Showing 300001 words to 303000 words out of 411050 words
Chapter 101 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
iya cigaba da zama da shi ba ..
Kuka ya ci ƙarfin ta , zuciyar ta na mata zogi ,
Yakaka ma hawayen take yi a dai-dai lokacin bata da sauran kalmar da zata yi amfani da ita ta rarrashi Falmata , ta ta zuciyar ma jinya take .
****
Washe gari da safe bayan sun shirya sun yi karin-kumallo Amnee ta musu jagora zuwa wajen Prof da daman tun a jiya labarin zuwan su ya same shi , haɗi da dangantakar su da Amnee da Rahima .
Bayan ya amsa gaisuwar su , ya dunga bin su da kallo cike da tausayi , can daga ƙasan ran sa yana jin tamkar yana da kamasho mai yawa na kasancewar rayuwar su a haka ,
Ba domin shi da danginsa da suka ƙi auren Rahima da ɗan uwan su ba da hakan ya kawo barin Rahimar gidan da wataƙila yaran basu tashi 'ya'yan ƙauye marasa galihu irin haka ba ,
Da ace ko da mahaifiyar su da sauran 'yan uwan su sun ƙi auren , shi bai biye musu wajen nuna tsanar lamarin ba da har ya kawo saɓani tsakanin sa da Matar sa ba , ya tsayawa Rahimar har ta samu wani mijin ko da ba ɗan uwansa ba , da Rahima da yaranta basu sha wahalar rayuwa irin haka ba , da suka faɗawa hatsararruka da dama mafi munin su hatsarin Ƴan tawayen Boko Haram , da ko babu kome mutumin birni zai aura mata mai daraja da ƙima kamar ta sa .
Yana jin yanzu lokaci ne yayi da zai gyara kuskuren sa , har yanzu yana da damar sake zaɓowa Rahima wani mijin muddin ta amince , 'ya'yan ta kuwa daman Allah ya faɗo da taimakon su ta hannun sa , ashe akwai abunda Ubangiji ya ɓoye ,
Dan haka ƙudirin haɗin Auren Hamza da Yakaka da ya yi niyyar yi tuntuni ya ji ya sake kaurara a cikin ran sa , har ma ya ji dacewar matso da lamarin kusa , wataƙila da jajircewar da zai yi cikin Rayuwar Rahima da 'ya'yan ta a sauran rayuwar da ta yi masa saura zai samu ya ragewa kan sa girman laifin da yayi wajen tayawa a wargaza rayuwar Marainiyar yarinyar da take amana a wajen sa .
Cike da nuna tsantsar kulawa ya shiga jan su da hira ba tare da ya shigo musu da wata tambayar da ta shafi ɓangare na rayuwar su ba , cikin hirar da kusan su biyun ke yin ta a tsakanin su Amnee tace ,
" Baa Alaji , a ƙira yaran nan duk a sanar da su dawowar ƴan uwan su , saboda a sa rana su zo su gana da juna ko kuwa ?
" Hakane , to amma tun da daman nan da ƙasa da sati huɗu ya rage bikin ita Rahima ƙarama kuma a halin yanzu ita da Zainab ɗin duk basa ƙasar suna can Dubai ko da an sanar da su dawowar ƴan uwan nasu sai a bar batun haɗuwar su har zuwa nan da sati biyu da duk zasu hallaru domin bikin Rahima .
" to shikenan Baa Alaji bari yanzu zan ƙira idan mun koma ciki idan ma ya kama a haɗa su a waya su fara gaisawa ,
" to babu laifi , ya zarce da cigaba da cewa,
" Rahima baku da wata damuwa ko ? Da sauri Khaalty Rahima ta amsa ,
" babu damuwar kome Yaya , Allah ya saka da Alheri ya ƙara nisan kwana .
Amin yace yana Gyaɗa kai ya mayar da ganin sa kan su Yakaka ,
" Yarana kuma babu wacce take da wata matsala ko ,? Idan kuna da ita ku sanar da ni , ni tamkar Mahaifi nake a wajen ku Mahaifiyar ku ƙanwata ce ,
Girgiza kai Yakaka tayi , a hankali tace "Baa babu matsalar kome mun gode , Falmata wacce kan ta yake sunkuye ta ɗago kai kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru tana sake sunkui da kai ,
Prof da duk yake kallon su yace ,
"Fatima akwai matsala ko ? Meye kike son ki faɗa min , ina jinki ƙaramar 'yata ?
Dukkanin su sai suka mayar da ganin su kan Falmata wacce kan ta ke sunkuye ,
'Baa so nake Dan Allah ka raba auren mu , bana son cigaba da zama da shi ko kaɗan Dan Allah Baa ka sa ya sake ni .
Muryar Falmata ta ratsa wajen cikin alamun da take gaf da fashewa da kuka ,
Shiru ne ya ratsa falon , tamkar ruwa ya cinye su , kafin Prof yayi gyaran murya yana karantar yanayin ta yace ,
"Fatima shi mijin naki laifi ya yi miki ? Ko kuwa wani abu aka miki daga danginsa ? Ko kun samu saɓani ne da shi ?
Shiru tayi bata amsa ba , sake maimaita mata tambayar yayi nan ma tayi shiru , Khaalty Rahima zata yi magana ya dakatar da ita ,
Ya sake cewa
"ko kuwa kawai daina son shi kika yi ? Ko gajiya da zaman ku tare kika yi ? Ko kuma can ƙasar tasu ce bakya so ?
Da sauri ta gyaɗa kai ,
murmushi mai sauti yayi , cike da tausasawa yace " to babu laifi , ki ƙira shi kice na ce ya zo ina son ganin shi , idan ya zo sai a yi miki yadda kike so kin ji ko ?
" to Baa nagode .
Murmushi yayi bai ce ƙala ba .
****
Niamey Police nationale
Maimounatou wacce take zaune daga kan wani ɗan dandamali da aka tanada shi musamman domin zaman waɗanda ake tuhuma da laifi a cikin babban ofishin 'yan Sanda na ƙasar Niger baki ɗaya .
Ta muskuɗa tana cigaba da wasa da awarwaron hannun ta , tayi kunnen uwar shegu da duk wasu manya da ƙananun tambayoyin da babban ɗan Sanda da yake tsaye daga kan ta yana jefo ma ta ,
Ganin taƙi yin magana ya sa ɗan Sandan ƙutawa cike da kaiwa maƙura a jin haushin ta , ya mayar da ganin sa kan Mammadou bayan ya ɗaga takun sa zuwa gaban sa ,
" Mammadou ko za ka iya faɗa mana dalilin da yasa ku ka ciyar da ɗan ouwan ka guba ?
Da sauri Mammadou ya ɗago da kansa ,
" Wallahi ni bani da wata masani kan abunda yake faruwa a shiyar gidan Youssouf , matar sa ita tayi ƙira na kan cewa na zo fa ga ɗan ouwana ya faɗi yana biɗar taimako na , shine na runtuma da niyyar kai masa ɗauki , da shigata na tadda shi a halin da ku ma kun ka zo ku ka taddo shi , wallahi ni iyakar abunda na shina kenan ban.....
Wata dariyar mai sauti da Maimounatu ta sanya , ita ta katse masa jawabin sa ya mayar da ganin sa kan ta yana ƙif-ƙifta ido , ba tare da ta dube shi ba tace
" Mammadou wallashi cikkin ragwaye kai na ƙurya ne , yo me kake tsoro idan ya tabbata gubar da shi wannan Azzalumin ya ci ta hannun ka ta fitto ? hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kouwa ɗaurin rai da rai muddin rayuwa ?
" Burina labarin mutuwar sa ta jishe ni , daga nan koume shi faru dai-dai ne , ai hukuncin wadda ya kashe a kar shi , shi da kansa bisa turba nasa hukuncin yake , fansar ran Ghaddafi tare da gudan jina na da na rasa na ɗauka bissa kan sa , kai gudumawa ka bada bisa turbar naka cikar buri ko kouwa ?
Laɓɓan bakin Mammadou har rawa suke cikin in'ina yace ,
" kadda ki mini ɓakin sharri ɗiyar nan , ni yaushe na kawo miki gubar da kika ciyar da ɗan ouwa na da itta ? Ki yiwa Allah kadda ki tunkuɗa ni cikin masifa ,
Wani kallon banza Maimounatou ta wurga masa , idanun ta jajir tace .
" Yau ba rana ce ta yin wassan ƴar boye ba Mammadou ka daina yin kamar baka san kome ba , kamar kai da Mahaifiyar ka baku taya ni ba , bana son muyi rabuwar tsiya doumin kun bani taimako wajen biya hakkin Ghaddafi tukuici ya kamata na baku .
Ɗan sanda da yake rubuta duk wasu kalamai da suke yi , ya ɗan karkato ga Maimounatou , ganin kamar ta shirya bada wasu bayanai ,
" Wanene Ghaddafi menene kouma alaƙar sa da kashe Mijin ki da kika yi ta hanyar ciyar da shi guba .
" Ghaddafi masoyina ne .
****
Ghaddafi Yacouba Dango asalin iyayen sa ƴan ƙasar Mali ne da suka hauro sahara suka shigo ƙasar Niger , suka yada zango a yankin Agades , inda suka yi mazauni cikin wani kongon gida da yake daga baya sosai da Babban gidan sarkin Agades ( fadar Maimartaba sarkin Agades ) .
Bayan shi iyayensa suna da wasu 'ya'yan sai dai tsantsar talauci ya sanya su fantsama a cikin gari yin barace-barace , duk kuwa da cewa a lokacin shi Ghaddafi saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da ɗoriya ,
Lokacin da ya fara bara sai ya fahimci babu mai kula shi bare har a ba shi , dayawa daga cikin mutanen da yake roƙo ma ƙorar sa suke da zagi kowa na faɗin ya tafi ya nemi sana'a .
Ganin haka ya sanya shi daina bara ya koma tsince-tsincen matattun ƙarafuna a kan bola yana kaiwa yana sayarwa ,( jari bola ) babu laifi yana tallafawa iyayen sa da hakan .
a wannan yawon ya haɗu da wasu kangararrun yara sa'o'in sa da suke jeruwa bisa tsohon hanyar wucewar jirgin ƙasa wajen da aka mayar sa bola su kuma suka mayar da shi matattarar ƙananun shaye-shayen su da yin karta .
Su suka jawo sa cikin su ba ɗau lokaci ba ya zama ɗaya daga cikin su ya kangare , tsince-tsincen ƙarafunan ma ya daina , basu da wani aikin yi sai zaman banza a bakin layin jirgi ko kan katagun kwangayen gidaje , suna ƴan shaye-shayen su , babbar sana'ar su ita ce ƙananun sace-sace , daga sun ga gidan da ake barin sa galala sai su faɗa su yashe mutanen cikin sa , ƴan ƙananun dabbobin mutanen unguwa basu tsira ba , akuyoyi ,talo-talo kaji , agwagi , a taƙaice dai su Ghaddafi sun addabi mutane sun hana su sakewa .
Ganin haka yasa Mutane suka yi ɗango suka kai ƙarar su wajen Maimartaba ,
Da kansa Maimartaba ya sa aka kamo su , aka basu horo tare da haɗa su da aiyuka a cikin gidan sarkin mai wahalarwa na tsawon satika biyu duk saboda a hora su
Ghaddafi yana cikin samari huɗun da aka tura bargar dawakai domin kula da su da share musu waje gami da basu abinci .
Kafin kwanaki huɗu Ghaddafi ya saba da aikin yana kuma jin daɗin aikin saboda ko babu kome yana ci ya ƙoshi fiye da sau uku a rana
Ranar da yake cika sati a kan aikin sa , Babban bawan da ainahin kula da bargar yake ƙarƙashin sa , ya danƙa masa linzamin wani kyakkyawan matashin jan doki ,
Yace ya kaɗe jikin sa da kyau dokin gimbiya ne , yau zata ɗan hau ta kewa akan sa nan cikin filin dake gaban bargar .
Zuwa la'asar sakaliya , gimbiya Maimounatou tare da bayunta biyu suka iso
Ba ɓata lokaci ya jaa limzamin dokin zuwa gaban ta yana mai tsare ta da kallo ganin ta da yayi yarinya ƙarama da bata wuce sa'ar ƙanwar sa ta uku ba ,
Gimbiya Maimounatou tana ɗago kai ta sauke ganin ta a kan sa , zuciyar ta ta wani irin bugawa , a iyakar shekarun ta goma sha shidda alokacin bata taɓa ganin wani ɗa Namiji mai kyaun sura irin sa ba , kasancewar Ghaddafi kyakkyawan balarabe ne na sosai jazur da shi .
Tun daga wannan lokacin sai ta faɗa jarabar ƙaunar sa , bata da aiki sai zuwa barga dan kawai ta kalle shi , a lokacin ita tana hutun kammala makarantar ta ta secondry ,
Sai dai kamar ɗaukewar ruwan sama sai ta rabu da sake ganin sa bayan wasu ƴan kwanaki , duk yadda ta so ta daure ta manta da shi , ta gagara a hankali damuwar rashin cigaba da ganin sa ta fara duƙushe walwalar ta , saboda wannan ne karo na farko da zuciyar ta ta fara son wani ɗa namiji ,
Ganin damuwar ta na neman kai ta ƙasa , sai ta nemi Gnala da ta bincika mata wanene wannan sabon balaraben bawa ? me kuma yasa ta daina ganin sa ? Ko an sauya masa shiyar aiki ne ?
Ba'a ɗauki wasu kwanaki ba ta samu duk wasu bayanai game da Ghaddafi , sunan sa , asalin sa , iyayen sa da laifin da suka yi har aka kawo ƙarar su ga Maimartaba aka hukunta su .
Kuka ta zauna tana yi sosai , so take ta tunbuƙe son shi daga ran ta ji da tayi ko kusa basu dace da juna ba , shi ɗin maƙasƙanci ne ko a cikin maƙasƙanta ko ɗaya ba shi da nagarta da ya dace da samun soyayyar ta .
To sai dai ita zuciyar da so na farko ya fara fasawa ya dasu a cikin ta tauri ne da ita tare da ƙwalafaci , dan haka bayan wasu kwanaki kaɗan sai ciwon son shi ya dawo mata sabo fil ,
Jin ba zata jure rashin ganin sa ba yasa bayan ta samu tabbacin inda yake zama da la'asar sai kawai tayi badda-kama cikin baƙaƙen kayan su na buzaye ta rufe rabin fuskar ta da mayafin ta , ta ratsa sorayen gidan su ba tare da ta bari kowa ya gane ta ba ta fice daga gidan su rana tana daf da faɗuwa , bata ko damu da iskar hunturu wacce ke tayar da rai-rayi da take ta busawa tana tila ƙasa a idanu hanci har ma da kunnuwan al'umma ba ,
Kasantuwar bata saba fita ita kaɗai ba hasalima yau ce rana ta farko da ta taɓa tako ƙafafun ta shiyar unguwar da take baya da Masarautar su da take ta talakawan liƙis , sai tayi ɓatan kai , ta gagara gane kwatancen da Gnala ta yi na inda aka ce Ghaddafi yana zama , ta nemi hanyar jirgin ƙasa ta rasa .
Ƙura tayi buɗu-buɗu da baƙaken kayan jikin ta , magariba kuma ta kawo kai , da kyar ta samu ta tsayar da wata budurwa ta tambaye ta ina ne tsohon hanyar jirgin ƙasa ?
Budurwar ta gwada mata hanyar da hannu, juyawa tayi da sauri ba tare da ta ko yi mata godiya ba ta fara taku zuwa kan hanyar da ta mata nuni ,
" hala can kike noufin zouwa ? Ko kouwa kin san da kwai hatsari bissa hanyar kou ? Kin san fa an sau waɗannan tsinananan samari da suke ratse bissa hanya nan , a shawarce kadda ki bi ta wannan hanyar war hakka .
Tsayawa tayi cak , ba ta juyo bata kuma ce ƙala ba , sai ta sake kaɗa kan ta tayi gaba ta miƙa sosai a hanyar har ta tarar da matattciyar hanyar jirgin ƙasan da duk bola ta mamaye ta ,
Warin da yake wajen ya sanyata rufe hancin ta tana tsallaka tsumi-tsumin bolar da take wajen ,
Shal hanyar take babu kowa ko ƴan dabbobin da suke kiwo akan bolar babu kowa ya kaɗa dabbar sa gida kafin a sibare masa ita gobe kasuwa .
Sai hange-hange take yi cike da burin son ganin sa ,
Taku ta fara ji daga bayan ta kafin warin taba ya mamaye ƙofofin hancin ta ,
Da sauri ta juyo karaf suka haɗa ido da shi tare da waɗansu samari biyu daga dama da hagun sa ,
Daga cikin mayafin ta ta saki tattausan murmushi zuciyar ta na cika da farin-cikin sake ganin sa ,
Warware mayafin fuskar ta tayi , ranar da tayi jazur gaf da faɗuwa ta haske ta tana ƙarawa farar fuskar ta jaa da kyau , cikin siririyar muryar ta tace " Ghaddafi wajen ka na taho .
Zaro ido yayi yana daɗa kallon ta , babu shakka wannan gimbiyar nan ce ɗiyar sarki to me ya kawo ta wajen nan me kuma take nema a wajen sa ?? Hayaƙin tabar da ya cika bakin sa da ita ya fesar ta hanci ta baki .
Tun bayan wannan ranar sai soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin ƙananan matasan biyu ba tare da tunanin me ke je ya dawo ba , soyayyar junan su ta rufe musu ido daga hango tarin banbancin dake tsakanin su ,
Cikin watanni shidda sun yi wata irin shaƙuwa ta ban mamaki duk kuwa da cewa daga ɓangaren ita Gimbiya maimounatou babu wanda yasan da batun soyayyar su ita da Ghaddafi , sau biyu kawai suka taɓa haɗuwa , rana ta farko da ta je wajen sa sai kuma rana ta biyu da ta kai masa kyautar wayar tafi da gidanka sabuwa dal , da ta sa Mahaifiyar ta ta saya mata lokacin ma wayar sai hannun wane-da-wane tare da wasu kuɗaɗe masu yawa .
Zancen tafiyar ta makarantar jami'a ta babbar birnin Niamey shine ya tayar da hankalin su , saboda nisa da zasu yi da juna .
A gobe zata tafi makaranta , ta saci jiki kamar yadda ta saba ta je wajen sa da hantsi ,
Akan ƴar rusasshiyar katangar wani kangon gida ta tarar da shi , a shirye tsaf yake cikin wandon gonjo da rigar sanyi mai haɗe da hula da ya saya daga cikin kuɗin da ta masa kyautar su .
Yana daga sama yayi mata nuni da gefen sa kan katangar akan ta hauro ta zauna ,
Dariya tayi da haƙoranta tana kaɗa kai tace
" Bani iya hawa bissa nan ai kaima ka sani ,
Murmushi yayi ya diro ƙasa bata