Showing 81001 words to 84000 words out of 411050 words
Chapter 28 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
miki lale marhaban ,' zama tayi daga ɗaya bangaren shimfiɗar ,'
Suka yi kallon kallo na tsakiyar ido , kafin saratu ta ce ,'
Yau yariman maraɗi ke cikkace shekarun sa talatin cikkin duniya , kou ba hakka ba ?
Kallon mamaki hajiya safiyya ta bi ta da shi tana jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa a hankali mafarkin ta na jiya ke dawo mata da fuskar saratu da ta gani cikin mafarkin ," janye idanun ta tayi daga kan ta ,"
Ƙaƙa kin ka sani ? Kafin ta rufe baki saratu ta amsa mata cikin wani yanayi mai tattare da ma'anoni ,ƙaƙa uwa zata kasa sanin ranar haihuwan ɗiyan ta ,? ???
Guntun murmushin fatar bakin ta safiyya tayi ,'haka ne kin yi gaskiya ,!
Kiraye ma ni shi na taya shi murna shine abu da ya kawo ni gaba gare ki ,"
Tsam hajiya safiyya tayi tun haihuwar youssouf yau shekaru talatin saratu bata taɓa taya shi murnar zagowar ranar haihuwar sa ba sai yau ,? Sama ta ka zata ce zata taya shi murna ? Wallah banza bata kai zomo kasuwa ,!
Ta bangaren biyamuradi youssouf kuwa tun yana cikin yin waya da umma yake jin kira yana shigowa wayar ,
Yana gama magana da umma ya bi bayan kiran da ya gani daga wata bakuwar lamba daga ƙasar su , sai dai har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba , yana shirin ajiye wayar ɗan guntun sako daga lambar ya shigo wayar sa ,"
Mon frère, je t'aime tellement. Que toutes les meilleures bénédictions te parviennent aujourd'hui et pour toujours. !Bon anniversaire.!
Sakon taya murnar zagayowar haihuwa ne ,duba lambar ya sake yi yaga bai san ta ba dan haka kawai sai ya share , ya fara koƙarin kiran layin maimouna kamar yadda suka saba kullum safe
Neman iznin shigowa aka yi ya bada izni aka shigo , abincin karyawar sa ne , aka shigo masa da shi,
Da hannu yayi nuni da a ajiye masa abincin ,
Allo ma jolie fille
Allô joyeux anniversaire mon amour ,
Ɗan jim yayi yana tunanin ta yaya maimouna ta san yau ranar zagayowar haihuwar sa ,? Shi dai ba shi ya sanar da ita ba , '
Princesse wa ya fadi miki wagga batou ?
Cikin dariya ta bashi amsa a iska ta ji , murmushi yayi tare da share batun , suka cigaba da hirar su cikin nutsuwa tare da ƙaunar junan su ,
Wayar su ba mai yankewa da wuri ba ce ,musamman yau da daɗin soyayar ya juyo , dan haka riƙe da wayar ya fita ya wanko bakin sa ya dawo ya zauna cin abincin sa ,
Tashin farko ya kai abincin bakin sa ba tare da bismillah ba , saboda hirar maimouna ta ɗauke hankalin sa , haka har ya cinye abincin tas tana zuba masa zantukan soyayya , sai dai me ? yana gama ci ya ji marar sa ta murɗa , ba shiri suka yi sallama ,' ga mamakin sa sai kuma ya nemi ciwon ya rasa ,
Dan haka ya tashi yayi shirin sa tsaf cikin kayan sa na soji , ya fito
Ya tarar da duk sauran da ke ƙarƙashin sa ma sun shirya domin a yau zasu ɗan yawata ne cikin daji ta sama ta hanyar jirgi mai saukar ungulu,'helicopter"domin su ga wuraren da ƴan tawayen boko haram suke da mafaka su tabbatar basu tsallaka iyaka sun shiga yankin ƙasar su ba ,'
Suka hau jirgi ya ɗaga da su , sun ga wuraren da boko haram suka yi bigire na dindin-din cikin dazuzzuka tare da matan su da ƴaƴa suna rayuwar su cikin walwala tare da jin daɗi fiye ma da al'ummar cikin gari , abun da ya ɗaure kan youssouf kenan , ƙaƙa ƴan ta'adda irin wannan suka samu bigire cikin ƙasa kamar nigeria ? Shin wake ciyar da su ? Wake kai musu makamai ? Waye ke da alhakin basu magunguna zuwa kaƴan bukatun yau da kullum ?? Tabbas akwai lauje cikin naɗi ,'
Sun samu kimanin awa guda a sama suna shawagi kafin suka sauko , kai tsaye ya wuce cikin tantin sa ya kwanta , gaba ɗaya yau ya gaza gane kan sa wani iri yake jin sa tamkar akwai wanda ke sarrafa shi a gefe , yana ji kamar su biyu suke gudanar da kome , amma kuma shi baya ganin kowa ,"
Haka ya yini babu walwala , sun yi waya sau biyu da umma wacce take sake jaddada masa ya riƙe addu"a tare da yawaita karatun kur'ani sai dai kuma abun da bata sani ba shine yau sam-sam ya gaza yin addu'a a yanzu haka da yake kwance ya gagara tashi yayi sallar azahar alhalin kuma la'asar har ta gota , karfe huɗu ma ta wuce , sannu sannu ya fara jin wannan yanayin da yake ji na safe yana sake tado masa , " wata irin mahaukaciyar sha'awa yake ji kamar zai fidda wani sashi na jikin sa ya ajiye koh ya huta ," shi kuwa yau wacce irin masifa ce ta same shi ? Ita ce tambayar da yake yiwa kan sa ,"
Sau biyu sojojin da ke da alhakin kula da lafiyar sa suna leƙowa su duba shi domin sun ji shirun yayi yawa , koh ɗan masallacin da suka tayar suke jam'i cikin sa bai zo yayi sallah tare da su ba a yau baki ɗaya ,
Ga mamakin su duk shigar su a zaune suke tadda shi , sannan kuma yana tabbatar musu da lafiyar sa lau babu abun da ke damun sa , dan haka sai suka kƴale shi ,
Zuwa magariba youssouf ya fara gagara iya riƙe kan sa domin tashin hankalin da yake jin kan sa a ciki ya wuce tunanin sa ya wuce yadda yake ji idan bai sha burkutu ba , wannan karon ji yake yana gab da mutuwa idan bai samu biyan bukatar sa ba ,
Ina zai samu mace a yanzu alhalin yana cikin jeji ? Yaya zai yi ? Dama a cikin gari yake sai ya fita ko'ina ne ya samo wacce zata taya shi ya kauda bala'in da yake ji ,'
miƙewa yayi a dudduƙe ya ɗauki walet ɗin sa tare da ID card ɗin sa , har yayi nufin fita sai kuma ya fasa lokacin da ya kalli jikin sa ya ga yadda ya ke , wani kunya da takaici suka dirar masa , lokaci guda wani duhu ya mamaye masa kwakwalwa da ya sa nan take ya mance da wani batun kunya illah umarni da yaji ana bashi akan ya tafi ,
Yana daga cikin ɗakin ya danna kiran masu kula da shi ta wayar hannun sa , ba tare da jinkiri ba suka zo , yace su kawo masa mukullin mota zak ɗan fita , " jim suka yi ,toh sai dai basu da ikon musa umarnin sa dan haka suka kawo masa mukullin motar suna jiran su ji yayi musu umarnin su mishi rakiya wani wurin , sai suka ji ya sallame su , ficewa suka yi suka bar shi ," suka nufi bakin masallaci domin yin shirin sallar isha'i
Suna tafiya shima ya fito ya buɗe motar ya faɗa ,' ya jaa ta da mugun gudu , ya hau titi tare da nufar cikin garin maiduguri a wannan daren ,'
Gudun da yake ba na hankali bane , bai ko tsoron dare da yadda garin yake haɗe da hadari sai walƙiya ake yi, bai tsagaita ba sai da ya shigo da'irar birnin maiduguri lokacin sha ɗaya da rabi na ɗare har ta gota, cikin garin babu kowa kan titi sai sojoji ƴan uwan sa da suna hango motar ta sa mai ɗauke da fentin launin kakin soja suke buɗe hanyoyin da suka bi suka tottoshe saboda tsaro, shawagi ya fara yi da motar marar sa na cigaba da karta masa har yana ganin duhu-duhu , ya haɗa zufa sai tsuma yake yi, ina zashi ? Shi ba wani sanin kan garin yayi ba guri ɗaya zuwa biyu ya sani , daga barikin garin wurin abokin sa , sai kuma wurin sayar da burkutu ,
karya kan motar yayi ya lokacin da ya ji kamar an umarce shi da ya tafi zuwa wurin sayar da burkutun , a chan zai samu wacce zata iya kula da shi ,
Yana yin fakin ɗin motar ya fito ba tare da ya damu ya rufe murfin ba ya fara taku yana bin hanyar da zai sada shi da cikin gidan hannun sa ɗaya ya riƙe marar sa , da layii ya ƙaraso cikin rumfar , sai dai bakikkirin ya tadda wurin , babu kowa an watse kujerun gurin kansu a tattare suke, wani irin jiri ya ji yana kwasar sa , ya tabbata yau mutuwa zai yi ,
Tun shigowar sa yakaka wacce bata daɗe da kwanciya ba, bayan ta tattara cikin shagon ta kintsa kome, sai dai ta gagara bacci saboda tsinkewar da zuciyar ta ke yi wanda ta danganta hakan da tsoron tsawa da walkiyar da ake yi ,
Taji shigowar sa a tun takun sa na farko a cikin shagon , tsumu tayi cikin zanin rufuwar ta , tana sake jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa da duk wani motsi da yake ,wanene cikin daren nan ? Koh wani ne yayi mantuwa ? kaƙƙarfan kamshin turaren sa shi ya ziyarci hancin ta , kamshin da ya ɗauki tsawon kwanaki a hancin ta kafin ta daina jin sa a wancen haɗuwar ta su ,'
Kamshin na musamman ne dan haka sai ta zame abun rufuwar daga kan ta dan ta samu damar shaƙar ƙamshin da kyau cikin ran ta kuma tana ƙwaɗayin ganin fuskar sa ,
Da ɗan tazara a tsakanin su domin shi yana tsaye daga bakin kofar ta ciki yana fuskantar inda yakaka ke kwance sai dai bai kai ga fahimtar mutum ba ce saboda babu wadatar haske kuma baki ɗaya bai cikin hayyacin sa ,
Sosai ta buɗe fuskar ta tana ƙare masa kallo ta cikin ɗan hasken da yake shigowa ɗakin da taimakon hasken hadarin da ya gangamo cikin duhun daren , bata gani ainahin kamannin fuskar sa sai dai siffar jikin sa da take gani , gani tayi ya sunkuya yana riƙe da cikin sa
Tsawa aka yi tare da walƙiya da ya haddasa yakaka tsorata har ta miƙe zaune , motsin ta ya sanya shi ɗago kan sa ,walƙiyar da aka sake yi ta hasko masa farar fuskar ta ta zuba masa ido tana kallon sa daga inda take zaune ,'
Wani tsallen farin ciki zuciyar sa tayi, da sassarfa ya fara takawa yana nufar ta tamkar mayunwacin zakin da ya kwan uku ba abinci ,
Baya ta fara yi akan bencin tana matsawa , cikin in'ina tace ,'
Babu ruwa ya ƙare ,mun ruga mun tashi an gama aiki sai gobe da rana ,'
Kalaman ta sun zo dai-dai da ƙarasowar sa gaban ta , baiyi wata wata ba ya miƙa hannu ya ɗago ta daga kan bencin ta hanyar ɗago kafaɗun ta ya tsaida ta akan kafafun ta , ba kuma tare da ya ce da ita ƙala ba ya juya tare da jaan hannun ta da ya riƙe nufin sa ta biyo shi ,'
Waiwayowa yayi jin ta turje tana ƙokarin zame hannun ta da ya riƙe tamau ,
Cikin wata irin dusasshiyar murya da take fitowa daga ƙarƙashin maƙoshin sa yace ,"
Ki taimaka min kar na mutu ko nawa ne zan biya ki ki taimake ni ,"
Daga haka ya juya yana jaan hannun ta , bata yi turjiya ba ta fara bin sa kafafun ta ko takalma babu ," kalmar taimako da ya ambata tare da wani abu da take ji yana fisgar ta a game da shi ya sa ta bi shi ,'
Sun zo tsakiyar filin gidan aka fara yayyafi ,' yakaka ta sake tsayawa saboda gargaɗin da zuciyar ta ke yi mata akan yunƙurin bin mutumin da bata sani ba cikin dare zuwa wurin da bata kai ga sani ba wai shin ina hankalin ta yake ne ??
Juyowa yayi aka saki tsawa da walkiya tare da ƙaruwar ƙarfin ruwan sama , haɗa ido suka yi ta hasken walkiyar suka kalli juna na wasu dakikai ba tare da kowannen su ya samu damar magana ba ,"
Cikin idanun sa ta hango ruɗanin da yake ciki , tare da wani abu da ya taɓa zuciyar ta da bata kai ga fahimtar yanayin sa ba , sai dai koma menene yayi tasiri matuƙa wurin raunana mata zuciya ta yadda ta ji kowanne irin taimako ne zata iya yi masa , zata mishi kome yake so , tana nufin kome ,
A bangaren biyamuradi youssouf kuwa shi ma kallon cikin idanun ta ya taɓa shi , ya hango rauni tare da zallar ƙuruciyar da ke tattare da ita ,sai dai sun gaza tasiri agare shi domin daga lokacin da ya riƙo hannun ta ya fara jin wani irin nutsuwa tare da ɗaukewar ciwon da yake ji ,har da wani danshi danshi yake ji a ƙasan ran sa wanda ya tabbatar masa ita zata iya fidda shi halin da ya ɗauki tsawo awanni ashirin da huɗu cikin sa , yana jin zai iya biyan ta ko nawa ne domin ta yadda da shi ,
Ganin bata ce kome ba ya sa shi ya cigaba da tafiya riƙe da hannun ta sai dai wannan karon tare suke jefa kafafun su a jere tamkar sabbin masoya cikin samun amincewar yakaka da ta hakiƙance zata taimaka masa , "
Bai saki hannun ta ba sai da ya dangana ta da cikin motar sa ba tare da fargaban kome ba yakaka ta shiga ta zauna tana shaƙar ƙamshin turaren sa da ke da matuƙar tasiri agare ta ,"
Da ƙarfi ya fisga motar wanda yayi dai-dai da fara saukar ruwan sama da matuƙar ƙarfi ,
wani ƙaramin Guest house ya nufa wanda yake ganin sa akan hanyar shigowa gari , cikin su babu wanda yake ce da ɗan uwan sa ƙala ba har suka isa , bai wani sha wahala ba wurinnsamar musu da ɗaki zamantowar sa jami'in tsaro ,
Riƙe da hannun yakaka wacce ta zamto tamkar rakumi da akala ya danna kai cikin ɗakin ,'
Daga lokacin da suka sanya ƙafa cikin ɗakin kome ya fara kasancewa nan ne mafarin hargitsin rayuwar su , sun gudanar da kome cikin amincewa tare da tallafin junan su , yakaka bata hana biyamuradi kan ta ba wanda ita da kan ta baza ta iya faɗin dalilin ta na sadauƙar masa da mutuncin ta ba ita dai ta san koma wanene wannan mutumin da ya kasance mutum na farko da ya fara kasancewa da ita a wani bigire kuma cikin wani yanayi irin wannan ,akwai wani al'amari mai girma a tare da shi .'
A bangaren biyamuradi kuwa tsintar kan sa yayi a wata duniya mai nisa wacce take tare da wani irin daɗi da sanya nishaɗi da bai taɓa jin makamancin sa ba , ji yayi ko da dakika guda baya fatan wani abu ya gifta da zai katse masa jin daɗin sa ,
Yana jin zai iya mallakawa yarinyar nan kome ta buƙata , idan ya ce kome yana nufin kome ."
Ta hasken ranar da ya hasko ɗakin ta tsakanin ɗan yalolon labuƙen ɗakin yakaka take ƙarewa fuskar biyamuradi kallo , komen sa mai kyau ne babu abun da ya fi ɗaukar hankalin yakaka irin jajayen laɓɓan sa ," tambayar kan ta take daman maza ma na shafa jambaki ? hannu take niyyar kaiwa fuskar sa ta ga ya buɗe idanun sa a firgice kamar ba wanda ke bacci ba ,"
Da sauri ta jaa baƴa tare da maƙurewa a jikin gadon ,"
Zama yayi yana me ƙarewa ɗakin kallo kafin ya waiwayo kan yakaka tare da wani irin kallo da ta kasa tantance ma'anar sa ya watso mata tambayar da ta shayar da ita mamaki ,"
Wacece ke ??????
Assalamu alaikum masoya, ku min afuwa da jinkirin da aka samu kafin zuwan wannan shafin , da kuma rashin baku amsoshi n sharhn ku a shafin baya duk hakan ya faru ne sakamakon aiyuka da suka sha kaina , ina fatan na wanke kaina da wannan mafi tsawon shafi da na rubuto muku ?? Idan haka ne nima kar ku min rowar sharhin ku ,' ku faɗi ra'ayoyin ku,akan wannan tafiya tamu, a wannan karon zan bada lokaci mu tattuna tare domin ƙarin armashi , na gaishe ku kyauta !!!
[10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI .......
Hargitsin Rayuwa
umm"muaz
20
Yakaka tana shiga gida Kai tsaye sashin samy baby ta nufa , ta ci sa'ar samun kofar ɗakin ta a buɗe kai tsaye ta danna kai cikin ɗakin idanun ta a rufe da ruwan hawayen da yake ambaliya ,"
Zube guiwar ta tayi a ƙasa tare da yin jifa da kuɗaɗen hannun ta suka tarwatse a tsakiyar ɗakin ,hannuwan ta biyu ta sa ta rufe fuskar ta lokacin da take sakin kukan da yake cin ta a zuci .
Sautin kukan da yayi sanadiyyar tashin samy baby a firgice daga baccin tofon girar da take shaƙa ,"
Da sauri ta zo ta kama ta
Yaks meye ya same ki ? Duka aka miki ? Ko meye ?
Kusan ba a hayyacin ta ba ta riƙo hannun samy baby ,
Dan Allah ki ce masa ya dawo kar ya bar ni , idan bana ganin sa mutuwa zan yi , kin ga nan ,"ta ɗora hannun samy baby akan zuciyar ta ,"ciwo take min ina jin wani abu ya tokare ni ," INA SON SHI WALLAHI INA SON SHI,"
Kalmar ta ta ƙarshe ita ta sa samy baby kwashewa da dariya bayan fitar ta daga ruɗanin da kukan yakakar ya haifar mata shi da farko ,"
Shashashar banza yanzu ke yaks akan soyayya kike wannan uban kukan ? Kamar wacce aka cewa uwar ta ta mace ? To wai ma tsaya yaushe kika fara soyayya ban sani ba ? Duk kuwa da kashedin da nake yi miki ? Koh daga tafiyar da nayi ta sati