Showing 219001 words to 222000 words out of 411050 words
Chapter 74 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
da wannan , dan haka sai ya jiyo baki ɗayan sa yana fuskantar ta bayan ya fizge jikin sa ,
Hasken walkiya da na fitilun gefen hanya sun gaza wajen fiddo masa da ainahin kamannin fuskar ta da take rufe da niƙabi illa idanun ta da suka jirkita da zallar tsoro , da ya gaza jurar kallon su .
A hankali ya janye ganin sa daga kan ta ya dubi gefen titi inda ta ɓullo , ko alamun karnai babu , dan haka ya juya da sassarfa yana nufar ƙofar motar sa , cikin ran sa yana aiyanawa wannan wani sabon salo ne na matan banza .
Ki koma gida dare yayi .
Yace da ita .
Halin ruɗanin da take ciki bai isa jirkita mata tunanin da zai sa ta gaza gane shi ba , zuban ruwan sama akan kamilallar fuskar sa ba zai taimaka ba wajen hana ta shaida kamannin sa duk kuwa da rabuwa da yin tozali da tayi da shi na tsawon wasu shekaru , shi ɗin ne dai mutumin da Allah yake kawo mata shi a duk lokacin da take tsaka da neman agaji me girma a cikin rayuwarta ,
Wani irin yanayi ta tsinci kan ta a ciki me nawi , da ya sanya ta sauƙe ganin ta ƙasa ,
A hankali ya tada motar sa ya gifta ta tana me cigaba da tsayuwa a wajen ruwan sama na sauƙa kan ta cikin yanayi na rashin madafa ,
Tsaki yayi a karo na biyu lokacin da yake sake kai ganin sa jikin ɗan madubin saman motar sa yana hango ta , cikin nutsuwa ya murɗa kan motar sa ya taka ta yayi baya tare da dawowa inda ya bar ta ,
Shigo na kai ki gida .
yace ga ita ba tare da ya dubi sashin da take tsaye ba .
A hankali ta buɗe gidan baya na motar ta shiga ta rufe ƙofar tare da takurewa da jikin murfin motar tayi ƙasa da idanunta , wata irin kunya da nawin sa take ji ., girman laifin ta ninƙaya yake cikin tunanin ta yana ƙara girmama a idanun ta , zuciyar ta na raɗa mata ai ita ɗin bata cancanta da sake samun wani taimako kome ƙanƙantar sa daga gare sa ba .
ko motsi ta gaza yi , gani take cikin duk wani motsi da zata yi zai iya gane ta , zai fahimci ko ita wacece , da zuwa yanzu ta tabbatar bai shaida ta ba .
me zai faru idan ya gane ta ? Wataƙila ya wurgata kan titi .
Tana son tace wani abu ko da kalmomi biyu ne ,
ina Falmata ? A wanne hali take ciki ?
A sama ta tsinkayi muryar sa ,
Wacce unguwa kike
Muryar ta a dushe ƙasan maƙoshin ta ta sanar da shi ,
Babu wanda ya sake magana a tsakanin su har zuwa lokacin da suka kawo unguwar , ƙofar gidan malama maryam ta nemi ya dakata zata sauƙa , baice ƙala ba ya tsayar da motar ,
Na-nagode
ta furta tana barin motar kai tsaye ta isa jikin ƙofar gidan malama maryam ta shiga ƙwanƙwasawa sannu kan hankali .
Jaan motar sa yayi yana barin unguwar lokacin da zuciyar sa ke nace masa wajen son bijiro masa da tunanin waccen tana haɗa su da yanayin wannan , amma bai bari tunanin yayi tasiri ba ya kunna karatun Al'qur'ani yana cigaba da saurara .
bai son tuno wani abu da ya shafe ta , ita ɗin ai bata cancanta da kutsowa cikin tunanin sa ba ko kaɗan .
A hankali ta zame ta zauna a jikin ƙofar bayan shuɗewar ƙugin tayoyin motar sa bisa kan kwalta, ruwan saman na cigaba da sauƙa a jikin ta , kukan da take riƙewa tun shigarta motar ta saki da ƙarfi , kukan ha'incin da samy baby ta yi mata , kukan nadamar kuskuren da ta aikata a rayuwar ta, babu abunda take so a dai-dai lokacin irin ta buɗi ido ta ga falmata da mama a tare da ita , ta haƙiƙance sune kaɗai jinin ta a duniya sune baza su taɓa cutar da ita ba ,
Takurewa tayi a wajen tana karkarwar sanyin iskar ɗaukewar ruwan sama da yake busa ta .
Washegari
Samy baby tana tsakiyar baccin ta na tofon gira misalin ƙarfe goma na safe ta tsinkayo bugun ƙofar gidan ta tamkar a tsakiyar kan ta ,
Mummunan tsaki ta jaa , bayan ta miƙe tana haɗa maballan gaban rigar baccin ta , kan ta ko ɗan kwali babu ta fito , dai-dai lokacin da aka kaiwa ƙofar wani mugun bugu tamkar za'a ɓalla ta ,
Kai wai wanne ɗan^ yake ƙoƙarin ɓalla min kofa , tamkar na ci bashin sa ban biya ba ?
Ta furta hakan a tsawace tana ƙoƙarin zare sakatar ƙofar , bata gama zarewa ba ta ji anyi ciki da ita da ƙofar , tayi baya taga-taga ƙiris ya rage ta faɗi ,
A fusace ta ɗago kan ta hannun ta dafe da goshin ta , da ƙofar ta buga
Kutumelesi ,....
Kar ki yadda ki zage ni tsohuwar ƴar damfara , kuɗaɗena na zo ki mayar min da su account , saboda ƙaramar ƴar iskar da kuka haɗa baki kuka damfare ni tun daren jiya ta gudu , dan haka ko naira ɗaya ban yadda a samu giɓin su ba a cikin kuɗina ki dawo min da su yanzu-yanzu .
Wani irin fargaba ne ya dirarwa Samy baby , me Kamal yake cewa ? Yakaka ta gudu ?
Da kƴar ta tattaro guntuwar nutsuwar ta ,
Ta juƴa ta fara taku tana cigaba da murza goshin ta ,
Kamal ka shigo muyi magana a ciki , zancen ba na tsaye bane ,
Ke duba Samira ba inda zan shiga kawai kuɗaɗen nan zaki dawo min da su domin ko hannun ta bata yadda na taɓa ba tayi tafiyar ta tun jiya , bayan wahalar neman ta da ta saka ni cikin ruwan sama ƴar^ ke daman kin san yarinyar nan wata gara ce irin haka har zaki karɓi kuɗina akan ta ? Yi sauri dallah ki dawo min da su , da akwai inda zan tafi daga nan bani da lokacin ɓatawa .
Kallon ba yadda zan yi Samy baby take bin Kamal da shi , ta fahimci a bugen sa yake tatil kamar koyaushe , idan har ta nemi yin gardama kan zancen kuɗin nan kome zai iya faruwa da ita ,
Bani account number
Ta ce masa tana shigewa ɗaki ɗauko wayar ta , daga ƙasan ran ta take jin mummunan ɓacin rai na taso mata akan abunda Yakaka tayi mata , ashe rashin mutumcin Yaks har ya kai haka ? Ta gudu ta jawo mata irin wannan babbar asara ? Allah ya so bata riga ta kacan-chala kuɗin nan ba da yanzu yaya zata yi da tijarar Kamal ? Tabɗi dole ne ta ɗau mataki akan Yaks , ta nuna mata kuskuren ta saboda gaba kar ta sake gwada mata irin wannan mugun wasan .
Cikin mintoci biyar Samy baby ta ɗibga asarar Naira miliyan biyun da suke mallakinta daga jiya zuwa yau , har gumi ne ke tsattsafo mata , lokacin da ta koma falo ta zauna bayan tafiyar Kamal da bai bar gidan ba sai da miliyan ɗin sa biyu ta koma account ɗin sa .
Ina Yakaka ta kwana ? Shine tambayar da Samy baby take yiwa kanta ,
Zumbur ! ta miƙe tsaye lokacin da ta ayyana inda Yakaka ta kwana , gidan Malama Maryam .
Ɗan siririn mayafinta da yake ajiye a falon shi ta ɗauka ta yafa akan rigar baccin jikin ta , ta fito a fusace bayan ta rufe ƙofar gidan da makulli ta zagaya layin bayan su kai tsaye ta doshi gidan malama Maryam da tunda take sau ɗaya ta taɓa taka gidan , Sai fa yau da zata kuma zuwa .
Ko sallama bata yi ba ta danna kai cikin gidan , ilai kuwa tana shiga falon ta tadda Yakaka tana zaune ta jingina da jikin ɗaya daga cikin kujerun falon da farantin cin abinci a gaban ta wanda bata kai ga sa hannun cikin sa ba .
Da shigowar ta Yakaka ta miƙe da alamun firgici a fuskar ta wacce ta ɗan kumbura kaɗan tayi jaa ,
Anty Samy ..
Da hannu ta dakatar da ita , ki min shiru Yaks , ashe baki da mutumci haka daman? Ƙyat ! tayi Kwafa ki wuce mu tafi gida inason yin magana da ke .
Malama Maryam wacce tashin muryar Samy baby ya sanyata fitowa daga cikin ɗakin ta , ta ƙaraso wajen tana bin Samy baby da kallon nazari
Yayar Yakaka lafiya dai ko ? Anan Yakaka ta kwana tun jiya cikin dare take ta kuka taƙi sanar da mu abunda ya sameta , dan Allah idan laifi tayi miki kiyi haƙuri ki yafe mata
Wani kallon banza Samy baby ta jefawa Malama Maryam saboda ta fara fahimtar duk wani taurin kai da take hango alamun Yakaka zata gwada mata har da taimakon koyarwar Malama Maryam wacce ta lura duk wasu sabbin ɗabi'un Yakaka daga gurin ta ta kwafe .
Ki wuce mu tafi
Ta sake maimaitawa tana mayar da duban ta kan Yakakar
Da wani irin yanayi cikin muryar Yakaka , wanda yake fallasa halin baƙin cikin da zuciyar ta ke ciki , tace
Bazan bi ki ba Anty Samira ni daga nan Maiduguri zan koma wajen Falmata da ƴa ta , bazan taɓa yadda nayi yadda kike so nayi ba . BAZAN SAKE YIN ZINA BA
Kif-kifta ido Samy baby tayi tamkar bata ji da kyau ba ,ta karkata kai tare da ɗage shi sama ta ce :
Kika ce me Yaks ?
Bata jira ta amsa mata ba ta ɗora da cewa .
Maiduguri ?? Sai ta kwashe da wata gajerar dariya ,
Wa kika sani a Maidugurin ? Waye naki a can wa kike da shi a duniya ?
Da sauri Yakaka ta amsa mata har muryar ta na sarƙewa
Ƙanwata Falmata da ƴata Mama !
Hahaha !
Yaks kenan ai Falmata da ƴar jaririyar da kika gudu kika bari duk sun riga sun mutu , au ashe ban faɗa miki ba ko ? Sorry lokacin kina tsaka da jarabawa ne kin san fa ke mayyar karatu ce ...
Kukan kurar da Yakaka tayi ta tura samy baby ta faɗa kan kujerar bayan ta , ta hau ɗare-ɗare kan ta , tare da maƙure mata wuya shi ya hana samy baby cigaba da zancen da ta shiryo shi a yanzu ,
Me na miki Anty Samira ? Me na miki ? Ƙarya kike min koyaushe Ƙarya kike min baki taɓa faɗa min gaskiya ba Ƙarya kike Falmata na bata mutu ba , Ƙarya kike yi bata mutu ba , ki faɗa min gaskiya me kike shiryawa game da rayuwata ? Me na miki ?
Da taimakon Malama Maryam suka ɗaga Yakaka daga kan Samy baby wacce duk Yakaka ta yakushewa wuya , gabaɗaya ta birkice musu kamar me tashin Aljanu , ihu kawai take tana cewa
Falmata bata mutu ba ƙarya ne ,
Addu'o'i Malama Maryam take tofa mata tana riƙe da ita ,
Bata cikin hankalinta ta ɗago kan ta hawaye wani na korar wani a fuskar ta ,
Ummi , ki kaini Maiduguri yanzu-yanzu dan Allah , ki kaini naga Falmata
Zan kai ki Yakaka ki nutsu ki daina wannan ihun babu kyau , kiyi innalillahi wa inna ilahi raji'oon , kiyi addu'a ki bar kukan nan haka .
Gƴaɗa kai take ba domin tana fahimtar kalmomin Malama Maryam ba , bakin ta ya gaza furta kalma guda illa karkarwa da laɓɓan ta ke yi , zuciyar ta ke wani irin bugu da tsananin tsoron da yake barazanar tarwatsa mata zuciya , kalmar Mutuwa ga Falmata tayi mata tsauri da girma ta yadda zuciyar ta gaza ɗauka , tunanin ta ya guntule cikin rashin sanin takamaimai a halin da take ciki , ƙiyayyar samy baby sabuwa fil take yaɗo cikin ran ta .
Da baya-da-baya Samy baby ta ƙarasa barin falon tana jin yadda tsoron halin da ta ga Yakaka a ciki na cika mata zuciya ,
Niamey Niger
Cikin makonni uku da ƴan kwanaki visa Falmata da Mama ta fito , Biyamuradi Youssouf bai jinkirta ba wajen fara shirye-shiryen tafiyar su , bayan ya ɗauki hutun sa na kwanaki talatin a wajen aikin sa , tare da gudurtawa cikin ran sa idan kwanakin sun gaza wajen yin abunda ya kai su , zai dawo ya rubuta takardar neman iznin hutu batare da biyansa albashi ba ya koma .
Cikin satin zuwan sa Maradi sau biyu , bayani sosai ya tsarawa Maimartaba tare da hajiya Umma kan cewa aiki ne zai kai shi zouwa ƙasar Amurka ,
Babu shakku cikin ran su suka masa addu'o'in samun nasara kan abunda za shi nema , tare da fatan dawowa lafiya .
Bangaren matan sa ma bai samu matsala da Siyama ba , wacce take da tsananin yarda ga mijinta , dan haka ta hau shirya masa ƴan kayan cimaka da zai iya yin guzurin su zuwa ƙasar da za shi , zuciyar ta cike taf da kewar sa da ta fara tundaga yanzu , lokaci-lokaci tana sharar ƙwalla rabuwa da masoyi duk da cewa ba sabon abu bane shafe kwanaki masu yawa irin haka basu tare , amma haka kawai taji wannan tafiyar tasa ta tsaya mata a zuci ko domin ƙasar zai bari bakiɗaya zuwa wata nahiyar ?
Ga Gimbiya Maimounatou kuwa sam bata gamsu ba da zancen barin sa ƙasar , hasalima batun tafiyar sa ya kawo mata tsaiko ne kan wani Al'amari da take ɗorarwa akan sa , sai take ganin tamkar da gayya ya tsiri tafiyar ,hakan ba kome bane face salo ne na kauda-bara da ya sha faruwa a duk lokacin da take kan gaɓa na son cimma ƙudirin ta , sai dai baza ta fasa ba , ba kuma zata gaza ba wajen cigaba da bibiyar kome a sannu har sai haƙar ta ta cimma ruwa .
Dan haka babu ƙarsashi a tare da ita suka yi bankwana bayan ta haɗa masa ƴan nata kayan cimakan da basu cika yawa ba saboda zuciyar ta da take shaƙare da takaici , duk da cewa tayi iyakar ƙoƙari kamar yadda ta saba ta boye abunda ke binne ƙarƙashin ran ta .
Daga Tafeeda kaɗai ya so samun tangarɗa wanda yake da sani sosai akan harkar aikin su , ya kuma titsiye Biyamuradin da tambayoyi akan aikin da yace zai kai shi US , sai dai ga mamakin sa hanya-hanya da zamiya iri-iri Biyamuradi ya dunga yi masa da ya hana shi sanin takamaimai gaskiyar lamari game da tafiyar ta shi ,
karshe dai ya fahimci babu shakka akwai abu me girma da Aminin sa ke ɓoye ma sa wanda kuma lalle wannan abun ya shafi rayuwar sa ta kurkusa , sai ya ɗiga ayar tambayar . Cikin ran sa ya ƙudurci bin diddigin kome .
Duk wani shirin tafiyar su ya kammala , kamar yadda Biyamuradi ya Alƙwarta ga Hajja , ya ƙira direban da zai kai ta ana washegarin ranar tafiyar su , ya sanar da shi gobe da safe ya zo su kama hanyar Nigeria da Hajja .
Jakar matafiya karama da Babba Ya kawo musu ,
Ya miƙa Babbar ga Hajja , yana cewa
Hajja ga wannan jakar ki shirya suturun ki ciki , wannan ƙaramar kouma na Fatima ne , kayan ta kaɗan zata ɗauka ba wasou masou yawa ba kawai aboubouwa masu muhimmanci da zata iya bouƙata su zata zouba a ciki, ita kouwa Mama ba sai an ɗauka mata wasu suturu ba , kaya biyu kawai sun isar mata idan munka kai can duk za'a saya wasu suturu sabouda yanayin mu da nasou ba ɗaya bane .
Au Babban soja wai da ni har mun shirya kayan a cikin manyan akwatuna ? Fiye da rabin kayan nasu ma ai mun loda su a akwatuna har huɗu , ashe tafiyar ba ta guzurin kaya bace ikon Allah .
Ɗan murmushi yayi , a ah hajja a ajiye waɗannan suturu a gida zamu sayi wasu a can .
To ai babu kome , huta-roro ( waken gizo ya ƙi 'Ya'ya ) wannan babu neman masu dakon kaya a tashar jirgin sama , oh duniya kullum cigaba ake watau ita turai ba'a zuwa da kayayyaki dayawa ? Dayake ma can gidan kaya ne , kamfaninnika ne da su na suturu sai ka zaɓa ka darje , kuma fa irin atamfofin nan namu arhar bulus ne da su a can ko Babban soja ?
Cikin gundura da hirar hajja , yace
hajja ai can basou sanya tufafi hakka irin namou , su suturun su duk kananun kaya ne sai kouma kayan sanyi ,
Firfito da idanu tayi bayan ta rafka tagumi fuskar ta cike da alhini ta ɗora da :
Ƙananun kaya ni hauw'u ? Da kai da Falmatar watau duk ƙananun kaya za ku dunga sawa ? O'o ana bariki a turai , to ita dai Mama ku dunga suturtata da kyau saboda yanayin lafiyar ta daman ba kumari ta cika ba . Kai tir da rayuwa da ba ta Musulunci ba
Sai kuma ta ɗan saki murmushi tunowa da tayi da wani abu ,
Kuma ka ga ƙananan kayan zasu amshi jikin ku Babban soja , musamman ma ita Falmata , ƴar riga da wondon nan na zamani ka daure ka saya mata ɗanɗasa-ɗanɗasa ba ƙaramin haska ta zasu yi ba .
Ɗan zunkuɗawa yayi akan kujerar jin an taɓo masa inda yake masa ƙaiƙayi ,
Hajja ina Fatima tare da mama sun ka tafi tun shigowata ban ji motsin su ba ,
Nan suka shiga gidan su Zainaba ta je ayi mata kitso da kunshin tafiya . Ai tana gaf da shigowa ma .
Ƙunshi kuma hajja ?
Tafiyar mu ai ta neman lafiya ce hajja ba'a buƙatar duk irin wannan shirye-shiryen ,
Ta gefen ido hajja ta dube shi , Babban soja ai shi ƙunshi ado ne ga ɗiya mace ...
Sallamar Falmata ita ta hana ta ƙarasa zancen ,
Da gudu mama ta saki hannun Falmata da take yiwa jagora