Showing 138001 words to 141000 words out of 411050 words
Chapter 47 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ta ga Tafeeda wanda a zahiri bai shirya ba baya kuma fatan wani nasa makusanci ya san irin ta'asar da ya aikata a rayuwar sa , duk da yasan Tafeeda aminin sa ne , amma bashi da karfin guiwar sanar da shi wannan auka-aukar da yayi , to ma me zai ce ? Ta ina zai fara ?
Ko babu kome shi ɗan nasaba ne , ɗan sarauta , ɗan manyan mutane wanda wurin su ake hangen kyaun tarbiyya tare da nagarta har mutane suyi koyi ,
yana jin zuciyar sa na nawi a duk lokacin da ya tuno da matsayin sa tare da martabar sa ga idanun tarin wasu mutane YARIMA ne shi wanda ake sa ran bayan shuɗewar wani lokaci idan da rai ya zama SARKI , JAGORA kuma SHUGABA abin KOYI ,
Anya-anya shi bai faɗa cikin wata babbar musifa ba kuwa ??
Ya ɗauki tsawon lokaci a haka yana kwance ba kuma bacci yake ba har zuwa lokacin da ya tabbatar bacci ya ɗauki Tafeeda , sannan ya miƙe gami da shiga banɗaki ya ɗauro Alwala ya zo ya fuskanci Al-Qibla yana mai fatan Allah ya kawo masa mafita ya kuma yafe masa zuban sa !
Kewar da take binne cikin ran yakaka tare da tsananin son biyamuradi youssouf sune suka yi toroƙo suka hana ta sukuni tun bayan rabuwar ta da samy baby , har ƙamshin sa ta dunga jiyowa lokacin da ta sanya kafafun ta cikin sashin doctor hamza wanda yayi mata jagora har zuwa cikin falo , illahirin tsukin wajen ya ɗauki kamshin kakkarfan turaren biyamuradi youssouf wanda yayi tasiri matuƙa wurin ƙarasa lugui-guita rarraunar zuciyar yakaka ta ƙarasa narkewa cikin so da begen biyamuradi ,
Hatta Falmata da Rahima sai da suka fahimci tana cikin damuwa , juyin duniya suka nemi sanin meke damunta ?? Tace musu babu kome a ƙarshe da ta ga sun damu ,musamman Falmata da ta gaza cin abinci dare na kirki , kamar yadda ita ma yakakar ta gaza ci , sai kawai tace kan ta ne ke ciwo , " nan ma dai wani sabon tashin hankali ne ga Falmata domin kuwa kalmar ,"sannu," bata yanke daga bakin ta ba har bacci ya ɗauke su !
Washegari
Misalin ƙarfe 8am Hamza ya ƙira Rahima a waya inda yake sanar da ita su buɗe masa ƙofa zai shigo ya shirya , " daman sun riga sun jima da tashi dan haka.saƙon nasa kawai ta sanar ga su yakaka su dukkanin su suka miƙe ,
A bakin kofar sashin nasa suka haɗu da ladabi suka gaida shi ya amsa cikin gaggawa yana amsar ɗan mukullin sa da yake hannun rahima,'
Ku jira ni anan na gama shiryawa yanzu na fito , kar ku tafi ko'ina ," ya furta hakan yana shigewa ," har yayi ciki sai kuma ya kira Rahima suka shiga tare ,"
Hankalin yakaka ya kai ga manyan rumfunan da ta gan su a kakkafe a harabar gidan birjik wanda bata san lokacin da aka samar da su ba , ana ta faman shimfiɗa manyan dardumai da kilisai a ciki , babbar ƙofar gidan a wangale take ana iya hango kai kawon da ababen hawa suke akan titin da ya bi ta gaban gidan , wata mota ƙirar bus ce ta tsaya a ƙofar gidan ,
Manyan Mata ne su rai shidda suka fito daga motar sai kuma ƴan mata sun kai su biyar , dukkanin su suna yanayi da juna farare ne sol-sol dogaye , mafi akasarin su lafaya ce a jikin su wacce bata ƙarasa ƙasa ba iyakar sangalalen kafafuwan su, hannun su zuwa kafafun su da manyan zanen lalle , jazir "
Manya-manyan jakar bacco sun kai guda biyar suka kinkimo zuwa cikin gidan , waccen da wannan sun kama wannan ma da waccen sun kama , uku daga cikin manyan matan ne basu sa hannu ba wurin ɗaukar kayan ,
Daga gefe suka tsaya tare da ajiye kayan hannun su ,
Ɗayar da ta tsaya biyan direban motar itace ƙarshen shigowa ,
Magana tayi musu kafin ta nufo sashin Hamza kai tsaye , su kuma suka dakata daga inda suke , duk abun da suke idanun yakaka yana kan su ta nacewa kallon su , yanayin su ya mata daban da na mutanen da ta saba gani ,
Idanun ta ya sauka akan matar da take nufo su , wacce ita ma hankalin ta ya kai kan su yakaka , sosai suke kallon juna ita da yakaka lokacin da take ƙarasowa gurin ,"
Da wata irin murya da ta fito da sauti sosai tace RAHIMA ,
Dai-dai da fitowar Rahima wacce jin sautin muryar da ko a mafarki baza ta mance ta ba tana ƙiran sunan ta ya sa ta ƙarasa takowa da gudun gaske ta rungume ta bakin ta na kiran ,
Amne ! Amnee !
Rungume Rahimar itama tayi idanun ta na nacewa kallon yakaka wacce ta sunkui da kai tare da riƙo hannun falmata , saboda wani irin yanayi da take hangowa a cikin idanun matar mai kama da idon wata wacce tayi wa farin sani ,"
A hankali ta zare Rahima wacce take ta murna tana dariya daga cikin jikin ta ,
Abnatay wacece wannan ? Ta furta hakan tana nuna mata yakaka da hannun ta da ya sha awarwaro da jaan ƙunshi ,
Yakaka da Falmata ne ,
Su waye su ƴan uwan ku ne ?
Da ɗan murmushi tace , " ƴan gudun hijira ne yayan mu ya kawo su ," ta ɗora da jawo hannun yakaka ,
Yakaka ga maman mu ,"
Nan take yakaka da falmata suka buɗe haƙoran su suna dariya kafin duk su kai guiwowin su ƙasa ,
Mama sannu da zuwa ina kwana , suka haɗa baki wajen gaishe ta ,"
Da sauri ta ɗago yakaka ,
Tashi - tashi yarinya ta babu kyau durƙuso a halin da kike ciki , sannun ku kuna lafiya ?
Lafiya lau duk su biyun suka amsa ,"
Ɗauke idanun ta tayi daga kan yakaka tana saita nutsuwar ta tace ga Rahima
Ina yayan ku ??
Yana ciki ta bata ansa
Janye idanun ta tayi daga kan su falmata ,lokaci guda ta miƙa hanya zuwa ciki wajen Hamza ,
zuciyar ta na cigaba da kambama mata wasu kamanni masu karfi dake tsakanin yakaka da Rahimar ta , da a tashin farko da ta ɗaura idanu akan ta ta firgice , ƙewar ƴar uwar ta na mamayar ta har idanun ta suna tara ƙwallar tunowa da ita a take taji gidan ya fara mata duhu ,
kome yana da sanadi kome yana da mafari , nan gidan , nan sashin shine mafarin kome , nan inda dugadugin ta ke takawa a yanzu shine mafarin tarwatsewar rayuwar Rahimar ta da yayi sanadin rabuwar su , ko tana ina ?? Allah shi kaɗai ya sani ..
sai dai jikin ta na bata Rahimar tana raye kuma zasu haɗu zata dawo gare ta , abu ɗaya ne fargaban sa ke guiguiyar ran ta kullum wayewar gari shine Rahimar zata dawo mata ne a matsayin Rahimar ta ƙanwar ta , ko kuwa zata dawo ne da ƙudirin ɗaukar FANSA ,...... ?
******
Nan sashin Hamza , mahaifiyar sa tare da ƴan uwan ta da tsirarun ƙawayen ta , 'tayi bigire daga yau zuwa gobe da zasu yi tafiyar su !
tsakanin ta da dangin mahaifin su Hamza kallon nesa-nesa ne ko gaisuwar fatar baki bata haɗu su da kannen mahaifin su hamza ba ,tamkar ma gudun haɗuwa da junan su suke ,
saboda ta riga ta ƙullace su irin ƙullata mai tsanani domin tana musu ganin sune SANADIN KOME , kowanne daga cikin su su rai shidda yana da tabon sa a idanun ta idan aka cire UNCLE SALMAN wanda shi kuma a halin yanzu baya raye a duniyar ,...
Su ma a ɓangaren dangin mahaifin nasu kowannen su ya ɗarsawa ran sa tsanar AMINA AL-ARABI SHUWA , saboda wasu manyan dalilai nasu ,"
Cikin awa ɗaya jal da haɗuwar ta da su yakaka , ƙaunar yaran ta gauraye zuciyar ta , dan haka bata jinkirta ba wurin tambayar su labarin su da na iyayen su ,
Cikin sakewar da suka yi da ita suka bata labarin su tirƴan-tiryan , kafin su gama tausayin su ya sa zuciyar ta tayi laushi , sau uku tana maimaita musu tambaya game da mahaifiyar su akan menene sunan ta ,
Amsar su ɗaya ce , su basu san ana kiran ta da wani suna ba bayan maman Yakaka , su kuma suna kiran ta Mama ,!
Ta jinjina da jin cewar mahaifiyar ta su kurma ce bata magana, ta kuma tausaya , sannan ta cire tsammanin da take ko yaran suna da wata alaƙa ta kurkusa da ita/da Rahimar ta , tasan Rahimar ta ba naƙasasshiya bace ba cikakkiyar lafiyayyar mutum ce , dan haka ta danganta kamannin da take gani na rahima tare da yakaka a matsayin kawai halittar ubangiji ,"
Karfe 10am aka ɗaura auren zainab da angon ta colonel Tahir Ma'aji , inda aka zarce da walima wanda mahaifin Amarya ya shirya ƙarƙashin jagoranci tare da kulawar Hamza ,
A daddafe Biyamuradi Youssouf ya tsaya aka ɗaura auren tare da shi , saboda hankalin sa da yake a tashe da son tafiya gidan madam saly dan jin ko an kai ga samun ta ,? "
A gurguje yayi wa ango gaisuwar taya murna , sannan ya jaa Tafeeda gefe ,
Ɗan ouwa ni zani koma bakin aiki ,ils ne me donnent que quarante huit heures , zuwa lokacin da nake issa bakin aiki , awanni sun kai ga cika ,"
Bai damu da kallon tuhumar da Tafeeda ke bin sa da shi ba , ya miƙa masa hannu suka yi musabaha ,
Idan ka cimma gidaa ka kiraye ni ɗan ouwa ,' Allah shi kiyaye hanya ,saduwar Alheri
Zame hannun sa daga cikin na Tafeeda yayi tare da juyawa ya fara taku domin barin wurin ,"
A takaice Tafeeda yace da shi ,"
me zan ce ga hajiya umma tare da mai martaba idan sun ka tambayeni halin da na riske ka ciki ??
Juyowa yayi da wani guntun murmushi a fuskar ka kace da su ,"
Yarima na a halin lafiya a bigire mai tsaro ,! Sannan ina miƙa gaisuwa ta a gare su tare da fatan Alheri !
Gyaɗa kai Tafeeda yayi yana mai juyawa ya shige taron jama'a cikin ran sa ya ƙudurce dawowa ya cimma youssouf su fuskanci matsalar sa tare , yanzu ma domin yana cikin ujila ne shi da kan sa awanni arba'in da takwas ɗin aka ba shi , dan haka su dukkanin su basu da isasshen lokaci a halin yanzu !
Motar sa ya jaa da gudun gaske ya ɗauki gwadaben da zai sada shi da unguwar madam saly ,
Bai ko rufe motar ba ya taka ya shiga gidan , " a ƙufule ," sai dai tun daga bakin rumfar ya fara fahimtar sauyin da yake wurin domin dai babu kowa a cikin rumfar hatta kujerun cikin rumfar a tattare suke a gefe , da alamu yau ba'a shirin yin aiki ,"
Kai tsaye ya sa kan sa cikin gidan hanyar da ya bi jiya ita yau ya bi ya zo har bakin ƙofar ɗakin madam saly , har lau bai ga giftawa kowa ba tamkar gidan ba kowa ,"
Garam ! Ya ga ƙofar ɗakin madam saly garƙame da ƙwaɗo har biyu ƙarami da wani fankacece iri na rufe ƙofar babban gareji ,"
Duka ya kaiwa ƙofar ɗakin da ƙafar sa da matuƙar ƙarfi wanda ba domin ƙofar ta ƙarfe bace da ta karye,
Ya ɗaga murya yana cewa
Ina masu gidan ??
Ina masu gidan ??
Ko giftawar kadangare bai gani ba , bai buƙatar a sanar da shi , ya fahimci sun gudu ne ," nan take wani malolon bakin ciki ya maƙale masa a maƙoshi ,"
Murza fatar goshin sa yake yana kokarin saita kan sa lokacin da yake kan hanyar barin gidan cikin ran sa yana aiyana zai dawo kuma haɗuwar su ta gaba baza ta taɓa yiwa madam saly kai dama duk mutanen gidan kyau ba ,
Cikin takun da bai ko duba inda yake jefa kafafun sa ya bar gidan yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa da ya ɗan kora ruwa ko zai samu sa'ida azabar damuwa da yake ciki ta isa haka , amma tunowa da tafiyar ratsa daji da take gaban sa ya sa shi yakice tunanin shan barasa a wannan lokacin ,
ya fisgi motar da matsanancin haushin rashin cikar buri ya bar wajen bai ko kula da taron ƴan cha-chan da suke baje akan wata babbar tabarma daga ƙarƙashin bishiya a gefe suna faman yin karta tare da dara , da ya watsawa ruwan kwatami daga jikin su har zuwa fuskokin su ba ,
Wucewar sa kenan ɗan liti ya fito daga banɗaki inda yayi maɓoya , bayan ya tabbatarwa da su madam saly su watse kaf su bar shi shi kaɗai a gidan zai jira zuwan kurtun ɗan sandan , ayi wacce za'ayi ɓera ya zubda garin kyanwa!
Banten uba ! Kuturi ai yau da na yadda ya ganni sai ɗan buzu na , ai wallahi da sai dai Baba malmo ya auro wata safara'un ta haifi wani ɗan litin ba dai ni ba ,! Chab kai ka ga mutum kamar safurarren doki ??? Yana tafiya haka - haka - haka ,"kamar jarumin sadauki a fagen daga ?? Ko a mafarki na gan ka ai nayi sadaka !
Ahayyeee saly fara ta zo ta lale min kuɗin gadin gida da nayi mata ta biya ni ,," kurtun ɗan sanda kuwa cewa zanyi na gama da shi ," ah to meye ?? Ko banza ai na shaƙi tsoro da bugun zuci, " Rikicin duniya kuwa ai da me rai ake yin sa ehe ,!
****
Bayan kammala bikin zainab da sati guda doctor Hamza ya sanya yakaka a makarantar islamiyya da Rahima take zuwa , amma ta ta bangaren matan aure take zuwa kullum da safe karfe 8am.zuwa 12pm falmata kuma aka cigaba da koyar da ita arabi da bokon a gida ,'
A makarantar yakaka ta san sabon sunan da doctor hamza ya laƙaba mata a matsayin sunan ta na yanka ,watau AMINA MUSTAPHA DILMARI ,
Sosai take mayar da hankalin ta kan karatun ta kamar yadda doctor hamza kullum yake gargaɗin su , a gefe guda kuma cikin ta na cigaba da bunƙasa ta yadda har girman sa ya so yin yawa dan haka a awun da ta je cikin satin nan aka hana ta shan su madara da sauran cimakar da take sa yaro ya girma sosai a cikin mamar sa ,"
Da wata safiya tayi shirin makaranta ta fito zata tafi sai ga motar samy baby ta tsaya a gaban ta , gaban kaɗan da gidan su doctor Hamza
Nan ta nemi ta shigo suyi wata maganar da take tafe da ita , tayi murna ma da suka haɗu anan waje ,"
ba musu yakaka ta shiga motar tana murna sake ganin samy baɓy a dai-dai wannan lokacin da ran ta yake cike taf da son sani game da youssouf
Nan cikin motar samy baby ta fara yiwa yakaka huɗubar da ta zamto kuskure na biyu da yakaka zata afkawa a rayuwar ta ,
A sanyaye ta fito daga motar bayan ƙarasowar su gaban makarantar , ta luluƙa a duniyar tunani , ta yadda har bata san lokacin da samy baby ta jaa motar ta tayi tafiyar ta ba ,"
Idan aka zo ga batun ƙaunar ta ga youssouf kome kunce mata yake , tana son shi sosai , yana birge ta fiye da kowanne mahalukin da ta taɓa cin karo da shi a rayuwar ta , amma anya ? Anya girman son da take masa ya kai mizanin da zata dai-daita shi da falmata ? Ƙanwar ta jinin ta ? Abar batun cikin jikin ta shi wani sabon abu ne da yanzu yake kan hanyar shigowar sa cikin rayuwar ta , duk da cewa akwai ƙauna irin ta ɗa da uwa a tsakanin ta da abinda yake cikin ta wanda tasirin son da take yiwa shi youssouf ɗin yake mamayar abun da yake cikin cikin nata tare da ninka mata ƙaunar son gudan jinin sa da ke tare da ita ,
To amma falmata ba ?? Falmata haske ce kuma sanyi ce sannan cikamakin farin ciki ce cikin rayuwar ta , tun asali akwai shaƙuwa da so mai tsanani a tsakanin su fiye da wanda aka saba sani tsakanin saƙo-da-saƙo na haihuwa , ya zarce ƙauna irin ta tsakanin ƴa da ƙanwa sai dai a kwatanta shi chakuɗuwar jini da soyayya irin ta tsakanin tagwaye wanda ƙarya ɗan adam ya zare wannan tsananin wannan son da shaƙuwar da ya samo asali tun daga ranar faruwar halitta a cikin mahaifiya , sai dai fa ikon rabbi ,"
Zata iya kome domin ganin ta samarwa da falmata farin ciki a kowanne bigire na rayuwa fatan ta a koyaushe ta hango farin ciki bisa fuskar miskiniyar ƙanwar ta , sai dai wannan lamarin da yau anty samy ta zo mata da shi , yarda da shi tare da yin aiki da shi tamkar ta ɗau takobi ne ta gille duk wani farin cikin da Falmata zata iya shinshinowa a rayuwar ta , tamkar ta kassara ruhi da gangar jikin falmata ne , wacece FALMATA idan babu YAKAKA ???
Ba ta san ta kawo karshen makarantar ba sai da ta ji ta kaiwa bango karo ,
Zamewa tayi ta zauna dirshan a cikin ƙasa gami da fashewa da kuka , a sarari take furta kalmar," bazan iya ba , bazan iya ba, !
****
Cikin satittikan da suka biyo baya samy baby ta cigaba da zirya tsakanin makarantar su yakaka inda take killace ta tana cigaba da cusa mata ra'ayin da take ganin zai iya tsallakar da yakaka daga faɗawa hannun sofi , ta hanyar yin amfani