Showing 246001 words to 249000 words out of 411050 words

Chapter 83 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14338



"Papa mu tafi wajen Mama yanzu ,

"zamu tafi idan kin ida cin abincin ki kin ji kou ?

Shiru tayi tana kallon sa ba tare da ta buɗe baki ta karɓi abincin da yake miƙa mata ba ,

Gajiya yayi da riƙe chokalin , ya ajiye gami da miƙewa yana jin yadda zuciyar sa ke cike da kewar ta , baki ɗayan hankalin sa na kan ta ,

Ya daɗe a zaune yana mata addu'a akan sallayar da ya idar da Sallar Azahar ,

Shafa kan Mama yayi wacce tayi bacci a gefen shinfiɗar sallar sa ,

Cikin ran sa yana aiyana irin yawan kewar Mamar ta da tayi wanda ya duƙusar da walwalarta

Ɗaukar ta yayi ya kaita ɗaki ya kwantar tare da rufe ta da bargo , ya zauna daga bakin gadon ,

Wayar sa ya ɗauka ya latsa ƙiran layin  Tafeeda da ya yi ƙiran sa a ɗazu lokacin da ake yiwa Falmata aiki , bai samu damar ɗaukar kiran nasa ba

Bayan sun gaisa , tare da Tambayar lafiyar juna Youssouf ya ɗora da tambayar sa Leila matar sa da ɗan su Imran , ?

" duk lafiya suke ɗan'ouwa , Yarima kana ji na kou ?

"ina jin ka da kyau ɗan'ouwa ,

" Yarima kou kana da labarin mutanen da ka baro shekarun baya a Nigeria ?

Da ace Tafeeda na gaban shi a lokacin da zai iya hango firgicin dake zane ɓaro-ɓaro bisa fuskar sa ,

"waɗanne mutane Tafeeda ke magana kan su ?

Tambayar da zuciyar sa ke yi ya bayyana kan harshen sa ,

Jim! Tafeeda ya yi yana nazartar firgicin da yake iya jiyowa daga Muryar Youssouf ɗin ,

"wannan ɗiya da tsautsayi yassa ta samu a duniya , nace kou ka sake waiwayar ta ? Tafiya ta kama ni zouwa Nigeria shine nake biɗar izni kan na tai na gan ta ko da ba kai tsaye ba ne na....

Cikin sauri Youssouf ya katse sa muryar sa a ɗan sama kaɗan ,

"Tafeeda ban ma izni ba , batun wannan ɗiya ai mun jima da ajje shi ghefe kou , ka kyale kawai wani lokaci idan Allah ya ida nufi ni naje da kaina na duba ta ,

  Ajiyar zuci Tafeeda yayi ,

"tou babu kome 'dan ouwa Allah shi gwada mouna lokacin da lafiya , Allah kouma shi ƙara rufa asiri ,

'Amin Amin 'dan ouwa ,

Shiru ya gifta tsakani sakamakon tunani mai zurfi da kowannen su ya faɗa ,

Babu shakka Tafeeda yana da wani dalili da ya sanya shi bijiro masa da zance Mama a dai-dai wannan lokacin da tsawon shekaru wajen shidda bai taɓa tambayar sa game da lamarin ta ba sai fa yau .

a daddafe ya iya kaiwa bayan la'asar a gida , ya sake shirya Mama da ita ma duk ta damu da son su koma wajen Falmata ,

Ko da ya isa asibitin har lau bai samu damar shiga ɗakin da Falmatan take ba .

Haƙuri likitar da take da Alhakin kula da ita ta bashi , akan ba zai yiwu ya shiga inda take a yau ba sai ko zuwa gobe da yammaci

Haka suka ƙaraci zama daga gefen ɗakin da take ciki har duhu ya fara shiga, dan dolen sa ya miƙe da Mama ya ƙarasa jikin ƙofar ɗakin da take ,

Ya yi mata addu'a , kafin su bar asibitin zuwa gida ,

Daren ranar bai zo masa da sauƙi ba , baki ɗaya sai juye-juye yake yi ya gaza yin baccin kirki , bai san da haka ƙaunar ta ta rarake masa zuciya ba sai da ya gaza bacci saboda damuwa da son sanin halin da take ci gami da kewar ta mai tarin yawa ,

Abunda bai taɓa jin kwatankwacin sa kan kowacce ɗiya mace ba , ko da kuwa Maimounatu ,

Salon ƙaunar da yake yiwa Fatima daban ne da yake tafe da wani irin yanayi mai tasiri sossai a gare shi ,

Sai gefen asuba bacci ya ɗauke shi cike da mafarkai iri-iri , da har ya sanya shi makara wajen yin sallar asubahi .

Tara na safe suka samu isa asibitin , inda kuma cikin sa'a ya samu damar shiga ɗakin da Falmatan take ƙarƙashin jagorancin likitan ta ,

Da takun ƙafar su ta san da shigowar su ɗakin da take da ita ma ta kwana cikin kewar su duk kuwa da zogi da idon ke yi mata lokaci zuwa lokaci , amma ta fi damuwa da ta san a wanne hali Mama da Baban ta suke ?

"Mama , Maama

Suka haɗa baki wajen ƙiran sunan junan su ita da Mama wacce da shigowar ta ɗakin ta hango Falmata , ta tafi da gudun ta ,

Ɗago ta Falmata tayi ta rungume ta a jikin ta , tana jin yadda sanyin ƙaunar ta ke ratsa zuciyar ta , babu shakka ƙaunar Mama magani ce ga ta ta zuciyar , 

Da murmushin samun nutsuwa ya ƙaraso bakin gadon ,

"Fatima yaya jikin naki ? Babu inda ke miki ciwo kou ? Baki cikin damuwa kouma ?

Waigawa tayi sashin da take jin tashin muryar sa ,

"Baban Mama ina kwana ? Yaya Mama ta kwana ? Bata yi ciwo ba ko ? 

Ɗan tsayirtawa tayi , kafin ta ɗora da cewa

"bana jin damuwa ko ciwo mai tsanani , amma ina son a warware min idon nawa wannan abunda suka rufe min ido da shi yana damuna ,

"likitan da duk yana jin abunda take faɗi tare da taimakon na'urar kunnen sa ,

Ya matsa yana sake rarrashin ta tare da yiwa Youssouf bayani kan cewa kafin su warware mata idon zuwa gobe anfi buƙatar idon ya zauna a rufe haka , har sai bayan awanni arba'in ,

A cikin ɗakin suka wuni tare ,  sau biyu Gimbiya maimounatu na ƙiran wayar sa , ya gaza ɗaukar ƙiran . 

Bai san dalili ba amma can cikin ran sa ya gujewa yin hira da maimounatu ne saboda gudun ɓacin ran Falmata .

Washegari kamar yadda suka sharɗanta , awanni arba'in da huɗu da 'yan mintoci ,

Misalin ƙarfe goma na safe likitocin suka yi da'ira , a kan ta ,

Babba daga cikin su wanda kuma shine ainahin wanda ya yi mata aikin , shi ya warware mata idon ,

Bayan sassauta haske tare da sauya launin hasken zuwa marar kaifi , cike da fatan nasara likitan ya umarci Falmata da ta buɗe idanun ta ,

Babu karsashi ta fara wara idanun da suka mata wani irin nawi , hasken da ta ji kamar ya chaki idon shi yasa ta saurin runtse idanun ta kai tafukan ta biyu ta rufe fuskar ta ,

Cikin sauri likitar da ke gefen ta ta sauke hannunwan nata ,

Rarrashi da kalaman ƙarfafawa suka shiga yi mata cikin kwantar da murya , suna umartar ta da ta buɗe idon ta zata ga duniya ,

Sannu kan hankali ta ware idanun da suke rawa kaɗan-kaɗan , baƙon yanayi ne ya ziyarci ƙwaƙwalwa zuwa gangar jikin ta lokacin da raunanan jijiyoyin idanun ta suka fara ɗaukar jirkitattun hotuna suna aikawa da shi zuwa cikin ƙwaƙwalwarta da sauri ,

Wajen ya ɗauki shiru , likitocin suna ƙure ganin su akan ta da take gwale idon cike da burin son samun ƙarin ƙarfin ganin da tare kuma da son fahimtar abubuwan da take iya ganin hotunan su duru-duru , shin wannan shine hasken duniyar ? Haka kuma suffofin mutanen yake a zahiri ?

A sama ta tsinto muryoyin su lokacin da suka cigaba da yi mata magana , dusu-dusu take iya ganin kusantowar motsin wani abu kafin ta tsinkayi muryar likitan yana tambayar ta ko tana iya ganin alamun motsin sa ??

Bata amsa ba illa kan ta da ta gyaɗa ,

Hannu ya kai yana ɗaukar wani baƙin tabarau mai haɗe da 'yar na'ura na musamman wanda cikin awanni arba'in aka yi shi domin Falmata ,

Ya sanya mata a fuska tare da daidaita mata shi , ya miƙe tsaye da murmushi a fuskar sa cike da burin nasara , ya tambaye ta ko tana iya ganin sa ?

Zuba masa ido tayi tana iya ganin shatin sa fiye da ɗazu , suffar sa ta mutum ta bayyana duk da ba tarwai take iya gani sa ba ,

a hankali ta juya ƙwayar idanun ta zuwa kan kome da yake sararin wajen daki-daki take ƙure musu kallo , duk da ba sosai take ganin abubuwa ba ba kuma fahimtar su take yi ba ,

A hankali likitocin suka dare , tare da bada hanya ga Youssouf da Mama da babban likitan ya yi umarnin su shigo ,

Hannun sa yana riƙe da Mama suka shigo ,

Kamar koyaushe takun Mama ya fara isa ga dodon kunnen ta ,

Dan haka take ware ido cike da buri , burin da ada ta ɗauka ta haƙura da shi ,

'yar ƙaramar halittar da ke kusantota ta ɗorawa ido ,

Ko ba'a faɗa mata ba , ko da cewa bata taɓa ganin wata halitta da idanun ta ba , ta san wannan ita ce Mama ,

" Mama ,

Mama ta ƙira sunan ta dai-dai da ƙarasowar ta gaban ta ,

Hannuwanta biyu ta sanya ta ɗago Mama , da wani irin yanayi ta matso da fuskar Mama daf da tata bayan ta ɗaura ta a cinyar ta ,

Ƙure mata kallo take yi , cike da son ganin ta fiye da yadda take iya hango ta dusu-dusu a yanzu ,

Runtse ido tayi ta buɗe a hankali

'Mama
   Ta ƙira sunan ta, 

Dariya Mama tayi tana ɗora 'yan hannuwanta akan hannun Falmata da take tallafe da kumatun ta ,

Ta ga hasken haƙoran Mama da fuskar ta , a yanzu ta yadda da cewa ta samu waraka , irin ganin da take yi dusu-dusu shine ganin da ta haƙiƙance kowanne ɗan adam yana yi ,

Irin haske marar ƙarfin da take gani shi ta aminta da cewa shine hasken duniya , ita kuwa mai zata yi da ya wuce godiya ga Allah da ya nufe ta da samun waraka ?

rungume Mama tayi tana faɗin kalmar Alhamdulillah , Alhamdulillah babu ƙaƙƙautawa ,

Raf-Raf-Raf likitocin da suke wajen suka ɗau tafi , cike da bayyana farin cikin su na samun nasara kan aiki ,

Youssouf wanda farin cikin sa bazai misaltu ba ya tako zuwa gaban gadon Falmata ,

" Fatima
Ya ƙira sunan ta , da amon muryar da take cike da shauƙi da zumuɗi ,

cike da ƙwaɗayin son ganin Fuskar wannan ma'abocin Alheri a gare ta ta ɗago kan ta daga fuskar Mama da take ta son sake gani tamkar mai son haddace kamannin ta a ɗan tsakanin lokacin ,

Dariyar haƙoran sa ta fara cin karo da su , kafin hasken farar fuskar sa irin na Mama da ta fahimci basu kai sauran mutanen wajen haske ba , ta bayyana mata , 

Kafe shi tayi da ido tana burin ganin kamannin sa ko da kuwa ace shine abu na ƙarshe da zata iya samun nasarar gani kafin hasken da ta samu ya koma duhu da har yanzu ta gaza yadda a zahiri ne ba mafarki ba cewa idanun ta suna ganin duniyar da ta rayu tsawon lokaci a cikin ta ,

Irin riƙon da ta yiwa fuskar Mama shi ta masa , ta kai hannun ta kan sajen fuskar sa ta tallafo fuskar tana kallon sa da irin ganin da ya sawwaƙa a gare ta  ,

Dariya Youssouf ɗin ya cigaba da yi da haƙoran sa ganin yadda ta riƙe masa fuska ƙam-ƙam , kamar wanda zai ƙwace ya gudu , ko kuwa ya ɓace mata ,

Da ƴar dariyar mai tafe da amon da  ke bayyana tsantsar farin-cikin ta , ta kai goshin ta ta haɗa da nashi , tsinin hancin su na gugar na juna ,

"Baban Mama nagode , nagode nago...

  "Fatima ki godewa Allah da ya baki lafiya , ni ma shi nake godewa , da ya nufa aka cimma nasarar aiki ,

Zama yayi daga gefen ta a bakin gadon ,

Mama tana tsakiyar su ya sanya hannu sa ya kewaye su da shi ya rungumo su jikin sa , yana jin matsanancin farin-ciki na zagaya ruhin sa ,

Tamkar a ire-iren shuɗaɗɗun lokutan da suka wuce cikin rayuwar ta da Yakaka , sautin ta ya bijiro cikin tunanin ta tamkar a lokacin take furta mata ,

" Falmata na ina ji a jikina watarana za ki warke , za ki ganni kamar yadda nake ganin ki .

Hawaye masu ɗumi suka silmiyo ta ƙarƙashin gilashin idanun ta , kewa tare da ƙaunar ahalin ta suka bijiro mata , a sarari ta furta

" Allah ya jiƙan ku Baba , Mama , Yakaka,  Bakura da Baana ,

'Amin 

Youssouf ya amsa mata .

*****

Cike da tarin sabbin dokoki da sharaɗin ziyartar likita a duk bayan mako guda na tsawon watanni biyu ,

Suka samu sallama daga asibitin , tafiyar ƙafa suka yi zuwa gidan su , inda Falmata ta dunga bin titi da ganin ta marar ƙarfi ,

Murna fal cike da zuciyoyin su ita da Youssouf , kome ta hango shatin sa sai ta tambaye shi wannan abun menene shi ? Meye sunan sa ?

Shi kuma babu gajiyawa cikin jin daɗin tambayoyin da take masa yake bata amsa tare da faɗa mata sunayen abubuwan .

Ƙofar gidan Musa suka tsaya , farin cikin da zukatan su ke ciki ya tunbatsa so suke su yi ɗaukanin sa da wani , alhalin babu wani nasu makusanci tare da su , dan haka gidan Musa suka yada zango ,

Musa da Ramlat sun taya su murna sosai inda a ƙarshe har 'yar walima suka shirya musu nan cikin falon su,

Yana riƙe da hannunta suka shigo gida ,

Suna shiga tun kafin su zauna ta ce  shi ,

"Baban Mama ka ƙira Hajja a waya na faɗa mata na warke nima yanzu ina gani ,

Yana murmushi ya zaro wayar sa daga Aljihun sa ya shiga lalubar layin Hajja ,

Ya san dole tana neman wani makusanci nata wanda zata raba farin-cikin ta da shi ,

Nigeria

Tsawon satikan da suka biyo bayan Rayuwar Yakaka tayi su ne wajen ganin ta cigaba da ƙokarin wanke laifin ta daga idanun jama'ar gidan Prof ,

Babu inda take zuwa kullum tana gida ita ke yin mafiya yawan aiyukan gidan ,

A hankali Hajja ta fara fahimtar kyawawan ɗabi'un Yakaka , na kawaici da gudun tashin hankali , sannan kuma me sakakkiyar fuska ce ma'abociyar murmushi ,uwa uba yawan ibadar da ya zauna mata .

Hakan ya sa ta fara sakar mata fuska har takan ɗan ja ta da hira a wasu lokutan ,

A yau ma zaune suke , suna 'yar hira Yakaka tana taya Hajja tsinke ganyen zogalen da zata yiwa Prof girki da shi

Wayar Hajja da take ajiye a gefe ta ɗau ƙara ,

Da sauri Yakaka ta ɗau wayar ta miƙa mata ,

"Ni hauwa'u waye ke ƙirana da wannan sanyin la'asar ɗin ? Allah jishe mu Alheri ,

ɗaga ƙiran tayi dai-dai da ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi , Yakaka ta miƙe da saurin ta tana cewa

" Oyoyo Rahima .

Ta nufi ƙofar ,

"Assalamu Alaikum Hajja ni ce Falmata ,

Muryar Falmata ta karaɗe kunnen Hajja ta cikin wayar ta mai maɗaukakin sauti ,

Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye ɗingis-ɗingis ta nufi ɗakin ta da yake gefe ,

"Lale Lale Marhabin da uwarɗakina Fatima mutan turai ,

Ta furta hakan lokacin da take ƙarasa shigewa ɗaki cike da son kar Yakaka ta san da wacce take waya ,

" Uwarɗakina ince dai duk kuna lafiya ? Ya Babban soja tare da 'yar rigima Mama , dafatan an samu nasara wajen neman magani ?

"Hajja Alhamdulillahi ki taya ni murna , na warke Hajja na samu lafiyar idona ,

"Da gaske Fatima kai Alhamdulillah nayi murna , nayi murna Allah Abun godiya kin warke Fatima ,? Buwayi gagara misali ,

Murnar Yakaka ta rikiɗe zuwa Fargaba lokacin da idanun ta suka sarƙe cikin na Sofi matar Yaya Dakta ,

Kallon-kallo na daƙiƙoƙi suka yiwa juna kafin ta tsinkayo muryar Doctor Hamza wanda yake tsaye daga bayan sofi ,

  "Malama kauce ki bada guri mutane su wuce kin yi wani sanƙanƙam a tsaye kina zarewa mutane ido ,

Da sauri Yakaka tayi baya tana komawa falon ƙarƙashin rakiyar mummunan tsakin da sofi ta bita da shi .

Ɗan diri-diri tayi a falon rashin ganin Hajja yasa sum-sum ta nemi mafakar ta a can ƙarƙashin kafar benen da yake falon ta samu guri ta zauna ran ta duk a dagule .

"Me ya sake dawo da shi yau kuma ? har ma da matar sa ?

Daga inda take tana iya jiyo tashin Muryar su ,

Da Sallamar da Docto Hamza ya yi ,

Basu ko zauna ba Sofi ta fara faɗin

"Wannan kuma wacce jemammiyar 'yar aiki aka samu haka a gidan nan ? Sai tashin ƙarnin man masu bleaching take ,  Doctor ba dai ita take yin wanke-wanke ba , ? Dan bana jin zan iya riƙe ko chokalin da ta wanke ,

A kaikaice Doctor hamza ya dube ta yana samarwa kan sa mazauni akan kujerar falon mai cin mutum guda ,

Motsa laɓɓan sa yayi kamar zai ce wani abu sai kuma yayi biris da ita yana zaro wayar sa daga Aljihu ,

Hannun kujerar da ya zauna ,Sofi tayi matsuguni a ɗosane tana cigaba da cewa ,

"Ni kamar ma nasan Fuskar ta a wani waje ?

A hankali ya ɗago kai yana duban ta da ita ma ta karkato gare shi , fuskar ta ɗauke da wani irin yanayi na tsantsar ɓacin rai da bai kai ga sanin dalilin samuwar sa ba ,

" akan wa kike magana ne ?

" wannan yarinyar mai kama da farar kura , "

Ta furta hakan lokacin da tunanin ta ya gama tuno mata da inda ta taɓa ganin Yakaka a gidan Samy baby ,

Dariya ce ta so kama Doctor Hamza jin an kwatanta Yakaka da farar kura ,

     " ko ina sofin sa ta san

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login