Showing 9001 words to 12000 words out of 411050 words
Chapter 4 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ta da wani al'amari mai girma irin wada bata taɓa jin sa akan sauran ƴaƴan ta ba"cikin nutsuwa ta ɗaga shi dai-dai fuskar ta gami da sumbatar goshin sa , da kuncin sa dama da hagu,
Dai-Dai lokacin da yarima Abdoul azizu ya karaso ɗakin , farin cikin zuciyar sa ya kasa boyuwa daga zuci har zahiri bakin sa ya gaza daina furta kalmomin godiya ga ubangijin sa , ba tare da lura da wurin da suke ba ya haɗa su baki ɗaya ya rungume su , zuciyar sa tana buɗewa tare da sabuwar ƙaunar uwar da ɗan ta ,
Biki sosai aka dunga yi tare da yanke-yanke ana sadaka domin nuna farin cikin wannan haihuwar , har zuwa ranar da takasance ranar raɗin suna , ɗaruruwan mutane suka hallarci wurin bikin raɗin sunan inda yaro yaci sunan "mai martaba "Youssoufa"
A nan wurin kuma mai martaba ya Sa aka yi shela akan bai amince ba a boyewa yaro sunan sa "laƙani " a kira yaro da sunan sa Yarima Youssoufa Abdoul-Azizou Baskore Sunan sa kenan .'''
Bayyana irin bacin rai da bakin cikin da hajiya uwa da saratu su ka shiga bai kwatantuwa "domin a ranar da labarin haihuwar ya iso musu kwana suka yi basu yi bacci ba suna jimami da taya junan su bakin ciki " Amma da yake dukkanin su sun ƙware a harkar kissa da kilbibi , sai suka shafe , hajiya uwa tayi ruwa tayi tsaki akan harkar mai jego da jaririn ta , tayi ƙabe ƙabe akan harkar kome , "ta nuna jika dai nasu ne "
Haka ita ma saratu take wuni a sashin safiyyah tana taya ta raino "a cewar ta " sosai ta sake a cikin jama'a ana ta hidima da ita "yayin da take nunawa mijin ta da ma ita safiyyar cewa youssoufa ita ma ɗan ta ne " (cikin rashin sanin su saratu da hajiya uwa suna nan ƙudurce da mummunan ƙudirin su da su kadai suka barwa kan su sanin sa , Sai kuma Allah wanda yake masanin kowa da kome )
kwance tashi youssoufa yana girma har zuwa lokacin da ya cika shekaru biyu a lokacin ne babban rashi ya samu birnin maraɗi , in da mai martaba sarkin youssoufa ya amsa kiran mahaliccin sa bayan ƴar gajeruwar jinya ,
haka aka gudanar da zaman makoki cikin alhinin rashin wannan adalin sarki nasu , bayan an share makoki akayi bikin naɗi inda "Yarima Abdoul azizou ya ɗare kujerar mulki "ya zama sarki " a kuma tsukin kwanakin Saratu ta sake haihuwa inda ta sake samun ɗiyar ta mace "wacce taci sunan mahaifiyar ta Maryam" bayan watanni biyu safiyyah ita ma ta ƙara haihuwar ɗan ta namiji ,"da aka sanya masa sunan lamiɗo "
Lokacin da Biyamaradi youssoufa ya cika shekaru biyar da watanni a lokacin ne wani babban rashin ya sake samuwa , Allah ya yiwa zainab kanwar mai martaba rasuwa a wurin haihuwa , ta mutu ta bar ƴar jaririyar ta da ta haifa wacce koh samun damar ganin fuskar ta bata yi ba mai rabawa ta raba " bayan share zaman makoki An samu saɓanin ra'ayi akan wacce zata yi rikon jaririyar zainab da ta ci sunan kakar ta ta wurin uba "siyama " A karshe an tsaida shawarar "safiyyah ita zata yi rikon siyama tare da jaririn ta da ta haifa kwanaki arba'in da suka wuce "Aminu " a dalilin sanin da kowa yayi cewar akwai aminci tare da ƙauna mai karfi a tsakanim marigayiya zainab da kuma safiyyah " domin tun ranar da akayi rasuwar ma jaririyar take karkashin kulawar safiyyah ita take kula da ita ,"take shayar da ita maɗarar da aka tanada domin jarirai sabuwar haihuwa "
Dan haka aka miƙa rikon siyama ga safiyyah tare da mayar mata da ƴar ta hannun ta zainab karama "ubbo" wacce a lokacin take da shekaru bakwai tana aji biyu na primary amma sosai ta shaƙu da uwar goyon ta , babar ta ,kuma takwarar ta marigayiya zainab a saboda rikon gaskiya soyayyah da amana da tayi mata " hakan ya sa ta ɗauki son duniya ta ɗora akan wannan jaririyar da take yi wa kallon ƙaramar kanwar ta take kuma son ta fiye da kannen ta da suka fito ciki guda "
Cike da ƙauna da tsaftataciyar soƴayyah safiyyah ta karbi riƙon siyama "gefe guda na zuciyar ta kuma ɗauke da wani babban burin da take fatan kasancewar sa , wanda ta riga ta ayyana shi akan jaririyar da aka bata amanar ta "
Bayan maryam ita ma saratu ta sake haihuwar ɗiyar ta mace "da ta amsa sunan hauwa"u " , kuma ita ce aka yi goyon su tare da su siyama da aminu "
Zuwa lokacin saratu kakaf ta gama bin gidajen bokaye da ƴan bori akan su taimaka mata ta samu haihuwar ɗa namiji "wanda ita ma zata ɗaga tace wannan ɗan ta ne namiji amma shiru ake ji "wai malam ya ci shirwa " akan cikin 'hauwa'u babu irin tsubbace tsubbacen da basu yi ba ita da hajiya uwa wacce har zuwa lokacin bata saduda ba .
A gefe ɗaya suna nan suna shirin kaddamar da mummunan aikinsu ,
kwanci tashi yara suna girma Arzikin iyayen su yana sake bunƙasa ,cigaba da wayewa yana sake yawaita , sauye-sauye suna samuwa , yanayi yana juyawa ,
*2005*
yanayin ya juya ta inda ya mayar da kananun yaran nan wasu matan aure wasu kuma samari " inda ƴaƴan sarki Abdoul azezou Baskore suka cika su Goma sha biyar cif-cif , siyama da ita ma take amsa sunan ɗiyar gidan ta cikace su suka zama su goma sha shiddah cif cif "safiyyah tana da takwas ,Huɗu maza huɗu mata "Saratu tana da bakwai shiddah mata ɗaya namiji ' , An rufe haihuwar da ɗiya mace kamar yadda aka buɗe ta da diya macen ,"
Biyamaradi yousoufa tun tasowar sa mutum ne miskilin gaske marar son hayaniya "yana da tsananin tausayi ko ma ace rauni akan mata da yara kanana " , baya shiga harkar kowa a gidan babu me ganin fara'ar sa idan aka ɗauke iyayen sa , sai kuma abokin sa , kuma Aminin sa Tafeedah da ya kasance ɗan uwan sa domin da mai martaba da mahaifin tafeedah da yakasance me riƙe da sarautar ɗan malikin maraɗi , ƴa ƴan wa da kani ne uwa ɗaya uba ɗaya .
Tun tashin su tare suka tashi tamkar ƴan tagwaye ance sai hali ya zo ɗaya ake abota toh abotar Biyamaradi yousoufa da tafeedah ta ƙaryarta hakan domin idan aka ɗauke ra'ayin su da yazo ɗaya akan karatu da aikin da suka yi haɗakar ra'ayi akan sa ,"watau aikin ɗamara " da ya kasance su dukkanin su sojoji ne sai dai shi tafeedah sojan sama ne , saɓanin yarima yousoufa da yake sojan ƙasa .
Bayan hakan kowannen su halayen sa saɓani da na ɗan uwan sa ne , inda Tafeedah ya kasance mutum me barkwanci , surutu da saukin kai, saɓanin yarima yousoufa , hakan ya sa suke yawan samun saɓani akan halayyar juna in da kowannen su yake ƙalubalantar ɗan uwan sa , a ganin yousoufa tafeedah ya cika sakarci da sakewa mutane , yayin da shi kuma tafeedah yake ganin yousoufa a matsayin bauɗaɗɗen mutum miskili marar dadin sha'ani ,
A tsakanin su ɗaya ya kasa sauyawa ɗaya halayyar sa kamar yadda saɓanin halayyar su sam-sam bata taɓa karfin aminci da abotar su ba ,tun suna yaran su har yanzu da suke kan shekarun girma ,basu da abokan da su ka wuce junan su , duk wasu shawarwarin su tare suke yi , sun san sirrin junan su daɗi da rashin daɗi basa rabuwa duk inda dare yayi idan har suna cikin gari ɗaya ,"aiki bai tura ɗayan su wata jahar koh wata ƙasar ba "toh dare yana yi ka gansu tare koh dai a sashin biyamaradi yousoufa koh kuwa a sashin tafeedah da shima yake bangare guda a gidan su da yake baya kaɗan daga shiyar gidan sarki " sosai abotar su me tsafta ce irin wacce take wuyar samu a wannan zamani "
Bayan Tafeedah babu wanda Biyamaradi yousoufa yake so da ƙaunar gani irin karamar kanwar su A'isha wacce ake kira "meram" kasancewar ta (meramar sarki) .
ƙwarai Biyamaradi yousoufa yake kaunar meram duk da cewa kanwar sa ce da suke uba ɗaya , domin meram ita ce ƙaramar ɗiya ga hajiya mama ( Saratu ) a cikin ƴaƴan gidan mata ita ce karama , A'isha"meram" yarinya ce ƴar kimanin shekaru sha uku a yanzu tana aji na uku a makarantar gaba da primary .
Aisha irin yaran nan ne da gatan da suke da shi bai sa sun lalace da rashin tarbiyyah ba , ta samu tarbiyya sosai a wurin uwar goyon ta "Safiyyah" uwa ga Biyamaradi yousoufa , hajiya umma "kamar yadda ƴaƴan ta suke kiran ta" ita ta ɗauki Aisha tun daga yaye wanda hakan yana da nasaba da ƙaunar da ta ga ɗan ta mafi soyuwa agare ta yana yi wa kanwar ta sa da tun daga lokacin da aka haife ta ya ƙyalla ido ya ganta ,Allah ya dasa masa kaunar ta ciki ran sa fiye da duk sauran ƴan uwan sa ciki har da waɗan da suke ciki ɗaya da shi da su .
Lokacin yana matakin farko a jami'ah ai kuwa ya mayar da sashin mama wurin yada zangon sa a duk lokacin da ya dawo daga ɗaukar darasi haka zai kwace aisha daga hannun masu rainon ta yayi ta faman hidima da ita, hakan sam baya yi wa hajiya umma daɗi ganin yadda ɗan ta ya tare a sashin da a da kafin haihuwar aisha sai yayi shekara ma bai taka kafar sa bakin sashin ba " hankalin ta ya tashi akan sanin da tayi cewa garin su baya jiƙuwa a ƙoƙo ɗaya tare da saratu"hajiya mama "
Baza ta iya hana yousoufa zuwa sashin hajiya mama kai tsaye ba kasancewar ta san shi kaifi ɗaya ne ,miskilin gaske da ba'a iya sauya masa ra'ayi ta daɗi , hakan ya sa ta bi hanyoyin da take ganin zasu taimaka mata ta dakatar da ɗan ta daga shiga sashin hajiya mama domin tana gudun ta janye mata ɗa tsaf "sanin halayyar saratu "(hajiya mama) " da tayi na tsantsar kissa da siyasa tare da hilatar mutum ya so ta a dole karshe kuma ta cuce sa "macijin sari ka noƙe ce " ( cikin rashin sanin hajiya umma aikin gama ya riga ya jima da gamawa )
Dan haka tayi mata shigar sauri ta bi duk hanyoyin da take da damar bi ya haɗu kuma da ita ke jaan ragamar gidan ta ɗauke Aisha can-cak daga wurin mahaifiyar ta a lokacin tana shekaru biyu a duniya ta dawo sashin ta baki ɗaya , ai kuwa murna gurin yousoufa ba'a cewa kome " yayin da hakan da tayi ya baƙan ta ran hajiya mama sosai amma sai ta boye bacin ran ta. (sanin da tayi ta riga ta gama rarake ƙasan hajiya mama )
Cigaban labari .
Yana shiga tamfatsetsen (palourde-parlour )falon nasa ko kafin ya karasa zama akan ɗaya daga cikin kyawawan fararen kujerun da suka sake haskaka falon wayar sa da take cikin aljihun sa ta hau ruri .
Ciro wayar yayi daga cikin aljihunn sa tare da tsira mata ido tamkar me nazarin ta ,har sai da ta kusan tsinkewa tukun ya ɗaga gami da yin sallama ya ɗora da faɗin "Comment vas-tu aujourd'hui princesse"?
Daga dayan bangaren aka amsa cikin wata narkakkiyar murya " je vais bien Mon amour comment va le travail"?
Ya amsa da Alhamdulillah daga haka suka ci gaba da hirar da ake yin ta cike taf da kasaita daga dukkanin bangarorin biyu da shi da wacce ga alamu budurwar sa ce .
Idan ɗaya ya furta kalma sai an biyo bayan wasu ƴan ƙananun daƙikai (seconde -seconds) kafin " ɗayan ya bada amsa , inda daga baya ma ya koma budurwar ita ke jaan ragamar hirar, shi daga yayi murmushi sai yace eh ko a ah.
Har dai zuwa lokacin da ya sako mata zancen tafiyar sa akan aikin sa har na tsawon lokacin da yake zaton zai iya kaiwa shekara .
Nan take ta katse shi tun ma kafin ya karasa yi mata bayani cikin tashin hankali take tambayar sa akan ina lamarin bikin auren su ya kwana ? Wanda ake sa ran zuwan ranar da aka yanke nan da ƴan wasu watannin da suke gaza da uku "lokacin da zata kammala karatun ta" ?
Cikin jin haushin tarar numfashin sa da tayi wanda yake ganin kaf duniya yana iya kirga mutanen da suka isa yi masa haka ,yace ke dakata MAIMOUNA lamarin ayki matsayin shi ya wouce douk yadda kike tounani don haka ki ajiye komi a guefe har sai bayan na cimma matsaya bisa aykina.
Ko kafin ya gama bayani budurwar da aka kira da maimouna ta fara shishiƙar kuka gama bayanin sa yazo daidai da fashewa da kukan ta bata ko kuma saurarar sa ba ta kashe wayar ta ,
Ta barshi riƙe da kan waya a kunne , ɗan jim yayi yana son fahimtar abun da ya sanya ta kuka cikin kalmomin da ya furta ,?
Rashin gano dalilin ya sa shi ɗaga kafaɗun sa biyu cikin nuna alamar rashin damuwa ya miƙe tare da nufar daya daga cikin fankama-fankaman ɗakunan da suke cikin falon nasa yana shiga ɗaki ya nufi ƙaton window ɗakin gami da buɗe sa a take ƙamshi damina da wata sassayan iskar maraice da ta fi ta ac da yake ɗakin dadi ,ni'ima da sanya nishaɗi ta buso zuwa cikin dakin .
Rage kayan jikin sa yayi tare da nufar bayi da alamun wanka yake da niyyar yi ,sai dai wayar sa da ya ajiye gefen gado ta ɗan jaa hankalin sa sakamakon hasken da tayi ,ɗan guntun murmushi yayi ganin sunan princesse da alamar sako a fuskar wayar ,ba tare da ya ɗau wayar ba ya faɗa bayi domin yin wanka.
Yana kammala shirin sa ya fito falo jikin sa sanye da uniforme riga da wondo me dabbare-dabbaren kore , ruwan kunkumadi, ruwan madara, da kuma jaa Wanda ko ba'a faɗi ba za'a san kakin soja ne .( Tenue Saharienne ).
Da sallama ɗauke akan harcen sa ya sanya kai cikin katafaren Palourdes (falon) mahaifiyar sa wanda yake kama da ɗakin taro "hall" dakatawa yayi daga gefe ya sunkuya tare da kwance igiyoyin jikin takalman sa da suke ɗaure gam-gam da kafar sa har kusan ƙwarin sa ,
Wucewa yayi niyyar yi (zuwa ciki wurin umma ) bayan ya amsa gaisuwar jakadiya wacce ya tarar tana zaune daga gefe a cikin palourn amma sai jakadiyar ta dakatar shi cikin cewa "Ranka ya dade biyamaradi " yanzu kuwa nake shirin zuwa sashin naka "ta furta hakan tana me satar kallon bayu uku da suke ta faman goge-goge da ƙwal-ƙwale cikin palourn daga can geufe ( umartar su tayi da su kauce su basu wuri ).
Gyara tsayuwar sa yayi bayan ya kammala sauraron bayanin bakin jakadiyar , sannan ba tare da ya nuna wata alama! Akan fuskar sa ba ya ce "madallah da ke jakadiyar sarki zan kuma yi taka tsan-tsan tare da sanya ido sosai domin gano gaskiyar wannan zancen da kika zo min da shi , "bayyanuwar wani abu wanda ya sha banban da wanda kika sanar da ni a yanzu " zai iƴa jawo hukunci me tsanani a gare ki dai-dai da yadda doka da shari'a ta tanadar ga masu yin ƙage da sharri , wanda kin riga kin san haka .
Daga haka ya juya ya fara tattaki domin nufar wurin mahaifiyar sa "cikin zuciyar sa kuwa cike taf da bakin ciki da baci rai ! Akan labarin da jakadiya ta zo masa da shi game da ɗan uwan sa muhamadou .'mamman"
Muhamadou shine ɗa na huɗu a ɗakin hajiya mama "kuma shine ɗan ta ɗaya tal namiji .
******************
Dai-Dai ya sanya kan shi cikin ɗan madaidaicin wurin "da yafi kama da dakin hutawa " ita ma ta kawo kai kiris ya rage su ci gware cikin sauri ta ɗago kai da niyyar buɗe baki amma ganin wanda yake tsaye a gaban ta ya sanya a take ta diririce "tare da yin ƙasa da sauri ta kai gwiwowin ta ƙasa cikin ƴar siririyar murya tace "ina kwana hamma youssouf " , kallon ta yayi na daƙikan da suke gaza da biyar ya ɗauke kansa tare da sake yin kicin-kicin da fuska daga bisani ya wuce yana me amsawa ciki-ciki da lafiya lau " bayan sa ta bi da sassayan kallo daga bisani ta miƙe daga durƙusan da tayi tana me kakkabe gefe da gefen fara sol ɗin rigar da take ɗore bisa kan kayan ta , gyara zaman farin gilashin idanun ta tayi " da saboda firgitar da tayi kiris ya rage ya subuto daga kan siririn karan hancin ta ",
Cikin sassarfar yake taku fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi da yake bayyana ƙatuwar wushiryar da take tsakanin fararen hakoran sa na sama" har ya ƙarasa gefen dardumar da farar dattijuwar take zaune hannun ta riƙe da wani ɗan ƙaramin littafin addini tana dubawa "zama yayi tare da miƙa hannun sa ya kamo nata hannayen da suke ciƙe da awarwarayen zinare da suke ta faman haske idanun me kallon su , ɗaga hannuwan nata yayi dai-dai fuskar sa ya sumbancin bayan hannuwan nata ɗaya-bayan-daya kafin ya sarƙafe dogayen ƴan ƴatsun sa cikin nata yatsun da suke ƙawace da adon jaan ɓakin lalle da yake ta faman sheƙi tare da tashin sassanyan kamshi "
Fuskar ta ɗauke da tattausan murmushi take bin duk wani motsin sa da ƙwarar idanun ta zuciyar ta fal! Cike da ƙaunar gudan jinin zuciyar ta
"ina kwana ummana kin tashi lafiya ? Yaya fama da jama" ? Allah ya ƙara miki nisan kwana da hakuri da mu umma " cikin murmushi take shafar baƙar kwantatciyar sumar kan sa tana me amsa addu'ar sa da Ameen kafin ta ɗora da tambayar lafiyar sa shima sannan ta ƙara da tambayar sa yayi karin kumallo ? Ƴar dariya yayi sannan "yace umma na makara sai naje officie zan sha café "