Showing 66001 words to 69000 words out of 411050 words
Chapter 23 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
yaks ,
Aikin gidan madam saly kuwa tuƙuru yakaka take yin sa domin gwanintar da take nunawa ya faranta ran madam saly da take ganin ta a matsayin ginshiƙin su cikin duniya a yanzu , bata da wani lokaci nata na kan ta sai na aikin burkutu wanda ba'a sanya ba ma yi take kamar su wanke dawa , juya ruwan dahuwar burkutun da kuma tace shi wanke kayan madam saly da gyara mata ɗaki , tun safe idan ta kama aiki sai dare karfe sha ɗaya take samun hutu ," wanda hakan ke matuƙar farantawa madam saly rai har take ganin wautar kan ta da farko, da ta so korar su ashe dai maganar ɗan liti dutse ,
Ga falmata ma sai sam barka domin kuwa har ɗan kumatu tayi ta sake mul-mul , sakamakon cika mata ƙundu da ɗan liti yake da cimar daɗi kullum dare kafin su kwanta bacci , ga kuma labaru masu sanya nishaɗi da yake bata har bacci ya ɗauke ta ,bata zuwa ko'ina daga ɗakin ɗan liti da yake daga wajen filin rawa sai cikin gidan madam saly da take aikin wanke-wanke kofuna tare da farantan aikin burkutu tsawon yini a cikin gidan , bata da wata matsala saboda duk lokacin da yakaka ta ɗan zagaya zata taho bakin fanfon da take zaune din-din a gefen sa ta shafi kan ta koh kuwa fuskar ta , ta kuma tambaye ta bata da wata matsala koh ? Nan zata amsa mata cikin farin ciki da ita bata da wata matsala ,
Haka zata sake komawa bakin aikin ta tana mai farin cikin sauyin rayuwar da suka samu , musamman farin cikin da take hangowa a fuskar ƙanwar ta wacce ɗan liti ya wadata ta da ƴan kayayyakin gonjo na ƴan matasan yara maza sa'annin ta fes-fes da ita hasken ƴar luwai ɗin fatar ta ruwan zuma yana bayyanuwa,
Ranar da suka kwana huɗu a gidan ɗan liti yayi mata kyautar kayan wanda daga ita har falmata kyautar bata wani faranta musu ba , saboda ƴan rigunan basu da wani girma kayan turawa ne , su kuma sun san kayan nan burguza burguza da falmata ke sanye da su sune rufin asirin su a kasantuwar falmata namiji saboda kayan ya boye ɗan tudun kirjin falmatan wanda suka fara tasowa tare da bunƙasa ,
Da kƴar yakaka ta shawo kan falmata wacce da farko ta tubure akan shawarar da yakaka ta kawo na falmatan ta dunga sanya riguna biyu bayan ta tamke kirjin ta da ɗankwali ,saboda boye tudun tare da yi mata gargaɗi kada ta yadda ta sauya kaya a gaban ɗanliti duk juyin duniya , ta kan ce
Kiyi hakuri falmata har mu ɗan tara abun da muka tara anan ɗin zuwa lokacin kuma mun san gari sosai idan ya so sai mu koma wani wurin da babu ƴan iska mu raɓa ki koma saka kayan mu na mata , kamar kowacce mace ina nan ina ware miki kayan ki cikin kayan da nake samu ,"
Ranar da ta fara ɗaure kirjin ta yini tayi tana fama da ciwon kirjin , amma da ta kwana biyu sai ta saba ta daina jin ciwon ,
Bata taɓa yin wanka sai sun tabbatar da ɗan liti ya bar da'irar wajen sannan zata yi wankan a gurguje yakaka ta raka ta ta sauya kaya tare da sake gyara mata ɗaurin kirjin ta wanda ya taimaka ƙwarai wurin boye halittun kirjin ta , sai dai salon takun tafiyar ta tare da tudun bayan ta ke sa samy baby tana yawan tsokanar ta da
"Kachallah me jikin mata ,"
tafiyar ka sai kace ta hamshaƙan mata , koh kuwa tace shege kachallah da kai mace ne da anyi manyan kaya a wurin ka ,"
Idan yagana tana wurin tayi ta sheƙa dariya ,wacce ita ma a yanzu sha'awar rayuwar su yakakan take , domin kuwa har kuɗi da suturu yakaka ta bata daga cikin wanda samy baby ta bata ,"
Haka kwanaki suka yi ta tafiya har suka samu wata guda da ƴan kwanaki a dafdalar wannan gidan , wanda zuwa lokacin yakaka tayi jazur wannan maɗaukakin hasken fatar ta ta ya sake bayyana dal tamkar fitila haka take a waje , ƴar kyakkyawar ƙaramar budurwa mai sanyi tare da yawan fara'a koyaushe cikin murmushi take , ko magana yakaka take haka zaka ga fuskar ta da yalwatattacen murmushi dasashin ta a waje , wanda hakan yake tasiri matuƙa wurin bayyana ƴan ƙananun kyaun ta wanda hasken da take da shi ya fi jaan hankalin mazan da suka fara ƙaraƙaina akan ta fiye da kyan nata ,"
Zuwa lokacin samy baby ta fara jaan ɗamarar wanke yakaka daga dauɗar datti gami da ƙazantar ƙauye a cewar ta yakaka haja ce me matuƙar tsada , wacce sayan ta sai alhajin da ya rufu ya tada kai , " sai ya so zama tamkar gasa a tsakanin ta da madam saly wacce ita ma take bada sumfurin tata kulawar ga yakaka domin ta farga gaba kaɗan yakakan zata zame mata hanyar samun arziki ,dan haka ta fara kokarin janye ta daga wurin samy baby da ta lura tana son kawo mata tsaiko domin kuwa ga alama so take ta fanɗarar da yakaka ta sanar da ita daɗin ƴancin kai kamar yadda ita take da nata ƴancin a hannu domin samy baby ba'a ƙarƙashin kowa take ba cikin magajiyoyin gidan , da karfin ta ta shigo bariki da kuma nawin aljihunta tare da gatan ta domin ba kukan yunwa koh na rashin wurin kwana koh kuwa na neman kuɗin zuwa asibiti zubda ciki ne suka kawo ta bariki ba , ƴar cikin ƙwaryar gari ce da gatan ta da kome iyayen ta ma manyan mutane ne sanannu , uwa uba bata da duhun jahilci domin kwalin digiri ke gare ta ," sha'awar rayuwar barikin take tare da taimakon matar uban ta wacce take sake ingiza ta , uwa uba shaiɗan da yake tsakiyar kan ta yana buga ganga ,
Gidan kakaf ba wata tsohuwar kilaki da take shakka , sai ma su da idan jarabar su ta busa sigari koh afa ƙwayoyi suka motsa , kuma suka laluba lalitar su suka ji wayam , su je wurin ta neman ƴan kuɗaɗe sanin da suka yi kaf cikin karuwan gidan ba wacce ta kai ta kama kuɗi , da kuma kyauta domin hannun ta a sake yake bata da rowa ,"
Ranar wata litinin da safe yakaka ta wayi gari da wani irin matsanancin ciwon mara wanda tun kwanaki biyu da suka wuce take jin sa kaɗan kaɗan amma ta daure ,
Har zuwa yanzu da take kan hanyar ta ta zuwa ɗakin samy baby domin ta gyara mata ɗakin ,bayan ta gama kintsa na madam saly kamar yadda ta saba kafin su duƙufa aikin sana'ar su ,"
A dudduƙe da jaan ƙafa ta ƙarasa cikin ɗakin samy wacce take kwance tana sharar bacci daga ita sai ƴar ficiciyar rigar bacci kan gadon duk a hargitse kayayyakin ta tun daga kan rigar mama da ɗan kafai duk a wurge a kan gadon , tayi ɗai-ɗai da kafafu gashin dokin da yake kan ta ya baje akan filon da tayi matashin kai da shi ," idan da sabo yakaka ta saba tadda ta a haka kullum .
Tana shiga ɗakin ta zube akan shimfiɗar kafet ɗin ta kwanta gami da dunƙulewa wuri guda tana murƙususu , dunƙulewar da tayi ta haɗe guiwar kafafun ta da kirjin ta sai ya sa taji rangwamen kartawa tare da murɗar da marar ta ke mata har ɗan wani bacci ta fara ji yana figarta saboda rashin bacci da tayi daren jiya a sakamakon ciwon cikin ," bata ankara ba bacci mai karfi ya fisge ta , ta sake jiki sosai tana baccin ta ,
Samy baby ce ta farka bayan da taji baccin ya soma gundurar ta , ta daina jin dadin sa , doguwar hamma ta hangame baki ta jaa babu neman tsari daga shaiɗan babu salati , ta gantsare bayan ta ya bada sautin ƙaƙas , tana zira ƙafar ta ƙasa ta sauke akan yakaka wacce baccin ta yake kai mata karo har tsibirin keemala na ƙasar bankok,"
Da farko ta firgita da ganin mutum kwance a gaban gadon ta sai dai fahimtar wacece a kwance ya sa ta ƙewaye ta gami da nufar kofar banɗakin da take ta cikin ɗakin nata , a ranta tana raya cewa gajiyar aiki da rashin bacci ne suka sa yakaka ta bingire anan ta na bacci , tare da sake aiyana niyyar taimakon yakakan har ta samu karfin tsayuwa da kafafun ta muddin yakakan zata yadda ta bi hanyar da zata ɗora ta ," yo ina ma zata ƙi ?? Ai duk wanda ruwa ya ci shi idan aka miƙa masa takobi sai ya kama ,"
A firgice yakaka ta farka lokacin da samy baby take tashin ta , "cikin inda-inda ta fara bata haƙuri bayan ta gaishe ta, tare da faɗa mata cikin ta ne yake ciwo amma yanzu ya lafa ,"ta daina jin ciwon sa sosai , sai dai lema-lemar da take ji ta ƙasan ta ya sa ta gaza miƙewa sai faman muskuɗawa take cikin ran ta tana Allah ya sa dai ba fitsarin kwance tayi ba , toh amma ai ita bata fitsarin kwance tun da ƙuruciyar ta bare yanzu da ta zama ƴar budurwa ,
Tunanin ta ya katse lokacin da samy baby tayi mata umarni bayan ta miƙa mata kuɗi akan ta sayo mata soyayyar indomi da ƙwai tare da shayi haɗin murtuku ya ji sugar sosai ,"
A sanyaye yakaka ta miƙa hannu biyu ta ƙarba tana mai taraddadin tashi kar samy baby ta ga yadda ta jiƙa mata kafet ," amma ba yadda ta iya haka ta miƙe tare da nufar bakin kofa
Bin bayan ta da kallo samy baby tayi tana tunanin me ya sanyayar mata da jiki ?ko cikin ke damun ta saboda ta san a wurin aiki da aike yakaka bata da sanya ," karaf idanun ta suka sauka a bayan yakaka inda shuɗin siket ɗin yadin da take sanya da shi duk ya baci ,"
Ke yaks dawo nan wai ke me yasa kin cika gidadanci ne ?? Yanzu har yau baki yi wayewar da zaki saka pad a jikin ki idan kina menses ba ? Haba mana yaks meyasa kullum ina kai ki kina dawowa , yanzu ba dan na gani na ƙira ki ba da kenan haka zaki fita ?? Ta ƙarasa zancen tana balla mata harara ,"
Ƙasa da kan ta yakaka tayi tana me satar kallon wurin da ta tashi domin ita duk bata wani gane kalmar pad da menses ba , ga zaton ta faɗa samy baby take yi mata akan fitsarin da ta saddaƙar shi tayi a kwance "ɓacin rana"
, sai dai ga mamakin ta wurin da ta tashin ɗan alamun danshin kaɗan ne kuma bai wani fidda kala ba saboda kafet ɗin ruwan kunkumadi ne ita ma da kƴar ta hango danshin toh akan me samy baby take mata faɗa ?? Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji samy baby ta ce ,"
Ki buɗe ƙaramin akwati na ki ɗauki sabon pant da pad ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki nan gaba kar ki sake zama babu pad alhalin kin san lokacin yin menses ɗin ki yayi kusa kina jin alamar sa ki tanadi pad idan ma baki da ita ki zo na baki koh kuma ki yi ƙunzugu da tsabatatatcen tsunma kin ji koh ,??
Da sauri yakaka ta gyaɗa kai tana rarraba idanu , domin ita har ga Allah ba wani fahimtar dogon bayanin samy baby tayi ba , koh ta so fahimta ma kalmomin da ta jefo guda uku da turanci sun hana ta gane kan maganar , dan haka kawai sai ta je ta durƙusa a gaban akwatin tayi zugui ,"
Fahimtar da samy baby tayi yakaka fa bata fahimce ta ba ya sa ta tashi ta zo ta buɗe akwatun ta tare da ciro sabon pant fil sai tashin ƙamshi yake ( ku sani mata tsabtace undies tare da wanke shi da kuma goge shi wani babban sirri ne na sanya nishaɗi a gangar jiki tare da bada kariya na musamman daga kamuwa da cututtukan da suke addabar mata daga ƙasan su a zamanin yanzu ,ki kasance kullum cikin wanke tare da goge panties ɗin ki bayan kin shanya su a rana sun yi a ƙalla awanni shidda a rana ) da kuma ledar pad mai guda takwas ta danƙa mata," ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki ,"
Da sauri yakaka ta amsa da toh ,
Kin iya amfani da shi koh ?
Gƴaɗa kai ta yi sai kuma ta sake girgiza shi ,"
Samy baby wacce ta fara zowa wuya da gidadanci tare da jahilcin yakaka tace ,"
Buɗe baki zaki yi kiyi magana ba ki dunga gƴaɗa min kai ya kadangaren gobara ba , kin iya amfani da shi koh na gwada miki ??
A sanyaye ta amsa ban iya ba ,"
Karɓa tayi tare da nuna mata yadda ake amfani da shi ta ɗora mata da ,"ki wanke siket ɗin naki a banɗakin zan miko miki wasu kayan ,"
Ƙiris ya rage yakaka ta kurma ihu lokacin da ta ga yadda jikin ta ya ɓaci da jini ,"tashin hankali na shiga uku na lalace fitsarin jini na fara shikenan nima zan mutu na bi su abba wayyo Allah falmata waye zai kula min da ke ," wannan shine tunanin da yakaka take yi lokacin da take wanke jikin ta da kayan ta , tana yi tana sharar hawaye ,"
Ido jazur ta fito bayan ta shirya kan ta cikin kayan da samy baby ta miƙa mata na wata koriyar atamfa riga da siket , sun zauna mata ɗas kasancewar ita ma samy baby ƴar madaidaiciya ce tamkar ta ,"
Sumi-sumi ta wuce tana share guntun hawaye ta nufi wurin aiken da aka mata ,' samy baby ta bi bayan ta da kallo tana me jin tausayin yarinyar na zaunawa cikin ranta , ta fahimci yau ne ta fara tsintar kan ta a yanayi na al'ada saboda tashin hankali da damuwar da ta gani tare da yakakar wanda ba kome ya jawo hakan ba illa jahilcin addini da na boko saboda da tana zuwa makaranta kowacce daga cikin ta boko koh ta islamiyya a shekarun ta da take sha shidda da ƴan watanni ya ci ace ta san me wannan jinin yake nufi saboda ana wayar da kai a makarantu ," nan take ta ji tana son tayi yunƙuri domin ganin yakaka ta ɗan samu ilmi ko kaɗan ne domin ita kan ta harkar da take son ɗora ta akai idan kana da ilmin boko kafi samun kasuwa wurin manyan wayayyun mutane irin wanda take yi wa yakakar yangen su , domin su basu cika harka da jahila ba ," zamani ya zo da kome zaka yi domin cigaban kan ka sai kana da ilmin zamani ilmi shine gishirin rayuwa ,"
Tana tafiya tana rarrakaɓewa ta jikin gini tafiyar kan ta ba yadda ta saba take yin ta ba tana tafe tana mammatse kafafu domin ji da take tamkar ƴar audugar da take jikin ta zata faɗo wacce rashin sanya ta a dai-dai ya sa take jin hakan ," cikin ranta kuwa kalmomin wasiyyar da zata barwa falmata take haɗawa ,"
Yaks baby , yaks baby , ke yaks ji mana wai yane ina miki magana kina wani ƙara wuta tamkar baki ji na , zo mana magana za muyi ,"
Muryar babasho mai sayar da wiski da su matallah , zuwa kan taba sigari da sauran kwayoyin sanya maye a cikin ɗan shagon da yayi da tsoffin kwanukan rufi da katako ,ta katse mata tunani , babasho yayi masifar maƙalewa yakaka , yana bala'in son ta kamar zai yi hauka ,sai dai samy baby ta kasa ta tsare ta hana ya samu damar koh ɗan zantawa da yaks , duk kuwa da cewa kullum sai ya je rumfar saly baby ya sai burkutu dan kawai ya samu ya ga fuskar yaks ," samy baby ta kan faɗa mata ," ta wuce ajin babasho fintinkau , me zata yi da wannan sauran tabar ? Da duka-duka idan aka haɗa jarinsa da shagon nasa ba zai fice dubu goma ba ,?? Ai sama tayi wa yaro nisa tsakanin ta da ire-iren su babasho sai dai ta kira su ta aike su ,"amma ita kalar manya ce kalar hamshaƙan da suka ci suka tada kai da naira ,
," kar ki kuskura ki kula shi yaks bashi ma da isasshen hankali idan ya sha ta kai masa karo yana iya shaƙe ki ya kar ki ya kar banza atoh kiyi hankali,"
Ga yakaka kuwa ita ba ma babasho ba da take jin mugun-tsoron sa saboda chukurkuɗaɗɗan gashin sa da ya tara akai baya wani kula da shi duguzum-duguzum ya fenta kan kalar jaa shuɗi da kuma yalo , uwa uba faranta hannunsa zaƙo-zaƙo da suke cike taf da annakiyar dauɗa suna tsorata ta har su sanya ta hasashen yadda zai kafa mata farce a wuya idan ya shaƙo ta kamar yadda samy baby take faɗa mata , ita gaba ɗaya maza ma ƙarƙashin ranta tsoron su take , babu wani ɗa namiji da ta taɓa jin sa cikin ranta idan aka ɗauke dakta hamza wanda shi ma ta ɗauki tunanin sa da yake faɗo mata jifa-jifa a zuwan tana tuna sa ne domin taimakon da yayi a gare su ita da ƙanwar ta , bayan shi babu wani ɗa namiji da yakaka take ɗaga kai ta dube shi iyakar ta da su harkar cinikayyar su ta burkutu su , su zo saya ta je ta kawo musu ta karbi kuɗin ," bata taɓa buɗe baki tayi tsiwa koh rashin kunya ga kowa ba duk kuwa da yadda suke kai mata wawura tare da maganganun banza da ita bata ma kai ga fahimtar wasu kalmomin su na batsa ba ,"ita dai ba'a raba