Showing 231001 words to 234000 words out of 411050 words
Chapter 78 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
Yakaka me kike roƙa haka mai yawa ? Ko dai har da shi ake yiwa addu'ar ,
Ta ƙarasa zancen tana ƴar dariya tare da kashe idonta ɗaya na ɗabi'a .
Ɗan zaro ido Yakaka tayi sai kuma tayi murmushi ,
"Rahima , Bawa baza'a tambaye shi me yake nema a wajen Ubangijin sa ba , Duk abunda nake roƙa bai wuce neman gafara da samun Rahamar Ubangiji ba gare ni da iyayena da 'yan uwa na ,
Jim tayi kafin ta cigaba da cewa ,
,"Ummin mu , Rashin sanin a wanne hali mamana take tsakanin Rayuwa da mutuwa yana matuƙar tayar min da hankali Rahima , kullum roƙon Allah nake ya ƙaddara haɗuwar fuskokin mu , idan kuma ita ma ta rasu kamar Baban mu , ina tsawaita musu addu'ar samun gafara a wajen Allah .
Hawayen da ya tsatsafo a idonta ta goge cikin ranta ciwo take ji na rashin iyayen ta .
Cikin tausayawa Rahima tace ,
"kiyi Haƙuri Yakaka , babu shakka abune mai ciwo naka ya ɓata har gara ma ace mutuwa yayi kaga gawar sa aka yi jana'iza aka binne , kowa ma jiran mutuwa yake ,
" Muma akwai Auntie na takwarata ce sunanta aka sa min , ita ma ɓata tayi tun ma kafin a haife ni ,
"Amne tana bani labari lokacin tana da ciki na , Khaalty Rahima ta bar gida tana yarinyar ta yadda Amne ke bani labari bata ma kai mu shekaru a yanzu ba ,
" tundaga lokacin Rayuwar gidan mu bata sake zama dai-dai ba , duk da bansan Ƙhaalty Rahima ba amma labarin kirkin ta da yadda Amne ke ƙaunar ta yasa nima ina sonta sosai , ina kuma so ta dawo wataƙila rayuwar gidanmu ma ta dawo mai daɗi , "
Cike da jimami da tausayi Yakaka tace ,
" Allah sarki Khaalty Rahima Allah ya bayyana ki daga yau zan dunga saka ta cikin addu'o'i na .
" Nagode Yakaka , duk ranar da muka je gidan Amne tare zan sa ta nuna miki hoton Khaalty Rahima .
Cikin zumuɗi Yakaka tace
" yaushe zamu je Rahima ? Ina so naje na gaishe da Amne .
"Weekend ( ƙarshen sati ) insha Allah .
" Allah ya kaimu ,
Rochester New York City
Tafe Biyamuradi Youssouf yake akan titin 3rd Ave, jikin sa sanye da kayan sanyi daga ƙafa zuwa kansa da ya ɗora hular da take da laɓɓa biyu da suka rufe masa kunnuwa elmer fudd da aka fi ƙiranta da Trapper hat .
Hannun sa ɗaya riƙe da 'yar jakar takarda da ya sayo ( Hot chocolate ) mai dauke da tambari tare da sunan kamfanin chocolate and Vines a jiki , domin su ɗumama cikin su ɗumin hot chocolate ya ratsa musu gaɓɓai kafin su fita zuwa cikin asibiti nan da awa ɗaya mai zuwa ,
Cikin kwanaki biyar da suka biyo bayan zuwan su ƙasar Amurka zuwa ganawar su da likita da duk wasu bayanai da suka samu game da Cutar dake tare da Mama .
Daga Biyamuradi Youssouf har Falmata sun rasa karsashi da nishaɗin su , musamman Falmata wacce tundaga wannan ranar take cikin damuwa da tunanin hanyar da zata iya bi domin ganin ta samar da abunda zai zama sanadi na samun warakar cutar Mama da sanyin ƙasar tare da sauyin ruwa suka haɗu suka sa ta ɗan fara kukan ciwo ,
Sai dai kasancewar nan Amurka ba kamar ƙasashen Africa da basu cigaba bane ta fuskar kula da lafiyar ɗan Adam .
Cikin ƙanƙanin lokaci a rana ɗaya aka bata magunguna tare da duk wani taimakon da ya dace a ƙarshe likitan ya gargaɗe su akan kiyayeta daga wannan sanyin mai tsanani , dan haka ciwon bai tsananta ba ya lafa .
Kwanaki biyu Biyamuradi yayi yana tsara abunda ya dace na daga sabon kuɗirin sa , da tunda ya samu gamsassun bayanai daga bakin likitan Mama ,
Ya dangana da nema mata lafiya a yanzu domin babu damar yi mata dashen ɓargo ko juyen jini da zai iya bata waraka , dole zasu cigaba da haƙuri tare da kula da ita , tana shan magungunan ta har zuwa wasu shekaru nan gaba da za'a samu wani cikin 'yan'uwan ta da zai isa sadauƙar mata da ɓargon sa .
Tun a washegarin ranar ya koma asibiti ɗauke da sabon ƙudirin sa bayan dogon nazari tare da kai komo a ƙarshe zuciyar sa ta amince ya haƙiƙance cewa zai kai Falmata ga Manyan likitocin ido dake Mayo clinic su duba ta , idan tana da rabon gani shi zai yi iyakar ƙoƙarin sa wajen biyan kuɗaɗen da za'a buƙata domin yi mata aiki zuwa kan magunguna domin samun warakar ta .
Babu shakka Falmata ta cancanci duk wata kulawar sa duba da yadda take nuna ƙauna ta haƙiƙa ga gudan jinin sa da yake da tabbacin ko mahaifiyar Mama baza ta so ta sama da son da Falmata take yi mata ba ,
Sannan akwai wani abu da shi yake ji game da Fatima da ya kasa fasaltawa a zuciyar sa sai dai yana yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa 'yarsa ne.
Bayan haka Halin mutum yana zama tsani wajen samarwa da mutum Alkairi ko akasin sa ,
halayen Fatima mafi yawansu masu kyau ne , ƙwari yake yabawa da Yakanah tare da Nagartar dake gare ta .
****
Yau ne Alƙawarin sa da Sabon likitan da zai Fara duba Falmata wacce bata kai ga sanin ƙudirin sa ba , domin bai kai ga sanar da ita ba .
Kasancewar ƙarfe uku na yamma shine lokacin da zasu ga likitan hakan ya sa shi fita sayo musu hot chocolate Su sha kafin fitar su domin zai taimaka wajen rage musu jin matsanancin sanyi .
Da Sallama ya tura 'yar ƙofar ya shiga inda ya tarar da su a zaune yadda ya fita ya bar su , da ɗan gudu Mama ta taho gurin sa
",Bienvenue Papa, que m'as-tu apporté? (sannu da zouwa Papa me ka kawo min ?)
Rungumar ta yayi suka ƙarasa kan doguwar kujerar da Falmata ke zaune fuskar ta ɗauke da siririn murmushi ,
", Sannu da dawowa Baban Mama ,
"Sannu da hutawa Maman Mama , yace da sigar zolaya yana kallon fuskar ta
Hot Chocolate ɗin ya ciro musu gami da sanya 'yan chokula ya sakawa Falmata nata a hannu,
Ya ɗauki Mama ya ɗora a cinyar sa ya shiga bata a baki tana kurɓa a hankali
Shiru ne ya biyo baya ,
ɗumin shayin da aka yi shi da garin koko ( cocoa ) da damammiyar Madara mai zafi yana ratsa sassan jikin su daɗin sa kuma yana basu nishaɗi , da yasa Falmata bata farga da tayi shan haɗama ba sai da ta ji 'yar robar hannun ta sakayau , ta kai chokalin baki , taji bata ɗebo kome ba .
Biyamuradi Youssouf wanda duk idanun sa ke kan ta ya ga irin shan da tayiwa chakulan ɗin, ya kai hannu a hankali ya zare robar daga hannun ta tare da musanya mata da nashi wanda bai kai ga fara sha ba ,
", Fatima bois ça aussi ( ki sha wannan ma )
" Baban Mama na ƙoshi fa , nagode .
Ta furta hakan tana jin kunya na taso mata ,
Murmushi mai sauti yayi , ganin yadda gefen bakin ta ya ɓaci ,
ya kai hannun sa kusa da fuskar ta , hannun sa na sauƙa a jikinta ta jaa baya da sauri tare da ajiye robar hannun ta ,
"Dakata Fatima , repérer zan ɗagga miki daga fuskar ki ,
Babban ɗan yatsan sa ya kai gami da goge mata gefen bakinta inda hot chocolate ɗin ya sauƙa bata sani ba .
Kanta a ƙasa tace
"Nagode .
bai amsa ba illa ɗibar chakulan ɗin da yayi ya kai bakin ta ,
" amshi lait au chocolat chaud ,
buɗe bakin ta tayi cike da kunya ta karɓa ,
"zan iya sha da kaina .
tace masa muryarta can ƙasa ,
yayi kamar bai ji ta ba , tare da cigaba da bata a lokaci guda shima yana sha , bata sha dayawa ba tace da shi ta ƙoshi ,
cikin nishaɗi ya shanye sauran , yana ƙurewa fuskar ta kallo da take sumul babu ɗigon ƙwalliya ,
Bayan sun gama , yace mata
"Fatima zamou fita zouwa hospitalisé ku shirya yanzou ,
" Baban Mama zamu sake ganin wani likita daban ko ? Wannan bai ƙware ba sosai ya zai ce cutar Mama bata warkewa bace ? akwai ciwon da bashi da magani ne ?
da wani irin yanayi yake dubanta yadda take maganar cike da son samun warakar Mama ya taɓa ransa , ita bata da wani sauran buri ne a rayuwa da ya wuce lafiya tare da walwalar Mama ? Bata yiwa kanta wani shiri ko tanadi ? Bata da wani buri ne na gina tata rayuwar ?
" Doctorat gasskiya ya faɗi Fatima , cutar Mama batta maganin waraka a yanzou sai fa kou ɗaya bissa hanyoyin da ya faɗi da kouma babu dama a yanzou , ba bissa lafiyar Mama zamou tafi hospitalisé ba ,
Shiru tayi ranta babu daɗi , yaya zai ce babu hanyar samun warakar Mama , shi baya irin tunanin da ita take yi ne ? Meyasa bazai yi wani yunƙuri ba domin taimakawa gurin samar da yadda zasu yi su tsaretar da Mama daga wannan ciwon me azabtarwa , ?
So take tace masa akwai hanya mana , sai dai tana cike da tsoro , da jin nawi tare da zargin ko matsayin da take da shi a wajen sa bai kai wannan matakin ba , mafi girman lamarin ya tambayeta ƙarin bayani , to tace da shi me ? Ko a mafarki bata jin ta san amsar da zata iya ba shi .
Cikin sanyin jiki ta tashi , da gudu mama ta sauƙa daga jikin Baban ta ta zo ta kama hannun Falmata , sannu kan hankali tayi mata jagora zuwa ɗaki ,
Ajiyar zuciya ya sauƙe bayan shigewar su ɗaki , bai ji daɗin sanyin da jikinta yayi ba kan amsar da ya bata ,
Mayo clinic
Doctor Omer Berat ɗan asalin ƙasar turkiyya ( Turkey ) da aiki ya kawo shi Amurka , shine ƙwararren likitan ido da zai duba lafiyar Idon Falmata ,
Bayan sun shiga wajen sa tare da taimakon na'urar fassara yare suka gaisa ,
Babu ɓata lokaci ya nemi da ya fara zantawa da marar lafiyar sa ,
A hankali Youssouf ya kamo hannun Falmata da take zaune a kujerar da take fuskantar ta shi yace ,
"Fatima ki saurara da kyau likita ke son yin magana da ke kan lafiyar ki .
" Lafiya ta ko ta Mama ?
"Lafiyar idon ki Fatima .
Ya amsa yana sake tabbatar mata ,
Mayar da hankali tayi ga likitan lokacin da ta ji ya ƙira sunan ta ,
Ta amsa , tana mamaki daman ita ya kawo asibitin a yau ?
Tambayoyi ne sosai Likitan yake yi mata da mafi yawan su Falmata bata da takamai-mai amsar su domin tambayoyin sun shafi asalin dalilin sumuwar rashin lafiyar idon nata da ita bata sani ba , amsar da ta bashi a ƙarshe ita ce
" Je ne sais pas, je viens de vivre dans la cécité , mes parents sont morts sans me dire à quel point j'étais aveugle . ( nima ban sani ba kawai na tsinci kaina cikin rayuwar makanta kuma iyayena sun mutu ba tare da sun bani labarin yadda makanta ta ta samo asali ba . )
Biyamuradi Youssouf da amsar ta ta taɓa masa zuciya , ya sake runtse hannun ta cikin nashi , yana jin yadda tausayin ta ya kawo masa .
bayan ɗan guntun rubutun da likitan yayi ya umarci Falmata da ta zo kan ɗan wani gado da yake daga gefe a ofishin ya duba idanun nata ,
Har bakin gadon Biyamuradi ya kama hannun ta , ya kaita tare da kama mata ta hau gadon ta kwanta ,
Doctor Omer ya haska ƙwarar idanun nata da penlight , ya ɗora da tambayar ta ko ta ga haske ? Tace ita bata ganin kome ,
Cigaba yayi da haska idon yana dubawa , a ƙarshe ya kunna slit-lamp ya dallare mata ido da haske ,
Wani irin kaifi ta ji ya soki idanun ta da ya sata kifta idanun da sauri tare da kai hannu biyu ta riƙe kanta da ya sara mata ,
"washh kaina .
" Sannu ', ita ce kalmar da Youssouf ya furta da sauri yana riƙo hannuwan nata ya sauƙe daga kan ta ,
Bata amsa ba illa riƙe hannun sa da tayi saboda yadda har yanzu take ji ba dai-dai ba a ƙwarar idanun ta .
Bayan likita ya gama dube-dube a ainashin cikin ƙwarar idanun ta ,
Biyamuradi Youssouf ya kamata suka dawo wajen zaman su suna fuskantar likitan da yake rubuce-rubucen sa cikin kwamfiyuta ,
Turo ƙofar ofishin akayi wata mace ta shigo , babu ɓata lokaci ta jagoranci su Youssouf zuwa wani sashi na daban inda aka yiwa Falmata hoton ƙwarar ido aka tura ga sakamakon ga Likitan ta ta kwamfiyuta kamar yadda ya turo musu da bayanan irin hoton da yake so su yi mata ta kwamfiyuta .
Kafin isowar su hoto tare da bayanan da duk suka dace sun riga sun iso masa , dan haka bayan ya kammala binciken sa , ya zunkuɗa yana mai gyara zaman gilashin idon sa , ya shiga yi musu bayani dalla-dallah cikin turancin sa yayin da su kuma pilot-in-ear yake fassara musu cikin faransanci ,
Iritis shine ciwon da ya haddasawa Falmata matsalar idanu da har ya kai ga ta rasa ganinta , shi iritis wata cuta ce da take samun ƙwayar baƙi/brown na tsakiyar idon ɗan adam , da take kumbura ƙwayar idon , sa ciwon ƙwayar idon da disashe gani ,gaza ɗaukar haske da sauran matsaltsalu da dama ,
wanda ake iya samun sa ta hanyoyin da suka haɗa da ƙwayoyin cutar maɗamfari ( infection ) , jin ciwo kai tsaye ga cikin ido , kamar bugu zuwa ƙwarar ido na daga kowanne irin abu , da kuma cutar da take kama ƙwayoyin halitta na jini tana kashe su.
Bayan dogon bayanin da likitan yayi musu ya ɗora musu da bayani kan matakin da cutar ta kai ga idon na Falmata wanda rashin samun maganungunan da suka kamata a kuma lokacin da ya dace , ya kai ga ta rasa ganin ta na tsawon wasu shekaru sakamakon mutuwa da wasu daga cikin jijiyoyin ƙwarar idon suka yi .
kai tsaye bazai yuwu ba ganin ta ya dawo kamar na sauran mutane masu lafiya , duk da cewa akwai yuwuwar kaso ɗaya bisa uku na ganin nata ya dawo tare da taimakon magunguna da allurai zuwa kan aiki na musamman da za'a iya yi mata a idon idan har magunguna da alluran basu taimaka yadda yakamata ba , wanda zai ɗora ta akai da zarar ya kammala binciken sa a yau .
Cigaba yayi da yi musu bayani har zuwa lokacin da ya tabbatar sun samu gamsuwa sun kuma fahimci duk bayanan da yayi musu ,
da kan shi ya jaa jinin Falmata ya fita da shi zuwa ɗakin gwaji saboda ya auna ya san irin magunguna da alluran da suka dace yayi mata bisa ga mataki na farko .
Basu bar asibitin ba sai da aka mata allurai biyu ta babbar jijiyar hannun ta tare da yi mata ɗaya a jijiyar da take daf da idonta na dama ,
Ba ƙaramar juriya ta nuna ba wajen tsayuwa da tayi cikin nutsuwa aka huda mata jikinta babu zilliya bare ihu da hatta shida kansa likitan sai da ta burge shi sanin da yayi allurar gefen idon tana da zafi ,
Ya dube ta bayan ya ƙare mata allurar gefen idon ,
" sorry It'll hurt but just for a few minutes .
Gyaɗa kai tayi tana jin yadda idanun nata suka yi nawi ga wani irin yanayi marar daɗi da take ji a idon ,
" Baban Mama , ta ƙira sunan sa tana lalubar hannun sa ,
Da sauri ya riƙo ta
" Na'am Fatima , sannu kina jin ciwou ? comment vous sentez-vous en général ? ( How are you feeling overall ? )
" Idona yayi jini ne ?
"bai yi jini ba Fatima , sannu .
****
Misalin ƙarfe tara na dare suka bar asibitin bayan sun ci abinci sama-sama daga kitchen ɗin cikin asibiti .
Suka yi bankwana da likita omer bisa ga yarjejeniyar sake dawowa asibitin nan da kwanaki huɗu masu zuwa , bayan ya haɗasu da mugunguna ɗore da dokoki da sharuɗɗan da ya gindaya musu .
Baki ɗayan su sun gaji Mama tayi bacci a jikin Babanta , Falmata kuwa tsukun da idanunta ke yi yana damunta wanda yake ta zubar hawaye , gaba ɗaya bata jin daɗin kome ,
damuwarta ta tayar da Hankalin Youssouf da yake amfani da kalmomin rarrashi iri-iri yana jera mata sannu , har suka dawo gida , kai tsaye ya zarce da mama ɗakin baccin su ya kwantar da ita ya lulluɓa mata bargo tare da kunna hutar ɗumama daki ya fito falo inda ya tarar da Falmata ta rufe fuskarta da hannu biyu , ta jingina kanta da jikin kujerar da take
A sanyaye ya ƙaraso wajen fuskar sa na nuna damuwa ƙarara ,
Zama yayi a kusa da ita jikin sa na gogar nata , ya kai hannu a hankali ya sauke hannun ta daga fuskar ,
Hawayen da idanun ke yi ya goge da hankicif ɗin da ya zaro a aljihunsa ,
"Fatima yaya ne ? Ciwo ne har yanzou ? Kou zamou koma ga doctorat ?
" Baban Mama idanuna ciwo suke kamar zasu fita , idona bai taɓa ciwo haka ba , bazan warke ba kar kayi asarar kuɗi dayawa , lafiyar Mama yafi samun lafiyar idona muhimmanci kuma ..
" Shittt , yace yana kai hannun sa kan ɗan bakin ta .
" Fatima baki ji abounda Doctorat ya