Showing 24001 words to 27000 words out of 411050 words

Chapter 9 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14339

, amma nikam bazan iya wannan halayyar taku ta rashin godiya ba

," wuce su yayi tinƙis-tinƙis yana tura cikin sa tare da mita ,"haba ace mutane sam baku da godiyar Allah a ɗau nawin ku ci da sha da gurin kwana ba tare da koh sisin kobo ba amma duk da haka kullum ta Allah sai kun zo da sabon tsirfa ,"yau ku ce wance gobe wannan koh da yake ba laifin ku bane ," gwamanati da ta ƴanta ku daga noma da shan ruwan kududdufi ita ke da laifin ",

An ɗauki tsawon mintuna biyu babu wacce tace ƙala tsakanin su ukun , kowacce da abun da take saƙawa cikin ran ta ,"

Yaraf ,"yakaka ta ƙarasa bajewa a ƙasa daga durƙuson da suke ," a sakamakon bangaje ta da wata mata tayi wacce take tafe tana ta zabga sauri har zanen ta na kuncewa bayan ta kuwa wasu mata ne su ma gungu sun doshi wajen su hamsin koh fin haka ," wucewa suka yi tare da nufar sashin da su ka ga ɗazu wasu maza sun bi da buhunhunan abinci .

Cikin sanyin jiki suka miƙe tsaye Falmata tana me sake lalubar jikin yakaka wacce ta ke riƙe da ɗayan hannun ta ,"
Yakaka ya akayi kika faɗi baki ji ciwo ba koh ?
Banji ciwo ba falmata ," ku muƙarasa daga can .

Watau nan shine masaukin da gwamnati ta tanada domin ɓaki ƴan gudun hijira ,"? Yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da suke zama a bakin ɗaya daga cikin fasasshiyar barandar wurin ,"

a toh ga zahiri dai kin gani ,"cewar yakaka wacce gaba ɗaya ta gama tsinkewa da irin rayuwar da ta hango musu a wannan matattarar kazo na zo ɗin ,"

Wai yaya fasalin tsarin wajen yake yakaka ?. Yanzu fa ba zama yakamata muyi ba , dacewa yayi mu fara zuwa mu ƙarbi abinci mu ci sai muyi sallah mu bazama neman mama kamar yadda muka tsara ko kuwa ?

Haɗa ido yagana da yakaka suka yi kafin yagana ta ce hmmm ai falmata bamu kai ga fahimtar tsarin wajen ba tukun ," ga mu nan dai kara zube kamar yadda muka lura kowa ma a zuɓen yake a wurin nan ," amma bari naje na fara da tambayo mana inda banɗaki yake domin ni mara ta ma cike take dam ,"
***************
Lalee ,sannun ku jama"a dan Allah ina ne inda banɗaki yake ? Sannan kuma ina ne wurin cin abinci mu ɓaki ne yanzu muka zo ," yagana ke yin dogon bayanin nan bayan da ta tadda wasu gungun mata da su da ƴaƴan su a zaune cikin ɗaya daga cikin ɗakunan nan ,

Ga mamakin yagana ba wacce ta ɗago kan ta ta ɗube ta bare ma ta sa ran za'a amsa ma ta ," duk kuwa da cewa cikin yaren su tai maganar kuma zanen da yake ɗauke a fuskokin mafi yawan matan wurin da suka kusan tasamma su arba'in ya isa sanar mata cewar daga ƙabila ɗaya suke ita da su ,"

ɗai ɗaya take kallon su yayin da ta ke jin wani irin ɗan banzan wari da zarnin futsari yana cunƙushe mata kofofin hancin ta ,' ƙudajen da suke yanyame cikin ɗakin da babu koh shimfiɗar tabarma sai ɗaben suminti ," sai kuka suke yuyuyuyu , gami da kukan ƙananun yaran da wasu ma koh ɗan kanfai babu a jikin su , sai tarin layu da zaren jigida a ɗaure a ƙugun su ," shi ya sanya yagana tayi hasashen koh hayaniyar cikin ɗakin ne ya sanya wasu basu ji ta ba ,"

Sake maimaita bayanin da tayi da farko tayi ," Can baya zaki zagaye kiyi abun da zaki yi maganar abinci kuma ba'a kai ga kammalawa ba ," ki adana sauran tambayoyin ki domin mu ma nan duk da kika ganmu riƙe mu ke da tarin tambayoyin da muke son samun amsoshin su ,"

Tsam yagana tayi a tsaye bayan da ta gama jin bayanin matar nan ,"jan ƙafafun ta ta soma yi da nufin barin wurin alokacin da taji matar nan ta ɗora da cewa kika ce ku ɓaki ne ? Ke da su wa ? Ba tare da ta jira amsar yagana ba ta ɗora da cewa kun kaima barka domin kuwa a yau gwamna ke kawo ziyara ƙaron farko a sansanin nan ," nan da kika gan mu a zazzaune dakon jiran sa muke ," domin ance tafe yake da tarin kyautukan alkhairi .

Ai nan take yagana ta washe baki ji da tayi sun taki sa'a lokaci ɗaya ta ji ta nemi sanyi jiki da taraddadin da ya fara mamaye ta a sakamakon bayanin matar nan na farko ta rasa ," farin cikin albishirin da matar tayi mata na ganin gwamna ra'ayul'ain a yau ya wanke mata bacin ran da take ta shaƙa tun fitowar ta daga garin su ai da gudu ta kwasa har tana murguɗe kafa tayi wurin da ta bar su yakaka .
[6/24, 9:58 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association

*MAFARI......*
( _HARGITSIN RAYUWA_ )


*Umm'muaz*

5

Yakaka yakaka ," da sauri yakaka wacce ta maida hankalin ta gaba ɗaya ga mutanen da suke kai kawo a wurin tana nazarin su,"cikin ranta tana hango musu irin rayuwar rashin sakewar da zasu yi ita da ƙanwar ta a cikin waɗannan ɗaruruwan mutanen da basu taɓa sanin koh ɗaya daga cikin su ba ,sanin da tayi su ɗin ba mutane ne waɗan da suka saba da shiga cikin jama'a ba , hasalima su ko a garin su a ƙebe da su da mahaifiyar suke , basa shiga cikin taron jama'a saboda wasu dalilai ,"

Da sauri ta juya gami da miƙewa tsaye hankali a tashe take duban yagana wacce ta ƙaraso gaban ta yanzu tana ta haki a sakamakon ɗan gudun da tayi ," yagana lafiya ta furta hakan hannun ta ɗaya dafe da kirjin ta ?
Lafiya lau yakaka Albishirin ku , ?
Da sauri falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye ,"
Da sauri kuma cikin zumiɗi tace goro ? ta zarce da cewa...kin ga maman mu ne ?

Ɗan kallon ta da gefen ido yagana tayi cikin ran ta kuwa tausayin su ne ya kawo mata ,! ," Falmata kin manta ni ban san mama ba ?,"ta ɗora da sake faɗaɗa fara'ar ta tace ,"wai yau gwamna ne zai zo wannan sansanin , Yakaka-falmata mu yau mun shigo maiduguri a sa'a ,wallahi yau zamu ga gwamna ta ƙarasa zancen tare da yin ɗan tsallen murna,"

Ɗan guntun tsaki falmata tayi ,' kana cikin sanyi jiki ta silale tare da lalubar inda ta tashi ta sake zama tare da rafka tagumi hannu bi-biyu , sam a gareta wannan ba Albishir ba ne ," toh ita ina ruwan ta da wani ganin gwamna ? Tukun da wanne idanun zata ga gwamnan ? Sannan koh da tana gani ma a halin da take ciki a yanzu bata jin ganin gwamna zai iya ƙarar da ita wani abu da ya shafi farin ciki da har za'a yi mata albishir a kan sa ,' a halin yanzu jin ɗumin mahaifiyar ta tare da sauraron gwalatun maganar ta ,irin ta kurame shine kaɗai abun da zai sanya ta farin ciki ," hawaye ne ya silalo daga gurbin idanun ta sakamakon amsa kuwwar muryar mahaifiyar ta da taji yana shawagi da yi mata gizo a kunnuwan ta ,"

Da ɗan guntun murmushi ɗauke akan fuskar yakaka ta koma ta zauna ita ma ," kai yagana saboda haka ne kike ta ihun ƙira na har kika tsinka min zuciya ?

Ɗan yaƙe yagana tayi ganin yadda ya da ƙanwar suka gwale ta ," cikin ranta tana cewe ku ai daman alamu sun nuna ba'a yi muku gwaninta

Yakaka ni kam ki kaini banɗaki fitsari nake ji kuma fa har yanzu ba mu yi sallar azhar ba har ga shi kamar kunnuwa na suna jiyo kiran sallar la'asar ,"
Da sauri yakaka ta sake miƙewa lokaci guda tana kai duban ta ga yagana wacce tsabar murna ta gaza tsayuwa guri guda ," yagana inane banɗakin ne ?
Ɗan diri-diri yagana tayi domin ita har ga Allah ta ma manta ina aka gwada mata banɗakin yake ,"saboda tsabar ɗoki ," amma ganin wani mutum ya fito daga wani ɗan ɗaki da yake daura da ɗakin da suka fara cin karo da shi a wurin (office ɗin mutumin nan ) hannun sa riƙe da buta ga alama kama ruwa yayi , hakan yasa yagana tayi nuni da wurin ta ɗora da faɗin ,' Kamar cewa aka yi nan baya haka yake koh ,?

Bin inda ta nuna da ɗan yatsanta manuniya yakaka tayi ,"cikin shakku take kallon inda yagana ke gwada mata ," domin dai ɗakin da yake gefe da ɗakin (office) ɗin mutumin nan da yayi musu korar kare take nunawa ,"
Yagana nan baya kika ce kuma gashi kina nuna gaba ? Anya kuwa can ne banɗakin ?

Yakaka kina gani dai mutum ya fito daga banɗakin hannun sa riƙe da buta kin dai gan shi ai koh ?,"

Toh muje falmata ," yakaka ta furta hakan dai-dai lokacin da take kamo hannun falmatan suka jera har bakin barandar ," mu karasa bakin kofar sai na jira ki ,"

Ɗan turus yakaka tayi lokacin da falmata ta ce toh ina ruwan da zan yi amfani da shi yakaka ?

Bari na tambayo matan can inda ake ɗibar ruwa , ta furta hakan lokacin da take mayar da kallon ta kan wasu gungun matan da suke tsaitsaye hannuwan su riƙe da wasu manyan farantai irin na rabawa jama'ar gidan biki abinci ,

Toh ni zan shiga dan gaskiya a matse nake yakaka idan kin kawo ruwan ki ajiyemin a bakin kofar ," falmata ke furta hakan a lokacin da take laluban ƙyauren kofar ," ɗan bin ta da kallo yakaka tayi cikin ran ta fal tausayi da ƙaunar ƙanwar ta ke ƙaraƙaina ,"

falmata koh na kama ki mu shiga tare saboda koh banɗakin bashi da kyau sosai ," ?

Yakaka zan kula da kaina ki kawo min ruwan da sauri dan Allah kar wasu su shigo kaina ," falmata ta furta hakan a lokacin da ta tura kofar ,"

Da sassarfa yakaka ta juya ta dumfari matan nan cikin ranta tana jinjina irin karfin zuciyar falmata da kuma yadda a koyaushe take boye tsaraicin ta sosai ,bata taɓa ganin mutum a shekarun falmata da yake da kunya tare da suturce jikin sa irin ta ba ," tun falmata na da kananun shekarun da yakamata a dunga kula da ita irin su wanka ,tsarki da sauran su ," ita bata yadda , sai dai tayi da kan ta duk kuwa da naƙasar da take tare da ita ," tun mahaifiyar su na dukan falmatan idan taƙi yadda tayi mata wanka ," har ta haƙura ta kyale ta .

********

Da lalube take bin bangon banɗakin tana shaƙar wani daddaɗan kamshin da yake game da wurin ,tsam ta tsaya lokacin da ta ji ƙafar ta da koh takalmu babu ta sauka akan wani lallausan abu ,"kamar shimfiɗa ? Da sauri ta ɗan janye ƙafar ta , cikin ranta tana tunanin toh shi banɗakin birni haka yake da laushi kamar anyi shimfiɗa ?

Koh da yake ance gidan gwamnati muke ,zata iya yiwuwa ma ayi shimfiɗar a banɗakin dan jin dadi ," Fitsarin da ya sake mintsilin marar ta shi ya sa ba shiri ta ɗan ƙara gaba kaɗan ta sunkuya da nufin tsugunnawa lokacin da taji kan ta yayi karo da wani abun da bata tantance ko menene ba ," ɗan shafa goshin ta tayi lokacin da ta fara sauke larurar ta ,'cikin ranta tana mitar su mutanen birni sai a bar su yanzu me ya kawo tarkace cikin banɗaki ?

Ji tayi ana ƙokarin turo kofar da saurin ta tayi gyaran murya cikin siririyar muryar ta tace " a dakata akwai mutum ,"

Turus yayi sakamakon jin muryar mace da yayi a cikin office ɗin sa ," waiwayawa yayi ya dubi ɗayan saurayin da suke tare da basu wuce sa'o'in juna ba yace ," suleiman ko kaji kamar muryar mutum a cikin office ɗin nan yana dakatar da ni ? ," eh hamza naji mana muryar mace ba ,? "wanda aka kira da suleiman ke furta hakan fuskar sa ɗauke da ɗan siririn murmushin da ya yi kyau akan madaidaiciyar fuskar sa ,"

Ba tare da jinkiri ba hamza ya murɗa hannun kƴauren gami da danna kan sa ciki"

Jikinta babu inda baya rawa a saboda duk ta riga ta gama jin zantukan su , cikin office nake ba banɗaki ba toh inane office ɗin ? kar dai wani wuri ne na musamman wanda bai da alaƙa da banɗaki ni falmata na shiga uku yau ," shine kalaman da suke ta maimaituwa a cikin ranta lokaci guda kuma tana gyara zaman zanin ta da rigar ta har ma da adikon da ke kan ta bayan ta miƙe tsaye ,"

Ware idanun sa sosai yayi yana kallon ta tamkar dai yaga sabuwar halitta ,tun daga sama har ƙasa , wata irin zabura yayi ya jaa baya sakamakon ganin ruwan da yake kwance male-male akan tattausan shuɗin kafet ( Carpet ) ɗin ofishin daga gefen kafafun ta ,

tattare fatar goshin sa yayi tare da ƙanƙance idanun sa a lokacin da tunanin sa tare da abun da yake gani suka tabbatar masa da abun da ta aikata masa a office ɗin sa da dazu-ɗazun nan masu shara suka share kowanne lungu da saƙo tare da goge shi haɗi da feshe shi da turare a saboda manyan ɓakin da suke tafe,

Da gudu-gudu ta ƙaraso wurin hannun ta rike da zundumemiyar gorar ruwa wacce koh murfi babu , a cike taf da ruwa har yana ɗiga ," ɗan satar kallon saurayin da ta tadda a bakin kofar banɗakin tayi ," da sauri ta ɗauke kan ta sakamakon haɗa idanu da suka yi ta ga yana bin ta da wani kallon da yake nuna alamun kƴamata ,

Cikin sanyin murya da gurbatatciyar hausar ta tace kayi hakuri yanzu zata fito ɗan ƙwanƙwasa kofar tayi ," falmata ga ruwan kiyi sauri ki fito akwai mai jira ," yakaka ke furta hakan ,"

Jin ihun fashewar kukan falmata ya sanya ba shiri yakaka ta danna kanta cikin wajen da suke zaton banɗaki ne ,"

Suman tsaye tayi lokacin da tayi arba da kyakyawan ofishin da yake tashin kamshi ,' hasaso abun da ƙanwar ta ta aikata a ofishin ya sanya ta jin numfashin ta na mata wuyar shaƙa .

Muryar sa ta dawo da ita cikin hankalin ta wanda a farko bata lura da wanzuwar sa ba ma a wurin

Banza ƴar ƙauye dakikiya , dan ke dabba ce zaki shigo office kiyi min fitsari akan Carpet , ? Ke mahaukaciyar ina ce ? Koh a can ƙauyen ku kin taɓa cin karo da banɗaki da irin wannan tsarin ?

Cikin razana yakaka ta maida duban ta ga falmata , ganin ƙanwar ta ɗurkushe dafe da kumatun ta duka biyu ya sanya ba shiri ta saki robar ruwan , nan kuwa take ruwan ya tuntsure ya fara malala a wajen , amma koh ta kan ruwan yakaka bata bi ba ta karasa ga falmata wacce take ta shishiƙar kuka ta ɗago ta tare da rungumo ta baki ɗaya zuwa cikin jikin ta .

Falmata meye ya miki ? Dukan ki yayi me ya same ki ? Waɗan nan sune tambayoyin da yakaka take ta faman furta su ga falmata,"

Ɗagowa tayi tare da falmatan da ta kama jikin rigar yakakan ta maƙalƙale kamar zata koma cikin ta saboda tsabar tsoro da zafin marukan da ta sha , wanda tun da take ba'a taɓa yi mata makamanta su ba ," sai shishiƙar kuka take ta kasa buɗe baki ta bawa yakaka amsoshin tambayoyin da take jero mata, ita burin ta ɗaya kawai su bar cikin wurin da aka kira da offishi ,"

Da matsanancin bacin rai yakaka ta ɗago idanun ta ta sauke akan fuskar sa wanda yayi kicin-kicin da ita kamar zai kurma ihu hannun sa harɗe a kirjin sa yana ɗosane daga baki-bakin kofar da alama baki ɗaya ma kyamar offishin yake ji a yanzu ,"

Sauke idanun ta tayi ba domin ta ji raguwar bacin ran da ta tsinci kan ta aciki ba a dalilin fahimtar da tayi ya dokar mata kanwa sai dan wani girma tare da kwarjini da ta ga ya yi mata , gefe ɗaya kuma zuciyar ta na tunasar da ita tare da girmama mata girman laifin da kanwar ta ta aikata da ya sa har wannan gabjejen ƙaton ya mare ta.

Ka-kayi hakuri dan Allah bamu sani ba ne , ' shine kalmar da yakaka ta furta a dai-dai lokacin da ƙara taku biyu cikin son ficewa daga offishin ,

Wani sabon bacin rai ne ya taso masa ganin yadda falmata ta wani ƙwaƙume a jikin yakakan ta ƙi ko da duban sa bare ta bashi hakuri duk kuwa da cewa ita ce mai ɗauke da kaso chasa'in cikin ɗari na girman laifin ,

Ganin bai motsa ba bare yayi magana ya sa yakaka tayi zaton koh ya haƙura ne ,' dan haka ta saƙalo hannun falmata suka fara taku da shirin barin wajen , sun zo dai-dai ficewa daga offishin

Cikin bazata ta ji ya fizgo wuyan rigar falmata ta baya da nan take rigar ta bada sautin ɓarr alamun ɓarkewa , wurgi da ita yayi cikin fitsarin ta faɗa ciki ragwaf ,

Mahaukaciya waye zaki bar wa aikin goge fitsarin da kika yi min ? Sunkuya maza ki goge shi tas idan ma kuma zuƙewa zaki yi da bakin ki ki maida abun ki inda ya fito ya rage naki , bukata ta kawai kar na ga damshi ,"

Ke ma kuma ya juya ga yakaka wacce fuskar ta tayi jawur , tare da wani irin mabayyanin bacin rai da har ya sa laɓɓan bakin ta karkarwa , ki sunkuya ki goge ruwan da kika tuttular a nan kafin na kira sojoji su baku horo

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login