Showing 114001 words to 117000 words out of 411050 words

Chapter 39 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14381

na kare martabar ta ko da anan gaba ya aure ta , domin a halin yanzu kowa ya san ba shi da mata , to kuma duk sauran likitocin da zai iya haɗa yakaka da su , abokanen aikin sa ne da suka riga suka san juna sosai ,ya kai ta wurin su a zuwan matsayin me take a gare shi ?

Bai son a kodayaushe ya dunga yin ƙarya dan haka ya fi son ya kaucewa duk wani abun da zai sa shi yayi ƙaryar ,"

  Sai da ya bari rahima ta zo misalin karfe huɗu da rabi , ta hau sama ofishin sa tare da ajiye masa na shi abincin , nan yake sanar da ita zata Zauna tare da falmata , shi da yakaka zasu je wani waje su dawo ,"

Tare suka shiga ward ɗin inda suka tarar da su suna ƴar hirar su , babu laifi cikin sati guda falmata ta ji sauki sosai saboda kulawar magunguna masu kyau da take samu zuwa abinci mai inganci , uwa uba kwanciyar hankalin da ta samu , yini take a kan gado iskar fanka tana kaɗa ta , ga ta ga yakakar ta a gefen ta , wanda hakan shi yafi kome sanya ta farin ciki ,
 
   Cikin fara'ar da jin muryar su ya sanya ta take gaishe da doctor hamza da zuwa yanzu take matuƙar girmama shi tare da ganin ƙimar sa har ma take jin sa a matsayin wani jigo cikin rayuwar su ita da yakaka ,

Shima faram-faram ya amsa mata yana mai sake tambayar ta yanayin jikin nata , kafin ya maida duban sa ga yakaka wacce take zaune bisa kujerar gaban gadon , "suna gaisawa ita da rahima wacce suka yi sabo da juna cikin ƴan kwanakin ,"

Duban ta ta mayar kan doctor hamza tana mai gaishe shi , cikin ƴar siririyar muryar ta ,
   Fuskar sa a sake ya amsa mata yana mai kallon fuskar ta da take fayau babu ko ɗigon kwalliya sai ƴan siraran shunkuran ta "zane" da suke tarwai akan farar fuskar ta ,

    Fatima zamu je na kai yayar ki wani wuri baza mu daɗe ba zamu dawo ga rahima nan zata kula da ke kafin dawowar mu kin ji koh?
   Toh yaya dakta sai kun dawo ! Yakaka sai kun dawo !

Zo mu tafi ,"
  yace da ita yana mai fara taku ,"

    Tiris ! tayi akan kujerar , ina kuma za su ? ? Ita fa sam bata son kaɗaicewa da shi , duk ya bi ya ishe ta da kallo ga warin wannan ƙaƙƙarfan turaren nasa da ba so take yi ba ,"

    Kallon fuskar rahima tayi wacce ita ma ɗin ita take kallo cikin nazari , dan haka ta miƙe a sanyaye gami da yi musu sallama bayan ta jaddadawa falmata akan yanzu zata dawo !

A motar sa suka fita a asibitin , duk da cewa har zuwa yanzu bai faɗa mata inda zasu ba ," sai da ya hau titi ɗoɗar tukun ya juyo ga kallon sa kan ta da ita kuma ta juya fuskar ta ga kallon titi ,"

   Ƴar kwantatciyar sumar da take gefen kunnuwan ta zuwa gaban goshin ta da tayi luf-luf yayi wa kallon daƙiƙai kafin ya maida kallon sa ga titin gami da yin gyaran murya ,"
      
  Asibiti zan kai ki a auna ki tare da duba lafiyar abun da yake cikin ki , dan haka ina son sanin sunan ki mai kyau , domin ayi amfani da shi wurin buɗe miki file ,"

     A hankali ta juyo da ganin ta kan shi ,"
      Cikin ran ta tana jin daɗin yau karo na farko bayan ita da falmata wani ɗan adam ya nuna kulawar sa akan cikin jikin ta har ma zai kai a duba lafiyar abun da yake cikin , "

    Sai dai tambayar sa ta ƙarshe ta bata mamaki daman duk zaman su bai taɓa sanin sunan ta ba ???

Babu shakka ita bata taɓa ji ya kira sunan ta ba , ko magana zai mata kawai yana jefa maganar sa ne a saitin ta kai tsaye ba tare da ya kama sunan ta ba ," amma ai yana ji koyaushe falmata tana kama sunan ta a gaban shi , sai dai idan wani walakanci ne hakan ," zai ce bai san sunan ta ba .

   Kamar ya san tunanin da take
   Ba tare da ya dube ta ba yace ,"
   Sunan ki mai kyau nace ,"wannan sunan da ake kiran ki da shi ba suna mai kyau bane dole akwai ainahin sunan ki ,
   Bani da wani suna bayan wanda ake kira na da shi ,"
   Ta bashi amsa ƙasa-ƙasa , a ran ta  Kuwa tana jin haushin kalmomin sa ya za'a yi yace sunan ta bashi da kyau ??

  Ba wanda ya sake cewa ƙala har suka ƙaraso ɗan ƙawatatcen asibitin mai zaman kan sa da yake cikin unguwar G.R.A ,

Jerowa suka yi suna tafe tamkar sabbin ma'aurata , ta wutsiyar ido ya kalle ta tana sanye ne da wata atamfa ruwan ɗorawa da aka yiwa dinkin doguwar riga wacce ta buɗe daga ƙasa ,  ɗaya daga cikin kayan da rahima ta ba su ne ," nan ya ga yadda ɗankwalin kan ta yayi baya sosai har ya bayyana lallausar sumar da take gaban kan ta , gyalen ta da ta rufu da shi daga kafaɗar ta iskar juyin yanayi da ake na ta kaɗa shi ,"
      gani yayi ta yi masa kyau ba kaɗan ba ,"

Sam baza'a ce mace mai ciki bace , domin idan ban da cikar da ta sake yi tayi ƴar ƙiba kaɗan tare da ƙarin haske , babu wani alamun ciki , cikin bai bayyana a sarari ba ,"
     
      Ki gyara ɗan kwalin ki , kuma ki rufa gyalen zuwa kan ki ,"
   Ta tsinkayi muryar shi yana bata umarni ,"

ba tare da ta ce uffan ba tayi yadda yace lokacin da suke ƙarasawa cikin ainahin asibitin ,

Ba tare da ɗaukar lokaci ba ya shige gaba ya kammala kome da ake yi a dokar asibitin kafin a ga likita , wanda kuɗaɗe ne tsababa saboda asibitin na manya ne ,

  Wurin bada sunan ta ne ya so shiga ruɗani kafin lokacin da zuciyar sa ta yanke masa shawarar abun da ya kamata  ,"

Aka yi musu jagora zuwa wajen ainahin babban likitan mata da yakasance shine mamallakin asibitin baki ɗaya ,"

  Nan ya tare su da fara'a duk da cewa ba wai ya san doctor hamza bane amma yanayin sa ya bayyana masa wayewar sa tare da ilmin da ya hango tare da shi , "
      Bayan bayanin da doctor hamza yayi masa akan a duba lafiyar uwar da abun da yake cikin ta tare da son sanin ranar da zata iya kasancewa ranar haihuwar ta ,"
   Likitan ya fara aikin sa cikin gwanancewa, nan ya fara da ɗaukar jinin ta domin yin gwaje gwaje , ya kuma bata wata ƴar roba yace ta kawo fitsarin ta tare da ƙiran ɗaya daga cikin nurses akan ta gwada mata banɗaki  , bayan ta dawo yayi mata awun blood pressure,  ya ga jinin ta dai-dai ne , sai yayi umarni da ta hau wani ɗan gadon duba marasa lafiya da yake gefe guda cikin ofishin domin yayi mata scanning ,"

Da jaan ƙafa ta ƙarasa bakin gadon ta hau ta zauna ,"
   Kallon ta likitan yayi lokacin da yake jona na'urar da jikin babban tv da yake kafe a gefe ,"
    Amarya gyarawa zaki yi ki kwanta mai kyau ki miƙe kafafun ki ,"
   A ɗarare tayi yadda ya umarce ta tana mai sake gyara rigar jikin ta da kyau ,"
   Da ido doctor ya yi wa hamza alama akan ya mata bayani yadda zata gane ,"
       Ki ɗaga rigar ki , ki buɗe cikin ki hoton jariri za'a yi ta haka za'a gane lafiyar sa ," ya furta hakan yana mai maida ganin sa ga fuskar wayar sa ,"
   Hoton jariri??
Ai kuwa zata so ta ga hoton abun da yake cikin nata ," wataƙila yayi kama sosai da baban sa ? ," tuno da hakan da tayi ya sa wani siririn murmushi ya bayyana kan fuskar ta ,
   ta tashi tsaye ta tattara doguwar rigar ta , dogon wondon da ta sa ta ciki ya bayyana ,"
     Cikin nutsuwa ya fara mata scanning ɗin , yayin da shi da dakta hamza suka maida hankalin su baki ɗaya ga fuskar tv lokacin da ƴar jaririyar da take cikin mahaifiyar ta ta bayyana tana ta hidimar ta hankali kwance,  a yau tana da sati goma sha tara da kwanaki biyar , "komen ta yana lafiya ƙalau a yanayin da ya dace ,hasashen ranar haihuwar ta ya nuna biyar ga watan goma ," nan da watanni huɗu da ƴan kwanaki kenan ," 
     Wow what a beautiful busy baby girl , ? See those wee fingers are very close to the mouth,!
    Doctor ya karasa zancen da ƴar dariya a fuskar sa yana mai maida duban sa ga fuskar doctor hamza ,"wanda shima ya ga wutsilliyar da ƴar jaririyar take da hannuwan ta,"wani abu yaji ya taɓa ran sa , fuskar sa kadaran-kadahan yace ,"

   Yeah the baby looking super comfy and growing perfectly ,

ya furta hakan yana mai jefa kallon sa ga yakaka wacce ko kalma guda bata gane ba cikin ƴar gajeruwar mahawar da suka yi , sai faman raba ido take tana daga kwance ,

Congratulations once again Mr and Mrs Hamza Mustapha Dilmari

Likitan ya furta haka tare da miƙawa doctor hamza hannu suka yi musabaha , dai-dai lokacin da suka tashi domin tafiya , bayan da likitan ya kammala shigar da duk wasu bayanan da ya tattara akan yakaka da abun da yaje cikin ta zuwa cikin computer Ya aika da shi ainahin wurin wanda zasu cigaba da yi mata anti-natal , bayan ya duba duk wasu gwaje-gwajen da ya yi mata , yaga bata tare da wata babbar matsala ,"  nan ya miƙa musu takaddar magungunan da ya kamata ta dunga sha tare da wani ɗan kati wanda da shi zata dunga amfani wurin zuwa awo ,"

    Har sun yi taku biyu , yakaka ta tsaya tare da juyowa ta fuskanci likitan , bayan ta sauke idanun ta ƙasa tace ,"
     Likita toh ina hoton jaririn da ka ɗauka ?
           Ta furta hakan tana mai jin ƙwalla na cika idanun ta domin ta so ƙwarai ta ga jaririn , sai kuma ta ga har zasu tafi bata ga hoton na sa ba ,
   Tiris likitan yayi yana duban ta , domin shi a idanun sa bai ga alamun ƙyauyanci har haka a tare da ita ba ,

   Wani takaici ne ya rufe hamza , shi dai gidadancin yakaka na ci masa tuwo a ƙwarya ,"
         Lokacin da ake hoton ina hankalin ki yake ?? Wuce mu tafi gaba idan mun sake zuwa kya ga hoton , ya furta hakan yana mai kokarin danne ɓacin ran sa akan tsantsar son cikin da yake hangowa cikin idanun yakaka ,
     Waye uban cikin ?tabbas yawan soyayyar ɗa wurin uwar sa tana da alaƙa da son da take yiwa mahaifin sa ,"

   Bayan sun kama hanyar komawa gida yakaka ta katse shirun da suka yi da faɗin ,"
   Inaso na je bakin kasuwa na ɗauko kayan mu da suke shagon da muke kwana a bakin sa ,"
    Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba saboda zuciyar sa da take ta kai kawo akan son sanin ko yarinyar tana da wata alaƙa da uban cikin jikin ta ,?  ko zaton sa ba gaskiya bane , ? ko dai da amincewar ta ta bada kan ta ga wani ƙato ??
     Babu buƙatar ki ɗauko kayan , ki bar su kawai zan saya muku wasu nan gaba !
     Ta bar kayan ? Yana nufin rabuwar ta da duk wani abu da ya shafi bature kam silum ɗin ta ,!' bata jin zata iya ,'domin kome da ya shafe sa abun so da ƙauna ne a wurin ta , baya ga haka kuma ba ƙaramin taimakawa  suke wurin ɗebe mata kewar sa da ke cin zuciyar ta a kullum ba ,

  Ni dai Dan Allah ka kai ni na ɗauko , akwai abu masu muhimmanci a cikin jaka ta,"

    Duban sa ya mayar kan ta
  Abu masu muhimanci , meye su ?

Agogon sa da hoton sa ta amsa masa kai tsaye babu ƙunbiya-ƙunbiya ,!

   Gangarawa yayi gefen titi ya tsaya , tare da maida hankalin sa baki ɗaya kan ta ,"
    Agogo da hoton wa ??
  Ya jefa mata tambayar yana mai tsare ta da idanu ,"
   Ɗago da kan ta tayi tana kallon tsakiyar idanun sa , ƙwarai yayi mata kwarjini kuma tun farko shi ɗin bai taɓa zuwa mata da sigar wasa ba , uwa uba zuwa yanzu ta san cewa abun da suka aikata da bature kam silum har ta kai ga samun ciki ba abu ne mai kyau ba , dan haka ya zama dole ta koyi boye ainahin yadda kome ya faru da dangantakar ta da shi ,"

   Da inda-inda tace masa
Hoton baa-baban mu ne da agogon sa ,
    Tsai yayi yana kallon cikin ƙwarar idanun ta a koƙarin sa na son gano gaskiyar ta ,"
   Dan Allah ka kai ni
Ta sake yi masa magiya tana marairaicewa,"
   Ɗauke kan sa yayi tare da tada motar , sashi guda na ran sa na tabbatar masa da bata da wayo da wayewar kan da zata iya masa ƙarya , sam alamun ta bai yi kama da na wacce zata iya lanƙwasa zance ta sauya masa launi ba ,"

A dai-dai ƙofar shagon ya tsaida motar ƙarkashin umarnin ta da tace masa nan ne shagon ,"

Ba ƙaramin farin ciki abuwar mai shago yayi ba da ganin yakaka cikin ƙoshin lafiya , ya ɗora da tambayar ta falmata , domin labari ya isar masa na abun da ya same ta , ya kuma ga shaidar jini a bakin shagon sa washegarin ranar da abun ya faru ,

Ya shiga dumuwa sosai ta yadda yake ganin har da rashin taimakawar sa ya sa suka afkama masifa ," ga yadda suka samu labari falmata ta riga ta mutu , hakan ne ma ya sa bai ko je neman su asibiti ba ,"

Bayan gaisuwa tare da jajantawa yakaka ta buƙaci ya bata jakar baccon su , nan kuwa ya fiddo mata da su , suna nan yadda suka bar su , " a cewar sa yayi niyyar cigaba da ajiyer su domin ya san zata dawo ɗauka , nan dai suka rabu suna mutunta juna ,!

   Daga yanzu baza ku sake dawowa bakin kasuwa da sunan zaman kan ku ba ," idan ƙanwar ki ta samu sauƙi zan tafi da ku gidan mu ku zauna tare da su rahima , har zuwa ....
      sai kuma yayi shiru gami da juyowa ya dube ta , ta nutsu tana saurarar sa ,"
    maida duban sa yayi ga tukin kafin ya jefa mata tambaya
    ko baza ku bini gidan mu ?

   da sauri ta ɗago kan ta , ita kuwa da daman kullum da tunanin inda zasu samu mafaka bayan barin su asibitin take kwana take tashi ,Ta yaya zata ce baza su bi sa ba ? To ina zasu da ya wuce inda zai kai su ?? Babu !

     zamu bika yaya dakta , kuma mun gode Allah ya saka da alheri ya baka abun da kake so duniya da lahira , yadda ka taimaka mana kai ma Allah ya ɗaukaka ka ,!

  sosai kalaman ta suka burge shi tare da dadaɗa masa rai , a yadda yake mata ganin bagidajiya bai taɓa zaton ta iya kalamai masu nutsuwa haka ba ,"
   da murmushi a fuskar sa ya amsa a bayyane da ,
          Ameen Nurii .

Bayan sati biyu

Falmata ta warke ras kamar ba ita ake sallama daga gadon asibiti a yau ɗin ba , tayi ƴar ƙiba mul-mul , fatar ta mai ɗan haske ta sake washewa , fes da ita cikin jar doguwar rigar da yaya dakta ya saya mata , kafafun ta sanye cikin sabon farin silafa ɗan madina , ta ɗora ɗan bakin hijabi akan ta ,"

Duk wani abun da ake kafin a ba wa mutum sallama daga gadon asibiti doctor hamza ya gama yi inda likitocin ta suka buƙaci ta dawo bayan sati shidda su sake duba ta , " 

Rahima ita ta taya su suka harhaɗa ƴan kayan su domin tafiya da su gida , sai dai da zuwan doctor hamza yace duk su bada bokitaye zuwa buta tabarma da sauran tarkacen kayan ciye-ciyen da basu riga sun cinye ba ga marasa lafiyan da ba'a riga an sallame su ba masu ƙaramin ƙarfi ,

daga su sai ɗan ƙaramin akwatin da rahima ta basu wanda suka juye duk ƴan kayan su a ciki suka fito ," zuwa jikin motar sa da yace su tsumaye shi a wurin , bai ɗauki lokaci ba yazo ya buɗe motar yayi musu iznin shiga , yakaka da falmata suna mazaunin baya yayin da ƙanwar sa take daga gefen sa , sannan ya tada motar suna masu barin harabar asibitin ,"

Kai tsaye ya wuce da su shagon telan da yake yiwa rahima ɗinkunan ta da shi doctor hamza ya saya atamfofi , yadiddika da ƴan lesuka , ya bata yace ta kaiwa telan ta ya ɗinkewa su yakaka , kowaccen su shiga takwas-takwas ,"
     Telan ne ya buƙaci a kawo su

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login