Showing 264001 words to 267000 words out of 411050 words

Chapter 89 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

19977

bai ji daɗin dawowarta ba , bai ji daɗin bayynuwar ta ba , ya so da ta cigaba da zama a matatciyar ta tulin addu'o'in sa na riskar ta ,

Taku ɗaya yayi yana ajiye na biyu , yaji sun ƙira sunan sa a kusan tare ,

"Baban Mama ,
"Yusuf ,

Hatta hantar cikin sa sai da ta kaɗa , da jin tashin muryar ta da kaushi a ƙiran sunan sa ,

A firgice ya waigo idanun sa cikin nata da yake iya hango ƙiyayya da tsana masu ɗinbin yawa , ji yayi kamar ya durƙusa guiwa biyu ya roƙeta kadda ta fasa sirrin dake tsakanin su a yanzu . 

Da sauri ya mayar da ganin sa ga Falmata wacce ya ga ta sunkuyar da kan ta yana iya hango bayyanar wani irin yanayi a tare da ita ,

"Na'am Fatima yace ,

Falmata wacce ƙiran sunan sa da Yakaka tayi ya ankarar da ita tare da tuno mata da matsayin Youssouf ɗin Na asali ga Yakaka , jikin ta yayi sanyi da tasowar wani yanayi mai suffar tsoro-tsoro daga ƙasan ranta , cikin dabarbarcewa tace ,

" un daman nace ga Maman Mama fa ? Baku gaisa ba ? Zaka fita da Mama bata gaishe da Maman ta ba ,

Da sauri ya saki hannun Mama , bai yarda ya dubi fuskar Yakaka ba , yace

" sannu dai ,

Da sassarfa ya ƙarasa barin falon Mama ta ƙara da gudu ta bi bayan sa duk ita zuwan Yakaka ya takurata ,

Kallon tsanar da Yakaka ta bi Youssouf da shi akan idanun Hajja wacce ta kasa ta tsare tana bin duk wani motsin Yakaka da ido ,

Moɗe baki tayi kafin ta ce ,

" ke Yakaka tashi mu shiga daga ciki , ita Falmata ta bi sawun Mijinta tunda dai bata bar shi shi kaɗai ba , wannan zaman naku na ke kuka ita juyayi baya haifar muku da ɗa mai ido ba ,

" Abunda ya wuce ya riga ya wuce a bar tuna shi ana koke-koke kun ji ko ?

Daga Yakaka har Falmata babu wacce ta amsa mata saboda kawo yanzu hankulansu ya dawo jikin su daga ruɗanin murnar da suka shiga na sake ganin juna ,

Kowacce kuma ƙwaƙwalwarta ta fara aiki cikin gaggawa da fuskantar ƙalubalen dake gabanta ,

Ga Yakaka yadda zata tunkari Youssouf yaso ruɗata da ta ga ya ƙara girma da haiba , ƙwarjinin sa yana neman tsorata ta sai dai daga ta tuna shi da munanan ɗabi'un sa sai ta ji duk ya koma fanko a idanunta ,

tafi shiga damuwa akan yadda zata fayyacewa Falmata gaskiyar kome , yadda ta hango nutsuwa a fuskar Falmata ta san zuciyarta zata yi baƙi idan ta san gaskiya wataƙila ma ta tsaneta ita da kan ta da ita kuma bata fatan hakan, ita yaya zata yi ne ??

Falmata kuwa wani irin tsoro ne ya cika zuciyarta tare da zullumi , bayan murnar dawowar Yakaka , zuwa yanzu abunda zai biyo baya takewa Fargaba .

na farko tsoron rabuwa da Mama , Allah ya shaida bata fatan rabuwa da Mama ko na yini guda , sai kuma ga Allah ya dawo da Mahaifiyarta , ta san dole Uwar ta buƙaci 'yar ta , Yakaka zata rabata da Mama ne ko zata barta ta cigaba da riƙon Mama ? Tsoro take ji.

Tare da zullumin rabuwar su da Baban Mama ,  mutumin da Alkhairin sa ya yawaita ya tunbatsa a gareta , mutumin da tarin Alherun sa da haƙurinsa da ita ya huda tattaurar zuciyar ta tare da kafa soyayyar sa a ciki ,

Mutumim da ya zama tsani na samuwar ganin haske a idanunta , mutumin da sanadin sa ta samu ilmin boko da na addini dai-dai gwargawdo, 

mutumin da ta riga ta mallakawa gangar jikinta ya tarɓeta da so mai tsanani cike da tausayi da tausasawa  ,

mutumin da ta riga fara gina rayuwar ta da shi ,mutumin da wani ɓangare na jikin sa yake a cikin ta yana rayuwa ,

Wani irin narkewa ta ji dukkanin lakar jikin ta na yi ,

Lokacin da ta tuno yiwuwar rabuwar ta da shi , tunda daman rashin Yakaka ya kawo yiwuwar auren su har ta kai su da rayuwar aure tare yanzu kuma da ta dawo , dole ita zata matsa kenan  , zata tafi kenan , za su rabu kenan ina ma ina ma ?

Sanyi ta ji ya fara kaɗa ta duk kuwa da cewa a zahiri zafi ake yi ,

Hannun ta da yake cikin na Yakaka ta dunƙule , jin haka ya dawo da Yakaka daga tunanin da ta nausa a ciki , da sauri ta riƙe hannun Falmatan ,

"Falmata kun dawo baku ci abinci ba ke da Mama ? Mun yi muku girki fa , kuma ma na kawo miki tsaraba ban san ko Mama ma zata iya ci ba , ƙuli-ƙuli ne mai sugar irin naki kina so  ?

"ina so Yakaka kawo mun zanci , na daɗe ban ci ba , kamar kin san yana raina , yanzu na cewa Bab...

Sai tayi shiru bata ƙarasa ba , ji tayi tana tsoron ƙiran sunan sa a gaban Yakaka ko me yasa ?

Yakaka ta miƙe a hankali , ta nufi ɗakin da suka yi masauƙi ,

Hajja wacce tayi jugum a zaune tana binsu da kallon tsanaki , tace

'Uwarɗakina kar fa ki sanya kan ki cikin damuwar kome ko domin abunda kike ɗauke da shi a jikin ki damuwarki hatsari ne maigirma , da yardar Allah haƙuri tare da ƙaunar ki ta gaskiya da riƙo da zumuncin da kika yi basa bari ki tozarta ba , ke dai ki cigaba da yin kome domin Allah kin ji ko ?

Gyaɗa kai kawai tayi ,

"nayi muku tuwon shinkafa da miyar kubewa , ga kuma farfesun dantsen sa , akwai dafadukar shinkafa 'yar uwar ki ta mata sarrafawar turawa a ciki wacce zaki ciki ?

Ƙarasowar Yakaka ya sa bata amsa ba , hankalinta ya koma kan Yakaka da take tahowa , ƙewar 'yar uwar ta tare da wannan ƙaunar mai tarin yawan suna taya ta binne duk wata damuwar ta tare da ƙarfafa mata ,

"Yakaka ashe kina da tsawo haka sosai , ga ki kuma fara sol Yakaka mai kyau da ke tubarakallah ,  bani labarin kamannin Maman mu da Baban mu da wa ni nake kama a tsakanin su ?

Yakaka wacce take sunce ledar ƙulin ta gama kuncewa ta ɗibo biyu a hannun ta , tana murmushi ta kai ɗayan bakin Falmata da ta ga tahowar hannun Yakaka ta buɗe baki ita kuma ta jefa mata ƙulin ,

" Da Baa kike kama Falmata sak ma kuwa kawai tsawon sa ne baki samu ba , ni kuma da Maman mu nake kama sak kawai ban kaita haske ba ,

Ƙurus-ƙurus ku-rus , Yakaka ta taune ƙulin da ta jefa a nata bakin , ta cigaba da cewa

" Daman an raba , ni da Bulama kamar mu ɗaya ke kuma da Baana kuma kamar ku ɗaya (sulum fut ) baƙaƙe siɗik , ta ƙarasa zancen da sigar tsokana ,

Yamutsa fuska Falmata tayi , kafin ta ce ,

"Amma ai Baa kullum yana cewa fararen mutane basu da ƙarfi da dauriya , mu baƙaƙe mun fi ku , Yakaka kin tuno da karon mu da Biri a gonar Baa ?

Wata sassauƙar dariya suka kwashe da ita lokaci guda , Yakaka wacce ta fi Falmata dariya muryar ta cike da amon dariyar da take yi ta ce cewa za kiyi ranar da kika sumar da ni a garin dukan Biri ,

Wannan karon hatta Hajja da take kallon su sai da ta murmusa , sannan ta ce tayaya ta sumar da ke Yakaka daga dukan Biri ??

Siririyar Muryar Falmata cike da dariya ta fara cewa ,

"Hajja lokacin girbi ne Baa ya kai mu gonar sa domin muyi masa gadi , muna zaune yin gadi da rana tsaka , sai wani ɗan Biri ya shigo gona , Yakaka ita ta gan shi ta dunga binsa da wata sandar da Baa ya bamu tana son doke shi amma Birin nan sai tsalle-tsalle yake yana gudu yaƙi barin gonar , ƙarshe dai yayi tsalle ya hau kan Yakaka char ya tsaya atsakiyar kan ta , Sai yakaka ta ce

"Falmata nace "Na'am ,tace Birin nan yana tsaye akaina ga sandar nan zan wurga miki , inda kike jin muryar ta za ki doke ta sama kaɗan ki buga masa da ƙarfi ɗan iskan Biri ɓarawo ,

Nace "to Yakaka , ta kuwa wurgo min sanda na ɗauka ,

"Hajja na faɗa miki da na ɗaga sanda kin san dai ba gani nake yi ba a lokacin, na ɗaga ta da ƙarfin gaske , lokacin da. naji Yakaka tana cewa kai-kai-kai amma na riga na wulwula sanda sai kawai na rafka a zatona alama take min na inda zan bugawa sandar watau a kanta ,

Ɗif na ji Yakaka tayi shiru ,

"Hajja ashe Yakaka na rafkawa sandar Biri kuwa tuni yayi tsallen sa , Yakaka kuma ta some ,

Ta ƙarasa bada labarin tana sakin shisshiƙar dariya tare da kwanciya bisa kujerar da take kai , ba Yakaka ba hatta Hajja , dariya take yi sosai ,

Yossouf da yake tsaye ta bakin ƙofar falon saboda hankalin sa da ya kasa kwanciya a zaman sa a falon sa , cikin duk daƙiƙa guda zato yake yi Yakaka zata sanar da Falmata kome ,

Da shi kuma ko kusa a yanzu bai shiryawa tarɓar tashin hankalin da zai iya biyo bayan hakan ba .

Baya yayi yana dariya da haƙoran sa kwarai labarin wannan ƙatoɓarar da Falmata ta yi ya bashi dariya ,

Yana shiga Falonsa wayar sa da take ajiye akan kujera ta sake ɗaukar kiɗa sunan Tafeeda ne ke yawo akan fuskar wayar ,

Ji yayi damuwowin sa sun sake yi masa rubdugu , zama yayi daga kan kujera ya ɗau wayar ya riƙe , ya akayi ma Tafeeda yasan dawowar sa, ?  duk ƴan mintoci kenan da sanya layin sa na nan a waya ,

Shi a yanzu baya buƙatar ƙarin wasu damuwowi , yasan Tafeeda ƙudirinsa shine ya raba shi da Falmata da shi kuma ba shiryawa hakan yayi ba , ba kma ya jin zai taɓa shiryawa har abada,

Danna wayar yayi ya sa a silent saboda Mama da ta samu bacci kar ƙaran waya ya tadda , tagumi ya rafka da hannunsa biyu yana jin yadda cikin sa ke ƙugin yunwa amma ba damar cin abinci ,

Bayan sun tsagaita daga dariya , Hajja ta kallesu tana nazarin tarin ingantatciyar ƙaunar da ke ga junan su , a hangen ta irin na manya ta fuskanci kowaccen su tana ƙokarin binne damuwar ta ne daga 'yar uwarta saboda zallar ƙaunar da suke yiwa juna , idan kuwa hakane Madallah da irin wannan ƙauna ta tsakani da Allah ,

Miƙewa tayi tare da cewa ,

"Yakaka yayar Falmata zo muje daga ciki ki ga irin 'Ya'yan itatuwan su na nan Niger ba irin namu na Nigeria ba ,

"Uwarɗakina Falmata a kaiwa Mama abincin kadda yunwa tayi mata lahani  , tana sashin Baban ta ai kin san hanyar ko ? Kin kuma san kitchen ɗin ga shi nan ,

"nasan Hanya Hajja ,

Falmata ta furta hakan tana jin son ta tafi ga Mijinta ta ga halin da yake ciki , sannan ta fuskance shi ko zata iya ganin wani sauyi a tare da shi na daga zallar ƙaunar da yake nuna mata muddin suna tare , a sanadin bayyanar Yakaka ?

Yakaka bata ce ƙala ba ta bi bayan Hajja , har ta ɗan gifta Falmata , sai ta ji ta ƙira sunan ta ,

"Yakaka nyei

Juyowa tayi fuskarta da Murmushi

"Na'am Falmatan nyei

"Yanzu zan zo da Mama tayi miki hira duk da bata da lafiya sosai , amma ta iya hira sosai , zan kawo miki ita .

Murmushi kawai Yakaka tayi ta juya tana ƙarasa barin wajen ,

Suna shiga ɗakin ta cewa Hajja ,

"Hajja ina 'ya'yan itatuwan ? Mu ga irin su ?

Kallon tsakar ido Hajja ta yi mata ,

"Yo ina kuwa wasu 'ya'yan itatuwa nan ? Kin tsare yarinya kin hana ta kaiwa mijinta tattattun 'ya'yan itatuwa tayi aikin lada ubangiji ya samar mata da lambun 'ya'yan itatuwa a Aljanna , ke haka ake yi yanzu tsakani da Allah ? Haba Babba uwar Mama .

Kallon Mamaki Yakaka tayi mata , ta samu waje ta zauna daga gefen gadon dake ɗakin

"kenan Hajja dai ba gaskiya kika faɗa min ba wayo kika min dai ko ?

Hajja bata dube ta ba ta fara ninke gyalen ta , ta bata amsa da

" to kuma dai , karo ɗaya ai ko da ƙwai da dutse a yi sa .

Shiru Yakaka tayi bata ce kome ba , cikin ranta damuwarta ce ta dawo sabuwa fil akwai wani alamu da ta hango tare da Falmata wanda bata fatan tabbatuwar sa ,

Falmata bayan ta jera abincin su da ta tarar a rurrufe cikin mazubi , sai ta ɗauka ta nufi sashin Youssouf da ta san yana ta harabar gidan duk kuwa da cewar bata taɓa zuwa ba , sannu-sannu take tafiya saboda duhun dare da ya fara shigowa daf ake da ƙiran sallar Magariba ,  tare da taimakon hasken fititulun da suke girke a harabar gidan da suka kunna kan su , ta iso Bakin babar ƙofar ta tsaya tayi sallama ,

daga ciki Youssouf wanda tuntuni yake kai kawo a cikin falon ya taho da saurin sa jin muryar ta ya buɗe mata ƙofar

Tunda ta shigo falon Biyamuradi yake binta da kallo mai wuyar fassara , so yake ya tantance yanayin da take ciki , amma ya gaza gano wata alama, maimakon haka sai ya shagaltu wajen kallon tsarin kyakkyawan jikin ta da take sanye da doguwar rigar roba da ta bi jikin ta lafe , koyaya ta motsa sai wani sashi na jikinta ya ɗau hankalinsa .

gefe guda Mamakin kansa yake yi yadda yarinya karama take mamaye tunaninsa a duk lokacin da suke tare ko ya koma gida. Akwai wani abu game da Fatima Zahra da ya kasa fasaltawa a ransa da a farko yake yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa 'yarsa ne.

Sai dai zuwa yanzu ya hiƙaƙancewa kansa cewa ƙaunar Fatima ɗarsuwa tayi a cikin ransa tun a ranar da ya soma ganinta , alhalin lokacin bai san cewa ma zata zam mariƙiyar ɗiyar sa ba .

Akan ɗan teburin dake tsakiyar falon ta ajiye farantin hannunta wurin da yake zaune ta waiga , cikin kwantatciyar murya tace

"ga abinci".

Shiru taji kamar babu kowa waigawa tayi sai dai duhun da yake falon tare da rashin ƙarfin ganin ta sun hana ta damar hango shi , wanda yana sane ya rinka tafiya a hankali ,

Ji tayi kamar abu na nenam rufeta ta baya ta dan ja jikinta kadan sai kawai taji tayi karo da mutum. Gabanta ne yayi wata irin faduwa ta rikice tana neman hanyar barin wurin saboda tsintar kanta kawai tayi da kasa sakewa da shi yadda suka saba ,  shi kuma yaki matsawa sai ma hannuwa da ya saka ya zagaye kunkumin ta tare da haɗa bayanta sosai da ƙirjinsa

"Hankali Zahra" yace da wata irin murya a daidai kunnenta har tana jin saukar numfashinsa.

"Uhmmm zan wuce ka matsa" ta hado kalaman ta furta a hankali.

"Baki zuba min abincin ba zaki tafi?" Ya ce yana karewa kyakkyawar fuskarta kallo, bayan ya juyo da ita ya kamata suka zauna ,

Turo baki tayi tana jin kanta a takure 

"ni da kasan bana gani sosai idan dare yayi ?" kuma ai kasan ban iya zuba abinci ba .

Ya dage gira daya "yau kuma? Na dauka Zahra ta iya komai ashe da sauranta tunda bata iya zubawa miji abinci ba." Ya sake matsawa kusa da ita daga zaunen da suke ,

Sai dai bai bari jikinsu ya hadu ba saboda ko kadan bai yarda zai iya mallakar kansa ba a yadda yake ji ba , saboda shi da kansa buƙatar inda zai sanya kansa a rarrashe shi yake ,

da kuma ya tabbata Fatiman tasa a wannan gaɓar bata isa bashi kulawar da yake so ba , 

"gashi yau da hannunki nake so ki bani"

Yace mata yana murza ƴan yatsunta da ya riƙe cikin hannunsa

Yana kallon yadda idanunta suka kara girma kirjinta yana hawa da sauka cikin sauri da firgicin da bai san dalilin samuwar sa ba a dai-dai lokacin ,

"me zan baka?"

Tace muryar ta na ɗan rawa ,

"Abinci mana yadda kike bawa Mama"

Bata san lokacin da tace "kai alanguro Yarima" cikin wani irin amon murya mai nuni da tsoro da mamaki ba.

Murmushi yayi , tare da kai hannunta bakin sa ya sumbata ,

  "me kika ce ? Aina kika ji wannan sunan ? Sake ƙira muji kamar naji kince wata kalma ta daban me kalmar ke nufi ?

  Shiru tayi tana murmushi ,

"to shikenan idan baza ki zuba min ba  , bakya ƙara fita a ɗakin nan sai gobe ,

Bai rufe baki ba ta laluba ta ɗau farantin ,

Tana turo baki ta zuba abincin tana faman kunkuni "yaushe kaji nace ba zan baka ba to?"

"Afuwan nayi tunanin kin fada a zuciyarki ne"

ta dauki cokali ta ciko shi taf "bude" tace kamar tana magana da baby.

Cokalin ya kalla a tsorace "duk wannan a bakina Fatima?"

Tayi murmushin keta "ba irin na Mama kake so ba? Haka nake bata"

"Amma ni da hannu nake so"

Tunanin yadda za ta tsere takeyi ta ajiye ta diba da hannunta tayi sama dashi tana laluben bakinsa,Hannu taji irin na mazan da suke gwagwarmayar yau da gobe ya rike tsintsiyar hannunta

a hankali ya kai bakinsa ya ci kadan sai da ya hadiye ya kara sai a karo na uku taji yatsunta gabadaya cikin bakinsa. Ita kanta bata san yanayin da ta tsinci kanta ba bare kuma shi uban gayyar da yake jin inama bakin tsiwar ya samu haka ba yatsunta ba kawai,

"Ashh Alangubro zaka cinye min yatsu ne ?

" da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login