Showing 36001 words to 39000 words out of 411050 words

Chapter 13 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14378

,kafafun ta sanye cikin takalma marasa dunduniya bakake , hannun ta ɗaya rike da bakin mayafin ta ɗaya hannun kuma ƴar ƙaramar jaka ce da kallo daya za'a musu asan tare aka ƙera su da takalman kafafun ta ,

Cikin takun ta na rangaji wanda ya dace sosai da zubin ta na doguwar mace samɓal take takowa bayan ta bayun ta ne biyu biye da ita ɗayar rike da jakar kayan ta ɗayar kuma ta riko jakar da take ɗauke da computer ta da kuma wasu tarkacen takaddun su na likitoci ,"

Wani banzan kallo me tafe da sumfurin harara iri daban-daban da biyamuradin ya watsa mata lokacin da take ƙarasowa falon shi ya sa ta kusa faduwa ba shiri ta ɗauke idanun ta da tsautsayi yasa ta jefa su cikin nasa ta mayar da hankalin ta kan ummu wacce take ta faman sakar mata murmushi ,"umma na fito ,"

A fusace biyamuradi ya miƙe gami da yiwa umman sallama tare da tabbatar mata cewa zasu kasance akan waya a kodayaushe ," ba tare da ya sake kallon sashin da take tsaye ba ya sanya kai ya fita a karkashin rakiyar addu'o'in mahaifiyar sa .

Risnawa tayi tare da yiwa umman sallama wacce take jaddada mata da ta kula kan ta , kuma ta tabbatar bata wuce iyakacin kwanakin da ta ɗiba zata yi ba a karshe ta ɗora mata da tarin addu'o'i ,"maza je ki kar su jira ki Allah ya kiyaye hanya ,"

Da gudun ta , ta karaso har tana ɗan haki jikinta rigar wankan ce sai katon tawul ɗin da ta rufu da shi ,"kar dai hamma nah ya tafi ta furta hakan tana mai taro ƙwalla cikin idanun ta ,"

Ba tare da siyaman ta amsa mata ba ta ɗaga kafafun ta tana me ƙarasa ficewa daga falon tana jin lokacin da hajiya umma ta fara rarrashin aishan wacce ta ɗauke ta tamkar ƴar cikin ta ba ƴar kishiya ba ,"

Ta ɗauki tsawon mintoci biyar a tsaye gaban jerun gwanon motocin su biyar bayan da tun fitowar ta wani soja ya amshi jakankunan hannun bayun ta ya sanya su a bayan mota, bayun suka koma suka tsaya daga bayan ta sanin cewa basu da ikon tafiya su bar wajen har sai idan ita tayi musu umarni koh kuwa sun ga tafiyar ta .

Bangaren sojojin su ma suna ƙarƙashin umarnin ubangidan su ne wanda yake cikin ɓakar motar sumfurin ( purchase ) mai ɗauke da ɓakaken gilasai daga shi sai direban shi , ya shaƙa har iya wuya , a saboda haɗa hanyar sa da ta siyama , sosai yake jin zafin yarinyar shi da kan sa kuma ya rasa dalilin hakan kullum abun sake gaba yake ,

Sai da ya mula dan kan sa ya ɗago ya kalle ta yadda har ta fara haɗa gumi a ƙwaleliyar ranar damina ," yayiwa direban sa umarni da ya buɗe mata gidan gaba ,"

Cikin nutsuwa tayiwa kanta matsugunni a gaban motar tana me sauke ajiyar zucin wahalar tsayuwar da tayi , karaf suka haɗa ido ta mudubin gaban motar , da hanzari ta janye idon ta , dai-dai lokacin da direban ya tada motar ,sauran motocin suka bi bayan su ,

Suna gaf da barin gari ya cewa direban nasa ,"agades muka nufa ",  cikin cika umarnin ubangidan sa ya amsa gami da karya kan motar ya ɗauki hanyar da zata kai su ga hawa titin katsina ,zuwa zender ,sannan yankin agades ,"

Ɗas ! Kirjin ta ya buga ta maimaita kalmar ',Agades ' me kuma zasu je yi agades su da suka nufi niamey wannan wane irin bahaguwar tafiya ce mai kwan gaba kwan baya ,a maimakon ayi gaba an sake nausawa baya ,? Gimbiya maimouna ta garin agades ", sunan da yayi amsa kuwwa kenan cikin ƙwaƙwalwar ta ,

Tabbas yankin su maimouna suka nufa , hakan yana nufin biyamuradi wurin budurwar sa yake nufin zuwa tare da ita ,!

Tunanin ta ya katse lokacin da ta tsinkayi muryar sa yana yin waya " hello Princess ,
dan kyakkawan murmushi ta hango saman fuskar sa,"da ya bata tabbacin wata kalma aka furta masa me daɗi,"
"Gamu bisa hanya,'
", ameen sai mun iso je t'aime ",
.
  Ji tayi ran ta yana tuƙuƙi ,kwantar da kan ta tayi gami da lumshe idanun ta ranta cike taf da tunanin gamuwar su da gimbiya maimouna tana kuma saƙawa da warware yadda zata yi amfani da duk wata damar da zata iya zuwa mata wurin yaƙin neman ƙwato biyamuradi youssof daga wurin kowacce mace , kamar yadda tun farko ta tsara wannan tafiyar tata zuwa wurin 'ubbo' da nufin fara dasa harsashin ginin ta ... Toh fah!


# *vote*
# *comments*
# *share*
*THANKS*
[6/24, 9:59 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association


*MAFARI.......*
_( Hargitsin rayuwa_ )


*Umm'muaz*


8







Miƙa tayi bayan ta ya bada sautin "ƙaƙas" sakamakon zaman awanni baƙwai da tayi wanda zata iya cewa wannan ne karon ta na farko da tayi doguwar tafiya irin haka a mota ,"

Wara idanun ta tayi sosai tana bin jerin gwanon bayin da ba sai an mata bayani ba tasan bayun yankin masarautar agades ne ,"cikin ranta kuwa mamaki fal take na ganin irin didima tare da sarewar da ake busa masu ,"wanda ya bata tabbacin anyi shiri sosai domin taryar biyamuradi,  nan take taji wani malolon bacin rai ya tokare ta a maƙoshi .,

Bata fargar ba sai gani tayi bayun nan sun jagoranci biyamuradi zuwa ainahin cikin ginin masarautar wasu ta baya wasu ta gefe da gefen sa ," yayin da sojojin sa suka dakata daga inda suke ,"

Ganin haka ya sa cikin sassarfa ta soma taku tana bin bayan su da har suka riga suka danna kan su cikin shigifofin gidan  ,"cikin ranta kuwa tarin nadama tare da bakin cikin biyo biyamuradi take ,"wanda duk da sanin cewa da tayi basa shiri amma bata zaci kiyayyar sa da walakancin sa sun kai har haka ba a gare ta , duba da cewa tun da suka ɗauko hanyar tafiyar awanni bakwai koh kalmar sannu bata sake haɗa su ba ,"sai ita da  take ta faman satar kallon sa haɗi da sauraron amon muryar sa ,"

Basu yi wata tafiya mai nisa ba a faffaɗan filin da yake mazaunin harabar gidan sarautar wanda yake rairayi ne tas-tas lallausa ,da ya ɗauki yanayin damina da sanyin la'asar yake bada wani irin sanyin ni'ima da kamshin ƙasa mai sanya nishaɗi a zukata .,

Amon sautin muryar biyamuradi taji ,"wanda ba ta kai ga fahimtar abun da yake faɗi ba , sai dai ta fahimci umarni ne ya basu ganin wasu tsiraru daga cikin su sun juyo gami da ƙarasowa gaban ta da take da ɗan tazara da su ƙadan ,"

"Ranki shi daɗe yarima yai umarni da a sada baƙuwathei ga shigifar gimbiya "
Gyaɗa kai tayi yayin da dogarawan nan uku suka shige gaba ta juya ta bisu a baya tana waiwayar tawagar biyamuradi wanɗanda suka nausa shiyar gabas ba tare da ta samu arzikin da zata samu koh da kalma guda daga gwarzon nata ba ,"

Fiye da yadda tayi zato gini da tsarin masarautar agades ya tafi da hankalin ta tare da burgeta sosai da sosai ,"ware idanu tayi tana bin kowanne zane da taswirun da aka ƙawata bangon kowacce shigifa da ita ,da kallo mai bayyana shauƙi tare da burgewa ," kafafun ta da suke babu takalma tun a shigifar farko suna waɗakata cikin lallausan shimfiɗun alfarmar da suke ƙwance a kowacce shigifa,"

Cikin kowacce shigifar da zasu gifta bayu mata ne su huɗu suke zubewa gami da kai gaisuwa tare da tambayar inda suka nufa ,"amsa guda dogarawan suke badawa ."

    Wagga diya baƙuwace da suke tafe tare da yarima biyamuradi ,kuma wurin gimbiya aka biɗa da a sada ta ,"

Har zuwa ga shigifar da tafi kowacce tsaruwa inda daga nan dogarawan suka juya bayan sun damƙa ta a hannun wata baiwa wacce tayi mata umarnin zama akan ɗaya daga cikin shimfiɗun alfarmar dake wurin ,tare da sanar mata ta jira gimbiya na nan fitowa bayan almuru ,"

Cikin takaici take duban baiwar da ta miƙe bayan kammala bayanin ta ,"

   "Tou ki sada ni da inda zan yi alwala na kimtsa domin ina da bukatar yin haka ,

Siyama ta furta hakan ba tare da ta kai duban ta ga baiwar ba domin zuwa lokacin ta fara shaƙar takaicin halin ko'in kula da rashin girmamawan da ta fara hango alamun su ga hadiman gidan wanda ta hakikance ba kowa ya jawo mata hakan ba illa biyamuradi da ya danganta ta da matsayin Baƙuwa a gareshi a maimakon ƙanwar sa ƴar uwa ," domin ta tabbatar da ace ya kiraye ta da matsayin ƙanwa agareshi da tabbas ya samar mata da girma tare da matsayi a idanun hadiman gidan .,

    Bayan idar da sallar ta "na magarib" tayi kimanin mintuna talatin tana zaune ,wanda har zuwa lokacin babu wacce ta sake bi ta kan ta cikin tarin bayun da suke ta kai kawo da manyan tire da tasoshi na alfarma a hannayen su waɗanda suke rufe ruf da mayafai iri guda masu launin ruwan sararin samaniya ", suna nufar wani sashi da ƙofar sa take rufe ta hannun dama ,

Cikin ta kuwa idan ban da ƙugin yunwa babu abun da yake ,"yayin da ita kuma ta sha alwashin baza ta sake tuntubar hadiman gidan kan wata bukata tata ba ," hasalima kishingiɗa tayi gami da lumshe fararen idanun ta ,gefe guda na zuciyar ta tana nazarin yadda lamuran suke tafiya .,

Wani sassanyan ƙamshin turare ne ya fara bugar hancin ta kafin taji tashin muryoyin hadiman da suke cikin shigifar suna kirari tare da ƙwarzanta uwargijiyar su ,"

Ta ɗauki kimanin mintuna biyu kafin ta buɗe idanun ta a hankali ,"fes suka sauka cikin manyan idanun kyakkyawar budurwa da take zaune cikin shiga ta alfarma akan wata shimfida da ita bata san lokacin da aka samar da ita ba ,"kallon - kallo suka yi na adadin wasu daƙiƙai kafin siyama ta mayar da nata fatar idanun ta lumshe zuciyar ta kuwa bugawa take ɗas,ɗas,ɗas ,

tabbas wannan ce gimbiya maimouna , babu shakka ta amsa sunan ta ,' ganin ta kuma ya zo dai-dai da jin labarin ta ," sai dai koh kusa bata ji ta karaya ba bata ji ta tsorata ba ,sam ƙwarjinin ta bai ɗimautata ba ," hakan ya sa ta cigaba da lumshe idanun ta tamkar mai bacci wanda babu wanda ya lura da buɗesu da tayi ta rufe sai ita gimbiya maimouna wacce hasken lantarkin da yake tarwai ya bata damar hango cikin ƙwarar idanun siyama wacce bata kai ga sanin wacece ba hasalima bata san da zuwan ta ba ,"

  Gnala wagga ɗiya daga ina ta tahou ?
   Wacece ita ? Gimbiya maimouna ta furta hakan tana mai kai duba ga inda siyama take kishingiɗe

Cikin girmamawa wacce aka kira da "gnala" ta amsa

      "afuwa take biɗa , wagga ɗiya baƙuwa ce da suke tafe tare da mai girma yariman maraɗi tun da yammaci ta samu isowa nan ƙarƙashin rakiƴar dogarai su sunka isar da sakon wanzuwar ta anan daga bakin yarima ,"

Mayar da duban ta ta sake yi ga kyakyawar hausa/fulanin fuskar siyama ," nan take ta hango yanayin kamannin masoyin ta akan fuskar siyamar da take da tabbacin ba bacci take ba ,"ginshiri ne kawai tare da ƙasaita wanda ta danganta hakan ga kasancewar ita ma siyamar ɗiyan sarki ce kamar yadda tayi zato ,"siyamar ƙanwar youssouf ce wacce bata kai ga sanin ta ba , domin duk cikin tarin ƙannen sa da ta hakiƙance yana da su bai taɓa yi mata zancen kowa ba sai na "Aisha merama" ta kuma tabbatar ba ita bace wannan domin ya sha gwada mata hoton meramar maraɗi ,"

Nan take ta hango kuskuren da hadiman ta suka aykata na barin gimbiyar maraɗi bisa wannan shimfiɗar da bata kai ba a wurin ta .

Gyaran murya tayi cikin yaren su na azbinawa tace ,"

    Gnala a samarwa gimbiyar maraɗi kyakyawar shimfiɗa a wadata ta da abin sha da na ci haɗi da bigire mai kyau domin tayi wanka ta sauya kaya ta huta kafin mu gaisa ,wagga ɗiya gimbiyar maraɗi ce , kar a sake ayi wani abu na rashin ɗa'a da zai taɓa martabar mu har zuwa tafiyar ta ,ɗiyar girma ce maza a girmamata,"

Duk da cewar siyama bata jin yaren su na azbinawa amma ta fahimci zancen ta aka yi jin an ambaci "maraɗi " 

Tunanin ta ya katse lokacin da taji hadima ngala wacce ga alamu ita ce shugabar bayin gimbiya maimouna," duba da cewa tun da gimbiyar ta fito duk sauran bayin suka kai gaisuwa tare da ficewa daga shigifar sai ita ta rage",  ta ɗurkusa tana ahuwa cikin girmamawa take neman iznin ta jagorance ta zuwa wata shigifar ,"

Ware ido tayi tana me sake tsuƙe fuska ta gƴaɗa kai ," abun mamaki kunnuwan ta sai suka tsinkayo mata ngala na mata ƙirari "ɗan murmushin gefen baki tayi tana mai bin bayan ta  ,"

Cak ta tsaya sakamakon sallamar sa da ta tsinta cikin amon muryar sa mai samar mata da kasala ,"

Waiwayowa tayi suka dubi juna ido cikin ido ,"dai-dai lokacin da gimbiya maimouna ta miƙe tana mai nufar sa cikin takun ta ," fuskar ta ɗauke da tattausan murmushin da duk cikin maza shi yayi zarrar samun irin sa ,"

Juyawa tayi cikin sauri ,kafin idanun ta su hango mata irin tarɓar da zasu yi wa juna wanda zai haifar mata da damuwar da zata hana ta bacci ,"

Cikin nutsuwa ta sauya kayan ta zuwa na barci bayan taci abinci ta getse ta sake yin wani wankan duk cikin ƙarƙashin kulawar gnala da take hidima da ita cikin girmamawa hatta ruwan wanka da kayan baccin ita ta haɗo mata ," yayin da a halin yanzu take kishingiɗe kan makeken gaɗon kwatankwacin nata sai dai wannan ya fi shi girma , gnala tana daga ƙasa ta miƙe bisa guiwarta tana tausa mata kafafu ,"

Tare da nazari take kallon ta tana son samo bakin zaren ta inda zata fara yi mata maganar da take son yi wato yi mata tambayoyi akan uwargijiyar ta ," sai dai kuma tana shakka akan koh zata samu haɗin kan gnala ɗin ,"

A hankali ta murɗa kofar ɗakin gami da shigowa ƙarƙashin rakiyar sassanyan kamshin ta mai shiga zuci ,cikin sabuwar shiga mai banbanci da ta ɗazu domin a halin yanzu sanye take da doguwar rigar siliki ruwan zaiba da duwatsun jiki suke ta faman ɗaukar ido ,miƙaƙƙen gashin ta ya zubo har gadon bayan ta yayin da madaidaiciyar fuskar ta mai ɗauke da manyan fararen idanu ta faɗaɗa da lallausan murmushi ,"

Sallama tayi musu tare da zama bisa gefen gadon da siyama take a zaune bisa a halin yanzu ," maida duban ta tayi ga gnala ,"

          daɗa a bamu wuri mu zanta tare da ƙauna ta ,"

       Toh ranki shi ɗaɗe ku tashi lafiya ɗiyan saraki ,

Barka da zuwa ƙauna ta siyama kin iso lafiya ? Yaya umma da fatan kun baro kowa lafiya kun iske mu lafiya ?

Cikin murmushi siyama take amsa mata kafin daga bisani hira ta fara gudana cikin taka tsantsan daga kowaccen su ," domin ita ma gimbiya maimouna koh da ta tambayi biyamuradi youssouf wacece wacce suke tare ya tabbatar mata ƙanwar sa ce kuma sunan ta siyama ,sannan ita ma niamey ta nufa shiyasa tafiyar su ta zo guda ,"

Daga haka bai wani bata fuskar da zata sake zouwa mar da batun siyaman ba ," yayin da ita kuma hankalin ta yafi karkata ga batun tafiyar sa da yayi ta faman rarrashin ta da kyar ta amince suka rabu cikin aminci tare da alkawarin kasancewa akan wayar tafi da gidan ka a har kullum ,"

     Ƙauna ta daga shigowar ki cikin garin mu zuwa saduwar ki da masarautar mu menene yafi burge ki yafi baki sha'awa ?

   Ɗan jimm siyama tayi tana nazari "ga dama ta samu ," murmushi tayi tsarin ginin masarautar ku sosai ya burgeni , sannan na biyu girke-girken ku na gargajiya sun ƙawatar da ni kuma sun min daɗin ɗanɗano wanda har zan so na dunga samun irin girkin lokaci zuwa lokaci

     Murmushi maimouna tayi jin siyamar ta yabi masarautar su ,idan kuwa haka ne zan baki baiwa ƙwararriya ɗaya daga cikin masu min girki ki tafi da ita zuwa duk inda zaki ta dunga yi miki irin girkin mu a duk lokacin da kika biɗa ,"

Cikin farin cikin ganin tarkon da ta ɗana yayi kamuwa kuma zuwan ta yayi alfanu domin zata tafi da wani bangare na kusa da gimbiya maimouna tayi mata godiya tare da yabawa akan karamcin da tayi mata ,"

Tare da nishaɗi gimbiya maimouna ta amsa tana mai jin daɗin zuwan siyamar domin ta daɗe tana son ta samu dama irin haka da zata tura wani na kurkusa da ita zuwa maraɗi "saboda wani boyayyan dalili nata ",  tunani ta fara yi cikin amintattun bayun ta wa zata tura ?

      *GNALA*

   Hasken alfijir ya fara haskowa ta tsakanin labulen tagar ɗakin nata ,tana zaune daga bakin wata doguwar kujera jal da take ɗakin nata da ta sha shimfiɗun alfarma , gefe daga ƙasa baiwar ta ce ngala

       "zaki tahi zuowa maraɗi a matsayin kyautatciyar baiwa da na ba da ki ga ɗiyan sarkin maraɗi siyama ,"zaki tahi a matsayin mai yi mata girke girken gargajiya irin namu ," zaki yi duk wani kokari ganin kin samu mazauni mai kyau wurin sabuwar uwargijiƴar ki ,"ta yadda zata sau miki jiki ki samu shiga cikin lamuran ta wanda ta haka zamu san lamuran da suke gudana baki ɗaya a cikin gidan tun kafin wanzuwa ta ,"wanda hakan shi zai sa naji

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login