Showing 3001 words to 6000 words out of 411050 words
Chapter 2 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
randar su wacce ita ƙadai ce ba'a tarwatsa ba a gidan su ,"dalilin tana binne ne cikin ƙasa" ta sunkuya tare da buɗe randar , hawayen idanun ta da suka ƙi tsayawa suna ɗiga cikin randar , ta yi goho tare da sa kwanon cikin randar da nufin ɗibo ruwan ciki amma sai taji hannun ta ya tokare bai karasa ƙasan ba sannan kwanon ya bigi wani abu a cikin randa a firgice ! Ta mike jikin ta yana rawa tafara jaa da baya ,tana tunanin menene a cikin randar ?
Ji da tayi kamar wata karamar dushashiyar murya tayi magana Daga cikin randar da ya sanya ta sake shiga cikin fargaba !, kuma kamar wacce aka zabura ! Sai ta nufi randa da gudu gami da durƙusawa ta leƙa cikin randar zuciyar ta cike da zumuɗin Allah ya sa tunanin ta ya zama gaskiya .
Ai kuwa da sauri ta sa hannu gami da taya ƴar uwar ta ta fitowa daga cikin randar da tayi maboya a ciki wacce bakin ta ya riga ya guntule ya farfashe daga sama , tana gama taya ta fitowa ta rungume ta cikin kuka yakaka take tambayar Falmata ina mamar su ? ina sauran ƙannen su ?
Cikin kuka da dushewar muryar da bata fita sosai tsabar kuka take cewa lokacin da muka fara jin harbi sosai sai mama ta ɗauki bulama da yaana, ni kuma ta saka ni cikin randa "saboda tasan bazan iya gudu da sauri ba dan bana GANI " ta ce min zata kai su yaana gona ta boye su ta dawo nima ta ɗauke ni , shine har yanzu bata dawo ba, Yakaka ina baban mu ? Ki kaini gurin sa ya nemo mana mama da su yaana ,,, ina jin tsoro dazu naji mutane har gida suna neman mu inajin ihu a gidan su modu da gidan su yanziye naji suna ihu da cewa wuta wuta , ana ta kuka da salati ina ji ana harbin mutane , meye yake faruwa yau a garin mu ?
Jin shiru ya sa falmata ta fara lalube har ta kama hannun yakaka wacce tun da falmata ta fara bayanin take kuka , kukan mutuwar mahaifin su , da batan mahaifiyar su da ƙannen su , kukan tausayin falmata da take MAKAUNIYA , marar gata marar galihu , daman gatan su Allah sai kuma iyayen su to gashi sun rasa su a lokaci ɗaya , ba iyaye kawai suka rasa ba har da dangin su ƴan uwa , makota da abokan arziki , gidan su da garin su baki ɗaya , dan ko ba'a fada musu ba ta san garin su ya tarwatse , hakan yana nufin sun rasa kome nasu .
Wani irin kuka me karfi ne ya kwace mata ta sake rugume kanwar ta tsam-tsam tana jin bata da kowa bata da kome sai Allah sai *FALMATA KANWAR TA* ,
Kukan su ya tsannanta lokacin da yakaka ta gama sanar da falmata kome game da mutuwar baban su , kuka suke an rasa me rarrashin wani a tsakanin su , ga wani irin mugun tsoro da zukatan su ke ciki na rashin jin motsin kowa a unguwar su kusan ma garin nasu baki daya , ga baƙin hadarin da ya hado bakikkirin wanda ya kara wa sararin samaniyar garin da dare ya riga yayi duhu sai walkiya da cida ,alamun ruwan sama gaf yake da fara zuba .
A hankali yakaka ta ɗago falmata daga jikin ta tana share mata hawayen da suke zubowa daga gurbin idanun ta wanda idan ba an fada maka ba ko kuma ka lura kaga yadda suke tsaye kem alamun basa amfani uwa uba kagan ta tana lalube , baza ka taba cewa bata gani ba domin tar idanun ta biyu suke a buɗe ,ko meye sanadin makantar ta ? Ko haihuwar ta aka yi da shi ?
Ɗaga kai tayi ta sake kallon sama tana tunanin ina zasu samu mafaka daga dukan ruwan saman da yake daf da tsugewa , da sauri wata dabara ta faɗo mata cikin dusashiyar muryar tace falmata muyi sauri muyi sallah kin ga ruwa za'a fara ke kuma kin san kina rashin lafiya idan ruwan sama ya doke ki "zazzabi da mura" dan haka idan mun idar da sallah sai ki koma cikin randar ki bani hijabin ki na haɗa da zani na na rufa a bakin randar sai na daura murfin "wani ƙuzajjen farantin kwano ne" na rufe ki a ciki zuwa lokacin da ruwan zai tsaya sai musan in da zamu yi .
gƴada kai kawai falmata tayi , cikin sauri-sauri suka yi alwala suka duddungura sallolin su wanda kana gani kasan akwai ƙarancin ilmin addini a tare da su, ko kafin su gama an fara yayyafi da karfi da ya sanya yagana yanke doguwar addu'ar da ta fara ta kama hannun ƙanwar ta tare da kama mata ta koma cikin randar .
ko kafin ta gama toshe mata bakin randar ruwan ya riga ya tsinke, cikin hanzari ta gama rufewa ta tsugunna a bakin randar daga ita sai rigar ta da ɗankwali sai kuma siket ɗin ciki, haka ta takure jikinta ruwan nan yana dukan ta , ta ɗaura kanta akan gwaiwar ta hawaye yana sauka a idon ta tare da zubar ruwan saman da yake sauka a fuskar ta yana wanken hawayen da yake sauka, bakin ta ɗauke da addu'o'i iri-iri da take yin su cikin yaren ta.
Ruwan saman sai yayi kamar zai tsaya sai kuma ya sake tsugewa , a hankali sai da tsakar gidan su ya cika taf da ruwa, " kamar yadda ya saba" cikin karamar muyar falmata ta ankarar da yakaka wacce ta yi nisa cikin tunani har bata jin yawan ruwan da ya haura idon kafar ta ,"ruwa ya fara shigowa cikin randar yakaka,' cikin tashin hankali da sauri ta zame dankwalin kan ta ta matsa ruwan jiki ta sa dankwalin ta toshe hudar jikin randar da ruwan ya ke tsiyaya ciki ta ɓulin,
Ta sake tsugunnawa gami da takure jikin ta cikin jin matsanancin sanyi da wani ciwon kai da suka dirar mata lokaci daya , hakoranta sai karo da junan su suke tsabar karkarwa,
a hankali ruwan ya fara tsagaitawa bayan kwashe kimanin awa daya da kusan rabi ana tsugawa , sai iska me karfi da matsannancin sanyi ne yake busawo tare da sauran feshin ruwan saman .
*************
*MARAƊi Niger République*
Jihar maraɗi itace cibiyar kasuwanci a kasar Niger wacce Allah ya albarkace ta da masana'antu , masu kudi, da ma'aikata sanan kuma tana daya daga cikin garuruwa na kudancin Niger karkashin manyan garuruwan kasar hausa kuma ta kasance karkasin mulkin katsina shiyasa ma ake mata lakabi da katsinar maradi domin katsina ta mulke ta tun lokacin yakin kasar hausa kuma hasalima yanzu idan za a kira sarautar maraɗi sai ance sarkin katsinar maraɗi.
Kenan zamu iya cewa maraɗawa katsinawa , tun asali Maraɗi tayi yake yake sosai a kasar hausa inda taci nasarar wasu garuruwa wasu kuma su ka bata kashi amma dai tarihi ya nuna bamaraɗe jarumi ne kuma baya tsoro wanan shi yasa ta bunƙasa har zuwan turawan mulkin malaka a kasar hausa inda suka sha gwagwarmaya da turawa a wancan locakin ,a zamani sarkin katsinar maradi tsakanin shekara ta 1892 zuwa 1894 .
Bayan jihadin sheik usmanu fodio inda ya yaki sarakunan kasar hausa ya kuma jaddada addinin islama a wanan nahiyar ya kuma canza sarakuna da dama musaman wadanda suka bijirewa kaidodin sa maradi ta shiga cikin jerin kasashe da wanan abu ya ritsa da su
Kuma tasamu sarakuna 23 Tun daga kan Sarkin katsinar maradi Dan kassawa 1817, 1830
Har izuwa kan na yanzu .
Wannan kenan
Cikin Tafkeken falon wanda yake ɗauke da kayan ado da alatu , irin wanda ake samun su kaɗai gidan sarakai ,cikin masarautu irin namu na gargajiya ,
Mutane biyu ne cikin falon Mutumin da kallo daya za'a yi masa a hango girman cikar kamalar sa ,kasaitar sa da mulkin da ke gare shi yana zaune kan ɗunɗumemiyar kujerar da take ware daga tsakiyar falon tana fuskantar duk me shigowa cikin falon .
Gefe da gefen kujerar ƴan kananun teɓurin gilas ne dayan teburin saman sa ɗauke yake da ƴaƴan itatuwa nunannu lafiyayyu tun daga kan inabi,ruman ,zaitun,tuffa,tanjari, da sauran manyan ƴaƴan itatuwa masu daraja , ɗayan teburin kuwa ɗauke yake da wata kyakkyawar butar shayi da take kan wani babban farantin da suka zo tare ruwan zaiba tare da kananun kofunan ta da chokulan da daga gani du tare suka zo ,
Daga kasa kuma tsakanin kewayen manya-manyan kujerun da suka yiwa tafkeken falon ado , wani dogon saurayi ne wanda bayan sa kawai za'a kalla a gane tsawo da cikar halittar sa ta ɗa namiji kansa a sunkuye ,kafafun sa a tanƙwashe yayi zaman raƙumma gaban wannan mutumin yana sauraran duk wasu kalamomi da suke fitowa daga bakin sa ɗaya bayan ɗaya , da yake cewa ,
YOUSSOUFA na samu sakon bukatar da Ka zo da shi ,sai dai ina bukatar jin ƙarin bayani daga gare ka ,? Cikin kwantar da murya wanda aka kira da youssoufa ya ce ranka ya dade kamar yadda na fada wa jakadiya , wani aiki ne ya taso daga gwamnatin kasar nan wanda ta zabi sojoji kimanin dubu ɗaya da ɗari biyar, ta kuma wakiltani a matsayin shugaban su da zan jagorance su zuwa kai tallafin gaggawa ga yankin makociyar mu kasar Nigeria akan ƴan tawayen nan na boko haram da suka addabi yankin arewacin kasar wadda idan muka yi wasarere mu ma annobar tana iya shafar kasar mu nan Niger saboda boda da makoftakar da muke da juna ta kurkusa ,ya ɗan tsagaita gami da ɗaga kai ya kai kallon sa ga fuskar mutumin da ya zuba masa ido yake saurarar sa da dukkan hankalin sa.
Sake sunkui da kai yayi gami da cigaba da cewa shine nake neman alfarma akan a ɗaga biki zuwa lokacin da zan dawo wanda nake tunanin ba zai gaza nan da shekara ɗaya ba , do Allah ayi mini alfarma mai Martaba ,"ya karasa furta hakan cikin marairaicewa da kwantar da murya " ?
Ɗan gyaran murya yayi kafin yace ,wagga lamari naka da ban mamaki ike kai youssoufa anya aikin taimakon ƙasa zai wucce raya sunnah ? ɗan jim yayi ɗaga bisani yace tashi kaje du shawarar da muka yanke tana iso maka ta hannun jakadiya ,
Ras-ras yaji zuciyar sa ta tsinke tun da Mai Martaba yace sai yayi shawara yasan bai gamsu ba bai amince da alfarmar da ya nema ba hakan yana nufin bazai amince masa ya tai zuwa nigeria wanda kuma hakan yake dai-dai da rasa aikin sa da tun da yayi wayo a duniya ya san soja ya kasance bashi da wani burin da ya wuce ya zama SOJA , duk da kasancewar sa ɗan sarki kuma BIYAMARADI , haka ya dunga kawar da duk wasu kalubalen da zasu shiga tsakanin sa da cikar burin sa ya shaa gwagwarmayar da ta kawo sa kan matsayin da yake na yanzu me amsa cikakken sunan COLÓNEL YOUSSOUF ABDOUL AZIZOU BASKORE !!!!!!!....
[6/24, 9:49 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association
*MAFARI.......* ( _HARGITSIN RAYUWA_ )
*Umm'muaz*
2
Cikin sanyin jiki tare da rashin kuzari yake takawa yana wuce zauruka da sashi sashi kamar yadda aka San tsarin ginin masarauta yake.
Jerun gwanon bayin sa su rai biyar suna biye da shi tun daga ƙofar fada inda ya amsa kiran Mai martaba , tafe yake cikin kasaitar da ta amshi tsarin zubin sa na ingarman namiji dogo da ya kere dukkanin mutanen da suke tare da shi tsawo a lokacin.
fuskarnan tasa a murtuke kitib ya fito a SOJAN sa sak kuma BIYAMARADI, baya ko amsa gaisuwar bayin da suke ta faman zubewa a ƙasa suna kai gaisuwar su tare da kirarin da suka saba yi masa.
Biyamaradi dan sarki mai jiran kujerar mulkin kassar mu
albarka, kayi gadon mai martaba. Biyamaradi jarumin jarumai, biyamaradi namijin, ayi yau ayi gobe sai gaskiya jibi rago ya kassa.
Dan sarki mai makaman yaki, Dan sarki mai ado.
Biyamaradi kai zaki ne mai watsar da taron maza Dan sarki mai tarin illimi to kayi ga arabi ga boko wallahi ka kure tunanin Masu tunani.
Allah.ya kare ka gwani na hattara biyamaradi. hattara biyamaradi. Hattara biyamaradi HATTARA BIYAMARADI
Sai dai ga Biyamaradi yousoufa a yanzu sam basa burge shi basa sanya shi nishaɗi , babu abun da yake sanya shi nishaɗi a yanzu irin karar kafafuwan sojojin da suke jaan tunga su ƙame masa idan sun hango shi , babu muryoyin da suke burge shi irin na amsawar sojojin da ke karkashin ikon sa idan ya basu umarni ,
Dai-dai ya zo shiga sashin sa da yake bangare guda ko kuwa ɗaula guda a cikin gidan nasu ya ga wani hadimin sa ,wanda yana karasowa wajen ya zube ƙasa yana ƙirari tare da kai gaisuwar sa , bayin da suke tsaye a bayan sa su suka amsa da " Biyamaradi ya amsa gaisuwar ka meke tahe da kai ? " yana daga durkushe yake isar da sakon dalilin tsayuwar sa anan "jakadiya" ce tace ya zo ya jira shigowar yarima ya koma ya sanar da ita .
yana jin abin da bawan nan ya faɗi ya sanya kansa gaba gaɗi ya shiga gidan sa tare da yi wa bayin alama na kadda su biyo bayan sa , ( domin shi ya tsani taron bayun nan da suke zuwa du su zagaye shi su hana shi sakat ko wanne motsi yayi idanun su na kai suna yi masa surutun banza"kirari" a cewar sa)
babu wanda ya motsa daga inda yake cikin bayun nan domin idan da sabo yaci ace sun saba da tsarin halayyar BIYAMARADI"
Yousoufa shine ɗa na biyar a wurin mai martaba ɗa na huɗu a wurin mahaifiyar sa , kuma ɗa namiji na farko a gidan baki ɗaya , mahaifiyar sa ɗiya ce ga sarkin birnin gaoure, ita ce ƴa ta biyu cikin jerin ƴaƴan mai martaba Lamiɗo " Bafullatana ce gaba da baya kamar yadda kowa yasan birnin gaoure garin hullanin usul ne ,
Mahaifiyar yousoufa da mai martaba(sarkin maraɗi ) auren so da kauna suka yi , tun lokacin mai martaba bai kai ga hawa kujerar mulkin birnin maraɗi ba suka haɗu a wurin bikin yaye ɗalibai ƴan makarantar gaba da primary ta makarantar "École Bedir" da ke birnin Niamey a wancen zamanin da sai ƴaƴan wane-da-wane ke yin makarantar ,kanwar mai martaba " Zainab tana cikin ɗaliban da aka yaye a wannan shekarar ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da tara 1979, "wanda shi mai martaba Abdoul azizou ya wakilci mahaifin su wajen taron a lokacin shi ɗalibi ne a jami'ar Abdoul Moumouni Diof da ke nan cikin birnin Niamey"
Anan yaga safiyya , tana ɗaƴa daga cikin ƴan matan da aka zaɓa domin su gudanar da ƴar kwarya-kwaryar wasan koikoyo da akan yi lokacin bikin yaye ɗalibai , kallo ɗaya yayi wa ƴar fulanin yaji ta kwanta masa ya kuma ji cewar ya samu matar aure ,
Bai yi ƙasa a gwaiwa ba ya sanarwa zainab tare da gwada mata yarinyar daga nesa lokacin da aka kammala taron ana shirin watsewa nan take kuwa zainab ta shaida ta domin ta san safiyyah farin sani hasalima tamkar kanwar ta take domin koh lokacin da aka kawo safiyyah ajin farko a makarantar ita kuma tana aji na uku a lokacin ɗakin kwanan su guda su biyu ne rak a ɗakin kasancewar haka tsarin ɗakunan kwanan ɗalibai na makarantar yake, mutane bibbiyu ne a kowanne ɗaki , sun shekara guda tare cikin aminci har zuwa lokacin da ita zainab ta shiga ajin manyan ƴan secondry "aji huɗu" a lokacin ne aka sauya mata ɗaki ta koma saman bene a hawa na farko ,
Hakan ne yasa koh da yayan ta ya nuna ra'ayin sa akan safiyyah taji dadi sosai kuma ta wuce masa gaba ta gabatar da shi a wurin safiyyah duk da cewa dai ita a lokacin ne ma take aji na huɗu , Amma tayi na'am tare da maraba da bamarɗe Abdoul azezu .
Haka dai tafiya sannu-sannu suna tare cikin aminci da so da ƙaunar junan su har zuwa lokacin da safiyyah ta kammala karatun gaba da primary a shekarar mai martaba sarki Youssoufa Baskore mahaifin "Abdoul azizou ƴa tura da takardar neman aure da kayan nagani ina so ga masarautar sarki lamiɗo na barnin gaoure inda shima bai yi kasa a gwaiwa ba ya amsa cikin tsantsar farin ciki da lamarin "domin a garesu hakan babbar nasara ce kasantuwar kowa ya san sarautar maraɗi ita ce ta biyu a karfin mulki kaf kasar niger "
Aka tsaida ranar auren su sha biyar ga watan satumber na shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da ɗaya "15-sept-19981, rana ta zo aka sha biki amarya ta tare a gidan mijin ta sasahi guda a cikin gidan sarautar maraɗi .
Kwance tashi rayuwar su ta fara miƙawa cikin aminci fahimtar juna da tsantsar ƙaunar junan su , Allah ya Albarkace su da haihuwar ɗiya mace shekara ɗaya da auren su wacce ta ci sunan marigayiya mahaifiyar su Abdoul-azizou wacce ta jima da rasuwa tun su na yara ,"Halimatu'sa'adiyyah" ana kiran ta "Ammi"
Tsakani shekara biyu cif da safiyyah ta sake haihuwar ɗiya mace aka sanya mata sunan mahaifiyar safiyyah "Suwaiba" ana kiran ta "dada "
Bayan watanni tara da haihuwar "dada "
safiyyah ta sake samun ciki ta haifo "zainab" wacce ta ci sunan kanwar Abdoul-azizou sai ake kiran ta "ubbo"
Tun daga nan fa sai mai martaba sarki Youssoufa ya ce Abdoul-azizou sai ya sake aure koh ya samu magaji tun da ga alama matar sa uwar ƴan mata ce , babu yadda Abdoul-azizou bai yi ba akan ya fahimtar da mai martaba haihuwa kyautar Allah ce babu ɗiya mace koh ɗa namiji dukkaninnsu ɗaya ne har kullum masu albarka ake nema .
Sai dai fir mai martaba yaki saurarar sa domin a gefe guda "hajiya uwa " da takasance matar sarki ta biyu "wacce take matsayin babbar matar sarki tun bayan rasuwar mahaifiyar su Abdoul-azizou " a lokacin ta samu wuri