A tsugunne suke bisa gwaiwowin su tamkar mai laifi a gaban hukuma ," maza ne kimanin goma a zagaye da su dukkanin su hannun su rike da makamai kama tun daga kan ,sanduna , gatari ,takobi,kwari da baka , wuƙake , da ma bindigar harbi ka buya ,

Fahimta da suka yi su yakaka basa jin yaren su na hullanci ya sanya ɗaya daga cikin su ya juya harce cikin yaren hausa
Yaro ku su waye ? Kuma daga ina kuke cikin daren nan ?

Nan take yagana wacce da alamu ta fi su yakaka fahimtar hausa ta ce mu ƴan gudun hijira ne daga garin Bama nake waɗanan kuma "tana nuna su yakaka " abokan tafiya ta ne daga nan kauyen mairambiri suke ," ƴan tawayen boko haram ne suka tarwatsa mana garuruwan mu ,"

Duk bayanin nan da suke yi yakaka da yagana basu samu damar ganin fuskokin su waye a tsaye zagaye da su ba su dai sun san mutane ne , kuma a ƙalla sun ji saukin tashin hankalin da suke ciki akan sanin da suka yi ashe akwai mutane dayawa haka kurkusa da su ,".

Juya harshe wannan mutumin da ya tambayi su yakaka yayi ,"tare da yi wa abokan tafiyar sa fassarar bayanin da yagana tayi cikin yaren su na hullanci ," nan take hayaniyar su ta ƙaure a wurin da alama Tausayawa yaran suke tare da Allah wadai da ƴan tawayen boko haram wanda sun riga sun san da zaman su ," kuma tsakanin su da su babu kare bin damo "abun nufi ko da sun haɗu cikin daji basa shiga harkar juna ," ( Makiyaya da ƴan tawayen boko haram )

Bayan doguwar muhawarar da suka yi a tsakanin su nan mutumin ya juya ga su yakaka yace ":
Yaro yanzu ku ina kuka nufa ?

Maiduguri zamu ," ance gwamnati ta tanada mana wurin zama ', za'a kula da mu cin mu da shan mu sutura da wurin kwana har ma ance za'a samu a makarantun gwamnati ," abincin cin mu ma na....

Katse ta mutumin yayi :
Yaro kun san hanyar Maidugurin ne ?

Nan falmata wacce take fahimtar mafi yawan kalmomin nasu ," mayar da magana cikin hausar ne ke yi mata wahala ,

Tayi tsagal tace Baba wallahi bamu san hanya ba", dan Allah ku taimaka ku kai mu Maiduguri dan Allah ta karashe zancen tana matsar ƙwallar wahalar da ta ciko mata ido,"

Yaro zamu taimaka muku amma mu ba Maiduguri muka nufa ba ," mu daga nan ikko muka nufa ,"amma zamu raka ku har inda muke ganin kun wuce hatsari sai mu gwada muku sauran hanyar ," nan wurin da kuke akwai hatsari sosai ,

Juyawa ya sake yi suka yi magana da ƴan uwan sa ," sannan ya juyo tare da cewa ku biyo mu ,"

Lumshe matsakaitan idanun ta tayi lokacin da ɗumin madarar saniyar sabuwar tatsa ya sauka a cikin ta ," dago kan ta tayi daga cikin ƙoƙon da yake cike taf da madarar ta maida kallon ta ga fuskar kanwar ta wacce tayi kasaƙe hannun ta rike da nata ƙoƙon da bata tunanin ma ta kai bakin ta ," idanun ta suna sheƙin ruwan da ya taru a cikin su a tsaye idanun na ta suke ƙem wuri guda ," da alamar tayi zurfi cikin tunani ," a hankali taga ƙwallar da ta taru a gurbin idanun nata sun silalo da gudu sun sauko bisa ƙuncin ta ," da sauri ta ajiye ƙoƙon madarar ta gami da ƙarasawa inda falmata take zaune akan wani ɗan dutse ," dire gwaiwowin ta tayi a ƙasa lokaci ɗaya kuma ta sanya hannu gami da goge mata ƙwallar da suke cigaba da fitowa

Yakaka yau kwanaki biyu kenan muna wayar gari ba tare da iyayen mu da sauran ƴan uwan mu ba ," Allah ya jikan Baba ya gafarta masa ,"insha Allah shi mutuwa hutu ce a gareshi ,"

To amma yakaka mama fa da sauran kannen mu a wane hali suke ciki ? Wataƙila suma ƴan tawayen boko haram sun kashe su irin yadda suka yi wa Baba ," idan kuwa har suna raye tabbas mama tana cikin mawuyacin halin da ya fi wanda muke ciki a yanzu ,"

Yakaka muna shiga birnin Maiduguri abu na farko da zamu fara yi shine neman maman mu ,"

Ƙai hannunta tayi ta lalubo fuskar yakaka jin tayi shiru bata cewa kome duk bayanin da take yi , nan taji ruwan hawayen da suka faca-faca akan fuskar ta ," share mata hawayen tayi kafin a hankali ta kai kanta ta ɗora akan kafaɗun ƴar uwar ta , idan ke kika yi kuka a halin yanzu ni me kike so nayi yakaka ? ,kiyi haƙuri ki daina kuka insha Allah zamu haɗu da maman mu ,"

Nemo yatsun hannun falmatan tayi ta sarƙe su cikin nata hannun "falmata ba ina kuka bane a domin wahala koh raunin zuciya akan halin da muke ciki ba," ina kuka ne akan tunanin halin da mama da ƙannena suke ciki ina kuka akan wahalar rayuwar da kike ciki a halin yanzu alhalin bani da karfin taimakon ki ,"dubi kafar ki falmata ta ɗago kafar falmatan da take ɗaure da ɗankwalin ita yakaka,"

Duk ƙafar ta soke da kayoyi daga idon sawun ƙafar kuma a kumbure yake in da ta faɗa rami a jiya ," Falmata tun tasowar mu ban taɓa ganin ciwo irin wannan a jikin ki ba ,"duk da cewa muna rayuwa cikin talauci amma iyayen mu suna tattalin mu ,da lafiyar mu" amma ki duba daga shekaranjiya zuwa yau da rikon ki ya dawo kaina na gaza wurin baki kulawa gashi duk kin ji rauni ," sai nake ganin laifin kaina da zan iya falmata da goyon ki zan yi nasan da mama ce da ta sauke Bulama ta goye ki amm dubi ni ...

Ɗago kan ta tayi tare da toshe mata bakin ta da hannun ta ," fuskar ta babu walwala tace yakaka daga yanzu ki daina ganin laifin kan ki akan duk wani abun da kaddara zata ɗoramin ,"
Sannan ki daina ganin kamar ni a dalilin bani da ido bazan iya yi wa kaina kome ba ," wasu abubuwan zan iya yakaka ,"a yanzu rayuwa ta sauya min ta inda nake ganin dukkanin wasu abubuwan da a baya bazan iya su ba a cikin sabuwar rayuwar da zamu fuskanta zan iya su ," abun da nake so kawai kar ki taɓa ɗauke matsayin ki na wacce take gaba da ni a koyaushe kika ga zan faɗa rami ki taro ni kin ji yakaka ?

Naji Falmata sai dai nima ina son ki bar min matsayina na yayar ki a duk lokacin da na nuna cewa nice gaba da ke wurin baki kulawa ,"kin ji koh ?

Ɗan siririn murmushi tayi
" naji yaa yakaka ,"

A hankali yagana ta sanya babban ɗan yatsan ta, ta ɗauke ƙwallar da ta gangaro mata daga cikin ido ," tana tausayin kan ta sosai da sosai tun tasowar ta kasancewar ta tashi ne ba tare da mahaifan ta ba mahaifiyar ta rasu tun tana yarinya yayin da mahaifin ta ya tafi ci rani ,"tun tana shekaru goma har yau bai dawo ba "dan haka a hannun kakar ta mahaifiyar Baban ta ta girma" sai dai daga jiya zuwa yau ta sake tausayawa kan ta a sanadin ganin tsaftatatciyar soyayyar ƴan uwan taka da take gudana tsakanin yakaka da falmata , wanda ya sa ta fahimci ba ƙaramin gibi take da shi a cikin rayuwar ta a sakamakon rashin dan uwa koh ƴar uwa da take da shi ba ," sosai soyayyar da ta lura tana gudana a tsakanin ƴan uwan biyu ta birge ta tare da bata sha'awa .

Ajiye ƙoƙon ta"wanda ta riga ta shanye madarar ciki tas " tayi a gefe tare da miƙewa ta nufi wurin da har yanzu yakaka da falmata suke zaune ,"sai dai saɓanin ɗazu yanzu a jere suke a zaune inda falmata ta matsawa yakaka ta zauna a gefen ta suna fuskantar mahuɗar rana da ta fara ɗagowa tana keto tsakankanin ciyayin , ranar ta bada wani haske mai kyau ,"

Dafa kafaɗun su tayi da hanun ta ɗai ɗaya ," idan an gama tattaunawar sirrin tsakanin ƴan uwa a tashi mu tafi mu mayar musu da ƙoran nasu kafi su gama shiri su fara jiran mu kuma ,"kun san dai sun ce da wuri zamu kama hanya saboda miƙaƙƙiyar tafiyar da ke gaban mu ," murmushi yakaka tayi ," yagana baki da dama ,"
Satar kallon falmata yagana tayi wacce ko alama bata nuna ma taji abun da yaganan ta ce ba ,"

Kamo hannun falmata ," yakaka tayi da sauri yagana ta zagayo tare da kama mata ɗayan hannun ,"amma ga mamakin su sai ji suka yi tace
"zan iya tashi da kaina ,!
Yunƙurawa tayi amma sai suka ga ta kai hannun ta gami da lalubar hannun yakaka ta rike gam gami da miƙewa a hankali ,"hakan da yagana ta gani ya sa ta fahimci falmata bata so ta ita ta taimaka mata sai ƴar uwar ta "ɗan tabe baki tayi cikin nuna ko oho ",

*****

To kun ga nan shine karshen dajin konduga daga nan ai gashi kuna iya hango gidajen da suke ta cikin yankin unguwannin Birnin Maiduguri ,"wadancen gidajen da kuke iya hangowa daga nan suna cikin unguwar da ake kira dalori ne , kuna ƙarasawa can kun riga kun shiga birnin Maiduguri ," mu daga nan muke sake komawa mu ɗauki hanyar in da muka nufa ," wannan dogon bayanin yana fitowa ne daga bakin bafullatanin mutumin nan ,"bayan sun kawo su yakaka iyakar dajin yankin konduga da cikin garin maiduguri ,"

Nan take su yakaka suka durkusa akan guiwowin su suna masu jero godiya da tarin addu'o'i ", zuciyoyin su kuwa ƙwal kamar an musu bishara da wani babban abun Alkairi,"

Da murmushi ɗauke akan fuskokin fulanin nan su biyar "da alama sun baro sauran a daji tare da dukiyoyin su (shanun su ) suke amsa jerun gwanon addu'o'in su yakaka ," kafin mutumin ya ɗora da cewa toh yaro sai ku kula da kan ku sosai ,maiduguri babban gari ne sosai domin haka sai kun yi taka tsantsan da kome , da mu ƴan gari ne da zamu sanya ku a hannun wasu da muka sani to mu ma bamu san kowa ba cikin maiduguri,"

Sanya hannun sa yayi a aljihu ya zaro wata tsohuwar naira ɗari biyu ya damƙa a hannun falmata wacce ya lura bata gani ," daga haka suka yi musu sallama tare da juyawa suka ɗau hanya abun su ba tare da sun sake waiwayawa ba ,"

Shirun dakikai biyu zuwa uku ne ya gitta tsakanin ƴan matan uku bayan juyawar fulanin zuwa inda suka fito ,"ga su dai ga birnin maiduguri bayan doguwar tafiyar da suka yi na kimanin kilomita 74-76, akan kafafun su daga ainahin garuruwan su , da kuma tarin ƙalubale da hatsarin da suka shiga a yayin tafiyar ," wanda ya kamata ace a yanzu da maɗaukakin farin ciki za su durfafi birnin na maiduguri , to sai dai a halin yanzu da fulanin nan suka juya tare da tafiya suka bar su a faffaɗan fili sararin Allah da ya tafi ɗoɗar daga nesa suna hango gidajen jama'a da fulanin nan suka tabbatar musu gidajen cikin birnin maiduguri suke ," sai duk suka ji zuciyoyin su sun raurawa ,'akan tunanin ina kuma suka dosa ? Ina zasu nufa ?

Falmata ce ta katse shirun nasu a yayin da ta tattaro gutun yawun bakin ta da ya gama bushewa a sakamakon ranar damina da aka bude a yau ", Yakaka tsayuwar me muke yi ne kuma ? Kamata yayi mu ƙarasa cikin garin mu fara da neman maman mu a yau ɗin nan kin ga idan Allah ya sa muka ganta kafin dare ,"yau baza ta shiga cikin lissafin ranakun da zamu ƙara kwana ba tare da ita ba ko kuwa ?

Mukut ! Yakaka ta haɗiye guntun yawun da ya saura mata a baki ," Falmata a yadda fa nake hango girma da yawan gidajen da suke cikin Birnin Maiduguri ya sha banbam da irin na garin mu" amma dai bari mu ƙarasa mu gani ,"

Yunkurawa suka yi tare da kama hanyar suna tafe babu me cewa ƙala ," sun yi tafiya me ɗan tsawo zuwa lokacin da suka fara cin karo da gidajen da suke farko-farkon unguwar dalori Qaurters .

Ware ido sosai yakaka tayi tana kallon tsarin gidajen tare da yawan mutanen da ta gani suna ta kai kawon su ," nan take taji zuciyar ta buga da tunanin ina zasu fara bi su nemo mahaifiyar su a cikin wannan faffaɗan birnin ?

Ta bangaren yagana kuwa yawan jama'a da tsarin gine-ginen , bai wani zama baƙon abu ba a saboda babu laifi garin su "Bama" shima babbar Alkarya ce wacce take cike da Al'umma da kuma cigaba dai-dai da zamani ," tunanin ta ya fi karkata ga inda zasu je su samu mafaka kamar yadda kafin su fito daga gida a lokacin da labarin shigowar ƴan tawayen boko

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login