Showing 6001 words to 9000 words out of 411050 words

Chapter 3 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14348

sai daɗa hura wutar kiyayyar ɗiyoyi matan da ake haihuwa a gidan abdoul-azezu take " a cewar ta sarauta ta kama hanyar barin hannun Baskore tunda ga alamu Sarautar tana dakatawa ne akan Abdoul-azizou da yake a matsayin yarima a lokacin ,

Ba tare da neman shawarar Abdoul-azizou ba mai martaba ya nema masa Auren ƴar abokin sa kuma yayan matar sa "Hajiya uwa "Babban Limamin Maraɗi "Malam muhammadou" wacce ake kira "Saratu " .

Tare da sa hannun hajiya uwa wacce tayi ɗare-ɗare akan harkar bikin nan tayi uwa tayi makarɓiya , ranta ƙwal ! tana ƙitsimawa "idan sarauta ta kuskure masu ta wani wuri kasancewar ita bata taɓa haihuwa ba toh tabbas ga sarautar nan dawo masu ta wani hannu " tana da tabbacin daga saratu ta zo ta haifi ɗa namji shikenan sarauta ta zamto tasu.

Saratu ita ce ɗiya ta shiddah cikin jerin ƴaƴan Liman muhamdou , mahaifiyar ta tun tana ƴar shekaru biyu suka rabu da mahaifin ta "mahaifiyar ta ƴar Nigeria ce a can wani gari da ake kira zuru a ƙasar kebbi Nigeria , Saratu ta taso tsakanƙanin matan uba , babu irin izaya da wahalar da ba'a gana mata ba , shi ya sa ta tashi a kangare sannan me mummunar zuciyar da take cike da ƙudirin ɗaukar fansa,

Lokacin da ta shekara goma sha biyar ta kasance fanɗararriyar yarinya ce ta kin ƙarawa wacce tun da ta fara girma ta buwayi matan mahaifin nata da fitsara da raini uwa uba saratu ta kasance me matukar fasahar iya shirya zancen ƙarya da tuggu domin ta tada husuma a tsakanin matan mahaifin ta duk a cikin mummunan ƙudirin ta na ɗaukar fansa .

A take -take zata haɗa zantukan ƙarya ta ɗora mutum kome girman sa akai kuma ya hau ya zauna daram , saboda tsabar yadda ta iya shirin ƙarya , wasa-wasa sai da ta maida gidan mahaifin ta sansanin yaki a wurin matan gidan , kullum cikin faɗa ake kamar garken karnuka , ita kuwa ta koma gefe tana wake-waken ta ,bayan idanun su ta shiga ɗaki ta ci dariya son ran ta ta fito tsakar gida tana karya wuya tare da bai wa wacce ta zuga hakuri .(Saratu kenan , ƴar malam wacce taƙi halin malam )

A tsakanin matan mahaifinta su uku babu wacce ta kai ga fahimtar hallayar saratu na karya da munafurci "sakamakon rashin haɗin kan su tare da zazzafan kishin su tun asali " sai shi mahaifin nata ne da kan sa ya fahimci "saratu ita ce matsalar gidan sa " yana tunanin yadda zai iyi ya samu ya kawar da ita daga gidan sa "( ya aurar da ita ) .

Sai ga sakon kira daga mai martaba "Liman bai yi ƙasa a gwaiwa ba "ya amsa kiran da ya sanya shi kwanan farin ciki bibbiyu na farko dai farin cikin zai zama surikin yariman maraɗi a yanzu , kuma surikin sarkin maraɗi a gobe idan da rai , uwa uba zai rabu da annobar da ta ke sanya shi fargabar shigar sa gidan sa a kullum,

Dan haka cikin rawar jiki da murnar sa da ta kasa boyuwa ya amsawa mai martaba sarki youssoufa , ya bawa yarima Abdoul azizou auren Saratu koh gobe ake so a ɗaura ya shirya ,

cikin farin ciki da karamci da aka nuna masa Sarki youssoufa ya tsayar da ranar ɗaurin auren Abdoul azizou da saratu ranar ishirin da biyar ga watan sha biyu shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da tamanin da biyar 25-Dec-1985 .

A daren ranar ya aika aka kira masa yarima abdoul azizou , in da ya sanar da shi hukuncin da ya yanke tare da bashi umarnin ya shirya gobe da Maraice ya je su ga juna shi da saratu ɗiyar liman domin kwanaki ishirin da ɗaya kachal suka rage a ɗaura musu aure ,

Ba tare da yarima Abdoul azizou yana fahimtar sauran kalaman bakin mai martaba ba ya amsa masa gami da yi masa godiya da sallama ya fito daga turakar mai martaban zuciyar sa cike da zogi da raɗaɗin bacin ran tashin hankalin da yake iya hango samuwar sa tsakanin sa da abar son sa "safiyyah "

Tabbas shi yasan yadda safiyyah take tsananin kaunar sa da kishin sa , yasan duk lokacin da ya je mata da labarin auren da aka riga aka nema masa ya kuma zama dole a gareshi ya amsa hannu bibbiyu , kasantuwar bai taɓa musantawa mahaifin sa ba akan duk wani hukunci da ya yanke a rayuwar sa domin shi mutum ne me ilmin addini sosai , yayi karatu sosai arabi da boko ya san irin haƙoƙin da iyaye suke da shi akan ƴa ƴan su hakan ya sa ya kasance ɗa mai tsananin biyayyah ga iyayen sa .

Dan haka a yanzu ma yayi aniyar karban auren da za'a yi masa da hannun aminci duk da cewa shi ba son auren yake ba asalima bai taba kawowa ransa sake yin aure nan kurkusa ba kamar yadda tun da yake bai taɓa son wata ɗiya mace irin son da yake yi wa safiyar sa ba kuma baya jin zai sake son wata ƴa mace irin son da yake yi mata " ya ajiye auren da za'a yi masa a karo na biyu a mizanin kaddara "

Sai dai babbar matsalar sa a yanzu tunanin hanyar da zai bi ya tunkari saffiyah da batun karin auren sa ,"a daren yau din domin baya son ma lamarin ya kwana ba tare da ya fitar mata da hakkin ta ya sanar mata ba a matsayin ta na matar sa da suke zaman aminci , kaunar juna da fahimtar juna " sai dai ya san mata idan aka zo batun kishiya ba dama ne '
Haka dai ya shiga gidan nasa baya sun natsa ya fuskance ta da maganar auren , sai dai ga mamakin sa ,' bata tayar da hankalin ta irin yadda yake zato ba hakan kuwa yana da nasaba da zancen ya riga shi isowa zuwa kunnuwan ta "

Abun nufi ta ji zance a cikin gida " abun ka da gidan sarauta da kuma yadda ya kasance hajiya uwa tana ta yamiɗiɗi da zance tana yada magana tare da fiffikar ta ta zata shigo gidan " da farko bata fahimci zancen ba sai da ta tambayi jakadiyar sarki ta wancen zamanin ita ce ta warware mata zare da abawa ta kuma kwantar mata da hankali tare da bata shawarwarin alkhairi da za su taimaka mata.

Amma duk da haka bayan dawowar ta sashin ta yini tayi tana kuka tare da tunanin ƙalubalen da yake fuskanto ta "abu ɗaya ne ya rage mata jin zafi ji da tayi matar da za'a aurawa mijin nata ba ƴar wani babban sarki bace ko kuwa wani hamshaƙin attajirin da kasa ta san da shi ba "

Ƴar Limamin Maraɗi ce hakan sosai ya rage mata zafi kasancewar safiyyah irin ƴaƴan sarautan nan ce masu ji da kan su da nuna isa sosai jinin sarauta na ƙasaita , da iko suke yawo a jikin ta ta yadda take ganin duk wani wanda ba ɗan sarautar da ya kai ya kawo ba a matsayin kasasshe a wurin ta,

safiyyah tana son sarauta tana alfahari da sarauta tana kuma ƙaunar masu sarauta , bata daukar mutanen da basu da sarauta da wani muhimmanci a rayuwar ta .

Dan haka koh lokacin da ranar da aka yanke na ɗaurin auren Abdoul-azizou da saratu ya zo , aka kuma ɗaura auren cikin kwanciyar hankali tare da bakukuwa kamar yadda yake a al'adar su , sam safiyyah bata bayyana matsanancin tashin hankalin ta ba duk kuwa da cewar abun yana nuƙurkusar ta a karkashin rai !Saboda yadda take kaunar mijin ta sai ga shi a yanzu ya zama nasu ita da wacce take ganin bata kai matsayin ta haɗa kafaɗa da ita akan abun da take so ba .

Hakan ya sa bayan tarewar Saratu "a sashin ta da aka gina mata daura da sashin Safiyyah ta hannun hagu "Sam safiyyar bata shiga harkar Saratu "A ganin ta saratu bata isa tayi gogayya da ita ba " "iyakaci idan sun haɗu a cikin gida 'idan sun je gaishe da hajiya uwa da sauran matan mai martaba biyu "Hajiya mai karamin ɗaki da umma Amarya " " su gaisa da juna sama-sama, sosai ita saratu take jin zafin yadda safiyyah ta tattara ta tare da shirgin ta ta watsar a gefe take nuna kamar bata san ma da zaman ta a cikin gidan ba , "

Hakan yana kona ran ta , domin ita ta shigo gidan ne da nufin ta dunga bi ta ƙasa-ƙasa irin yadda ta saba ( a gidan mahaifin ta) tana tunzura safiyyah tana tada bala'i a tsakanin ta da Abdoul-azizu har dai tayi nasarar dusashe karfin soyayyar da ta lura Abdoul-azizu na yi wa safiyyah ,ta yadda ya kasance idan suna tare koyaushe bakin sa cikin ambaton Alkhairin safiyyah da kyawawan halayenta tare da yabawa safiyyar yake ,"

Sai dai bata samu damar hakan ba domin duk wata kafar da zata bata damar aiwatar da mummunan nufin ta safiyyah ta toshe "ta hana ta fuska "

A cikin hakan ta fara laulayin ciki bayan watanni biyu da auren su "wanda kuma kusan tare suka ɗau cikin da safiyyah " domin ita ma tana ɗauke da ɗan tayin cikin ta na wata ɗaya " .

Nan fa Saratu ta samu abun yin lanɓo ,kitifiri da feleƙe , ita a dole ga mai juna biyu " cikin yana wata uku su ka fasa Sanarwar ai Malamar jinya a asibitin da take zuwa awo a wancen zamanin ta tabbatar mata da cewa "Ɗa" namiji zata haifa '

Sanarwar ta fito ne ta bakin "Ɗan Zagii" a karkashin jagorancin "Hajiya uwa "wacce ita ma saratu ce ta yi mata Albishir tare da tabbatar mata da abun da malamar jinyan ta faɗi gaskiya ne "cikin rashin sanin Hajiya uwa cewa zancen ƙarya ce tsagoronta wacce ita Saratu ita ta haɗa zancen ta sakamakon jin wata matar babban likita da suka haɗu da ita wurin awu tana bada labarin injin awun da yake bayyana jinsin jariri tun yana cikin mahaifiyar sa " ( Asalima a wancen zamanin injin yin awun da ke gano jinsin halitar da yake ciki bai riga ya bazu a kasashen africa ba )

Nan take zance ya kewaya fada har ya isa kunne mai martaba ta bakin jakadiya " sosai mai martaba yayi farin ciki tare da bada goron Albishir me yawan gaske"

A bangaren Yarima Abdoul azizu shima yayi matuƙar farin ciki da wannan albishir har ma ya gaza boyewa ya bayyana farin cikin sa a sarari gaban idanun safiyyah tare da nuna ɗokin sa akan samun ɗa namiji da zai yi nan ba da daɗewa ba "wanda hakan ya tashi hankalin safiyyah a karon farko tun bayan auren sa da saratu "Amma sai ta share ta taya shi murna a sarari "duk da cewa cikin ran ta taso a ce ita ta haifo magajin maraɗi saboda kaunar ta da sarauta ",

Sai dai kasancewar ta ƴar sarauta ta kasance me iya boye hakiƙanin cikin ta, ya sa ba wanda ya fahimci halin da zuciyar ta ke ciki , hatta Saratu wacce take yin duk wani kilbibin ta da biyu 'dan ta turawa safiyyah haushi " ta gaza ganin bacin ran safiyyar .

cikin watannin girman cikin kafin zuwan ranar haihuwar sa kaf an gama tanadin kayan jarirai na ɗa namiji wanda wasu ma mai martaba da kan sa ya sayo su a tafiyar sa Umrah , tarairaya da kulawa kuwa babu irin wacce Saratu bata samu tun daga kan surukan ta hajiya uwa da sauran matan mai martaba "da kusan suke karkashin ikon hajiya uwa "har zuwa kan shi kan sa mai martaba, da uban gayya yarima Abdoul-azizu wanda shima zuwa lokacin zuciyar sa sosai ta rinjaya ga son haihuwar ɗa namiji sakamakon "janye hankalin sa ta siyasa da hajiya uwa da saratu suke yi "

Wanda har hakan ya soma taɓa amintaccen zaman su na fahimtar juna da su ke shi da safiyyah.

Ranar biyu ga watan ɗaya na shekarar alif dubu ɗaya da dari tara da tamanin da bakwai ,2-jan-1987 Saratu ta wuni tana naƙuda taci wahala sosai , kafin zuwa maraice ta haifo Santaleliyar ɗiyar ta mai kama da ita sak "

An ɗauki tsawon mintoci uku a ɗakin haihuwar da yake cikin baban asibitin maraɗi bayan bayyanuwar kukan jaririyar da likitocin da suka karbi haihuwar suka tabbatar wa hajiya uwa wacce take tsaye a dai-dai kan saratu tana ta faman jera mata sannu , cewar Saratu ɗiya mace ta haifa har ma suka ɗago Santaleliyar jaririyar da ba'a ce yanzu aka haife ta ba saboda girman ta suka nuna wa hajiya uwa da saratu, shiru ne ya ratsa tsakani kafin Muryar hajiya uwa ta bayyana Cikin cewa".

Saratu kika ce Malamin jinya ya tabbatar miki Ɗa namiji ne a cikin ki ? watau ashe zancen ba haka bane ? ashe dai zance Altine "yayar saratun da suke uba ɗaya " zancen ta gaskiya ne da take cewa ke Saratu ba ƙaramar maƙaryaciyar yarinya bace " ,

Amma ban yi zaton karyar taki da yauɗarar ki ta kai har haka ba , da har domin rashin hankali zaki yi irin wannan ƙasurgumar karyar da yaudarar a gidan sarauta, toh Maza sai ki tanadi ruwan wanke kan ki a idanun mai martaba da shi kan sa mijin naki , ki kuma tabbatar kin riga kin gama zubda ƙimar ki a idanun mutanen gidan nan ciki kuwa har da bayun da suke karkashin ki , haba saratu me ake da wannan irin karyar taki "

Saratu dai babu bakin magana sai sharar ƙwalla take "wanda hakan ya jaa hankalin malaman jinyar da suke gyara ta har ta kai su ga tambayar dalilin kukan ta "hajiya uwa" ta faɗe musu biri har wutsiya akan yaudarar da saratu tayi mata da kunyar da ta jefe ta " Malaman jinyar su da kan su sun ga rashin kyautawa, tare da mamaki irin karyar saratu sai dai sun bada tabbacin akwai irin na'urar a kasashen da suka cigaba ,"sai dai koh na'urar ma ba koyaushe take bada bayanin gaskiya ba"( Sanin gaibu sai Allah ) jin hakan ya sa "Hajiya uwa jin wani farin ciki ko ba kome sun samu hanyar da zasu fidda , kan su "

Haka aka gama gyara ta tare da jariryar aka tura su ɗakin da zasu zauna "a lokacin ba'a sallamar mace daga haihuwar ta har sai ta zauna a asibiti kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatar da karfin jikin ta "

Bayan isar su ɗakin hutun kafin jama'ah su zo "Hajiya uwa ta sanar da Saratu shawarar da ta gama yankewa domin samun rufin asirin su ,nan take yanke "ba tare da jaa ba" Saratu ta amince .

Da zuwan yarima Abdoul-azizu "hajiya uwa ta sanar masa da ɗiya mace aka haifa ba ɗa namiji ba ta kuma ɗora da bayanin da malaman jinyan nan suka yi musu na cewa ana iya samun kuskuren inji wurin bayyanuwar jinsin abun da ke cikin mahaifiyar sa "

Ƙwarai yarima abdoul azizu yayi kokari wurin nuna rashin damuwar sa akan kuskuren na'urar da ya riga ya yadda akan cewa an samu " Amma cikin ran sa sam sam lamarin bai mar daɗi ba sun riga sun ƙwaɗaitar dashi son haihuwar ɗa namijin .

Bayan isar labarin haihuwar saratu "Fada " tare da sabon sauyin da aka samu daga haihuwar ɗa namiji da ake sa ran haihuwar sa zuwa samun labarin haihuwar ɗiya mace , Fada ta shiga Alhini da har hakan ya gaza boyuwa akan fuskar mai martaba ,

Haka aka yi bikin suna cikin rashin Armashi bayan dawowar su daga asibitin "inda yarinya taci sunan "hajiya uwa Asma'u " Sau ɗaya mai martaba ya sa aka kai masa yarinyar turakar sa "a washegarin dawowar su daga asibiti" in da yayi mata huɗuba tare da bata suna " tun daga ranar bai sake waiwayar su ba.

Ga bangaren safiyyah har ila yau dai bata bayyana wani alama ba ta bangaren ta ,na farin ciki koh saɓanin sa akan sauyin jinsin abun da Saratu ta samu . Ita ma tana fama da nata cikin , da yayi wani irin mugun girma fiye da sauran cikin ta guda uku na baya , hakan ya sa da zainab ta zo bikin sunan ɗiyar Saratu "ta nemi da ta ɗauki Zainab "ubbo"(takwarar ta )

Kasancewar tun da aka mata aure a lokacin shekarun auren ta bakwai bata taɓa samun haihuwa ba "sai bari da take ta faman yi " ganin yadda cikin yayi wa safiyyah nawi ga kuma rigamar zainab wacce ba ta kai ga cika shekaru biyu ba a lokacin "sannan gata da jarabar ƙiuya bata yadda da tarin bayu da suke cike da bangaren nasu da ma gidan baki ɗaya "sai jikin uwar ta , ya sa ta nemi tafiya da ita nan take kuwa safiyyah da Abdoul azizu suka bata zainab ɗin ta tafi da ita "

Ranar goma ga watan biyu na shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da bakwai 10-feb-1987 ita ce Ranar da ta zamto ranar farin ciki ranar da baza'a manta da ita ba a tarihin masarautar maraɗi ranar da ta shiga jeru ranakun tarihi, Ranar da aka wayi gari gimbiyyah safiyyah tana nakuɗa , zuwa hantsi ta haihu lafiya " farin ciki ne ya wanzu akan fuskar gimbiya safiyyah a lokacin da malaman jinƴar da suka karbi haihuwar ta su ke tabbatar mata da ta samun Ɗan ta namiji 'Ƙato da shi jazir ya ɗauko hasken fatar ta irin ta fulanin usul yayin da tun kallon farko da tayi masa bayan da "malaman jinyan suka gama wanke mata shi tare da shirya shi cikin kayan jarirai" tana yi masa kallo guda ta hango tsantsar kamannin sa da kakan sa"mai martaba sarki youssoufa " kamar an tsaga kara , kakaf cikin ƴaƴan da ake haihuwa a gidan babu wanda yayi kama da Mai martaba irin wannan jaririn "Cikin nutsuwa ta dunga kwararo masa addu'ar kariya kamar yadda take jin matsananciyar kaunar sa tana kwarara cikin zuciyar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login