Showing 111001 words to 114000 words out of 411050 words

Chapter 38 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14380

baya ,"

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin farin cikin sake ganin ta yana ratsa shi , ya zubawa bayan hijabin ta ido da duk jinin falmata ya ɓata , '

   A garin yaya harsashi ya same ta ?
  Ya jefa mata tambayar lokacin da ya ga ta gama shan ruwan ,"

Muna cikin rumfa ne a bakin kasuwa

Bakin kasuwa ? ya maimaita
   Me kuke a bakin kasuwa a wannan yanayin da gari yake ciki na hargitsi ?

Daman anan muke zama
   Ta amsa masa

Kamar yaya ? Yaushe kuka dawo garin ?

   Ɗagowa tayi ta dube shi
Daman muna gari , a bakin kasuwa muke kwana a cikin rumfar mai shago !

  Ji yayi kan sa ya wani irin juyawa , take alamun da ya gani na masu ciki a tattare da ita ya faɗo masa cikin rai ! Shi ƙwararren likita ne wanda ya san aikin sa ya kuma faɗaɗa tare da zurfafa bincike cikin duk wani ilmi da ya shafi lafiyar ɗan adam , ba sai wani ya faɗa masa ba ba kuma sai yayi gwaji ba babu shakka cikin kallon tsanaki da yayi wa yarinyar ya fahimci tana da juna biyu , toh amma ta yaya haka ta faru ?
Wani mummunan tashin hankali ya ziyarce shi lokacin da yayi hasashen abun da ya faru ga rayuwar yarinyar , da ta yadda aka yi ta samu cikin

  Tare da waye kuke kwana a bakin kasuwa ya tambaye ta yana tsare ta da kallon tuhuma .

   Mu kaɗai ni da falmata !

Bai san lokacin da ya birkito da ita tana fuskantar shi ba ,"
     Wacce irin rayuwa kuke yi a bakin kasuwar ? Baki da lafiya faɗa min waye yayi miki ciki ?

     a tsorace ta ɗago kan ta tana kallon sa , yadda taga jijiyoyin kan sa sun tashi idanun sa sun kaɗa sun yi jaa ya sa ta matuƙar razana ,"

Nan take hawaye suka ɓalle a idanun ta , ta sake maƙure kan ta da jikin kofar motar

   Sakin hijabin ta yayi tare da yin baya da kan sa ya ɗora a jikin kujerar da yake zaune bisa ya runtse idanun sa , tunani iri-iri suka rikito masa ,
        Wani ƙazamin ɗan iskan ya riga ya bata rayuwar yarinyar tun a ƙaracin shekarun ta , mutanen  duniya mafi yawan su azzalumai ne , sun cutar da rayuwar yarinyar saboda rashin galihun ta , ji yayi zuciyar sa ta raurawa idanun sa sun kawo ruwa ," wani irin tausayin ta da ya danne tasirin bacin ran sa da zafin kishin da yake ji ,ya mamaye ruhin sa ,
Allah sarki talaka !
  Ya furta a cikin ran sa ,
    Murya ƙasa ƙasa yace
Ki koma ki zauna a inda mutane suke jiran ƴan uwan su marasa lafiya , zan je na dawo ki tabbatar kin ci abinci , kar ki zauna da yunwa ,
    Kamar jira take yayi mata umarni ta ɓalle murfin motar ta fita , hankalin ta gaba ɗaya yayi kan falmata , bata damu ba sam da  sauyin yanayin da ta gani tare da shi da damuwar da ta bayyana a gare shi , bare har tayi wani dogon nazari akan hakan ,"
      Gyara zaman hijabin ta tayi tare da sake riƙo ledar hannun ta da kyau ,ta kama tafiya ,"cikin ran ta tana aiyana baza ta sha wannan kayan daɗin ba falmata zata ajiyewa tana farkawa ta bata ta ci ta sha !

 
Tuƙi yake yi akan hanyar sa ta komawar sa gida amma rabin hankalin sa bai tare da shi , yana ga tunanin halin da yarinyar ta tsinci kan ta a ciki , ba zai yiwa kan sa ƙarya ba tun da jimawa ya fahimci ya faɗa tsundum cikin so da ƙaunar yarinyar da ko a mafarki idan aka ce masa shi zai so mace irin ta zai ce ƙarya ne , toh amma tun da ya gagara kaucewa faɗawa a soyayyar ta , sai ya ɗauki hakan a matsayin kaddarar sa ce watakila matar auren sa ce ubangiji ya turo masa ita a haka , dan haka sai ya shiga neman hanyar da zai yi ya gyara ta ta zamto irin macen da shi yake son ta kasance matar aure a gare shi , karatu yake da nufin sa ta a farko bayan ya kai ta gidan su wurin mahaifin sa , tayi karatu mai ɗan zurfi zuwa ko da matakin diploma ne sai ya aure ta ,

Toh sai kuma ƙwatsam ta ɓace masa , ya sha wahalar neman ta bata nan ! , har ya fara dangana da rashin ta sai kuma ta ɓullo da wani al'amari mai girma a tare da ita ,"ciki ba tare da tayi aure ba , baya tunanin ko uban cikin jikin nata ta san shi ," Al'amarin ba ƙaramin firgita shi yayi ba ya taɓa ran sa fiye da zato , saboda soyayyar gaskiya yake yi mata ,"

A tun bayan barin ta da yayi yanzu ya kamo hanyar sa yake bincikar kan sa tare da ƙwanƙwasar zuciyar sa ko Allah zai sa ya ji wani sauyi na daga soyayyar da yake mata ta zuwa wani yanayi na ƙi ko kaɗan ne a saboda girman bakon al'amarin da yake tare da ita marar kyau ?
Wanda zai yi amfani da hakan wurin yakice ta daga cikin ran sa baki ɗaya ya shafe babin rayuwar ta daga ran sa ?

Sai dai ko kusa shi ya gagara ya ji alamun ya tsane ta , a maimakon tsanar sai yake jin wani matsanancin tausayin ta yana sake lulluɓar shi , zuciyar sa tana raya masa FYAƊE aka mata , fin ƙarfi aka gwada mata ba da son ran ta bane , ita ɗin abar a tausayawa ce , abar a tallafa ce a bata kulawa , a tsaretar da rayuwar ta daga faɗawa mummunan yanayi dangane da irin halin da ta tsinci kan ta a ciki a ƙarancin shekarun ta ,"

    Sashi mafi rinjaye na zuciyar sa ya ji yana ƙarfafar sa akan Ya tallafe ta , kar ya guje mata , ya zamto gata a gare ta kar ya ƙyamace ta , ya Aure ta ya taya ta riƙo tare da tarbiyyartar da abin da zata haifa HAKAN TAMKAR JAHADI NE a gare shi ,
   Da wannan dogon tunanin ya ƙaraso gidan su da yake kan titin danboa road yayi hon maigadi ya buɗe masa kofa ,

kai tsaye falon mahaifin sa yayi wa tsinke bayan ya ajiye motar sa ,

kamar yadda ya saba a  zaune ya tarad da shi bisa wheelchair hannun sa riƙe da Alqur'ani mai girma yana ƙarantawa da mabayyanin sauti .

Sai da ya ɗan tsimaye shi ya ƙarasa ayar da ya ɗauko ,
    Sannan suka gaisa cikin kulawa da nuna tsantsar ƙauna daga mahaifin sa ," ƴan tambayoyi yayi masa game da yanayin aikin sa kasantuwar mahaifin na sa professor ne da ya sha ya ƙoshi ya tumbatsa a harar ilmin kimiyya , yanayin rayuwa ya juyar da lamarin sa haka ya kasance zaune bisa kujerar marasa lafiyar ƙafa bai zuwa ko'ina .

     Ji yake batun yakaka yana zungurar sa akan ya faɗawa mahaifin sa , wani sashin ya dakatar da shi da ya bari har ya samu ƙarin bayani daga bakin yarinyar dalla-dallah ta yadda zai ji karfin zuwa da maganar tare da amsa duk wasu tambayoyi da ka iya zo mar daga baban sa !

    Dan haka ya miƙe yana mai yin sallama da baban nasa ,
    Har ya ɗauki hanyar sashin sa , sai kuma ya dawo ya kutsa kai zuwa ainahin cikin gidan sashin mahaifiyar su da yanzu ƙannen sa ne ke rayuwa a ciki ,
     A babban falon ya tarar da su suna harkokin su , ƴan mata ne su uku ya da ƙanwa , babbar cikin su zata yi kimanin shekaru ishirin da biyar sai mai bin ta sai kuma ƙaramar su ,

   Har suna rige-rige wurin gaishe da yayan nasu inda shi kuma ya amsa musu da yalwatatciyar fara'a bisa fuskar sa ,'
      Girls , so nake ayi girki mai kyau wanda marar lafiya zai ji daɗin ɗanɗanon sa a bakin sa , kamar girki kala biyu haka , a dafa tea da kunu nan da awa biyu zan shigo na ɗauka ,"

   Toh company

Suka haɗa baki wurin amsa masa tare da barin abun da suke suna nufar hanyar kitchen , ta cikin falon

  Ƴar dariya yayi yana girgiza ,"
   Nace muku sunan nan ya fita a bakin ku ko ? Ya furta hakan yana mai nufar hanyar barin falon
    Har ya fita ,  ya dawo ,"

   Zahra !
Ƙaramar su ta amsa gami da dawowa baya ,
   Na'am big bro

Nace ba ! a cikin kayan ki ki ware kamar kala biyar masu kyau ki ajiye idan na zo ɗaukar abincin marar lafiyar zan haɗa da kayan na kai musu ,
    Toh big bro zan ɗauko yanzu , biyar sun isa ko ?
  Sun isa!  ya ansa yana barin falon .

A duk ranar da ya kwana a asibiti toh yini yake yana bacci idan ya dawo , sallah kaɗai ke tashin sa sai ko cin abinci , kafin zuwan wani daren , saɓanin yau da sam ya gaza yin bacci sai juye juye yake yana kallon agogo , zuciyar sa ta zurfafa wurin son samar masa da mafita , shin daga ta haihu ne  zai aure ta ko kuwa zai bari tayi karatu kamar yadda yake da buri ??

Tunowa yayi bai san matsayin sa ba ma tukun a gurin yarinyar duk wannan tsare-tsaren iska yake , daga ta nuna ƙin amincewa kome ya rushe ,

ba shiri ya miƙe daga kwanciyar da ya samu kusan awanni biyu yana yi ,

Karfe ɗaya da mintuna goma agogon ɗakin ya nuna , lokacin sallar azahar ya shigo ,

    Kai tsaye ya sake shiga banɗaki ya sakarwa kan sa ruwa tare da sake ɗaura alwala ya fito ,"
   Mai ya shafa sama-sama ya buɗe ma'ajiyar kayan sa , ya ɗauko wani shuɗin yadi marar nawi mai haske ya saka , ƴar saisayayyar sumar sa ya taje har zuwa ɗan zagayayyen sajen da ya ajiye a gefe da gefen fuskar sa , ya ɗauko turarukan sa ya fashe jikin sa .

Ya zurara bakaken takalman sa yana ɗora igiyar ɓakin agogon hannun sa ,

  
Ficewa yayi a ƙafa ya nufi babban masallacin da yake bakin titin shigowa unguwar su domin yin sallar azahar .

Ƙarfe biyu dai-dai tayi masa a harabar asibitin , kai tsaye ya nufi emergency ward , hannun sa riƙe da ɗan kyakkyawan gwandon roba mai ɗan girma da aka zubo kulolin abinci zuwa ƴan ƙananun flask guda biyu da cups biyu , chokula biyu da plates guda biyu sai serving spoon , ɗayan hannun nasa kuma ya riƙo ɗan ƙaramin akwati ,

Da gudu security ya taso ya karɓi kayan hannun nasa yana masa sannu da zuwa ,"

Yana shiga ya tarar da babu gadon falmata , ya tambayi likitan ina yarinyar da take gado mai lamba goma ?
   Nan yake sanar da shi ta farka har an mata chanjin ɗaki zuwa cikin ward , dan haka ya nufi ward , security biye da shi .

Tun yana shiga ya hango su falmata daga ƙuryar ɗakin gado na ƙarshe , tana kishingiɗe an ɗago mata gadon ta wajen kan ta domin ta ji daɗin kwanciya ,"

Yakaka tana ɗosane a bakin gadon ta tattara hankalin ta baki ɗaya ga falmata tana shayar da ita hollandia yogurt sannu-sannu ,

Tana labarta mata irin jimawar sa tayi a sume da taimakon da dakta hamza yayi musu ,"

Sannu patient ɗina kin tashi ? Ah lalle jiki yayi kyau tunda ga shi har kina shan yogurt , to yaya me kike ji yanzu a jikin ki ? Akwai inda yake miki ciwo ?

Da ƴar fara'ar ta ta waigo inda take jin tashin muryar sa ,
Da sauki dakta , dai-dai wurin raunin kawai shine yake min zogi , sai kuma kaina da yake min ciwo kaɗan-kaɗan , mun gode dakta Allah ya saka da aljanna ,"
Murmushi ya mata , cikin ran sa yana jin tausayin makantar ta ,"
Babu kome ɗan pain ɗin da kike ji saboda sabon rauni ne , daga ya ɗan yi kwana biyu zaki daina ji , ciwon kan da kike ji saboda sabon jinin da ya shiga jikin ki ne , zai daina da zarar jikin ki ya dai-dai ta ,' akwai magungunan ɗauke zogin ciwo za'a kawo miki ," ki dunga cin abinci sosai saboda ki samu ƙarfin jiki ,"

Duban sa ya mayar ga yakaka wacce tun da ya ƙaraso ƙamshin turaren sa ya bigi hancin ta ta ji zuciyar ta ta hautsina , sam ƙamshin bai mata ba , dan haka ta koma daga gefe ta tsaya tana yatsina fuska gaba ɗaya gumi keto mata yake amai yana sasuƙar ta sai dai kuma babu kome a cikin ta idan banda ruwa ,"

Ga abinci nan ku ci , kiyi wanka ki sauya kayan jikin ki , ga kaya nan na taho miki da shi a cikin nan ,
Ya mata nuni da kayan da security ya ajiye a gefen gadon ya tafi, "

Kai ta gyaɗa kafin ta ce
Mun gode Allah ya biya ," cikin ran ta tana Allah-Allah ya tafi saboda warin turaren sa da ke neman kai ta ƙasa , babu abun da take so a yanzu irin ta shaƙi ƙamshin turaren bature kam silum , wanda ta san babu damar hakan domin kayan su yana kulle cikin shagon ", Abuwar mai yadi ," dan haka ta Kai hannun ta biyu ta sa ta rufe rabin fuskar ta daga kan hancin ta zuwa ƙasa ,"

Ware idanun sa yayi sosai yana kallon ta , yadda ta toshe hanci ya sa shi ɗan shaƙo numfashi ko zai ji inda wari yake tasowa amma shi bai ji ba ,"

Bai ce kome ba ya juya ya fara tafiya , tare da cewa watakila zan dawo zuwa yamma ," !



Gaskiya kwana biyu ina mutunci kut! 😂
Watau rubutu nake muku babu kakkautawa, duk domin na Baku nishadi. 😍

Da fatan nima zaku bani tukuici , ta hanyar fada min ra'ayoyin ku, / Me kuka tsinkayo zai faru nan gaba?

Wai shin bakwa cigiyar biyamuradi YOUSSOUFA ne? ? 😂


  
[10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI......
( Hargitsin rayuwa )

umm'muaz


23





Cikin sati guda da suka yi a asibiti sun ga gata tare da kulawa daga wurin doctor hamza , har ma da ƙanwar sa rahima, domin kuwa kusan kullum sai ta zo da yamma ta taho musu da abincin da take girka musu na dare , shi kuma doctor hamza ke zowa da na safen ," da rana kuma ya yo musu take away daga sidic's ,ruwa kan sa na roba suke sha , ga lemuka da kayan shayi irin na garari , biscuits, cake , lokar gadon su cike take taf da cimaka iri-iri , tamkar dai wasu ɗiyan attajirai ,

   Rahima tana da matuƙar surutu da wayon tsiya, yarinya ce da kaɗan ta girmewa yakaka , bai wuce shekaru biyu ta bata ba , ita ce ƙarama a ƙannen doctor hamza ," a halin yanzu ta gama secondry sch tana jiran sakamako , "

doctor hamza shi yace mata ta dunga zuwa ta na ɗan taya su hira ko da ta awa biyu ce , bayan ya nemi iznin mahaifin su ,  yayi masa bayanin su falmata da ƙudirin sa akan su na taimaka musu, sai dai ya boye masa cikin jikin yakaka na banza ne ,maimakon ya fadi gaskiya sai ya ce masa boko haram ne suka kashe mijin ta tun a garin su ,"

Maifinsa bai ƙi ya kawo su gidan su zauna ba , sai dai yayi masa gargaɗi mai karfi kamar yadda ya saba yi masa a kullum cewar ,"Ya tsoraci MATA tare da ƙaidin su yayi hankali da lamarin mata domin sau dayawa su ɗin ba'a gane gaskiyar su , wanda duk ya bada gaskiyar sa a gare su tabbas zasu takaita shi watarana ,"

       Kamar koyaushe ya amsa masa yana jin yadda wani ɗaci ke yawo a zuciyar sa , sam bai so ba da mahaifiyar su ta zamto silar da ya sa mahaifin su ya samu mummunan tabo akan mace da yakasance kullum kalaman sa masu tsauri ne akan MATA ,

*********

Yau yake da niyyar kai yakaka ayi mata scan tare da gwaje-gwajen da ya kamata ayi wa mata a tun farkon samuwar cikin su , duk da cewa har kawo yau bai sake tada maganar cikin ga ita yakakar ba wacce ya lura ita bata da wata damuwa da zaman cikin a jikin ta ,

abun da bai kai ma ga gama fahimta ba kamar son cikin take sosai  , saɓanin sauran matan da ya sani da suke shiga damuwa tare da ƙin abun da yake cikin nasu a duk lokacin da suka samu cikin ta haramtatciyar hanya irin nata ,

sai dai ya danganta hakan da kasancewar yakaka yarinya ce kuma akwai ƙarancin wayewa da rashin ilmi a tare da ita , ko ma menene shi daman ba shi da burin raba ta da cikin jikin ta wanda ya riga ya fahimci yayi ƙwari a mahaifar ta .

Ya zaɓi ya kaita wani asibitin daban a duba ta ne a saboda ƙoƙarin sa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login