Showing 87001 words to 90000 words out of 411050 words

Chapter 30 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

19997

mata zata nemo mata shi ta wurin abokin sa ,!

  Ta je barracks ɗin sai dai bata tarar da shi Colonel nuhu ba, an tabbatar mata da ya tafi bakin aiki ,! Wanda hakan sam bai mata daɗi ba kuma ta kirayi duk numbobin sa basa tafiya ta rasa dalilin haka ! ?

Zuwan ta daban-daban uku bata samun sa , dan haka ta ɗan tsahirta .tare da cigaba da lallaɓar yakaka wacce ta lura tayi zurfi cikin mahaukaciyar soyayyar mutumin da a yanzu take hasashen yayi wa yakaka nisa , sai dai a nemo madadin sa ! Wanda bata ga alamun samun haɗin kan yakaka wurin nemo madadin na sa ba ! , babu ranar da yakaka bata kuka akan soyayyar bature kam silum , ɗakin samy baby nan ne wurin fakewar ta ta sha kukan ta domin ita tasan matsalar ta ita tasan dalilin kukan ta , kuma ita take zaton zata iya share mata hawaye , sai dai a yanzu labarin ya sha banban kuma wankin hula na neman kai su dare ,!

A yau yakaka ta tashi bata da ko sisi domin satin da ya wuce ta kai falmata asibitin ido da kuɗaɗen hannun ta inda kuɗin magunguna da wasu aune-aune , ya lashe fiye da naira dubu takwas , a cikin sauran dubu goma sha biyu da ƴan kai da suka rage mata ,

Da sauran kuɗin tayi amfani wurin cigaba da hididimun yau da kullum , musamman abinci wanda shine kan gaba wurin lashe mata ƴan kudaɗen domin kwanan nan ta tsinci kan ta cikin wani irin bala'in kwaɗayi , bata iya cin abincin da bai wadatu da kayayyakin ƙawata girki ba , bata kuma cin abinci babu nama sannan a rana bata sha lemon kwalba "pepsi " ba tasha guda uku safe rana dare ,' idan kuwa bata sha ba babu zaman lafiya wani iri bala'in yunwa mai tafe da tashin hankali zata dunga ji ,"

Da haka kuɗaɗen hannun ta tas suka ƙare !

Duk da tarin damuwar da take cin ta cikin rai , kallo ɗaya za'a mata a gane ta sauya , ta sake fari har tana ɗaukar ido ta cika tayi luwai-luwai kyaun idanun ta kamar gilashi sun sake haskaka ,! Tana zuwa wuri take ɗaukar hankalin jama'ah .

Ture jakar kayan tayi gefe ta ƙarasa bajewa ta zauna daga durƙuson da tayi ta tallafe kumatun ta da hannu, wannan shine karo na uku tana chaje cikin kayan ta a safiyar yau ko Allah zai sa tayi gamdakatar da wani makararren chanji , sai dai koh alamar kuɗi bata gani ba idan aka ɗauke kuɗin sefa ,"niger", wanda basu da wani maraba da babu a wurin ta ,"

A hankali ta miƙe tana haɗa hanya saboda wata azababbiyar yunwar da take wuji-wuji da ƴaƴan hanjin ta ,'

Ɗakin samy baby tayi wa tsinke ,'
  Saɓanin zaton da tayi zata tadda ta tana bacci ta jira tashin ta , sai ta tarad da ita tayi shiri tsaf , tana zaune bakin gado tana shirya kayan ta cikin ƴar jaka ta matafiya ! Gaishe ta tayi cikin ladabi !

Yauwa yaks daman yanzu nake son na tura a ƙira min ke , tafiya ta taso min jiya-jiya cikin dare Honourable yake sanar min zamu yi tafiya tare da shi zuwa abuja inda zai je wani aiki watakila ma mu wuce dubai daga chan ," ga waɗanan kayan ki ɗauka na bar miki su , ni nasan a chan zan taho da wasu masu zafi ," ta furta hakan tana mai turawa yakaka wasu kayayyaki da ta ware su gefe,!

Yakaka wacce tun da taji kalmar tafiya jikin ta ya sake yin sanyi laƙwas ,! Ta durƙusa bisa guiwar ta ,' a gurin samy baby take ɗan samun nutsuwar zuci , take kuma ɗan taimakon ta da wasu abubuwa ,  baza ta so ba ta tafi ta bar ta a wannan halin tsaka mai wuya da take ciki ,
    Cikin sanyin murya tayi mata godiya , bayan ta haɗa kayan ta ƙulle su a ɗankwali ,'
    Cigaba tayi da zama tana bin kowanne motsi na samy baby da ido cikin ran ta tana ayyana dama ita ma da bature kam silum ya tashi tafiyar sa ya nemi rakiyar ta mana ? !

    Lura da yadda jikin ta yayi sanyi yasa samy baby , ta ce
      Ni bani ma lambar wayar ki idan naje ma dunga yin waya , ba kina da waya ba ?
    Gyaɗa kai tayi
Amma ban san nambar ba wayar ma tana ƙasan kaya na babu chaji ,
   Mts idan banda ke yaks waye zai saka waya ƙarƙashin bacco ? To wannan ai ko yariman ma ya kira ki ba sani zaki yi ba ," gidadancin ki yayi yawa yaks bari dai na dawo daga tafiyar nan inaga darasi zan fara baki dalla-dallah
   Ƴar takarda ta ɗauka daga jakar ta ta rubuta mata lambar wayar ta ta miƙa mata ,"
    Ga lamba ta nan ki kira ni idan kin saka wayar a chaji kuma ki daina ajiye wayar a nesa watakila ma shi baturen naki yayi ta nema bai same ki ba ,'
      Cikin ɗan ɓurɓushin farin cikin jin an ambaci sunan masoyin ta tace
    Toh anty zan dauko yanzu idan na koma ɗaki , anty kuma yaushe zaki dawo ?
    Ban sani ba yaks ni ƴar rakiya ce ! Sai lokacin da ya gam Abun da ya kaushi zamu dawo tare .
   Gƴaɗa kai ta sake yi !
Toh anty sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya ! ta furta hakan bayan ta miƙe tsaye da ƙullin kayan ta ,"  har ta je bakin kofa ta tsinkayo muryar ta
      yaks ungo wannan kƴa ɗan sayi pepsi ki sha tun da yanzu naga yayin ɗaga ƙwalbar pepsi kike ! Ta ƙarasa zancen da ƴar dariya

Dubu biyu ta bata , da murnar ta ta ƙarba ," tana jero godiya

     Zuwa tayi ta kai kayan da ta bata ɗaki ta dawo domin yi mata rakiya,

Tare suka jera yakaka ta ɗaukar mata jakar kayan nata , suna tafe tana sake karfafawa yakaka guiwa ganin yadda duk ta bi ta damu da tafiyar da zata yi , har zuwa bakin babban titi inda ta samu "mai adai-daita ", ta shiga tare da yin bankwana da yakaka !

Akan hanyar ta ta komawa gida tayi zurfi cikin tunanin ƴar ƙanƙanuwar duniyar ta ,wacce babu kome cikin ta sai tarin ƙalubale , mutanen duniya tausayi yayi ƙaranci a zuciyar su , son kan su tare da son dukiya sun makantar da su wurin duban na ƙarƙashin su da ƙyautayi da kyautatawa , kaɗai suna duban na ƙasa da su ne idan wata buƙata tasu ta tashi wanda suke buƙatar wannan ya kawar musu da ita ,

Da ƙarewar kuɗin hannun ta da tsayuwar rayuwar yancin da ta fara dai-dai suka zo domin tun lokacin da madam saly ta fahimci fa yanzu ta koma faƙiriyar ta kuma ta daina ganin gilmawar mutumin da ya tsaya mata tare da jin yayyafin nerar da yake yi mata , ita ma taci burki daga duk wani mutunci da lallaɓawar da take yiwa yaks , ta koma karta mata walakanci tare da bautar da ita ," ah toh me zata jira ? Ai kawai ungulu ta koma gidan ta na tsamiya , jaki ya tai gidan uban sa !

Ita ba gallazawar bautar aikin yafi damun ta ba illa yadda ƙarfi da yaji madam saly ta fara kai ta gaban ƴan iska tana tallar ta , ita baza ta jure hakan ba , bayan bature kam silum bata jin zata iya yadda da wani ɗa namiji har suyi abun da suke yi tare da shi ,  cikin su wanene mai kamannin sa ? Mai tsaftar sa ? Mai wayewar sa ? Mai gayun sa ? Mai irin ƙamshin sa ? Babu ! Idan kuwa haka ne ita baza ta yadda da kowanne ƙaton ɗan iska ba bata son su !

Zata jure kowanne irin aikin bauta da wahala , amma ban da harkar taimako ta wannan sigar , bature kam silum kaɗai yake da wannan ƙimar a gurin ta , zata zauna zaman jiran sa har ranar da zai dawo gare ta !

Da wannan tunanin ta ƙaraso shagon "fashe mai shayi ! Tace a fasa mata ƙwayaye shidda a soya su da indomi manya biyu , a haɗa mata shayi da madarar ɗari bonbita na hansin ! Ta miƙa kuɗin aka bata ƴan chanjin ta .

Aka sarrafa mata aka zuba a leda ta ƙarba , Shagon gefen sa ta wuce ta sayi lemon kwalba na pepsi mai sanyi ,

Ran ta ƙwal ta dawo cikin gidan kai tsaye ta wuce cikin ɗakin su falmata , a zaune ta tarar da ita , ta ajiye kayan hannun ta gami da ficewa taje ta wanko kofuna biyu da faranti ɗaya ta zo ta juye musu ,
      Falmata matso muci!

Lomar yakaka ta ɗaya ta biyu ta zare hannun ta daga cikin abincin sakamakon ji da tayi zuciyar ta ta wani hautsina ta yamutsa kamar zata fito ta baki , nan take tsinkakken miyau ya taru a bakin ta ," ta matsa gefe tana jan numfashi .

Jikin ta har rawa yake ta balle murfin pepsi da haƙorin ta ta kafa kai tana kwankwaɗa , ba dire ba sai da ta shanye ,"

Sai dai me wani irin ƙugi da cikin ta yayi falmata da kan ta ta jiyo , kafin ta ankara wani kakkarfan amai ya taho mata , nan ta dunga kwarara shi a ɗakin daga bakin kofa , kaf abincin da ta ci tun daga na jiya da dare da bai kai ga narkewa ba har zuwa ƴar indomi ɗin yanzu sai da ta amayo su , amai har ta hanci , ga hawaye da yake ta tsiyaya a idanun ta , yunƙurin aman ta har kofar rumfar su ana jiyo sautin sa ,' har ta koma sai kakaru bata amayo komai sai koren yawu ,"

Falmata ta gigice da ya sa ta fatali da kofunan shayin nasu tare da bi ta cikin farantin indomi ta ɓarar da sauran , cewa take
   Yakaka yakaka yakaka , meye ya same ki ? Meye ne ? Baki da lafiya ne daman ? Me kika ci kike amai ? Da lalube ta ruƙo yakakar zuwa jikin ta bayan tayi zaune dirshan cikin aman da yakakar tayi ,

    Rashin amsa mata da yakaka tayi wacce take ta yunkurin amai har muryar ta ta shige ciki ya sa falmata fashewa da kuka tare da fara kwala ƙiran neman agaji ,' ihu take tana neman taimako

    Daga bakin maƙwarari inda hema da larki suke wankin dawa suna jin su duk yunƙurin aman da yakaka take sun ji sarai sun kuma riga sun yi hasashen abun da ka iya sanya ta aman dan haka suka yi biris , ! Yo ina ruwan su ? Sun ga ire iren ta yafi sau shurin masaƙi , '
   
Rabu da shegiyar yarinya , ba dai ita tace bariki zata yi wa shigar sojan badaskare ba ? Sama ta ka ba tare da ta ɗau darasi ba , ai kuwa zata ɗanɗani kuɗar ta , wannan somin taɓi ne daga cikin illolin faɗawa bariki ba tare da an nemi ilmin sa ba ," cewar hema

    ihun da ya yawaita ya farkar da madam saly daga baccin tofon girar da take shaƙa a gigice ta bazamo kan ta babu ko ɗan kwali guiguyayyar ƙeyar ta da sanƙon ta sai ɗaukar ido suke a hasken ranar da ta fara ɗagowa , " cewa take
       Wace masifar ce ta faru da farar safiyar ne ? Waye ya mutu ? Waye ya sha azaba ? Ake faman kururuwa haka ?

   Kai tsaye ta nufi ɗakin su hema inda take jiyo tashin ihun falmata ,"

Turus ta jaa ta tsaya ," yawata idanun ta tayi cikin ɗakin tana ƙanƙan da ido kafin ta lailayo wata ƙazamtatciyar ashariya ta watso ," ta ɗora da
        Na shiga uku na lalace ni salaha dan uban uban ku yakS me nake gani haka ? Gasar amai kuke koh me ?wace iriyar shegiyar ƙazamta ce wannan irin taku ta ƴaƴan ƙauye kuke gwada min haka a cikin gida ? Tab toh da sakel wallahi baza ku korar min kostomomi ba , yo wannan ai idan ɗaya daga cikin kostomomi na suka ga wannan iskancin ƙazantar da kuke babu ni babu ƙara ganin wani ya zo sayan ruwa ," dan babu mai yadda ya ci abun da kazamtattu irin ku suka taɓa ,!

    Wata irin damuƙa tayi wa kafaɗar yakaka ba tare da ta kula da halin galabaita da take ciki ba , ta hankaɗo su waje tare da falmata wacce ta maƙalƙale jikin yakakar ," suka tafi suka faɗi tare nan yakaka ta ƙarasa bajewa a ƙasa cikin halin rashin sanin inda take ,

Shegiya tsinanna yo wani ɗan iskan ya aike ki kije ki maƙalo ɗan tayi a mahaifar ki ? Ai ni daman kallon ki kawai nake ina jiran ranar da cikin zai baiyana kan sa , ko ta arziƙi ko ta tsiya , amma tun tuni na farga da shi  , shegiya marar sa'a daga fara bariki har kin ɗauko ciki , to kar ki ji da wai ni bana rainon  ƴaƴan shegu a cikin gidana dan haka ku san inda dare yayi muku , arziƙi nake nema ba tsiya ba baza ki raɓe ni da shegen abun da yake cikin ki ku maƙalamin asara da rashin sa'a ba ," yo ƴaƴan halas ɗin ma wasun su amfanin me suke tsinanawa kan su da iyayen su idan ban da masifa ? Haure kafafun yakakar tayi , idan kin gama watangaririyar ki a ƙasa sai ki tashi ku hau shiri , ban ji zan iya ba rainon ɗan shege ! ki bar ni naji da kaina !

Wani irin bugu zuciyar falmata take da kalaman madam saly suke sauƙa a kunnuwan ta , wai me take cewa ?waye yake da cikin shege ? Ɗan shege waye zai haife shi ? ta san ɗan shege sarai domin kuwa akwai wata ƴar makotan su da ta taɓa yi , iyayen ta suka kore ta , kowa a unguwar su ya tsane ta , jama'ah suka ta yin Allah wadarai da ita ,  mamar ta ta dunga kuka har ta daina fita layi , bata san ma'anar cikin shegen ba sai da ranar ta nacewa maman su da tambayar ma'anar kalmar,"a taƙaice ta bata amsa haihuwar yaro ba tare da anyi aure ba shine cikin shege," har garin su ya watse ba'a san inda wannan yarinyar take ba , tabbas cikin shege abu ne marar kyau matuƙa , madam saly tana nufin irin shi yakaka tayi ?

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yakaka ta jaa wani numfashi tare da sake yin wani yunƙurin aman  ,"

    Wani sabon ihu ta sake saki ,"

   Dan Allah ku taimaka min kar yaya ta ta mutu dan Allah ku taimaka mana ," yakaka ki min magana dan Allah ki daina shiru , ki tashi yakaka ki tashi ,
     Larki ce ta bar abun da take gami da nufar bakin fanfo ta taro ruwa a wani kwanon silver gami da sanya wani bokitin a bakin fanfon , a kaikaice ta ɗago yakaka wacce take ta sakin numfashi'ita ba sumammiya ba ita kuma bata motsin kirki ," ta kafa mata kwanan a baki ,

     Bata wani shaa na kirki ba ta cigaba da yunƙurin aman,"

    Aifa lalle kin gamu da wahala , gwara ma idan zaki tashi ki ta shi domin a gidan nan babu wanda zai damu ko mutuwa zaki yi a nan a yashe sai dai a tsallake ki a wuce ,  masu mutuncin ciki sune zasu jaa ki gefe a samo mai miki salla a je a turbuɗe ki , dan haka ma gwara ki bar lamɓo ciki ba kan ki aka fara ba , laulayi kuma dole ne tun da har kika iya zuwa kika kai kan ki aka maƙala miki maƙalalliya, kin dai ji abun da ,"saly fara," tace ki fara shirin bar mata gida ,"
     Juye mata ruwan bokitin da ta ɗauko tayi akan ta baki ɗaya ta jiƙa su sharkaf har da falmata wacce take ƙwaƙume da yakakar , daga ita har yakaka ba sauraran bayanin bakin larki suke ba ,"

wacce ita ce ɗaya da ta kula su , ta zo kan su duk da cikin walakanci take musu Abun da ita a wurin ta taimako ne !
   Nan ta dangwarar da bokitin gefen su ta wuce bakin aikin ta tana cewa ,"
    Sai ke kuma ki tashi ki je ki wanke ɗakin da kuka gama chaƙuɗa shi da kazantar , sakarkarun yara ƙyauyawa !

Sanyin ruwan ya taimaka wurin farfaɗo da yakaka daga halin gigitar da ta shiga ," da taimakon falmata ta miƙe zaune ," yadda kan ta yake juyawa tare da wani irin bala'in ciwo ya sa ta kama kan nata da hannu biyu,"

  Falmata kaina zai fashe ,'!

Sannu yakaka ki tashi na kai ki ɗaki ki kwanta ,'

  A wajen kwanciyar  ta,  ta taimakawa yakaka ta kwanta , fita tayi ta lalubi bokitin da larki ta ajiye ta ɗauka taje ta taro ruwa a cikin sa ta komo ɗakin ,"ita bata san inda tsintsiya yake ba a gidan , dan haka ta laluba ta tattara kofunan da farantin ta haɗa su wuri ɗaya , kasancewar ɗakin daman Ledar sa ta riga ta ratattake ta zama gutsirarra ,ta wurin da suke kwanciyar , daga tsakiyar sa zuwa bakin kofar dandaryar siminti ne , sai kawai ta kwarar da ruwan ta wuraren da take jin lema-lema , ta sa takalman ta biyu ta kwarfe ruwan ta tura shi wajen kofar ,'

Duk abun da take yakaka wacce idanun ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login