Showing 57001 words to 60000 words out of 411050 words
Chapter 20 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ganin ku ," kun ji koh baku ji ba ???
Cikin sauri su ka amsa da toh !
Sauri-sauri suka haura tudu tare da barin unguwar suka tadda falmata wacce har ta fara gundura da jiran su tare da fara jin tsoron rashin dawowar su har zuwa yanzu da take jin hayaniya ta ragu a bakin kasuwar alamar an watse domin tun ɗazu baba modu ,"mutumin da take zama a gefen rumfar sa ," ya tattara kayan sa tare da sauke rumfar ta sa yayi mata sallama ya wuce gida ,"
Ajiyar zuciya ta saki a take fuskar ta ta yalwatu da murmushi sakamakon jin muryoyin su yakaka ,"
Yakaka yau kun daɗe a wajen aikin da fatan dai lafiya ? Dan har na fara tsorata .
Kamo hannun ta yakaka tayi tare da sarƙafe yatsun su cikin na juna,
Lafiya lau falmata uwarɗakin mu ce yau tayi baƙi shiyasa bata sallame mu ba da wuri , kin ci abincin rana dai koh falmata ?
Naci gƴaɗar naira ashirin yakaka ," ta furta hakan tare da miƙa mata ɗaurin bakar leɗar da take tara kuɗin barar ta a ciki ,"
Wannan karon yagana ce tace ,"
Gyaɗar naira ashirin ba abinci bace falmata ina ma laifin ki sayi koh ƴar awarar hamsin ,"ki daina zama da yunwa kullum muna faɗa miki ,ai yunwa tana daga cikin dalilin da yasa muka fito nema , toh me yasa zaki sake zama tare da yunwar bayan kuma akwai kuɗin sayan abincin a tare da ke ,"
Shiru falmata tayi ba tare da tace ƙala ba cikin ran ta kuwa tana sake kuɗurce niyyar cigaba da tara kuɗin barar ta , har sai ta samarwa da yakaka iya adadin kuɗin da zai isa ta jaa jarin kowacce irin ƙaramar sana'a ce da zasu iya dogara da ita ba tare da yakaka taje tayi aikatau ba ,"
Yakaka kuwa da ita ma bata ce kome ɗin ba idanun ta ne yake bisa kan wata mata da take soya doya da kwai daga gefen bakin tashar ," sakin hannun falmatan tayi ba tare da ta amsa tambayar da falmatan take yi mata ba na "ina zata" ?
Ta nufi me sayar da doyar , ta miƙa naira ɗari daga cikin kuɗin aikin ta ɗari uku ,"ta ce a bata doya ,"
Kamo hannun falmatan tayi tare da zaunar da ita akan wani ɗan fasasshen buluk ta tsugunna ta buɗe ledar doyar tare da ɗaukar yanka ɗaya ta nufi bakin ta da shi
,"buɗe bakin ki kici zaman ki tare da yunwa barazana ce ga kwanciyar hankalina falmata , babu amfanin wuni da nake ina aikayau idan har ke zaki wuni tare da yunwa , alhalin kina zaune a bakin hanya cikin rana kina bara , na kasa baki kulawar da ta dace , rashin amfanina zai yawaita a gare ki falmata idan har ya zama na kara miki da yunwa daga yau kar ki sake zama da yunwa duk kuɗin da aka baki na sadaka ki daina ajiye ko sisi duk ki sayi abinci ki ci , ki ƙara girma ki zama ƙatuwa ko bakya so idan mama ta gan ki ta ji daɗi tare da yaba min akan na kular mata da falmata mafi soyuwa agare ta cikin ƴaƴa ??",
Tun da ta fara maganar take taunar doyar da ta sanya mata cikin baki tana murmushi , kammala maganar ta ya zo dai-dai da fitowar ƴar siririyar dariyar da tayi jin an ambaci kalma mafi daɗin sauraro agare ta watau " dawowar mahaifiyar su"
Nagode yakaka a kullum ina alfahari da yawan ƙaunar ki gareni ina kuma rokon Allah nima ya bani damar da zan nuna miki kulawa koh da bata kai yawan wacce kike min ba ,Allah ya bayyana mana mama tare da su baana cikin ƙoshin lafiya ,"
Su duka suka amsa da ameen har yagana da take kallon su cikin sha'awar yawan kaunar da suke yiwa junan su ,"
A gijiye likis suka dawo sansanin nasu amma hakan bai sa ,"fanna da ajus sun tsahirta musu ba domin tamkar jira suke su sanyo kafafun su cikin camp ɗin su tare su da lodin aiyukan su da ƙyuiya tare da sanin cewa akwai waɗanda suka maida bayun su ya sanya suka ƙi motsawa suyi aikin ,"
Da ɗibo ruwa da suka tadda an tada injin yamma kenan suka fara , kafin yakaka ta ɗora da wankin kayan yaran fanne na kashi da fitsari , ita kuma falmata ta tafi aiken da ajus tayi mata wurin saurayin ta wanda shi ma a cikin sansanin nasu dai yake amma yana ta bangaren maza da yake chan-ciki inda tantunan maza yake ,"
Wannan shine karo na huɗu da ajus take aiken falmata ta karbo mata kuɗi koh kuwa ta tambayo mata saurayin nata kou zasu samu damar haduwa a wannan ranar idan dare yayi ," wanda ita kuma sam falmata bata son zuwa wurin tantunan samarin saboda wani da bata kai ga sanin sa ba da yake biyo ta a baya ta tsakankanin manyan bishiyun darbejiyar yana taɓa mata jiki ," yana faɗin wai tsarin jikin ta tun tana ƙarama yana da kyau ,"
Sai dai tsoron ajus ya hana falmata tayi wani yunƙuri na samarwa kanta damar kaucewa zuwa aikin ,
Cikin sanyin jiki ta kama hanya bayan ta biya ta sanarwa yakaka wacce take ta faman gurzar wanki ta gefen ɗakunan su duk da duhun dare da ya riga ya shigo domin har an idar da sallar magariba ina shirye-shiryen yin isha'i amma su koh sallar magaribar ma basu samu damar yi ba kamar yadda a yawancin lokuta haka take faruwa sai dai su haɗa magariba da isha'i suyi tare , abincin dare kuwa ba kullum.suke samun damar ci ba saboda ana idar da magariba ake zubo shi a daka wawaso kamar yadda aka saba , su kuwa a mafi yawancin lokuta basu kammala aiyukan bautar da ake basu ba ,"dan haka zuwa yanzu sai rana ɗaiɗaiku suke cin abincin sansanin kuma basu wani damu sosai ba sakamakon suna da ƴan kuɗaɗen su a kulle ," kou yagana da take take da damar cin abincin ma bata cika shiga cikin turmutsutsun ayi kokawar ɗibar loma da ita ba , a cewar ta daman dole ne ta sa take cin wannan cinkusasshen abincin marar daɗin ɗanɗano ,"
Tafe take tana juya jikin ta a hankali kamar yadda yake halittar jikin ta , duk da ƙarancin shekarun ta da yanzu ne ta fara fidda alamun budurci ," amma haka halittar ta take irin matayen da suke da maɗaukakin kyaun diri da ɗan madaidaicin tsawo ," tafiya take cikin nutsuwa baza a taɓa zaton makauniya bace ," saboda yadda take tafe babu ɗan jagora kuma babu sanda sai dai lokaci-zuwa-lokaci ta kan ɗan lalubi hanyar wanda hakan yake babbar baiwar da Allah ya yi mata , tana daga cikin makafin da Allah ya basu ikon gani da zuci , wanda kai tsaye baza'a kira hakan da gani ba domin ba ganin suke ba sai dai wata irin baiwa ce da ɗaukakar ubangiji da ya yi musu daga kwakwalwa zuwa zuciyar su ,"
Ta tsakanin dattin ganyen bishiyar ta ratso har ta bullo a gaban tantunan da suke duk a rurrufe saboda ɗan sanyi sanyin damina uwa uba tsoron kar muggan ƙwarin damina su buwaye su , "
Tsayuwa tayi a dai-dai bakin tantin da take hasashen nasu saurayin ajus ɗin ne tare da yin sallama cikin maɗaukakiyar murya ta kwala kiran sunan sa kamar yadda ta saba ,"
Daga ciki ya jiyo tare da shaida muryar ta nan take ya fito , nan ta isar masa da sakon ajus ɗin da take tambayar neman sanin kou yau zasu haɗu su zanta ? Inda shi kuma ya faɗawa falmata ta sanar da ita shi yau bai jin daɗi .
Tana kammala jin amsar sa ta juya tare da nufar hanyar komawa , signal saurayin ajus yayi wa wani saurayi ɗan uwan sa da yake tsaƴe a gefe wanda kuma tare suka fito daga tantin ," shafa shukurkuɗaɗɗan daddauɗan gemunsa daya saurayin yayi lokaci guda suka yunƙura tare da rufawa falmata wacce ta ɗan fara nisa daga da'irar su ,"
Ta cikin takun su da yake sauka akan busassun ganyayyakin ta fahimci akwai mutane fiye da ɗaya a bayan ta wanda bata kawo hakan a zuwan wani abu ba cikin ranta ,"
Cigaba tayi da tafiyar ta , sai dai kome ya tsaya mata ne lokacin da taji anyi sama da ita an ɗaga ta cak lokaci guda ana me sanya hannu a toshe mata bakin ta , kafin taji an zura da gudu da ita zuwa wani bigire da bata san ina bane duk kuwa da wuntsil-wuntsil da ƙoƙarin sauka da take daga kafaɗun wanda ya ɗaga ta da bata kai ga nasarar saukar ba ,," sauke ta aka yi akan wani abu da tashin hankalin bai bari ta fahimci menene ba , kafin kuma tayi aune taji an fara ƙoƙarin raba ta da suturar ta alhalin bakin ta yana danne cikin hannunwan wani daban , an hana ta damar ihu , wani irin bugawa zuciyar tayi tamkar zata fashe lokacin da ta fahimci mummunan nufin da suke son aiwatarwa a gare ta ,"
Bugawar zuciyar ta ya zo dai-dai da na yakaka da tata zuciyar ta fara sauya salon aikinta tun daga barin falmatan gaban ta zuwa yanzu da zuciyar tayi mummunan bugawa, " zuruf ta miƙe tare da zare hannun ta daga ruwan wankin ta kai hannayen nata duk biyu ta dafe kirjin ta ,"......!
#Fikrh
#umm'muaz
#son soFikrah writers association
MAFARI ........
( Hargitsin Rayuwa....)
Umm'muaz
15
Dafe da kirjin ta da yake cigaba da bugu ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakunan kwanan mazan sansanin su , domin haka kawai ta ji hankalin ta bai kwanta ba da rashin ganin ɓullowar falmata har yanzu dan haka ta tafi domin ta taro ta su dawo tare,'
Sai dai har ta cimma ɗakunan bata ga falmatan ba , sai tsirarun mutane da suke giftawa ta cikin duhuwar ," turus ta jaa ta tsaya saƙe-saƙe ta fara yi a zuci ,"
Toh ina falmata tayi ?
Koh dai ta koma ɗakin su ne wurin ajus ?
Ganin bata ga koh alamar ta ba kuma ga shi babu wadatar kafafun mutane a wurin bare ta cigita , ga kuma duhun dare da take tsorace da shi , sai ta juyo gami da kamo hanyar komawa da nufin zuwa ta duba ɗakin su falmata ,
A sanyaye take taku saboda har yanzu zuciyar ta bata bar tsinkewa ba sai ma ƙara dukan uku uku da take yi ,"
Bata yi nisa ba ta tsinkayo wani rishi da alamun fitowar kukan da aka ƙi bada dama ya fito ,' kiƙam ta jaa ta tsaya tare da sake kasa kunne lokacin da ta sake jin irin rishin ," a firgice ta juya laɓɓan bakin ta suna furta sunan ,"Falmata"
Tayi diri-diri cikin rarraba idanun ta a kewayen wurin ,tana neman inda zata gan ta domin tabbas kunnuwan ta muryar falmata suka jiye mata ,"
Cikin rashin sanin gaba zata yi ko baya ta taka da gudu tare da hawa kan barandar wasu tsoffin ajizuwan da suke gefe da ita waɗanda kou rufi babu a kan su ta wasu wuraren ma sun fara zaftarewa da alamun sun zama kango ,"
Da gudu take shiga cikin ajizuwan tare da kwala kiran sunan falmata , sai dai bata tarar da kome cikin ajizuwan sai tarin bola tare da yanar gizo-gizo da tayi dafifi a ciki , cikin tashin hankali ta jaa ta tsaya daga karshen barandar da take daf da katangar makarantar , daddagewa tayi ta sake ƙwala kiran sunan falmatan , sai dai bata kai ga rufe bakin ta ba taji an ɗauke ta da wani kakkarfan mari , kafin ta farga taji an shatile kafufuwan ta , ta tafi ta baya ta faɗi ƙasa tare da bige ƙeyar ta da katangar makaranta ,
zuruf ta miƙe bata koh ji alamun zafi ba lokacin da tashi sautin muryar falmata ya fito tar cikin wani irin kukan wahala tana ambaton sunan ta a kurkusa da ita ,"
Taku biyu ta ƙara ta ci karo da ita a kwance cikin tarin busassun ganyayyakin da ake sharewa a tara a wurin ya zamto tamkar bolar zuba ganye ,"
Ɗago ta tayi ta tarairayo ta tare da rungumo ta zuwa cikin jikin ta tana yi tana waige-waigen jin ta inda waɗan da suka bige ta zasu bullo wanda take da tabbacin sune suke shirin cutar mata da falmata cikin ran ta tana jin karfin yin ɗauki ba daɗi da ko su waye domin ta tseratar da falmata ,"
Tunanin ta ya tsaya chak ! Lokacin da ta ji gaba ɗaya kukan da falmatan take yi ya gauraye da wani irin numfashi tamkar na me shiɗewa , jijjigata ta fara yi tare da kokarin tayar da ita tsaye ,tana cewa
"sannu falmata me suka yi miki ? Duka ? Kin ji ciwo ne falmata tashi muje ki shaa ruwa ,"
Rinjayar ta falmatan tayi a domin ta gaza tsayuwa sakamakon numfashin ta da yake sarƙewa , su duka biyu suka zube ragwaf a ƙasa kafin falmata tayi baya lau ta tafi zata kwanta cikin sauri yakaka ta riƙo ta kwakwalwar ta na son fahimtar me ke shirin faruwa da ƙanwar ta ?
Jijjigata ta fara yi cikin zubar hawayen da suka balle sakamakon tashin hankalin ganin falmatan a kwance bata motsi sai wani irin shiƙar numfashi take ,"
Cicciɓar falmatan take son yi amma ta kasa saboda tayi mata girma da nawi baza ta iya ba , kwantar da ita tayi ta taka da nufin zuwa ta kira mutane su taimaka mata , har ta yi taku biyu a gigice ta sake juyowa , zuciyar ta na bijiro mata da hoton gawar mahaifinta da ta bari a wuri makamancin wannan cikin "gona babu kowa ,"
Da gudu ta taho gami da sake durƙusawa tare da ɗago falmatan da dukkanin karfin ta , ta rungumo ta a kirjin ta , ta yunkura da kyar ta miƙe gami da ciccibar falmata da jikin ta yake a sake bata motsi , kiki-kiki ta fara kokarin jaan ta ta tafi da ita , sai dai kou taku uku mai kyau bata yi tayi tuntube da wani ɗan kankanin dutse ta baya kafar ta ta zame takalmin ta ya tsinke , suka tafi baki ɗaya suka faɗi ta baya kan falmatan ya bigi haɓar ta nan take hakoranta suka datse laɓɓan ta na ƙasa ya fashe ,"
Da hanzari ta sake sunkuyowa kan falmata hawayen ta na ɗiga akan fuskar falmatan ta ɗago ta ta fara jaan ta cikin sautin kuka ta fara ƙwalla kiran naiman taimako , domin zuwa yanzu ta fahimci mutanen da suka jefa ƙanwar ta cikin wannan mummunan yanayin da zuciyar ta taki aminta da falmatan ta mutu kamar yadda ta ga alamu , mutanen sun gudu basa wajen ,"
Da faɗuwa da tashi ta fiddo ta tsakiyar hanyar da ake wucewa , sunkuyowa tayi tare da tallafo kan falmata tana cigaba da girgiza fuskar ta ,"
Meƴe ya same ki falmata ?
Falmata ki tashi dan Allah
Ki tashi falmata ? Ki tashi
Hasken tocila ne ya fara hasko su daga nesa kafin mutanen su ƙaraso ," tun kafin tayi magana suka yunƙuro da hanzari suna tambayar ta me ya samu ta kwancen kuma me suke anan ?
Cikin kuka take rokon su akan su taimaka su ɗauki ƙanwar ta zuwa asibiti , basu yi ƙasa a guiwa ba suka ɗauki falmatan chak tare da kai ta ɗan ƙaramin ofishin da aka tanada a matsayin ƙaramin asibitin bada taimakon gaggawa ,'
Yana zaune yana kammala shigar da wasu muhimman bayanai da suka shafi aikin sa ta computer suka faɗo masa duuu babu sallama bare neman izni ,"
Da ido ya bisu har suka shimfiɗe ta akan ɗan siririn gadon da aka tanadar domin marasa lafiya ," suka yi tsaye charko-charko sun tasamma mutane ishirin a cikin ofishin a tsai-tsaye banda waɗan da suke daga wajen baranda da idan aka haɗa zasu kai rai hamsi duk ƴan rakiya ne ,"
Cikin nazari yake kallon su ɗai-ɗaya ta cikin farin gilashin da yake manne akan fuskar sa bayan ya rufe computer gami da tokare hannuwan sa biyu akan teburin ya ɗago haɓar sa da su , cikin ranshi yana jimanta rashin hankali da gidadanci na wasu mutanen ƙauye ,"
Chan daga waje yake jiyo tashin ƴar siririyar muryar ta cikin kuka tana ambaton sunan "Falmata''wanda hakan ya sa da sassarfa ya nufo marar lafiyar da aka kwantar da bai kai ga sanin meye ya faru da ita ba ,"
Da taimakon hasken ƙwan lantarki fari sol da ya haske ofishin ya shaida fuskar ta duk da cewa ta ɗan kunbura a sakamakon shatin yatsu da suka kwanta tar a gefen da gefen fuskar ta ta da kuma laɓɓan ta da suka ɗan kumbura ,"amma hakan bai hana shi gane ta ba ,"
Me ya same ta ??
Ita ce tambayar da ya jefo musu a dai-dai lokacin da ya ɗauko abun auna bugun numfashi ya ɗaura shi a saitin kirjin ta ,' kallon-kallo aka shiga yi tsakanin mutanen da suke a cike a ɗakin domin duk cikin su babu wanda ya san takamaimai meye ya faru ga falmatan
Ganin sun yi shiru ya sa shi sake cewa " ina ƴan uwan ta ?
Mutane biyun da suka ɗauko ta suka ce ƴar uwar ta tana waje ,"
" Ku ƙira ta"
Da kyar ta samu hanya ta kutso cikin ɗakin idanun ta na yararin ruwan hawaye har ya jiƙe gaban hijabin ta ,
Gaban gadon da falmatan take kai ta zo ta tsaya ba tare da ta lura da wanene likitan ba ita dai babban burin ta , ta ga falmata ta motsa tsoron ta tare da taraddadin ta kar ace mata wani mummunan